Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   62 / 84

183K to 186K   out of 251.8K words

fa da faba dayan ta tare da sake wani irin kuka mai gumza,
A tsorace Anty Dije wace ke dafa falo ta kwasan yara,zuwa cikjn daki,
Karasowa tayi dakin da sauri inda take jin kukan kaunar na ta
Marayam so kike ki kashe kan ki akan wanan dan iskan mutumin ko yaya, ?
Jin kalaman Anty, ya sakata dakatar da kukan sai she,sheka takeyi,
A gaban maryam din anty dije ta dawo ta tsaya inda take iya ganin fuskan ta,
Abinka da dan uwa rabin jiki sai gashi ita ma Anty dijen kuka takeyi, cikin kukan take lalashin kaunar nata,
Cikin tausayawa da nuna kulawa, take ta cewa ai bai kamata ki kuka ba maryam
Wanda Allah ya hana ma A,A ya bashi Yusuf ai Alhamdullahi, ko ?
Dagowa maryam tayi suka hada ido da juna ita da yar na ta,
Sai kuma kawai tasa wani kuka, irin mai tsuma zuciya,
Anty Dije hannayen ta duka biyu takama sai ta kai zaune tana mai watsawa yar uwan nata ido,
Tace amma dai maryam kukan dadi kikeyi ko mai makon ki godewa Allah akan baiwar da yai maki da kuma wanda kike shirin riska,
Shine zaki din ga butulce mashi haka kina wana kukan,
A karshe dai bayan dogon nasihan da tasha sai ta sa hannun ta kamar karamar yarinya, cike da tausayawa tana cewa kiyi hakkuri haka kar kibari kowa yasan may kike ciki,
Maryam wace kan ta kawai ta kada a lokacin don baza ta iya magana ba irin yadda take ji, gaba daya tasa ta rasa A,A ke nan har Abada,
A haka anty ta samu maryam tai shiru, ta lafe tankar mai barci,
Kofan ta ta rufo mata a hankali, tafita zuciyar ta fam da tausayin maryam,din, wace ke bukatar kulawa saboda rabuwa da,wanda ka saba dashi akwai zafi,

Zaune su ke a falon gidan Yusuf din suna kallon wani plan din gina da akazana a wani farin takarda,
Zanen Gida ne mai kyau na gani na fada suke kallo a takardan,
Gaba dayan su, photo ginan ya burge su sosai duk sun mutu a kan shi,
KB ne yace kai Man irin wanan gidan kawai mutum ya samu lafiyyan mace ya saka ta aciki,
Kwashewa sukayi da dariya a lokaci guda gaba dayan su amma ban da Yusuf,
Wanda yace kai KB kai baka da zance sai na mata, ko ba mace ai a mutum zai iya zama ahi kadai,
Dariya suka kece mai dashi don jin abinda yace masu,
Sai,da KB ya dan gyara zaman shi sanan ya ce wa sauran abokan hiran nashi,
Wai ya zancen shi da Sadiya ce may ake ciki naji shiru mana,
Yusuf da,sauri ya ce mai tunda kaji shiru ba,sai ka tafi ka tambaye taba ko may yasa kaji shiru har yanzu,
Duk dariya suka kara sawa saboda irin yadda yayi mutum sam baya son ya zance mata,
Jibrin ne ya ce kai KB nifa zancen sadiya din nan yasa mun rudani wallahi,
Kamar ya ?
Inji KB wanda ke dan kurban drinks a hankali daga cikin cup,
Yusuf wanda yake a zaune idon shi na saman ties, kamar ba dashi a cikin hiran ba,
Ya ba Jibrin ansa a gajjarce da cewa kaso rudewa ne Jibrin,
Ni na fita cikin wanan zancen tun tuni ban ma son a tuna min akai,
Kallon kallon suke wa junan su, sai mamakin cewa may yake nufi da fadar haka,
Ya ce masu Yes now already ni har na samu wata wace, you all know her,
Da mamakin jin wai sun san ko wace ce ganin da yayi suna mamakin maganar shi,
Gyada masu kai yayi alamar eh tare da lumshe idon shi yana mai gyara zaman shin,
Jibrin yana shirin magana ke nan Yusuf yatare shi da cewa ba kowa bace maryam ce kaunar Sister,
Cikin mamaki wanan ya kalli wancan gaba dayan su sun rude da mamakin jin wai maryam,
Yace yes insha Allah da ita hankalina yafi kwantawa sauran duk ba suyi min ba,
Amma ita nasan tarbiyan ta da kuma halaiyar ta kaga abin zai zo min da sauki,
Daga haka bai kara cewa kala ba ya ma juya ya basu baya,
Ga magana a bakin su sai dai ba daman su yi ta saboda ba suga idon yin hakan ba,
KB yace ya zatayi da mr lecturer din ta, ne don naga ta mutu ga son shi,ban san ta da kowa ba sai shi,
Jibrin wanda ya ke kwance saman kujera yace kai wanan dama yan yan gidan su basu da mutunci
Brother din shi ne fa yaiwa yarinyar nan ciki wani lokaci har muka je gurin shi,
Yusuf yadan juyo gurin da jibrin yake zaune yace
Ok, ok family din su guda ko
Cikin tambaya,
Nan ya kwashe yadda sukayi da shi last zuwa da ya yi su kai ta dariya, suna mai Allah waddai da halin shi,


Da farko rayuwar jibrin yadan sosu da jin ansan da Yusuf ya bayar,
Akan maganar cousin sister din shi sadiya wace har gobe zancen ta akan Yusuf ne,,
Don haka jikin shi yaji duk ya mutu mai, tankar an aiko mai da mugun labari, sai kawai,
Bai wani dade ba yace masu zai tafi sai yadawo, Yusuf wanda a lokacin duk hankalin shi yana akan wayar shi dayake tura sako,
Fitan jibrin din gidan KB yace wa Yusuf mutumina fa bai ji dafin zancen ka ba,
Kamar Yusuf din bai ji zancen shi ba sai kawai ya share shi,,
Tafiya Jibrin ke yi a motar shi yana tunanen ya zasu kwashe da Sadiya idan har ta samu wanan labarin ,
Kodai ya kirata ne ya fada mata zai fi mai sauki
Sai kuma wata zuciya tace mai kada ka fara shi ya zama hadin fitina idan kai haka,
Kabarta kawai komin dadewa zata ji labari ai dole,

Duk kwana biyun nan a takure maryam tayi su kamar a kurkuku, take
Sam bata ko fitowa wahe tana daki a taure ba wani walwala a tare da ita,
Nobar safiya ce yanuna kira a wayan ta a hankali ta mika hannu ta dauko wayan cikin wani irin murya mai kama da ta mai jiya ta ansa mata,
Safiya din ce ta hauta da,sababi cewa yanzu ashe zaman su bana gaskiya bane tunda maganar ta ma sai dai taji shi gurin wasu,
Maryam bata gane may safiya din take nufi da zancen ta ba,
Sai take tambaya kamar ya wai, don ban fahince ki ba,
Safiya tace ai gata nan zuwa gidan da kan ta idan tazo za tai mata bayani,
Tana aje wayan takai kallon ta ga shimkafan dake acikin plate gaban ta kasa ci sai juya,shi takeyi da,spoon kawai,
Anty dije wace ko kallo bata ishe ta ba saboda duk yadda ya kamata tai mata tayi amma,still taki sake jikin ta,
Safiya ce ta shigo gidan tun daga nesa tagane cewa kawar nata na acikin yanayi don haka duk wani abin da ta nufi yi mata sai taji cewa bazata iya ba,,
Sun gaisa da Anty Dije a cikin nuna kulawa da kuma tambayar ta mutanen gidan su,
Safiya ta wuce zuwa dakin maryam don ganin maryam din ta tashi daga inda tske zaune zuwa ciki,
Ido ta kura wa maryam din duk da ta bata tausayi amma sai ta dake ta ce mata wai may ye haka maryam baki da lafiya ne, ?
Idon maryam da ya kawo hawaye take kokarin gogewa safiya din takai zaune tana mai kura mata ido,
Safiya tace ina fatan duk wanan abin bawai don A, A kikeyin shi ba maryam,
Shin maryam wai ke wace irin mutunce da bakya daukan kadara, ko shawara,
Ana fa son musulmi da tawakkali a ko da yaushe idan abu har ya faru da shi,
Sai a lokacin maryam ta dago idon ta da sukai lub, lub duk sun kumbure mata tankar ta yi jinya da dadewa,
Tadan kalli safiya din tana cewa cikin yar murya may kuma kikaga nayi da zaki ce min haka,
Baki safiya ta tabe tace idan har kina wanan haukar haka wallahi wata rana ke ce mai jin kunya ,
Shin maryam damay kikafi wanan bawan Allah ne wai,?
Wallahi ina mai shawartan ki da ki daina wanan halin tun dare bai maki ba,
Dubu naso ke Allah ya baki shine har kike butulce mashi,
Kallon SAFIYA maryam tayi don jin da tayi tace wai dubu na,so,
Suyi ta,so mana ni ina ruwa na kan su su ka,sani kaina na sani,
Manzan Allah fa ya ce muna kada mu aminta da kafirai don basu kaunar har a cikin zuciyae su,
Inna lillahi inji safiya
Maryam kanki daya ne kuwa ? take tambayar maryam din cikin budan baki kalar na mamaki,
Yusuf din ne kafiri kowa ye ?
A takace cikin bacin rai maryam tace yan uwan shi dai,
Wallahi safiya nayi ta ko,karin ganin na taushi zuciya na akan shi amma na kasa,
Duk lokacin da natuna cewa wai da su zanyi taraiyya amatsayin yan uwan miji sai inji raina yana baci,
Safiya yusuf furen kan juji ne,,,,,,


ZEE MAKAWA YALWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


_*Hakika fadin jin dadin yadda kuke min bazai yiwa da bazarku nike rawa tabbas na yarda masoyi masoyine kullum godiya gareku bata yankewa hakan yasa na baku wannan shafin dungurum gum masoya*_

❤❤
**********************
❤❤



Shiru suka yi gaba daya dakin kowa da irin abin da, yake sakawa a,zuciyar shi,
Gama ga maryam wace ke sauke ajiyan zuciya akai akai
Safiya ta kau da shirun da cewa ki tashi ki gyara jikin ki ki sake rayuwan ki tankar bake ce a haka ba,
Sai a lokacin maryam tai dan murmushi jin abin da safiya tace ,
Abincin rana da Anty ta,gama ne ta aiko masu da shi a daki,
Maryam tafito da kan ta ta daukan masu ruwan sha, a cikin fridge,
Sun fara cin abinci ba da wani dadewa ba suka tsinkayo muryan Yusuf a falo,
Anty Dije wace yan kan nen nata duk sun dagular mata lissafinta,
Saboda sun tayar mata da hankali, shi Yusuf yana fushin a kan anty taki yarda,ya,sai masu mota,
Ita ko maryam taurin kai kamar mutanen farko da basu yarda da sakonin su ba,
Safiya ce taiwa maryam inkiya da cewa taje tai ma Yusuf sannu da zuwa,
Ruwa yake kokarin tsiyayawa a cup don yasha,
Maryam wace ta fito saye cikin dinkin buje da riga na wani material lace, ja colour mai yan fararen duwatsu, ajikin shi,
Dinkin shi kamar maternity ya karbi jikin ta so sai yai mata kyau,
Kusan kwanaki ke nan rabo da ya sata a idon shi tun ranan da suka dawo unguwa a tare,
Cikin ladabi ta gaida shi ruwa ya ke tsiyayawa amma sai da mamakin gaisuwar da tai mai ya kama ta,
A nutse ya karba mata don zaka ce ai ba shi ba ne take gayar wa,
Sanin halin maryam da safiya tayi yasa ta fitowa ita ma daga dakin cikin fara,ar ta,
Tana gashe shi da shigowa tana kuma kokarin samun gurin da zata zauna a daya daga cikin kujerun falon,
Maryam wace duk a ta kure take saboda tana ganin cewa duk step din da tayi kamar a idon Yusuf yake,
Kitchen ta nufa gurin da Anty ke kokarin shirya mai a bincin shi,
Karban aikin tayi a hannun anty taci gaba da zuba mai,
A falon su ukune zaune a ciki Yusuf kewa Anty Dije, bayani akan tafiyar mahaifin su kasa mai tsarki,
Magana yake wa Anty dije a zahiri amma acikin zuciyar shi tunanen yakeyi maryam ce yake kallo a lokacin wace ke tafe ,
Ba komai yasa yake son yarinyar nan ba sai zaman ta irin macen da yake burin aure a rayuwar shi,
Kunya natsuwa, kamun kai, rikon Addini tarbiya da kuma sanin darajan mutane,
Itako maryam zancen da taji na tafiyan su baba shine ya ja hankalin ta,
Badon komai ba sai saboda adduan mahaifin su ke nan a kullun shi dai yatafi makka ya gano kabarin Annabi da Abubakar da nana fatima,
Duk addua sai kaji yasako wanan addu,an yau gashi Allah ya nufe shi da zuwa wanan shekaran,
Allah sarki baba ashe Yusuf ne mutumin da,zai yi sanadin sauke faralin ka
Tire din da ta dauko na abincin shi ta dire mai a gaban shi tare da kokarin jawo mai table din a gaban shi,
Nagode maryam ya ce a takaice tare da cigaba da zancen shi,
Wanan hali irin na godiyan Yusuf komai kamai kan,kantar abinda kai mai sai yayi ma godiya,
Muryan maryam ce ya dakatar da shi daga bayanin da yake wa anty, ta
A zuba ma ne ko ba yanzun zaka ci ba ta tanbaya cikin dukar da kai kasa,
No, barshi kawai na gode ya ce yana mai daga mata hannu,
Ta mike a hankali ta juya zuwa kitchen don ta rufo kofan da tabari a bude,
Ido Yusuf ya kara binta da shi yana kara mata kallo azuciyar shi ya na,addua Allah yasa haduwar su ya, zama alheri a rayuwar su da haka yadan lumshe idon shi,
Safiya wace ke gefe kuma tana nazarin duk halin da Yusuf din ke ciki ta dan murmusa daga gefe, batare da,sanin kowa ba,
Maryam wace a lokacin tadawo cikin falon tana kokarin shigewa daki safiya ce ta dan jawo ta da fira,
Tace maryam wayan nan naki ko yana yi yanzu ya daina hooking din da yake yi,
Tafida hakan cikin rashin nuna wani abu a fuskanta,
Sam mutum zai dauka cewa bada wani manufa tayi zancen, ba,
Wanan maganar na safiya yadan sa maryam din dawo wa falon
Gurin da safiya take a zaune ta nufa tana mai cewa cikinnmuryan nan na ta tankar ansa ta magana,dole ne,
Kinsan yanzu kira kawai nakeyi da shi sai kuma received din called, kawai,
Anty Dije ta mike a hankali tana cewa barin dan shiga cikin gida kafin ka gama yanzu zan dawo zan tura yaro can gidan mu gurin babane,
Anty dije tana fita gidan sai Safiya tace au na fa manta da cewa za,a kirani nabar waya daki cikin sauri ta mike zuwa dakin,
Tafiyan safiya yasa akabar su su biyu sai dan shiru ya ziyarci gurin abincin shi yake ci hankali kwance abinshi,
Jin shiru ya dan ratsa gurin yasa lokaci guda Yusuf ya juyo yana fuskantar ta,
Ba tare da yakalleta ba yana mai ci gaba da cin abincin shi yace,
Maryam kwana biyu lafiya kike ko ?
A bazata maryam taji maganar a lokacin hankalinta nagurin wayar ta da ke a hannun ta,
A hankali tadago kanta sai taga cewa ai su kadai ne agurin kawai,
Ko bakya magana ne kina tsoron kada na gudu dake tunda ba ki san koni waye ba ko, ?
Ita dai maryam murmushi kawai ta dan sake wanda iyakar shi iya fuska, batare da tayi magana ba,
Shima Yusuf di kamar yadda tai murmushin hakan ya yi nashi,
Dukawa yayi yaci gaba da,cin abincin shi a hankali kamar yadda yake yi tun farko,
Sai da ya kurba ruwa yadan jawo tissue yadan goge bakin shi ,
Sanan yace maryam nasan cewa kina mai jin zafin abinda A,A dinki yai maki ,
Maryam duk abinda babba zai hango yaro ba zai taba hango shi ba,.
Don haka kibar wa Allah al,amarinki gare shi yafi duk wani tashin hankali da zaki saka kan ki a cikki,
Ni har ga Allah idan zancen baba bai maki ba zan iya hakkuri da maganar Allah zai ban wata,
Duk da nasan cewa nadade ina mai rokan Allah akan yaban mata daidai ni ,
Bako wani irin rayuwa nake bukata daga mace ba akwai wasu hallaiya danake son macen da zan aura ta kasance dasu,
Sai ga shi ubangiji ya nufi baba da alkawaranta min
Da na diba sainaga cewa aiduk wanan abin da nake bukata kina dasu har ma kin zarta wanda nake bukatan,
Maryam kafin lokacin da baba zai bukaci jin hukuncin da muka yanke akai
Idan har kinsan cewa bakya sona ko kuma kinada wani still wanda kike so ,
To ki fada min tun zancen baiyi nisa ba saboda ni mutum ne da bani son inwa babba karya ko yaudara,
Dan shiru ne ya kara ziyartan gurin shiko Yusuf yana saurarenta ne ko za tai magana akan tambayar da yai mata,
Amma sai yaga alamar baza tai magana ba

62 / 84