Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
da halin dan shi wanda yasha warning din shi kan su,,,
Bawani abinci Joseph yaci ba sosai don haka suka ci gaba da shirye shiryen su,
Yau kam churchi ya yayi mugun cika makil da mabiya wanan akidar ta Catholics,
Bukine sosai babu kama hannun yaro anan aka shirya wani kungiya, wanda zasu dinga bi kauyuka suna jan ra,ayin mutane da abubuwan duniya,
Joseph na daya daga cikin wa yanda suka bada gudun mawar su don asai kayayyaki, da za,a rabawa kauyawa, dakuma masu bukata daga cikin su,,,
Wani irin ihu church din yadauka bayan jin abinda sukatara har yafi abinda suke tsanmani samu da farki yawa,
Wani dan gajeren mutum ne tsaye da lassifika yana cewa
"PRESS THE LORD;
Sai sauran su karba mai cikin murnan jin dadi suce "HALELOYA'
Nan take masu kida sauka hau kada ganga duk kowa ya mike akafara wankan JESUS DEY HEAR, HE, DEY,,,,,
Duk wurin yarude da wani irin ihu sai tafi kake ji, da rawa maza da mata,yara da manya,,,,,,
A hankali yazamay jikin shi daga cikin su yana dan tabe kamae may zuwa yin wani abu,
Sai alokacin ya zaro wayar shi daga cikkn aljihun shi yana ta kokarin bidan nobar waya,
Bai tsaya ko ina ba sai gidan, su Ànty Dije, ta kofar gidan gidan ya tsaya yace ace yana wa Assalam sallama,
Anty Dije bata gida maryam cs da yara kawai a gida suna kallo a falon gidan,
Shigowar yaron da aika aiko kiran Assalam ne yadan sa su daga labuken falo,
Maryam na zaune da waya a hannunta tun kusan minti ashirin suke waya da A,A, din ta,
Sam bataji yaron ba har fitan Assalam din sai dai ganin shigowar Joseph da assalam tagani ya na rike gam da hannun shi,
Muryarsa mai,taushi yai sallama da ita tankar musullumi,
Tuni zuciyar maryam ta tsinke, don ta rasa da wani kallama zata ansa mai sallamar tashi,
Mikewa tayi zaune daga kishingiden da take saman kujera,
Ganin da yayi tadan dadirce yasa shi samun daya daga cikin kujerun falon yazauna
Yana mai jawo Assalam zuwa jikin shi cikin nuna kulawa da kuma yar fara,a man,ne a fuskan shi,,,,
Sannu da zuwa ta iya furtawa a lokacin
A dakile ya amsa mata da yaiwa, saboda sanin halin miskilanci irin nata,
Issalam dake zaune tun shigowar shi ta tashi cikin murna ta nufi gurin shi tana cewa Uncle sannu da zuwa, kamar yadda uwar su tace su dinga ce mai,
Wani irin laulausar murmushi yasake mai yar sauti yajawo ta zuwa kusa dashi yana fadin,
Wai, wai, wai Issin mama may aka baki haka kikai girman nan,
Sai a lokacin Maryam tadan kalle shi a karo na farko tun shigowar shi falon,
Cikin sauri takauda kai a zuciyar ta tana fadin Wa,subbahanallahill, Azeem,
Saboda yada taga Joseph yakoma lokaci guda ,
Yazama wani irin, handsome guy, ,sai ka rantse kace ba,a kasar nan yake ba,
Sanye yake da dinkin shadda sai shining shaddan keyi sky colour,
Ga wani sarka da zakai ma kallo guda kagane cewa ta gold ce,
Akawo ma ruwa tasamu bakin ta da iya furtawa a lokacin,
Harara ya dan sakar mata ta gefen ido yace No ki barshi kawai,
Sai yaci gaba da hiran da yakeyi da yaran suna ta kwasan dariya, don jin dadin kasancewa dashi,
Wayan ta ta dauko taima antyn ta text cewa ga wanan kafirin mai zuwa yazo,
Saiga Anty ta kira layin maryam din tana tambayar ta Joseph take nufin yazo ?
Maryam tace eh shine,
Mikewa Maryam tayi tana mai hada kayan wayoyin ta da kuma wani takarda da take dibawa,
Ba,a dauki wani lokaci ba Anty Dije tadawo daga unguwar in da ta tafi karban, bashin ta,
Da murna Anty Dije ta tari Joseph suna ta kwasan dariya ,
Maryam dake daki duk sai taji haushin Anty Dije don may zata dinga washe baki da kafiri,
Sosai yake dan ba,Anty labarin irin abubuwan da suka dan faru dashi bayan wucewar shi,
Maryam mamaki irin shakuwar su tankar yan uwa takeyi,,
Don dai ko yan uwan su da suke mahaifi guda basu shaku da Anty kamar haka ba,
Wanan dibgegen motar da ya aje a kofan gidan su Anty Dije yasa mutanen gari sanin cewa yashigo gari,.
Kafin wani dan lokaci mutane sun farga da zuwan shi,
Abokin Damo, Tsari, sai ga KB da jibrin su ma sun shigo garin,
Abinda maryam bata so shi yadawo don kagin wani lokaci gidan su fam da yan zuwa maula,
Don sun figane masu samay shi a gidan anty Dije bisaga gidan mahaifin shi,
Dayake gab ake da afara azumin watan Ramadan,
Kowa kagani kokarin wanan shirin yakeyi, sam shi da ba musullumi ba bai san cewa wanan lokacin ya gabato ba,
Sai da wani dan uwan Jibrin yazo gurin Jibrin din neman taimakon abin da zai dan sai abinci,,,
Dubu biyar Jibrin yaba mutumin yana mai cewa kayi hakuri akwai mutane da yawa,
Mutumin ya juya yana zabga godiya,saboda dama duk tunane ya ishe shi, ta inda zai dan samu abin da zai fara sayen abinci kafin ai masu albashi,,,,
Haba dai man wanan mutumin fa kamar cewa yayi yanason abinda zai sayi abinci azumi ko,?
Joseph ne ke tambayar Jibrin din,
Jibrin yace haka yace, sai Joseph yadan kada kan shi alamar takaici,
Yo aiko sukarin azumi bazai sai masu ba, haba, haba man,,,
Kiramin shi pls,
Dubu hamsi yabawa mutumin nan ya rasa irin godiyar da zai ma Joseph don murna,
Yau shigan safe yai ma gidan nasu Anty, Dije saboda yana son shan kunun gargajiya da kosai,
Yana Sanye da farar T,shirt anrubuta agaban rigar, snow, da wani jan kala,
Sai dogon wando mai kyau ruwan baki,wani farin agogo ya makala a hannun shi na D&G,
Sai kafan shi dake saye da wani farin takalma rufafu masu kyau gani,
Maryam ce Anty tasa ta gabatar mai da kunu wanda yasha kayan yaji sai kamshi ke tashi,
Da kosai wanda shima yaji hadin kayan markade, da aka soya su tare,
Aikin kullun yake yi waya, don ko zama yayi kafin ya tashi sai yayi waya da kusan mutum ba iyaka,
Yana daga cikkn abinda yakesa shi zama a gidan anty in yana gari don yakan samu time din yin waya,
Tunda tadoso wurin fuskan shi na kallon gefe bayan shi ne,
Tana isowa yajuyo fuska a daure, tamau, yace dan Allah kawo min ruwa mai sanyi pls,
Mikewa tayi bayan ta aje dan tire din da tadauko kayan karin a ciki,
Wani harara ta,dan na masa, alamar kama raina ni,ke nan,
I don't have your time don ni ba yar aikin ka bace,
Azuci take tunanen ta fada ashe, har afili, ana jinta,,,,,
Cikin rashin damuwa yace mata sorry pls just bear with me for sometimes,
Da sauri maryam tabar falon cikin jin nauyi da kunya don sam batai tunanen maganar zai fito fili har yaji ba,
Tun shigewar ta bata kara fitowa waje ba saboda nauyin da taji,
Saidai tana jiwo hiran shi da Anty yana tambayar ta a gamay da azumi, Ramadan dake tafe,
Cikin hikima yakewa Anty Dije tamabayoyi tana bashi ansa yadda yakamata,
Maryam dake waje tana tunanen cewa anty zata sako mai zance addini aciki sai taji shiru,,
Ba wani tambaya ne yakewa Anty Dije ba, illa abinda mai azumi ke bukata, yasamu idan yai azumi,
Saboda azumin mu da nasu ba iri daya bane, don su daga sha biyun dare zuwa sha biyun rana suke azumin su,,,
Bayan wanan maganar tasu da kamar kwana biyu,
Basai ga kaya niki niki wata mota Peugeot mai budaden baya ta,o dasu ,
Sukace Anty Dije akace sukawo wa inji Joseph yace zai bugowa ya suyi magana shi yatafi, Abuja,
A cikin wayane yake mata bayanin cewa ta rabawa mabukata da sukafi bukatar taimako, wa yan nan ka ,,,
Sai kuma ga su gero da sauran kayan hatsi ankara kawowa,
Nan akaita bawa mutane sadaka saboda ba wanda yasan ko daga ina ne kayan suka fito,
Sai daga baya mutane suka fara ganewa cewa Joseph ne ya base taimakon,
Har gida wani mutum yazo yasamu Anty Dije da masifa cewa don may zata yaudare shi ta bashi abin kafiri yai azumi dashi,
Inda yake shiga banan yake shiga ba taso yatara mata mutane,
Kafin ma yabar gurin saibmutane gungu,gungu sunzo abasu sadaka idan akwai (Dan Adam,)
Unguwa unguwa yasa adinga dama kunu da sugar ana bawa almajirai sadaka,
Allahu akbar nan zancen ya tadu a gari cewa ai ya musuluntane kawai a boye,
Saiga shi magana har wurin mutanen su ya kai bayan sun bukaci yazo,
Nan yabugo masu waya cikin bacin rai yana sheda masu cewa ba ruwan su da shi balle su sa mai ido a harkokin shi
Shi yana yi ne "for god sake,,
Don haka bawai su za su nuna mai ga wanda ya kamata ya ba, ba,
Basu gane mai ba ganin cewa yawuce sanin su ko don haka dole suka sa mai ido da halin shi,,,,
Irin abin da yakawo ma gidan su Anty Dije ya ce ta rabawa yan uwan tav abin ba,a cewa komai,
Bakomai yasa yai haka ba don kawai yadda yaga ta kamanta mai gaskiya ga abubuwan kamar yadda yasa ayi,mai,,,
Malam A,A ma ya yowa Maryam kayan shan,ruwa nagani na fada,
Kamar su kayan tea manya gwagwani, millo, sugar eggs, butter, cooker oath, cornflakes, dasauran su kamar yadda akeyi wa mace wace zaka aura wanan sayayyan a kasar kwantagora,
Maryam taji dadin wanan kayan da malam,A,A yakawo mata badon komai ba saidon dama tana kyamar na gurin Joseph,
Duk da tasan cewa dole wata rana tayi amfani da dayadaga cikin abin da yakawo a gidan,,,
Ansa lokacin bukin KB sallah da sati guda don haka abubuwa suka dan cabe w anty saboda tana cikin masu gudanar da tsarin bukin
Duk da gidan amarya sun nuna cewa basu so asa masu Anty Dije acikin har kan su,
Don a cewar su, suma za,su iya gudanar da komi da kan su,
Don gani sukeyi cewa maganar Anty yan matasan ke kokarin bi,,,,
Sun manta cewa mutunci na iya sa komai don dai ita sanadin dantane duk yajawo mata wanan badakalar,,,,
ZEEE MAKAW
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Bakaji komai sai karan na,ura, dake ta shi cikin make,ken falon
Wanda komai da ake bida na hafuwar falo ya hadu,
Jin shirun da wurin yayi zakai tsan manin cewa ba kowa acikin gidan alokacin,
A, hankali yake dan tafita saman walking exercise machine din shi yanayi yana goge dan zufan da ke tsiyayo mai a goshin da wuyan shi,,,
Sanye yake da wani bakin wandon roba har kasa mai dan ratsin fari a gefe, sai, bakar singlet maikama da wondon wanda baida hannu,
Wayan shi sake gefe guda ne tai kara a lokacin badon yaso ba yasauko dan daukar wayan
Anty Dije yagani baro,baro a screm din wayan, shi,
Yai mamaki kwarai da ganin wayar ta da sassafen nan don bata taba kiran shi irin haka ba ,,
Asanin shi madai shine mai kiran Anty din indan har yana da bukatar magana da su,,,
Yana goge zufan jikin shi yana kuma mamakin kiran da safe hakan ga,
Jiran wayan yakeyi ya katse saiya kirata da kan shi don haka yakewa mutane da dama,
Kiran farko Anty dije tadaga wayar anata bangaren,
Cikin dassashiyar murya ta ke mai magana Joseph gamu asibiti da mutumin ka yau two days kenan,
Cikin daga murya ya ce what, Assalam baida lafiya har two days ban sani ba,
Tace wallahi muna ce ko abin baikai haka ba, shine, yasa ban fadama ba,
Yanzu ma shike tace wa wai baigan ka ba shine yasa yana buga ma,
Wai, May ke da munshine Anty, Anty tace yadawo daga school da zazzabi ,
Shine daga baya ya abin ya koma mai combustion, fever,
Cikin matsanacin tsoro da firgici, ya furta O God, da sauki dai yanzu ko, Anty tace eh to yau dai abin bai buga mai ba, gaskiya,
Assalam din ne akabawa wayan cikin dasssashiyar murya irin ta marasa lafiya yake cewa uncle, zan sha Keisha sweet, da apple juice,
Wani iri Joseph din yaji a lokacin don yasan cewa yaron baida lafiya a yadda yaji muryan shi, cikin waya,.
Joseph baisan cewa ya shaku da yaron ba sosai, sai yau din
Don haka, yinin ranan haka yayi shi cikin rashin kuza,ri don ji,ya keyi kamar ace yana agarin shima, a,lokacin don yaga yanauin yaro,,
Gashi yai ta kiran su amma nobar nasu baya shiga,
Sai zuwa dare yasamu layin, nasu, yashiga nan yakara tambayar su ,lafiyan yaro aka ce mai da sauki,,,
Jin haka yai tunane don yasa irin halin hausawa musullumai, duk irin halin da suke ciki sai suce ai da sauki,,,
Don haka ya yanke shawaran tun da safe yakama hanya kawai,
Don haka ya kwana dashirin tafiya, duk wani abinda zai bukata don tafiya yai ready din su,
Karfe shidda na safe ya bar garin Lagos zuwa kwantagora batare da,ya fadawa kowa ba, cewa ga shi tafe,
Ganin cewa tun jiya batai wanka ba yasa ta cewa maryam tazo ta zauna da yaron
Ita zata tafi gida tadan watsa ma jikin ta ruwa ko zataji dadi,
Lafiya lau suka rabu da Anty Dije, Assalam din na saman gado yana,dan wasa da wayan Anty,
Saida zata wuce takarbi wayan a hannun shi, a, lokacin yaron yadan kai kanshi saman filo,
Maryam da hankali ta ke ga wayar ta batasan cewa yaron na cikin wani hali ba,,
Wani irin kakari tayi yaron nayi ashe hakoran shi ne ke hadewa, yana bada wani,irin kara
Cikin matsana cin tsoro da firgici maryam ta mike tsaye, ,da gudu ta kwasa tai hanyar waje cikin rudewa,
Karo tayi da mutum yana kokarin shigowa dakin,
Kamar daga sama ta ganshi tsaye kofar dakin a lokacin ,
Cikin rude take kurma ihu tana ce mai ya mutu, tana nuna inda Assalam yake kwance cikin mawuyacin hali,
Gurin gadon yayi da sauri, ya dago yaron dake ta faman karkadawa,
Daukan shi ya yi din rudewa zuwa office din doctor,
Maryam na bishi a baya cikin wani iri tashin hankali,
Duk saurin da takeyi kamar mai gudu baisa ta cin masu ba,
Karban yaron sukayi suka cewa Joseph ya fito waje, ya tsaya,
Maryam na ganin yafito batare da yatmron ba takaraso da guda tana ce mai ya mutu ko ?
Innalillahi wa,ina alaihi raj,un take ta na,natawa cikin tashin hankali,
Waya ta dauko daga cikin yar pos din hannunta tana kokarin kiran layin Anty Dije,
Joseph wanda tun fitowar shi yake jingine da bangon dakin likitan,.
Fuskan shi murtuk, kamar bai taba farinciki ba, yana mai kallon sama,
Ganin tana kokari kiran layin wayar, Anty Dije ne yasa shi yi mata magana akaro na farko tun zuwan shi,
Yace "pls don't call dem,,
Wani kallo tai mai na baka da hankali,
Daurewa yayi cikin jin haushi yace may zaki ce masu,
Mamakin tambayar da yai mata tayi amma cikin dakewa ,
Tace in fada masu cewa yarasu, mana,
Ido yazoro waje yace waya fada maki cewa ya rasu da zaki fada masu,
Cikin mamaki take kallonshi don sam bata fahince shiba saboda rudewan da tayi,
Fuskan shi a,daure yace mata suna dibashi ne
Shiyasa na fito nan gurin har su gama aikin su,tukun,
Wani irin ajiyar zuciya mai sauti maryam tasake tana mai furta Alhamdullah,
Kafin wanin su yakara wani magana a,ka turo kofan wata yar nurse ce ta miko mai wani takarda tace ance kayi sauri ka sayo wanan,
Cikin sauri Joseph ya wuce sayen maganin sai a lokacin maryam dake tsaye tun dazu cikin tashin hankali takai zaune saman wasu kuherun karfe da akajera akofar dakin likitan,
Jafin yadawo aka fito da yaron zuwa dakin da yake da farko saida da alamar barci yake yi,
Da Joseph zai dawo saigashi da kayan tea manya,manya gwangwani da kuma kayan shaye shaye,
Nan ya zube kayan yadan je bakin gafo gurin yaron yadan dade tsaye yana kallon shi sanan yadan juya inda maryam take yana ce mata,
Idan ya tashi ki hada mai tea mai kauri pls sai a bashi maganin nan,
Zadu dawo zuwa