Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
tayi zuwa cikin gidan sai,dai wanan karon ta dan dade, Inda ta dawo dawasu kayan again,
Sallama taima shi ya dago kan shi ya karba a hankali,
Batai magana ba sai kokarin zaman da take yi shiru sukayi a lokacin da yafara tukin motar,
Kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi gamay da dan uwa,
Wayan shi tai kara inda a zaton maryam take tuhumar ko sadiya ce uwar naci,
Amma sai daga baya tagane da Ibrahim yake wayar don kiran sunan Ibrahim din da ya,yi
Sai dai da yaren su suke magana inda maryam ke ta mamakin yadda yake yare kamar bashi ba,
A falon Anty a,kazube kayan sako ne a ka aiko da su, daga Lagos,
Maryam ce ke fadawa Anty ta yadda Assamau tace kudaden kayan suke,
Yusuf eanda ke saman dining table yana zuba tuwon semovita da miyar kubewa danya,wanda akaiwa miyar stwee daban yaji, gadan manya,manya
Yadda maryam ke bayani acikin sanyi murya ya nuna mai alamar
Har yanzu rayuwar ta ajagule yake da zancen su,
Tun da har taki sake jikin ta har zuwa yanzu,
Kudin kowani kaya take fadawa antyn ta a hankali tana taya ta dubawa
Abincin shi yake ci a hankali kamar hankalishi baya gurin su,
Wayan maryam ce yai kara taciro shi daga cikin poss din ta,
A yadda take magana ko antyn ta dake kusa da ita bawai lalai, ne taji ta ba,
Mikewa tayi zuwa cikin dakin ta, karba wayan ta, dake a hannun ta,
Amma, wanda ke falo zai iya jin maryan ta,kamar tana waya har yanzu,
Sama sama tadunga jin muryan su don yakai wani lokaci agidan yana mata hiran kakar shi,
Sai yanzu,ne mutanenn gari suka gane cewa ya shigo garin,
Saboda duk kwana kin da, yayi agarin acikin gidan shi yake zaune, bai fita ba don gudu kada a rushe mashi plan din shi,
Wayar shi tai kaa alokacin da yake tuki motar zuwa gidan shi,
MY DAD
Yagani a rubuce yasan a kwai abinda ya faru ke nan tunda Dad yau yakirashi,
Ya dauka da cewa Alo,
Bai ansa mai ba sai magana cikin fada,fada ya keyiwa dan nashi,
Yace suna son kudin church don an,kawo masu sabon pastor ,
YUSUF yai mamaki kwarai da jin maganar mahaifin don alama ya nuna cewa har yanzu bawai ya saduda bane ke nan akan zancen shi,
Har yanzu yana mai kallon Christian ke nan ashe, ?
Dad iam not in your religion now,
So don't involved me in any church matters again pls,
Sai kuma ya juya da harshen su na ibo yace indai shi yake bukatar kudi kowani abu zai iya bashi a tsakanin su ,
Mr Ema wanda sam bai yi tsan mani Yusuf zai iya rufe ido yai mai haka ba,
Ahankali yadafa, kujerar da yake tsaye gefen ta yakai zaune,
Yana mai jin wani irin kunar zuciya atare dashi, lokacin,
Kwallar masu zafi ya matse daga idon shi saboda ya san cewa ya yi loosing din Yusuf ke nan har abada,
Shiko yusuf daga inda yake ya rintse idon shi saboda baiji dadin yadda sukayi da Dad din ba sam,
Amma yasan cewa hakan shine kadai hanyar da ta dace ya daina Dangantashi da akidar church,
Maimakon yaje gida sai ya wuce gurin Abdulsamad yafada mai yadda sukayi da mahaifin nashi,
Abdulsamad yace mai, ai da yabashi kudin kawai amatsayin kyauta idan yakai masu su suka sani,
Yace kasan cewa duk lokacin da zasuyi canjin pastor kashin kudi yazo kenan,
Shawarar Abdulsamad yabi inda yaturo mai dubu dari biyu chur washegari,
Shikuma yadauka yakai, church yace ga gudun mawar yusuf nan,
Aisai murna da shewa suna wakoki cewwa yusuf zaidawo soon,
ZEEE. MAKAWA
[3/18, 07:02] Anty Lantana: .🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Assalamu Alaikum yan uwa musulumai masoya novel din furen juji,
Nuna kaunar ga novel din shine taimakon kara min karfi cigaba daga gare ku,
Shawaran ku agare ni tankar taki ne mai kara min karfin hafbaka da cigaba
Nagode Nagode Nagode kwarai daga gaske 👏👏
Wasa wasa zancen Sadiya da Yusuf sai kara ci gaba yake yi,
Yanzu haka kokarin hada kayan mungani muna so
Da kuma kayan azumi da na sallah sukeyi, shida Anty Dije da Jibrin,
Yau ma kamar kulun a waya,suke zancen wasu materials da ya turo Ibrahim ya kawo mata, a sa acikin kayan,
Ganin kayan da kuma tsadan su yasa Anty Dije cewa Yusuf wa yan nan kayan ai sai a cikin lefe ko,?
Maryam wace ke sawa Abubakar Pampers, alokacin ta ce a to ku dai yi ta sawa in hau,kane abin,
Anty Dije ta manta cewa waya take yi sai tace wa maryam,
Abinda mutun ke so maryam a maida shi yake yi tankar kwai,
Dariya Yusuf ya yi daga cikin wayar yace Maryam ce ko ?
Anty ta bashi amsa da cewa itace ma na,
Yar bakar magana,wai muna sa kaya kamar bamu tunane,
Dariya yakarayi
Ya ce Anty
Ta karba mai yace don Allah duk kayan da Ibrahim yazo da shi jiya kiba maryan su pls,
What's,
Tafadi da karfin Allah ,har hankalin maryam ya dawo gurin ta da sauri ta dago tana kallon yar ta,
Lokaci daya maryam ta juyo tana fuskantar Anty nata, zuciyar ta tab da tambaya,
Ji tayi Anty nacewa Yusuf ban fahinci kalman abarwa Maryam kayan ba ?
Cikin wani irin razana Maryam tace wa Anty saboda may, ?
Sai kuma ta dukar da kanta kasa ta na mai jin kunar ran abin da anty tai mata,
Don may za suyi magana a tsakani su har anty ta daga murya Yusuf yaji su,
Tana gama sawa yaron Pampers din tamike tsam tabar gurin cikin kunar rai,
Da harara anty Dije ta raka ta har tabace mata dagani,
Kwance take rigingine fuskan ta na kallon silin din dakin ,
Sai,dai idon dake tab da hawaye,
A hankali tazauna bakin gadon tana kallon ta cikin jin takaicin irin halin maryam akan Yusuf,
Karan ledar kayan ne maryam taji yata dan dago kai,
Zaune tai kokarin tashi cikin mamaki take kallon yar uwar ta, ?
Mika mata tayi tana cewa Yusuf yace abar maki wanan kayan a matsayin kayan sallah ki namu in zai zo, zai zo da su,
Maryam wace ta bude baki da zumar yin magana sai Anty ta daga mata hannu alamar bata son jin komai,
Tace yai min bayanin cewa kayan sunyi yawa amfada mashi cewa sai za,a kai lefe ake kaiwa da yawa,
Don haka tun wutowar Ibrahim bayan Jibrin ya fada mai shine yai shawaran cewa bari yabar maki a matsayin kayan sallah ki,
Tunda wai rin su Jibrin ya sayawa safiyar shi don haka sai kuyi anko,
Bata san lokacin da tai yar ajiyar zuciya ba, don ta fahinci cewa ba fushi yayi ba ke nan,
Anty ta mike tsaye tana cewa sai ki daina fushi, ki, kirashi dai ki masa godiya don nasan halin ki, da basarwa,
A hankali tace to don har yan zu ba, wai ta gama sakewa bane gaba daya,
Batai saurin kiran shi ba kamar yadda batai saurin bude ledar kayan ba
Kayan suna aje a,gefe guda cikin ledar da akawo su,
Har zuwa yanzu maryam bazata iya cewa ga kalan kayan ba don bata diba ba ko, a,lokacin da Anty Dije take kokarin budewa dazu,
Saida ta tab batar da taga komai don haka ta tuna da ledar don ganin shi da tayi a gefen gado,ajiye,
Ledar ta jawo tafara zaro kayan a hankali, saida ta mike tsaye don ganin irin kayan dake ciki,
Materials ne da Swiss masu tsada har guda biyar a cikin leda kala masu kyau da daukar ido,
Kudin kayan zai kai kusan dubu dari uku da hayi,
Cikkn mamaki ta nufo waje inda Anty take tana goge kayan kitchen din su,
Anty kin ko ga kayan dake cikin ledan nan kuwa ?
Sai da ta juyu suna fuskantar juna take ce mata nagani maryam a shi yabani mamaki wallahi,
Ki diba fa yadda mutum zai maka,wanan irin alherin a lokaci guda,
Ni wallahi halin Yusuf tsoro yake bani mutun bai jin zafin kashe dukiyar shi haka,
Shin kin ma kuwa kira shi kun mai godiya maryam, ?
Wani irin kunya ya lulube maryam agurin cikin jin nauyi ta dukar da kanta tace ,a,a
Amma ko halinki sai ke maryam ban san wanan halin naki ko ina ki ka dauko shi ba wallahi
Ga baba nan ya ta yawon fadae alherin da akai mai ko ina ama ke irin wanan kyautar haka kin kasa kiran mutum ki masa godiya haba dai, haba Maryam,
Tsaki taja ta juya wa maryam din baya taci gaba da aikin ta,
A masife tana cewa idan kin ga dama kada ki kirashi ma maryam,
Haka tajuya takoma daki rungumay da kaya a hannun ta,
Wanka tashiga tagyara jikin ta tsab tai sallah shafa,i da wuturi, tadan kai zuwa tara da wani abu zaune saman sallayan ta,
Ta mike tsam zuwa bakin gadon ta da yasha gyara kamar ba a sama za,a kwanta ba,
Zauna wa tayi a hankali ta mika hannu ta ciro wayan ta saje makale yana caji,
Nobar Yusuf ne ta nema takai wani lokaci ta kurawa sunan ido ita kuma bata kira ba,
Can dai ta daure ta latsa nobar a hankali tare da gyara zaman ta, da kyau,
Yadawo agajiye don har dare yana office yau saboda kayan su da yashigo daga Korea,
Wanka yashiga saboda bai sha,awan cin komai ruwan tea kawai yake ra,ayi yau din
Dan karamin towel ya sa yana tsane run dake a kan,shi
Wayar shi ce yaji tai kiran Sallah alamar kiran ya shigo mai,
A hankali ya isa gurin da ya jona ta acaji ya ciro ta alokacin har ta kusa katsewa ko,
Maryam KG a karubuta a jikin sunan dake kiran nashi,
Furta sunan yayi a fili ya ce Maryam a hankali, kamar ta kusa,
Jira yayi kiran ya katse sai ya kirata, da kan shi don kada ya ci mata kudi,
Tana kokarin kiran shi taji kiranshi yashigo a wayar ta,
Bayan ta dauka sai kuma tai shiru a nata bangaren tana sauraren shi,
Shi ma dai shirun yayi a lokacin don yaji sallamar ta tunda ita tafara kiran shi,
Jin shirun da sukayi yai masu dan yawa ne yasa su yin magana alokaci guda,
Assalamu alaikum yace ita kuma tana cewa hello, duk alokaci guda,
Murmushi yayi wanda taji a nata bangaren kamar a fili yayi shi,
Ina wuni ta kara furtawa a cikin zakakan muryan ta mai kama da busa,
Kwaikwayon tayi da cewa lafia kalau, kamar yadda tai magana,
Kafin tai magana sai ce mata yayi matar lecturer halan yau ya cika maki waya da kudi ne dai,
Don naga yau an,kirani kai tsaye,
Murmushi kawai tayi don ta san cewa tsokana ce kawi yake mata,
Katse shi ta da cewa Ya Yusuf sai kuma naga kaya wai kace abani,
Ya ce eh maryam don dake naga kayan sun dace shiyasa nace kawai abar maki kuyi anko da budurwar Jibrin
Shiru tayi kamar baza tai magana ba sai kuma ta tuna cewa yin maganar ta zai jawo mata fada gurin Anty,
Sai kawi tace to nagode ya Yusuf amma dai da naga kamar doguwar budurwar ka ka sayawa su,
Wani irin malalacin dariya yayi yace sai kuma ga rashin da,cewar su da ita
Sai da yar budurwar mr lecturer suka dace kawai shi yasa na ce abarwa matan malam su tayi wa malam kwalliya yasha kallo
Ko yar kauna ta ?
Wani irin abu taji ya tokare ta a zuciya
Tace to zuciyar ta yana nufin cewa A, A ba zai iya saya min bane ko may ?
Kawai sai taji tamayar mai da kayan shi tace batason ta gode kawai,ya bar su,
Amma sai taji muryan shi a cikin sasautawa ya na cewa maryam,
Kayan sallah ki na aiko maki da su saboda kayan da na sayawa sadiya naji ance sunyi waya
Shi yasa nace wa Anty tabawa little sister dina kayan ta na sallah su,kuma idan zan zo zan shigo masu da nasu,
Kinga saura shoes da bags ke nan ko ?
Kamar ya,na ganin ta takada mai kai alamar eh,
Yace size din ki zaki fada mun kin ga zai fi idan kuma da akwai wani abin kina iya fada min sai a hado maki da shi,
Kwata kwata maryam bata so wani abu daga gurin Yusuf ba ,
Amma ya ta iya tun da gashi ya,dage har da cewa yasan ,
Ya,san bai isa sai mata abu ba saboda tana da dubun su
To amma yanzu tunda sun shirya yana son ta nuna mai cewa ta hucu kabar kayan zai nuna mai alaman hakan
Tambayar ta yakara yi in akwai wani abin da zai sayo mata in zai zo,
Ba komai ta furta a,hankali kamar mai shirin yin kuka a lokacin,
Sai yaji tabashi wani irin tausayi irin yadda tai mai magana a cikin damuwa,,,
A hankali tai mai sai da safe ta kashe wayan ta ba tare da ta kara furta wani kalma ba, a,kai ba, ta,katse wayar,
Lumshe idon shi yayi alokacin kamar mai jin barci tare da fadawa saman gado ta baya,,
Haka ya kwana da tausayin maryam a cikin ran shi wanda bai san dalilin hakan ba
Ita ko maryam ba yadda ta iya saboda har taji Anty na fadar irin dinkin da za taiwa kayan,
Sosai alakar mai nisa ta shiga tsakanin Ibrahim da Ejoma wace yanzu duk suna zaune a gidan yusuf ne dakw garin Abuja, a karkashin kulawar shi,
Tun suna kojarin boyewa maigidan nasu Yusuf har takai yanzu basu iya boyewa,
Maman choima da fara ganewa taiwa Ejoma magana acikin ka
,kausar murya cewa ta rabu da Ibrahim din tun Yusuf bai sani ba,
Amma sai Ejoman tace ma mama ai tafi son yasa don ya yanke masu hukunci,
Ran yar tsohuwar bai yi dadi ba sai tafito fili tacewa Ejoma ya zatayi da addin ta idan ta aure shi,
Sai da Ejoma tai yar dariya san nan tacewa mama ai su addinin su bai hana su auren yan addinin mu ba,
Sai,dai matan su ne ba,a yarda su auri mazajen mu ba sam,
Ehye, u see
Inji mama tana mai kada kai tace tana mai ba Ejoma shawarar ta tsaya a ,addinin xa iyayyen ta suka haife ta aciki yafi mata,
Ganin cewa ba,zata iya shawo kan yarinyar ba yasa ta kawar da kanta gefe guda,
Tsayin wani lokaci babu wanda yace wa dan uwa kala a cikin su
Don dai ita Ejoma gaskiya zata iya rabuwa da addinin ta tunda dama tadade tana sha,awar musulunci,
Yin Sallah da sa hijab na burge ta sosai, a rayuwar ta,
Har zuwa lokacin dawowar Yusuf da Ibrahim yayi daga office suna zaune a hakan,
Ibrahim wanda ya fara shigowa dauke da yar brief case din Yusuf a hannun shi,
Ya gaida mama acikin ladabi amma fafir yar tsohuwar taba shi baya taki karba mai sam,
Yana tsaye yana mai mamakin abin da yahana ta karbawa Yusuf yashigo cikin gidan,
Cikin irin takon shi na alfarma ya Wanan tafiyar tashi, guda guda tankar yana tsoron kasa,
Suit ne ajikin shi mai ruwan asshh, colour, hade da wandon shi sai far tie shirt da yasa daga ciki,
Isowar shi falon ne yaji muryan Ibrahim yana cewa mama idan har yai mata ba daidai ba ta yafe mai pls,
Da mamaki Yusuf wanda yadawo a gajiye ya tsaya yana kallon tare da tambayar ko may ke faruwa,
Kafin Ibrahim yai magana mamace tafara magana acikin fada tana cewa
Yusuf ya maida ita gida tunda taga kowan su yana musulunta
Gaskita ita bazata yarda azo da tsufan ta a cuce ta,
Da mamaki Yusuf ya juya inda Ibrahim yake. tsaye don karin haske, ga maganar,
Kafin wani yace wani abin Ejoma tafi daga ciki tana cewa ,
Brother zan koma ga addinin ku saboda wanda nake tare da shi yanzu dan addinin ku ne ,
Cikin mamaki Yusuf ke kallon Ejoma wace ke mai bayani a lokacim,
Cikin mamaki yake nunata da yatsar shi ya na cewa Ejoma ke, ke, ke,
Yace nasani sani cewa warana zaki gane hanyar gaskiya insha Allah,
Gashiko yau da kanki kin dawo saboda ra,ayin ki,
Baki sake da mamaki mama ke kallon su duk ta kawo iya wuya, saboda haushi,
Ciki tashige tana ta faman