Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   11 / 84

30K to 33K   out of 251.8K words

Don tun lokacin da diyar take zuwa da mijinta dayaran su idan sun zo daga Arewa,
Bayan fitinar da akayi ita da dangin mijin yarta yasa duk suka dauke kafar su da ita,
Duk da tasan cewa ita ba muguwa bace sheri ne kawi irin tasu,
A hankali ta dan fito daga can ta bayan gidanta inda take girki don taga ko waye a vidan ta,
Duk da girman da yayi da kuma nuna cewa yana cikin daula,
Hakan bai hanata gane jikan nata ba,, a lokacin don rabonta dashi yanzu kusan shekara ashirin ke nan,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣3⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA


Daga karshe hukuncin da aka yankewa Ejoma baima Joseph dadi ba,
Don Samuel ne yakira shi ta waya kamar yadda yabar mai maganar cewa ya kirashi ya sanar dashi duk yadda akayi,
Don haka yai kokarin samun nobar ta yace ta shigo motan da zai kawo ta Lagos,,,,
Wanan shine silar zaman Ejoma a Lagos cikin karkashin kulawan Joseph,,

Yadauki lokaci mai tsawo bai,shigo garin kwantagora,
Don har takai mutane sun fara maganan rashi shigowar shi ,
Saboda kawo yanzu angane amfaninshi a cikin al,uma, duk da zaman shi furen juji bai hana mutane kai koken su gurin shi ba,
Shirin kwanciya yake yi dai lokacin wayar shi tai kara,
Mika hannu yayi ya dauko wayar daga saman sidedrower, din shi,
KB yagani barobaro a screen din wayar yar murmushi yayi don ganin mai kiran nashi a daidai wanan lokacin,,
Yadai man inji Joseph yace wa KB
Kayi wuyan gani fa mutumina, shiru haka muna ta cigiyan ka a kasar
Dariyarn nan tashi ta kasaita yayi da KB yafadi haka na,
Yana dariya yana shafar sumar kanshi da ya kwanta mai lun har zuwa fuska,
Yace ai lamari ne na rayuwa sai a hankali, yanzu haka tun tree weeks ago olf man ke ta kirana, wai yaji ni shiru,
But ina son inyi kokari in shigo, uffer week, don akwai yan aiyukan da zanyi ma Dad,
Dariya KB yayi a bangaren shi yace ai ban zata zaka iya kai wa har dis time baka shigo ba kodon mutumiyar don tana ta bugo min waya wai bata samun ka,
I beg forget about her ni don old man da mutanen arzikina zan shiga,
Wai ya labarin jibrin ne mun kwana biyu ba muyi waya ba da shi,
KB ya ce bari kawai man ai old man din jibrin yasamu problem wallahi don ya biya kudin zuwa saudiya amma an cinye kudin case din har minna,
Wanan dalili har saida tsohon yai ciwo sosai haka yasa su jibrin cikin wani irin tashi hankali,
Wani iri Joseph yaji a zuciyar shi da kyat ya iya furta wa a hankali may yasa mutane suke hakane wai,
Mutumin nan ysi iya kojarin sa ya hada kudin shi sai cikin dan lokaci ku kwace,
KB yace wallah ma noman wake yayi dis year sosai ,
Sai yahada da saida dabbobin shi shine yabiya masu su uku shida matan shi,
Kaikaikai, haba dai gaskiya akwai tausayi wanan abin,
Kawai dai bari za muyi waya da jibrin din in masa jaje,
Da,wanan zancen ya kwana a zuciyar shi yana mamakin irin tsoron Allah da mutane basu da shi yanzu, sam
Tunda safe ya bidi layin Jibrin inda yake fada mai cewa KB ke fada mai abinda yasamu mahaifin shi,
Nan jibrin yakara mai bayanin duk halin da ake ciki tun farko,
Wai kudin harda yawa ne Joseph ke tambaya, Jibrin din,
A,kaiko akwai yawa ma,na har fa mutun uku ne,
Nan dai jibrin ke mai bayanin yadda kudin yake da kuma yadda ake komai,
A haka sukayi sallama bayan sun dan taba hiran yau she rabo a gana,,,
Tukun mota yakeyi don zuwa depot, yadibo wasu motocin su,,,
Amma azuciyar shi yana tunane cewa a she ma bawasu kudine masu yawa na ake biya,
Shine har zakaga wasu musulumai gasu da halin zuwa amma sai su tsaya tara duniya,
Basu damuwa da kokarin zuwa sauke faralin da aka sa masu,
Yanzu diba fa wanan mutumin noma yayi da karfin shi ya biya kudi don kawai yatafi ya sauke farali,
Amma aka samu marasa imani su ka yaudare shi saboda , tsaban damfara da yaudara, wanda yasamu ta rashin imani,
Wanan zancen yasa shi yin tuna nen cewa ya kamata yakai kakanshi tayi ziyara a Jerusalem,
Haka kawai ya tsinci kanshi da nishadin jin dadin wanan tunanen, da yayi
Don haka bai tsaya wani bata lokaci ba yafara masu shiri tafiya ita da shi,
Don haka ya yanke shawaran sheda ma maifinshi wanan zancen
Zaune Mr Ema yake a kofar gidan shi kasan cewa yau lahadi bai zuwa ko ina,
Ganin mai kiran nashi yasa shi jin zuciyar shi tayi mai fari kal,
Don dai yasan cewa Joseph na matukar kokarin shi wajen kulawa da shi,
Bakamar sauran yaran kabilar su da da,zaran yaro ya girma yafara cin gashi kanshi, yadaina yawan kula iyayye ke nan,
Ajiyan zuciya yasake daidai lokacin da yake daukar wayan, ya ce Hello Son how are u, ???,,,,,,
Shi din ma Joseph din ajiyar zuciya yayi mai kara yace mai, l,am fine Dad,
Yace ina ta kokarin kiran layin M,T N dinka baya shiga shine nace barin kira layin Airtel, dinka ko zai tafi,
Daddy din murmushi yayi yace ai matsalar services ne kawai,
Ya kuke can ya aiki inji Mr EMA, yana tambayar dan nashi,
Joseph din yace everything is fine Dad,
Mr EMA yace God bless you my child,,
Amen yace da murya mai yar karfi,
Dan shiru ya biyo baya, sai Joseph din ne yadan kauda shirun da cewa
Dad dama ina son shedama cewa zamu tafi Jerusalem ni da Grandma,
Which Grandma,?
My mother mother,
What Mr Ema ya fadi da karfi kamar wanda yaji tsoron hakan,
Kana cikin hankalinka yaushe har ka fara hurda da ita,
Idan ma baka fara ba bana son kafara saboda kasan cewa is weaked worman,
Don ana suspect din cewa itace ta kashe mamanku,
Yayi yar murmushi har uban najin shi yace bazata yi komai dashi ba ai
Don shi gaskiya bai yarda da zancen da akeyi a kanta ba,
Fada sosai Mr Ema ya,dinga yiwa Joseph akan cewa ya janye tafiyar da ya shirya yi shida ita,
Har sukayi sallama yana mai jaddada ma dan nashi cewa yafita harkan kakan shi ,,,,

Kwana biyu da yin wayar yana cikin damuwa sosai
Idan kagan shi basai an fada maka cewa bai ciki dafin rai ba,
Don haka yaje gurin wane father, yai mai bayani
Inda father din yace mai aida ita muguwa ce bazata tafi wan wurin ba,
Sai a lokacin hankalin shi ya kara kwantawa da kakar tashi wace yan uwan mahaifin shi suka azama kahon zuka wai muguwa ce,
Tabbas yaji dadin zancen wqnan pastor din don ko ba komai wanan tagiyan zai wanke zargin da ake wa matar,
Don haka saida yaga komai ya kammala yakama hanyar zuwa Niger state of Nigeria,
Ya iso cikin dare don haka gidan su Anty Dije ya nufa don ya kai mata tsaraba,, duk da yana jin yunwa, sosai,
Gashi yanzu in dai yana kwantagora sai abincin gidan Anty Dije yake iyaci,
Saboda kawai yardan da yayi da matar don daidai da rana daya bata taba nuna mai kyama ba kamar yadda ya fahinci cewa sauran musullumai nayi mai dan kyan kyami,
A falon gidan ya samay su gaba daya suna kallon season film na india,
Cikin murna da dauki duk wanda ke falon ya tare shi, banda maryam wace ke kwance saman dogon kujera tana, kallo, alokacin,
Anty Dije tace Oyoyo da bakin dare, haka shine baka fada muna cewa kana hanya ba Joseph,
Yai yar dariya yace tafiyan haka tazo min wlh Anty, kawai yau naji ina son shigowa kwantagora ne,
Bayan sun gaisa Assalam yana makale ajikin shi tun shigowar shi,
Yadan kalli Anty yace a tura yara su kwaso maku kaya a buth ko ,
Inda maryam take kwance Anty ta kalla tace Maryam tashi mana kitafi ku kwaso,
A cikin zoboro baki tai kicin da fuskanta, tace a shagwabe sannu,
Batare da tajira ansawar shi ba ta wuce tana kokarin daura dan kwalin ta, akai,
Har takai kusan kofa tace a bude buth din yake ne, ?
Key kawai ya miko mata batare da yai magana ba don ko banza dama shl tsarda magana gare shi,
Tayi gaba tana turo baki gaba tana zumbure zumbure,
Har takai bakin kofa sai Anty Dije tace idan fa baki iya ba kada kimai barna, Maryam,
Wuce wa kaiwai tayi don takaicin da take ji,
Kayane shake ga buth irin tsarabar kasar kurmi yakawo masu,
Maryan tunda ta samu da taimakon yaran shiya aka gama kwasan kayan
Ko kara juyowa hanyar falon batayi ba kawai tashi ge ciki abin ta,
Yadan kai wani lokaci suna hira da anty dije san nan yai mata sallama yatafi,
Inda Assalam yasa masu kuka sosai, wai sai ya bishi,
Sai bayan tafiyar shi ne Anty Dije takewa Maryam fada akan irin yadda take nunawa Joseph din,
Anty Dije tace abinda yasa take janshi ajiki dayan biyu ne,
Na farko dai ko Allah zai sa ya gane gaskiya, jin haka saida Maryam tadan daga ido ta kalli Anty din, tace a haka anty,
Kiga mutum kasurgumin ARNE haka har kike ganin cewa zai iya tuba,
Maryam kina ko da tunane akwai abin da yafi karfin Allah ne Maryam,
Kinga kuma na biyu yadda yake ra ayin yaran nan kamar wasu jinin shi,
Duk saboda Assalam yazo muna kingako badadi in dinga nu a mai tsana ko kyama a fili
To yanzu yaya zaki yi da wanan kayan da yakawo maku,
Don dai ni gaskiya bazan iya cin komai na kafiri ba,
Anty Dije tarasa abinda zatace wa yar uwan nata,
Wace gata yar karama sai shegen akida kamar wata malama,

Washe gari tunda safe ya nufi gidan su jibrin don gaida mahaifin jibrin din,
Yadda yake zato abin yafi nan don duk dan dattijon yaramay yayi baki,sosai,
Sundan dade zaune a dakin baban jibrin din da zaitafi yaba shi dubu hamsi yace ai sai mai lemo,
Sam yaki karban kudin saida kyat yakarbi kudin da farko Joseph ya zata ko baison abin hannushi ne,
Saida dattijon ya yace mai yarage sunyi yawa yabashi ko kadan ne,
Yace baba lemo kawai za ,a sai maka kasha,,
Bayan fitar su waje ne Joseph din ke cewa jibrin yanzu may ake ciki akan zancen,
Nan dai Jibrin ya sheda mai cewa kotu tace mutumin yabiya shi nan zuwa karshen shekara,
Joseph yace har lokacin ba,atafi aikin ba ke nan,
Jibrin yace kai haba har wasu na shirin zuwa ma alokacin ,,
Kai haba impossible inji Joseph gaskiya asan yadda za,ayi musamu baba su tagi wanan shekaran,
Jibrin yace yaya zamu man tunda duk dan abi da ke ga baba shine ya hada yabiya masu
Joseph dake kokarin bude mota yace ma jibrin a ina zamu samu kujerar, ne,
Mamaki karara a fuskan jibrin yace kai bafa maganar wasa bane man kudin mutum uku baba ya bita fa,
Joseph yace and so what,
Indai har zamu samu ai sai su tafi,
Murna jibrin zaiyi ko kuma may
Saidai kuma a zuciyar shi ya na tunanen in har mahaifin su zai yarda da zuwa makka da kudin Joseph,
Don haka ba bata lokaci suka shiga cigiyar kujerar makka
Saida kyat suka samu a wani local government kusa da kwantagora magama local government,
Saidai an masu karin kudi sosai akai amma haka ya juye madu yabiya, don dai kwai yadda yake jin kada a wuce baban jibrin bai samu zuwa aiki hajji ba kamar yadda ysi niyya,,,
Maganar nazuwa gurin baba aikuwa baba yace sam badashi za,ayi awanan aikin ba,
Ina zai tafi aikin hajji da kudin kafiri,
Da tambaya dakomai malamai sukace ya halatta su tafi tunda shi yaga dama yabasu kudin shi kyauta,,
,,,

ZEEEE MAKAWA
ZEEE MAKAW
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MA KAWA

Wanan tafiyan na mahaifan Jibrin da Joseph ya ba kudin zuwa Saudiya ya jawo muhawa sosai a cikin gari,
Har takai wa yanda basu san shi ba yanzu sun fara samun labarin shi,,,
Dashi akai komai har zuwa rakiyan su airport a Minna inda zasu tashi, zuwa kasa mai tsarki ,,
Wanan abin yabawa Joseph mamaki sosai don tun a nan sun fara ibada
Daga can ya wuce zuwa Abuja gurin zancen business din da suke so sufara jonawa,
Wanan tafiyar tankar tafiyar don jibrin a kayin don itace samuwar aikin jibrin din,,,
Anbashi In charge na supplying din duk wani shinkafa da mangyada da za,a shigo dashi daga wata kasa,
Zuwa kasar arewa da kewayen ta, kamar su Cameron da Chadi, Niger
Bakaramin sa,an samun wanan nasar yayi ba don mutane da dama sunyi ta korafi akai,
Wanan abin yaiwa mutane da yawa dadi saboda jibrin mutum ne mai tsimakon nakasa da,shi sosai,
Lokacin tafiyan su Joseph da kakar shi yayi kawai sai ji Mr Ema yayi cewa Joseph yafita tare da ita, zuwa Jerusalem,,,
Wanan fitar mutane kauyen suka,dinga mamakin cewa tunda ita witch ce yaya zata iya zuwa can wurin bauta,
Wanan tafiyar ta daure wa Joseph kai sosai saboda abinda yagani a can ya banbamta da yadda suke gudanar da tasu,addinin a nan,,,,,
Saboda sai yaga cewa ai duk kusan al,adun da akeyi acan kamar al,adan musuluman Nigeria ce da sauran duniya,
Hatta da alwala indan bakayi ba ba,za,a bari kashiga cikin massallacin ba,
Abubuwa da dama yagani a can sai kuma yaga cewa ai har da musulumai daga wasu kasashe suna zuwa yin bauta a cikin wanan masallacin mai tsohon tarihi watau masallacin, BAITI,MUKADIS,,,,
Ya dawo gida zuciyar sa fam da tunane kalala, acikin sa,
Kakan shi mai suna Ciyoma, tun acan tadinga wani irin kuka na farin ciki tana mai samai albarka,
Addu,an gamawa da lafiya da duniya yadinga mai aciki tasako zancen da ake mata zargi dashi tana mai cewa,
Tagode Allah da jikanta ya zama abin kwatance a cikin jamar su, har yafidda ita daga zargin mutane, cikin wani irin magana kamar waka,
Joseph dake zaune yana kallon ta a cikin dan gurin shan iska da suka tsaya a wani airport,
Yana saye da wani katuwar rigar sanyi,a jikin shi yataso daga inda yake zaune tun fara maganar ta,
Ya rugumay ta ajikin shi don maganganu da take fadi sun ratsa mai zuciya sosai a lokacin
Tunanen mahaifiyar shi wace a yanzu bata da rai ya fara ji dama ace tana da rayuwa ne da yanzu suna tare da ita a wanan gurin,
Saboda yasha tayawa mahaifinshi cewa suzo wanan gurin ziyara amma sai Mr Ema din yace bai son abin wahala shi,
Wasu hawaye masu dumu suka silalo mai daga ido zuwa kasar fuskan shi,
Yanajin mutuwar uwar su kamar yanzu ne abin yafaru mata mai hakkuri da sanin ya kamata
Don yana da wayon shi irin yadda mahaifin shi yadinga wahal da ita a lokacin zaman su,
Jin hawayen Joseph na diga mata a wuyar ta ya sa yar tsohuwar dagawa daga cikin jikin shi ta dubi fuskan shi,
Ta ce Joseph my child don cry pls,
Kara rike kakan tashi yayi saboda yadda yake ji a zuciyar shi ba dadi
Sun kai wani lokaci a haka sanan nan ya ja ta da kyar zuwa wurin da kayan su yake gefen wasu kujeru da aka tanadar wa matafiya,,
Sun iso gida Nigeria cikin farin ciki da walwala a zukatan su saboda, sun tafi inda kowani dan addin Christian ke burin zuwa,,,
Ta Abuja suka,sauka don haka yasa wani abokin shi ya kwaso su, daga airport,
Zuwa gidan shi da yake sauka a Abuja,indan yazo,
Sai da ya huta san nan ya kira KB yana sheda mai cewa sun dawo shi da kakar shi,
Kwanan su biyu abokanan shi suna ta zuwa yi mai barka da dawo wa,
Tun wanan tafiyar tasu josepy yasa wa ranshi cewa ba,zai kara barin wanan yar tsohuwar kakanshi cikin wahala ba saboda tana

11 / 84