Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   84 / 84

249K to 251.8K   out of 251.8K words

daukan wayan,yana cewa,
Sweet maryam, ya dai, kina lafiya, ?
Uncle banda lafiya kawai ta iya cewa ta kashe wayan,
Hankalin yusuf yai mumunan tashi dajin yadda maryam tai magana,
Kamar yai tsuntsuwa ya taso a lokacin, maman choima duk ta rude saboda irin yadda taga yare suna yi,
Amma ga maryam sai in idan nakudan ya cije ta zata murde baki,
Addu,a takeyi a bakin ta irin yadda aka koya ma su a islamiyar su,
Kafin Yusuf yazo har driver ya kai su asibiti ko don bazasu iya jiran shi ba,
Allah ya sauketa lafiya ta haifi diyar ta mace mai kama da ubanta sak,
Yarinyar farace tas da ita ga hanci da suma baki wulk kamar na maryam sai dar,daran ido irin na maryam din,
Daidai fito da yarinyar Yusuf ya karaso asibitin cikin rudewa amma yana ganin ana mikawa mama furera yarinyar a hannun ta sai ya sake murmushi,
Hamdala da istigifar yake tayi a cikin bakin shi har ya karaso gurin cikin rudewa,
Maman Choima ta daga hannun ta sama tana cewa press the Lord,
Sai kuma ta hau rera wakan yabo da godiya irin nasu, Christian,
Yarinyar ya karba ya nufi inda maman Choima take yana cewa mama,mama see my blood today woo,
Kara runguma yarinyar yayi a jikin shi tankar wanda za a kwace wa ita,,
Kunnuwan ta yakai daidai baki shi yai mata ikama kamar yadda Sunna ta umur ta,
Sai a lokacin ne ya dago kai inda mama furera take yake duba sai dai bata gurin,
Hakan yasa zuciyar shi gane cewa tana cikin dakin da maryam take a cikki,
A hankali ya tura kofan dakin maryam din tana kwance a aaman gado asibiti,
Idan badon dan fadawan da tayi ba bazaka ce itace ta haifi wanan dirkekiyar yarinyar ba,
Murmushi suka sakarwa junan su yana kokarin karasawa bakin gadon ne wata nurse ta shigo dakin dauke da abin allura a hannun ta,
Ce masu tayi, da su dan fita daga waje kadan har su gama da ita tukun,

Bayan komawn su gidane Yusuf yafara kiran yan uwa da abokan arziki yana sheda masu cewa Allah ya albarka ce shi da diya mace ,
Daga ciki har da Jibrin wanda suke yar wasan boya dashi,
Don tun bayan auren jibrin sau guda suka taba haduwa a massalacin sallah jumma,a,
Mahaifin Yusuf ya yi murna sosai da haihuwan da matar dan shi tayi ,
Har colanut ya raraba abokan hiran shi a church kuma yasa ai mai addun matar yaron shi ta haihu,
Kafin wani lokaci labarin haihuwan maryam ya isa gurin duk wanda ke da alaka da ita da Yusuf,
Aike na musan man Sonny yaiwa baby da mahaifiyar ta, kayane na baby,
Yusuf din wani irin mahaukacin sayayya yayi don har sai da maryam da Anty Dije wace tazo don diba yar uwan ta daga kwantagora, sai da sika ji tsoro,
Anty dije tace wa mama Furera ina mazan da ake haifa wa diya mace su dinga butulcewa Allah su zo suga yadda diya mace tai rana agidan Yusuf,
Kayan kusan ana iya cika daki dashi aka turo Nigeria,
Itama maryam kusan kayan da ya saya mata duk na alfarmane sai da ta kama hawaye don ganin ga na lefen ta ba ta ko fara amfani dasu ba ya kuma jibgo mata wasu,
Surprise din da yai masu shine na canza sabon gida da yai masu batare da sanin su ba,
Safiya da mai gidan ta da suke batun ketarawa waje haihuwan maryam ya tsaida su da rabon ayi a gaban su,
Mota biyu bus na mata guda na maza yan uwan su maryam suka zo gurin taron suna,
Yarinya taci sunan Nafisat,
Inda akaci akasha kowa ya koma da abin arziki a gidan shi,
Mutanen minna sun zo daga kano Alhaji sambo da kuma malam sunzo taya Yusuf din murna,
A gurin wanan taron ne Suleiman ya hadu da Ruth inda suka kulla soyayya mai karfi a tsakanin su,
Wasa, wasa kafin a wase magana tai karfi a tsakani,
Jibrin wanda yazo amma ya kasa shigo ciki ya gaida maryam sai daga waje ya tsaya a cikin rufa,
KB ne ke gwada mai mijin Safiya wanda kwarjin shi kawai ya ishi mutum,
Ba suyi wani dadewa ba Safiyan tafito cikin shiga ta kamilar mace inda yaga an bude mata wani irin galleliyar mota tashige baya tana dagawa mutane hannu,
Jibrin daga gurin da yaje yawani irin nisawa saboda irin abinda yaji a lokacin,
Nan kuma hira ya balke tsakanin su da Yusuf da yafito daga ciki ya samu guri,
Tambayar Jibrin Yusuf yayi da cewa yadai mutumi na garin yai maka dadifa kawani boye ba,a ko ganin ka,
Murmushi mai kama da yake Jibrin din yayi
Kb ne yace ina ko zaka gan shi yana can da yar amaryan shi a kwantagora,
Can fa yatare gaba daya bai ko xuwa Abuja yanzu ballr ya ne mi mutane,
Dariya itin ta yake din Jibrin ya kara yiwa abokan shi aminan yace,
Ai nasan kunsan halin da ma,aikatar mu take ciki bada dadewa ba, ko,
Gaba dayan su suka a,a Jibrin din yace ai yayi aure ba ai wani dadewa ba ,
Customers suka kama wa mutane kaya a border su yi kokari don a sako kayan abin yafi karfin su,
Shine yan kasuwan sukayi meeting da cgida sai an sauke wanan commety din na su gaba daya,
Yace over tree months zaune kawai nake agida ai ba wani hanyan da mutun income ke shigowa,
Yusuf ne ya tambaye cikin mamaki da cewa ya akayi har haka yafaru ban sani Jibrin?
Nayi ma wani abu ne, da har zaka shiga wanan yanayin amma banda labari,
Wani irin nauyi da kunya ne suka rufewa Jibrin din ido a lokaci guda, yaji nasama ta lulube shi ,
Amma kuma ya rasa ko may yasa hakan ya faru da shi a tsakanin shi da Yusuf din,
Mitumin da ke ji da shi tankar dan uwan shi na jini bai bakin cikin yimai ko wani nashi wani abin alheri,
Indai har don auren sadiya ce shi kan shi baiji dadin auren ba saboda Sadiyan kazama ce ta karshe ashe,
Bata iya gyaran jikin ta ko gida ko girki bata da time din yi,always tina zaune ko kwance tana charting,
Sanan shi kan shi kamar ba mijin ta ba don baida ikon kafa mata doka, tabi,
Gashi kuma mahaifinshi duk da auren gida ne tsakanin shi da Sadiyan bai son auren nasu sam sam,
Mutanen kwantagora kwanan su uku suka shirya suka koma inda aka bar maryam ita da su mama Furera da Zinatu,
Ruth wace sam taki komawa gida a lokacin don ta haukace da zancen Suleiman dan matashi mai tashen naira,
Naimat da ta fahinci shirin Ruth itace tai ta bata shawaran cewa idan ta musulunta a saboda shi zai yi hakkuri ya aure ta,

Suna zaune a falo maryam tana bawa diyar ta nafisa nono, Safiya takirata tana kuka wai zasu wuce a lokacin,
Kuka sosai maryam da safiya suka dinga yi don kamar wa yan da bazasu kara haduwa ba,
A haka Yusuf yazo ya samay ta inda abin ya bashi dariya,
Yace kukan may takeyi bayan bada dadewa ba zasu je suma,
Yana son sai Nafisat ta wayo ne su dan fita wani business da yake son yafara yi na international ,
Nan yazauna suna lbarin irin mutanen da yagani sunzo mai buki,
Ruth ce ta shigo saye da wani buje da rigan na tamfa ke a jikin ta,
Irin yadda ta shigo gurin a cikin natsuwa yasa hankalin yayan nata zuwa gare ta, don sanin halin ta da yayi da rawan kai,
Ruth ya abaci sunar sister din nashi cikin kulawa abinda yaja hankalin kowa gare su ke na,
May ke faru ne nagan ki so wick,? haka may akai maki ?ko may kike so ne pls ?
Irin yadda ya rude ganin yar uwar shi a cikin yanayin damuwa yasa kowa dake gurin yin shiru,
Kawai sai tasa kuka ta wani zuwa ta aza kanta asaman gwiwar shi,
Cikin tashin hankali duk gurin suke amna sai Ruth din cikin kuka tace brother I want change to Islam,
Wani iri Yusuf yaji a ruyuwan shi amma afili sai furtawa ya yi da ce wa why do you want to change to Islam ?
Ansa tabashi da cewa Suleiman nake son in aura,
Yusuf yaji wani iri a zuciyar shi sai furtawa yi da fadin Allahu,Akbar,
Kowa gurin yai farin ciki da jin abinda Ruth tazo da shi,
Abu guda e yazowa Yusuf a zuciya shine mahaifin su
Hakan yasa shi lumshe ido shi, saboda irin rikicin da ya hango za,a yi nan gaba, da mahaifin su,
Yadan kira sunan Ruth din tadan dago da jajayen idon ta ta kalke shi,
Yace zai kai ta gobe gurin da zata karbi shahada,
Amma fa tasan cewa bawai don Suleiman zata musulunta ba sai don Allah da zatawa bauta wa,
Kai ta gyada mai alamar to taji abin da yace nan ya fara mata nasiha akan yarda da Allah dakuma dokokin shi,
Maryam tana dakin ta kanta babu dan kwali sai dogon gashin kan nata da ta daure shi a cikin ribon yana sheki,
Kafanta a mike yake saman gado tana bawa baby Nafisat nono,
Zina tuna tsaye daga gefen su tariko kayan da,za,a canzawa baby din don kwanci sai faman lakatan kumatun yarinyar dake ta faman zukan nono,
Yusuf yashigo dakin cikin farar jallabiya ajikin shi,
Daga massalaci yake tunda zun ya na can zaune,
Gashi ya shigo dakin yasa zinatu saurin barin ba dakin muryan maryam ce kece wa zinatu zo ki tafi da ita ma zina,
No inji Yusuf wanda tunda, yashi dakin maganar shi kenan ta farko,
Hannu ya mika don tabashi yarinyar wace keta faman zukan nonon ta alokaci,
Kingama bata koshiba har kina cewa wai a fita da ita waje,
Ko nonon na sayarwa ne da ake mata rowa ana bata kadan kadan,
Murmushi kawai maryam din tayi ita dai kokarin cire yarinyar tayi a nono ta mika mai ita,
Barci yarinyar tacigaba dayi kawai abinta, batare da tasan inda take ba,,
Kallon yarinyar yajeyi part by part kamar mai son gano wani abu a jikin ta,
Maryam ta mike daga gurin da take ta dan gyara rigan ta da kyau,
Kumatun yarinyar yadan lakata yana cewa Sweetyna
Kinji aunt din ki ta zatayi sha hada ko albarkacin ki ta sanadinki zata musulunta,
Mun fara yawa a cikin family ko insha Allah watara har bazamu iya kidayuwa ba ko,
Tun muna furen juji zamu koma FUREN MASSALLACI KO ?
Yadan kara lakutan kumatun yariyar dake barci kamar wanda ke fira da babban mutum,
Maryam tana daga gefen shi tana kallin su cikin tausayin abin da yake cewa,
Gab da shi tadawo ta zauna jikin su na gugan juna tace,
Nayi murna sosai da wanan musuluntar da Ruth zatayi dafatan zata shigo da kafar dama,
Ya asa da fadar Ameen ya Allah yana mai lumshe idon shi, don jin dadin addun ta ga yar uwan shi,
Maryam din tace ta kayi magana da shi sule man din ya yarda cewa zai aure ta,
Yusuf yadan murmusa yace ai mun gama,zancen dashi don har mahaifiyar shi munyi magana da ita tasa muna albarka akai,

Washe gari ne Yusuf yakira mahaifin shi yaje sheda mai cewa Ruth karbi shahada takoma musulci don zata auri musulmi,
Tsohon sai da ya fadi don rudewa sai sambatu yakeyi yana cewa sai yakashe Yusuf,
Ruth yanzu tazama Aisha sunan da taci ke nan na musulunci,
Daga haka Yusuf bai ja wani lokaci ba yadaura mata aure da masoyin ta Yusuf,
Haka rayuwa taci gaba dazo masu a cikkin dadi da ci gaba don yanzu komai yakara bunkasa ma Yusuf,
Nafisat yanzu tana da kan nai biyu da Ahmad Mohammed Nasir,
Maryam ta zama big madam sosai tana tallafawa yan uwan ta ta hanyoyi daban daban,
Gashi kusan duk shekara sai mai gidan ta Yusuf yabata kujeran makka biyar tarabawa dangin ta, shikuma sai yazaba acikkn al,umma Annabi yakai,
Kaunar shi Aisha yanzu yaran ta biyu da Suleiman, Naimat tanada yara hudu da ibrahim,
Safiya dake can America tare da maigidan ta itama yaran ta biyu duk ka maza,
Jibrin yasamu Allah ya taimake shi sadiya ita da kanta tace batayin auren,
Fitan ta da kwana daya saiga shi Yusuf ya turo yazo an samu wani aiki da zai jaragaman gurin,
Aisha yanzu duniya yabata baya sosai don girma ya kamata ga yan matasan yan mata nan ba a yayin su,
Tana son aure amma ba taruhin kwarai arayuwa kowa gudu yajeyi,
Gida mai kyau Yusuf yaiwa mahaifiyar maryam da maigidan ta acikin kamfanin bobi,
Shima baba duk an buge tsohon gidan shi anyi mashi wani plat mai kyau na zamani,
A, A da kan shi yazo har gidan Yusuf don ya taimaja mai yasa mai hannu a takardan wani company nasu,
Inda yaga yaran maryam a fola nan taje yaji wani iri a rayuwan shi,
Assalam da Issalam yazu ko yaushe suna gurin little mum din su don ma shi Assalam kusan a can yake zaune,

Watara aka bugo masu waya cewa Mr Ema a asibiti ya kwana don haka gaba daya gidan su ka kwasa sai Kwantagora,
Sun samu yaji sauki don hawan jini ne ga kuma tsufa,
Ganin yaran uku yasa shi murmushi da jin dadi daga gadon asibitin,
Daya baya yake gaisawa dayaran suna mai kiriniya akan shi yana mai jin dadi sai shafan kan su yakeyi yana lumshe ido,
Alokacin maryam takaraso kusa dashi dauke da cup din fresh milk tana lalashin shi yatashi ya,sha,
Dad yaji sauki don haka bazu koma ba don suna kula dashi yakuma samu lafiya yanzu
Waya aka bugo masu daga garin su cewa maman Choima ta,mutu,
Haka suka kwasa zuwa gurin bukin rufe ta saidai maryam da yaran ta duk suna cikin shiga ta musulunci,
Mutane sai kallon su sukeyi ita da Aisha da Naimat yadda suka bammbanta kan su da,sauran, mutanen gurin sai wani irin kallon su sukeyi,
Maryam wace sai kafa kafa takeyi da yan diyan ta inda tadibi yawan yan uwan su Yusuf din mutane masu karamci amma duk ba muslumai bane,
Tabbas su Yusuf furen kan juji ne to indan anbar furen a cikin juji a haka zai tabbata har ya gaji da haskawa ya bushe,
Amma dazaran anciroshi daga cikin jujin sanu,san sai kowa ma ya manta cewa daga cikin juji a ka ciro shi,
Hakan yakara mata son mijin ta tare da yan uwan shi ,
Sun dawo ba,a dade ba Samuel yasamu kaunar Ibrahim inda shi ma yadage dacewa ita zai aura,
Wanan karon Mr Emanuel bai jaba shi da kanshi aba da bakin a yi bukin,
Su maryam sune sukayi shugaban cin komai akan sha anin,
Inda maryam takara samun wani ciki ta hai yarta mace wace taci suna Dije,
Anty Dije yanzu sanar ta yavigaba bisa taimakon Yusuf wanda akan taimakon da tabashi a baya bai mata ba,
Har yanzu jinta yake tankar uwa ko babban ya a gare shi,
Baba ya tsufa yanzu amna har yanzu yana da halin dattijan takar shi,
Duk Yusuf yai mashi slheri sai yai tafada cewa yai yawa yadaina hakana,

Yusuf yana tsaye yana kallon wani tarda sai ji yayi an rungumoshi ta bayan shi,
Murshi yayi don yasan kowacece maryam ya furta cikin jin dadi,
Yace cikin wani irin murya
Baki barci ba har yanzu tawani lunshe ido tace taya zan yi barci bayan Furen zuciyana idon shi biyu yana muna fafitar ka neman abin rufin asiri
Idon shi ya lunshe tare da dan dukawa ya aje takardun
Kamota yayi dakyau zuwa jikin shi yana cew maryam ban da abin dazance sai dai ince Almadullahi Allaqulli halin,,,,,,,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA

84 / 84