Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
ya kare bi gida jen masu hannu da shuni yana maula,.
Mutumin ya katse maryam da cewa ko zan samu ganin hajiyar gidan don magana ce tazo dani mai muhin manci sosai
Shiru Maryam tayi saidai gaskiya mutumi yabata tausayi sosai don ganin yanayin shi,
Marayam ta fadi cikin ladabi barin shiga in fada mata,
Bayan shigar ta da kaman yan mintina saiga Anty Dije ta leko sanye da hijabin ta,,
Daga nisa kadan suka dan gaisa da mutumin sai kuma yar shiru tabiyo baya,
Don Allah hajiya kiyi hakkuri pa don nasan cewa ba wai kin san,ni bane,,,
Sunana Abdullsamad anan gari nake, ni dan uwan yaron dake yawan zuwa gidan nan ne,
Watau Joseph,,,,,
Daga Anty Dije har maryam dake ta kofa tsaye wace ta takawa yar uwar ta baya don gudun wani abu ya samay ta,
Sai da suka dan kadu jin mutumin ya ambaci sunan Joseph,
Jin haka yasa anty ta dan kara gyara tsayuwar ta tana mai cewa lafiya dai ko malam,
Don a zaton su yazo masu da wani tashin hankali ne, a yadda suka gan shi,,,
Yadan hada hannun shi guri daya ya nuna alamar cewa a,a babu komai gaskiya sai Alheri,
Sai a lokacin anty dije tadan rage jin abinda take ji
Sai yadan waiga kamar may son yin wani maganar ta,siri ko kuma mai muhin manci sosai,
Hakan yaba anty damar gane cewa maganar da yake da ita kamar ta siri ce,
Don haka ba bata lokaci ta dibi inda Maryam take tsaye tun farkon fitowar su tace maryam bude mai kofar falo tukun,,,
Bayan an bude mai yadan shigo daga cikin ya zauna maryam takawo mai ruwa sanyi tare da dan abin tabawa,
Ya dauki yar ledar ruwan goje water da ta aje mai ga plate ya dan tsosa kadan yace Alhamdullah,
Nagode da wanan ruwan da kuka shayar dani Alkah yakara budi da daukaka,
Daga Maryam har Anty sunji dadi sosai da wanan kalamin tashi,
Hakan yakara basu damar sake jiki dashi don dama darrrr suke dashi saboda rashin sani ko da may yazo,
Sai maryam taji kawai mutumin ya kwanta mata arai,, saboda kalaman bakin shi na alheri ne,
Saboda ta lura cewa yana da addini atare da shi ,
Tsabar talauci ne kawai ke damun shi ya koma haka
Wani irin mugun tausayin bawan Allah sukaji cikin lokaci guda,
Maryam sai tunane take yi a ranta cewa,ashe daman wanan mutumin yana da yan uwa musulumai,,,
Maganar bakon ne ya katse ta, da cewa, dan Allah kuyi hakuri nazo maku a bazata, tare da kuma bakon al,amari,
Dama taimako da kuma shawara ne nakawo maku, akan cewa,
Wanan yaron da ke zuwa gidan ku Joseph don Allah tunda har naku yazo daya dashi ina son ku dan tallafa mai ,
Nan da nan daga Anty har maryam suka dan kali junar su,
Suna mamaki har may zasu iya tallafawa Joseph dashi su,,,
Ai kuma sai mutumin yai shiru ,alamar maganar da zai furta tana da nauyi,
Zuwa wani dan lokaci kamar mai tuna ne,,,,,,
Can kuma sai yace, ku yi mai tayin musulunci a hankali pls,
Yafadi cikin taushin murya,
Duk da dai nasan cewa abune mawuyaci , amma nasan cewa zaku iya insha Allah,,,,
Yakara fadi a raunane, cikin nuna damuwa sosai a fuskan shi,
Shiru wurin yayi daga anty har Maryam dake tsaye kamar mai wancin gadin, yar uwar nata, Saida maryam takai zaune a gefen hannun kujera, dake kusa da ita,
Saida Anty tadan nisa sai tadan daga kai zuwa kallon malam,Abdull samad tace
A gaskiya malam kazo muna da mawuya cin abu amma da ace mai gida na yana gari ne kaga sai kuyi magana dashi ta yadda za,a fahinta,
Katseta yayi dace wa ai koku da yake, zama daku a hankali zaku iya dan jan ra,ayin sa don dai yana da bukatar haka din
Idan har kunyi la,akari da yadda rayuwan shi take,,
Yakare zance shi da cewa ina fatan Allah ya baku sa,a
Gaba dayan su alokaci guda suka ansa da Ameen ya Allah,,,
Basu tashiba saida malam Abdullsamad ya basu labarin dalilin musuluntar shi, da kuma irin kalubalin da har gobe yake samu, daga mutanen shi nada,,,watau Christian,
Yace musam man mahaifin Joseph da yafi kowa son kuntata mai,
Saida duk kan su, suka tausaya ma halin da rayuwar ya shiga sukai mai fatan gamawa da duniya lafiya,,
Anan yai masu sallama ,akan cewa idan maigidan yadawo zai zo sukara,tataunawa da shi akan zancen Joseph din In sha Allah,,,,
Da zai tafi Anty Dije ta kawo dubu daya tabashi tace ya hau mashi zuwa gida
Yai ta sa mata albarka yana ta godiya kamar wanda,taba wani abu mai yawa,
Tun fitar wanan bawan Allah, duk sai jikin su,yai sanyi lokaci guda tankar, an aiko masu da wani labari, mai kashe jiki, duk su kai shiru zuwa wani dan lokaci,,,
Kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyar shi akan zancen,,,,,,,,
Barci takeyi amma sai juyi takeyi kamar wace aka danne ta daga saman ta,
Sai shure shure take yi da kafarta kamar mai bidan ceto,
Zubur ta samu ta mike tana mai kumar ihu cikin wani irin karaji tace, JUSES crisis,,,,
JOSEPH,,,,, tafadi da karfi tana mai dafe, kirjin ta,
Guda guda take mai da numfashin ta sai wani irin zufa da takeyi kamar wace ke cikin ovon
Wanan mafarki yana damun ta sosai yanzu,
Har takai yanzu sam bata son tai barci asuba saboda , da wuya tai barci a wanan lokacin batai mafarkin nan ba,
Still masu farin kayan da take gani suna kokari jan Joseph din cikin korarayen haki,, ko yaushe yau,ma su din ne dai tagani, suna ta kokarin jan shi,,,,
Sai,dai ta yau mafarkin nata yadan bam,bamta dana kullun,
Don dai yau,taga Joseph sosai a cikin mutanen,,,,
Tana bin shi ta kamo shi amma sai ya kubce daga rikon da tai mai, shine mafarin wanan shure shuren da take ta yi, a lokacin da take mafarkin,
Bible din ta dake gefe tadauko ta gyara daura dankwalin ta da kyau, nan ta fara jefo addu,oi da tasaba yi kamar kullun, har zuwa wani lokaci,,,,
Koda gari ya waye ranan sai ya kasance mama choima ta kasa sake jikin ta sam bata walwala, yau,
Duk abin duniya yadamay ta akan dan jikan na,ta
Tsoro take ji don tasan cewa akwai abin da zai sami Joseph din,
Saidai ta rasa ko may wanan mafarkin ke nufi, haka nan,
Ejoma ta lura da cewa yau mama tana cikin wani yanayi don ko yaron Ejoma da take kokarin rike mata yau sam bata ko kalle shi ba,
Inda take zaune tayi tagumi, Ejoma tazo tazauna gefen ta,
A hankali Ejoma ke kallon mama, sai can tace,
Mama yau may ke damun ki ne, wai ? da naga baki walwala, sam,
Kamar kada ta fadawa Ejoma wanan maganar,
Sai,dai kuma ta fara ba Ejoma labarin tun fara mafalkin nata akan Joseph din,,,
Da irin yanayi da take ganin ahi a ciki yanzu,,
Ejoma,tadan kwan,tar wa mama da hankali ta dan dafa kafadar mama kadan tace
Kinsan cewa shi mutum ne mai harka da mutane kala,kala, mama,
Don haka dole,
yasa ko da yaushe kike ganin shi tare da irin wa yan nan mutane,,
Har wani lokaci Ejoma da mama Choima suna zaune suna zancen duk akan Joseph din,
Joseph din ne ya bugo masu waya yana tambayar lafiyar su,
Anan mama tashiga tambayar shi labarin yaya yake can ya kuma aiyukan shi,,
Inda yake kara mata karfin gwiwar da cewa yana tafe kwanan nan,
Amma ita sam bata,yarda da zancen shi ba, don har yanzu idon ta na hasko mata masu fararen kayan da suka rike mai hannu suka wuce da shi tana ta kurma ihu,a daji,,,,
Shiko Joseph yanzu yakai kusan wata, hudu a can
Har kasar chaina, yake tare da wani abokin karatun shi,
Cikin dan kankanin lokaci mr Sonny, da suke tare ya dan kara gwada mai wasu yan dabarun kasuwan ci,
Allah da ikon shi ya kara daukaka shi sosai, ga harkan business,
Ga harkokin shi na Nigeria su ma suna ci gaba,
A, sannu yasamu ya kulla, a,laka da wayan nan mutanen suka yarda zasu zo Nigeria su kafa irin wanan masana,antar,
Wanan harkan duk ya,samay shi da ga taimakon da hamshakin maikudi a kasar IBO yai mai hanya, abokin karatun shi
Wanda tun kare karatun su shi yana can zaune yana harkokin shi, da turawa da chainawa,
Mr Sonny shine ya basu sunar Joseph saboda yabawa da hankalin shi da yayi,
Don tun a can da yasan halin Joseph sosai da rikon amana,
Abin mamaki,Joseph nadawowa,da wanan harkan,
Saiga shi ya dauki yaran hausawa cikin ma, aikatar company da aka bude Bunue,watau makurdi, wanda su yan kabilar su sam basu so hakan ba,
A, bangaren su maryam da Anty dije kuwa,
Tun bayan tafiyar wanan tsohon sai maganar tazauna ma maryam a zuciyar ta
Tunane takeyi ta yadda zata fara aiwatar da wanan shirin kamar yadda aka basu shawara, su tallafa mai,
Don haka tasawa zuciyar ta cewa zata bada nata gudun mawar amma ba tare da sanin kowa ba,,
Don haka shiri na farko da tafara yi shi sayen sabon sim card na layin,MTN,
Sabanin wanda kowa yasan ta dashi a da tana amfani dashi,
A cikin wayar anty Dije ta samu nobar wayan shi tai serving a sim din ta,,,
A wani dare bayan ta gama komai tana shirin kwanciya ne
Sai zance malam Abdulsamad yafado mata arai,
Tashi tayi tsam daga inda take kwance,ta dauko wayanta,
Ta rasa may zata rubuta da farko,sai can wanan
Sakon farko da tafara tuwa shine,
Come to the light of life, islam,,,,,
Joseph dake zaune yana searching din wasu kaya a cikin laptop din shi yaji sako ya shigo mai a wayar shi,,
Kamar ya share kada ya karanta saidai ya mika hannun shi yadauko wayar, a hankali,
Da niyar,yadan diba sakon yaci gaba da aikin shi,
Sosai yai mamakin ganin wanan sakon awayar shi batare kuma da da sanin mai nobar ba,, Nan da nan duk wani abin da ke gaban shi ya dushe mai,
Kafin wani lokaci idon shi ya kada yai jajir kamar yaci gauta ja,
A hankali ya runtse idon shi, yana sauke numfashi a hankali, ya fida wani huci ta bakin shi,
Tsayin lokaci babu abin da ya iya yi ko tunawa, wayar ya kara dauka ya diba sakon,
Ahankali, maganar mahaifinshi ya fado mai a rai,
Inda yake yawan ce mai hausawa basu da kyau, don wata rana zasu iya canza ka Joseph,,
Sai kuma inda Mr Ema ke cewa kadaina yawo da yaran hausaw don basu da tabbas,
Cikin wani irin yanayi ya aje wayan kamar mai tsoron wayar, na shi alokacin,,,
Da kyat ya iya mikewa zuwa cikin bedroom din shi jikin shi,duk ba kwari,
Duk da ya kwanta da ya runtse idon shi ba abinda yake gani sai wanan sakon na wayar shi,
Come to the light of life, islam,,,
Rintse idon shi ya karayi kamar wanda bai son tunawa da sakon,
,,,,,,
Maryam wace ke zaune bakin dan matsakaicin gadon su ita da Issalam,
Takai wani lokaci tana jiran replay din shi saidai taji shiru ba wani alamar da wani sako tafe,
Haka ta hakkure ta kwanta tare da tunane kasadar da tayi na tura mai wanan irin sakon duk da tasan cewa ba wai zai gane cewa ita bace,
Amma dai tasan cewa kasada ne haka din, don ina ruwan ta da addinin shi,
Tsuki tayi gami da juyawa tana may ganin laifin kanta, dayin katsalandar da shiga harkan da ba nataba,
Sim din tacire a hankali ta samu wani guri inda tasan cewa, ba mai taba ganin shi gurin, taboye
A hankali taja bargon ta dake gefe aje, tai rufe jikinta da shi ta,na mai lumshe idon ta,
Sai dai sam barci yaki daukar ta don tana tunane akan sakon da ta tura,
May ye,wai, amfani abokan shi su jibrin da KB da bazasu iya fadakar da shi gaskiya ba,
Tsuki tayi gami da kara juyawa ta wani gefe tanamai cewa
Ina zasu iya fada mai gaskiya tunda suna samu kudin agurin shi a kai a kai,
Wai may yasa mutane kudi ya rufe masu ido ne haka da yawa,
Kudiba fa, ba kunya yadda suke rawan kafa akan ARNE, wanda suke darajawa da kiman,tawa saboda kudi,,,
Shin wai basu san cewa shi kanshi yasan cewa sun fi shi daraja ba da kima mutunci, saboda hasken addinin su, yafi na shi,,,,
Amma saboda kwadayi duk sun zubar da damar tasu,
Kara jan bargon ta tayi ta lullube lif daga haka barci mai nauyi ya dauke ta, zuwa wata, nahiyar,,,,,
A,A masuga ne zaune a office din shi yai tagumi da hannun shi, guda ,
Ba komai yake tunane ba sai wanan yariyar da yafara ji a, cikin zuciyar shi,
Watau Maryam wace duk wani tsari da kuma diri da yake bukata ga mace tana dasu,,
Kafin ya kai karshen tunanen shi yaji an turo kofan office din nashi,
A hankali yadago kai da idon shi da suka dan sauya yanayi yana mai kallon kofar ,
Da sallamar ta ta,shigo office din cikin shigar atamfa, da dan hijabin ta mai kara mata kyau ko yaushe,
A nutse take kamar kullun yau madai kamar ba sabo a tsakanin su har yanzu,
A mutunce ta dan durkusa ta gaishe shi, sannan ta dan samu kujera guda ta zauna,
Sai a lokacin A,A yadago ido ya zuba mata su kamar na yan mintina,
A kunyace maryam ta kauda kanta daga kallon shi, saboda bazata iya jure kallon namiji ido da ido ba,
Yar murmushi yayi har fararen hakoran shi suka dan baiyana fili,
Magana yake yi mai kama da rada,maryam kina kokarin ki min illa a wani part na jikina,
Cikin dan razana da dago idon ta,akaro nabiyu suka kara yin arba da juna,
A,A yace yes, ba wai, ba gaskiya ce nafada, saboda duk second ina ganin ki a zuciya ta Maryam
Cikin mamaki maryam tace mai malam ni kuma ? ta fadi cikin sanyin murya,,
Kai yakada mata a hankali, yace akwai wata maryam ne nan a tare da ni,
Ido ta dan kura mai sai kuma tai saurin kawar wa , azuciyar tako tace ban taba tsan manin cuta da ga gare ka ba malam,
Ansar da yaba tane yasa ta gane cewa zancen zuci ya fito fili,
Don ji tayi yace har abinda yafi haka zaki iya ji daga gare ni ai,
Zan cena sam babu maganar cuta ko yaudara acikin ta,
Gaba daya suka kurawa juna ido cikin dan mintina,
Maryam ce tai saurin kawar da na ta idon again
Saboda in badon a zaune take ba da zata iya faduwa don kaduwa,
Sannu a hankali A,A masuga yaciga bada kafa gwaunatin shi a zuciyar maryam,
Cikin jin kunya da kuma nauyi Maryam tai mai sallama daniyar wucewa yau ita kadai,, don dai wani irin nauyin malam din take ji yau,,,,
Tafe suke ya na,takara kafa gwaunatin shi gare ta, ita ko har yanzu ta kasa gaskan ta zancen nashi a cikin ranta,,,,
ZEEE. MAKAW
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
2β£0β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Masoya novel din furen juji ina maku fatan alheri aduk inda kuke ina kara maku fatan gamawa da duniya lafiya ,
Rahama ,daukaka azurta,dacewa da alheri ubanginji Allah ya hada ku dashi,
Don nasan cewa bawai novel din kuke kauna ba kishin addinin mu ta isalama yasa kuke kaunar novel din, fatan alheri gare ku ko yau sheππππππππ
Tsaye yake a cikin dakin shi yana daura agogon a hannun shi wanda ke mai masifar kyau aduk lokacin da ya makala agogo a hannun shi,
Jerked din shi yadan aza saman wuyan shi, hannun shiguda ya rarimi yar Case din shi, da ita,
A cikin sauri yake kokarin yin komai hakan kawai zai sa mutum yagane cewa yana da wani abu mai muhinmanci yau agaban shi,
Da dan sauri sauri yake saukowa daga step din yana kokarin gyara tie din dake makale a wuyar shi,
Tun bai karasa sauko wa ba Ejoma dake tsaye a bakin dinning table take mai wani irin kallo,
Kofa yanufa don yau baiko tsaya zuwa gurin kakar shi ba,
Brother, abinda Ejoma ta furta ke nan kamar yadda take kiran shi, where, are u going
Your break fast is ready now,
Tafada cikin yar shagwaba kamar yadda yan kabilar