Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
tafi sallah lokaci yayi, pls,,,
Saida ya idar da sallah shi sanan ya kira layin maryam
Maryam wace a lokacin tana daki zaune ta idar da salla itama saboda time akwai dan tazara tsakanin yadda ake sallah a kwantagira da Abuja,
Cikin mamakin ganin layin Yusuf na kiran ta, ta mika hannu akai ta dau ko wayan,
Da muryan nan nata zakwaikwai ta,ansa sallamar tashi,
Gaisuwa ta fara yi mai tana mai kara wayar a,kunnen ta,
Sunan ta yakira cikin wani irin muryan nan cikin golden voice,
Maryam ta amsa da na,am
Yace may ye hikimar ki na kai anty gidan su sadiya pls ?
Shiru tayi kamar bazata ce mai komai ba,
Wani irin nauyi da kunya ne ya lullubeta don may anty zata bari yasan cewa itace ta bada shawaran a,tafi gidan su sadiya,
Karo na biyu ya kara kiran sunan ta cikin wani soft voice da yafi na farko taushi,
Yace kina ji na pls karki boye min komai akai, ki fada min dan Allah,?
Sani sanyi taji don ya hada ta da Allah akai,
Nan take ce mai ya Yusuf a gaskiya dai ka san cewa mutumin bai kyauta maka ba ko ,
Bai kamata ace yai maka wanan cin fuskan ba gaskiya,
Zataci gaba sai ya tare da cewa cikin yar murmushi maryam ai ba karya ya fadi ba ko,?
Tunda dai ni din duk yan uwana kafirai ne ni kadaine Allah ya cire a cikin su,
Kinga ii dole ne in ta samun wanan challenges din ko, ?
Ta gumi tayi da hannayen ta bibiyu tana sauraren shi cikin tausayi
Tana ji tankar ace itace a kusa dashi a lokacin a matsayin ta nadan uwan ta,
Amma afili sai tace to ya yusuf dan Allah kayi hakuri bazan sake ba
Abin ne yaci min rai sosai wallahi shi yasa nakai anty taji da kan ta don a dauki mataki akai,
Murmushi yayi yace aa maryam wani mataki kuma kawai na bar masu diyar su kawai,
Cikin sauri tace subbahanallah dan Allah ya Yusuf kadakayi haka pls,
Saboda may maryam kinfi son ta dani yayan ki ke nan,,?
Ya yariny ce wallahi akwai tausayi idan ka ganta
Nan dai yaci gaba da bata musalai akai har ta dan gam su sukayi sallama,,,,,,
ZEEE. MAKAWA,
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
5β£9β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Wanan shafin nasadaukar ga Shahararen Admin of Admins na,COOL NOVEL MAKEUP AND KITCHEN 1,2,3,4,&5
Hayatu Baba Zubuiru (Ya Hayatu), daukacin masoya Novel din FuREN JUJI muna tayaka murnan zagayowar ranan haihuwar ka,πππ Ubangiji Allah yasa albarka ga shekarun da aka diba,
Babu shakka ka kai a yaba maka musanman ta yadda kake ilmantar da koyarwa uwa uba girki da kwaliya ga nishadantarwa mai karatu Allah ya kara daukaka da Basira πππ
Zaune suke su biyu suna karatu inda maryam ke koyawa Na,imat yin tsarki da kuma alwala a musulun ci,
Maryam najin dadi sosai na yadda Na,imat keda saurin haddace karatun da suke yi,
Sallaman mutyn kawai suka ji daga sama saboda duk basu san da zuwan shi ba a,yau din,
Ku san lokaci guda sukai mai sannu da zuwa atare,
Na imata mike da sauri daniyar zuwa ta rugun may shi kamar yadda suke yi ada in ya dawo daga tafiya,
Da sauri Yusuf ya jaye gefe guda yana mai ce mata cikin kakasar murya
I warn you is forbidden in islam pls don't do dis again,
Cikin nuna jin nauyi Na,imat tai dan rau da fuska kamar mai jin ciwo,
Maryam ce ta kawar da shirun da yadan biyo baya da fadin sannu da zuwa ya Yusuf, ya hanya,
Daidai lokacin da yake zama ya karba mata da fadin Alhamdullah,
Sai kuma yadan waiga kamar may nemar wani abu agidan
Maryam ta mike a hankali ta tatara littafan da sukai amfani da shi, zuwa cikin wani dan loka da suke aje littafan addini aciki,
Muryam shi taji yana cewa ina Anty ?
A takaice tace sun tafi, gidan barka haihuwa,
Fridge ta nufa da niyar dauko mai drinks amma sai taji muryan shi yana cewa,
No, no,no iam ok, thanks,
Mun tsaya Bobi gurin su mama an bamu fura da nono mun sha nagode,
Da sauri maryam ta juya inda yake tana mai kallin mamaki don jin abin da yace,
Cikin fuska ba sauki yace yes daga can muke tana gaishe kuma,
Marfin fridge din maryam ta sake a hankali ta koma zuwa gefen kujerar ta zauna,
Na,imat, wace ke kokarin zama kusa da shi take tambayar shi labarin maman Choima,
Sai da ya dan furzan yace mama tana lafiya sai,dai fitina kawai data kara, maryam wace ke gefe guda tai murmushi,
Sallamar mukaji daga kofa gida ko ba,a fada ba sun san cewa masu shigo da tsaraba Yusuf ne,
Saidai wanan karon tsaraban ya sha bambam da na kullun,
Wasu irin set din akwatina aka dinga shigowa da su,
Mamaki karara ga fuskokin su maryam da Na,imat
Da sauri maryam ta shimfida wani dan karamin center carpet a tsakiyar falo suka dinga ajewa a sama ,
Kafin wani dan lokaci duk sun gama shigo da abin da yazo da shi,
Maryam batai mamaki sanin cewa yakanzo da motoci fiye da guda daya idan zai zo da wuya ya,shigo da guda garin,
Shigowar Anty Dije gida,ne ya sa shi dakatarwa da dogon wayan da yake yi tun zaman shi acikin yaren su,
Nan suka shiga gaisawa da ita tana mamakin ko ina yafito da wanan kayan,
Bai mata wani bayani ba akai ya mike yana cewa zai tafi ya watsa ruwa sai yadawo,
Fitar Yusuf Anty Dije ke tambayar mu ko kayan may ye wanan yazo da su,
Maryam wace ke kokarin mikewa don shiga kitchen bata, tace komai ba don in ma har sanin ko na may ye ai itace ya kamata tasani,
Tunda Yusuf yabar gidan bai dawo ba har suka gama duk wani aikin da yakamata suyi,
Sai zuwa bayan sallah isha,i Yusuf ya shigo gidan,
Wanda zuwa lokacin maryam ta fahinci Anty ta ta matsu tasan ko kayan may Yusuf yashigo gari da su,
Don ita azaton ta kayan lefen shine yashigo da su tun da ba shi hakkuri a kai,
Sun kara gaisawa da sister Dije inda take mai ya aiki ya bayan rabo,
A hankali maryam tai magana kamar wace ke, jin ciwon baki,
Tace mai a kawo maka abinci ne,
Haba dai maryam wanan ai tayin rowa ne ko,
Ina kin hada mai komai ko basai kawai ki kawo ba,
Anya Maryam za muko, sha ruwa agidan ki kuwa tana wa Maryam din ba,a,
Maryam ta dan turo baki gaba tace to anty idan kace zakaiwa mutum abu sai yace shi ai ya koshi,
Ido kawai ya bita da shi yasan cewa don dazu zata bashi ruwa ne yace ya gode shine takewa wanan zancen,
A bincin ta dauko mai har zuwa inda yake ta dora saman dan karamin stol,
Ita da kan ta tai serving din shi da kuma kawo mai ruwa,
Sai a lokacin ne ya fara yiwa anty bayani kamar haka,
Anty ki samu time ki bude boxes din nan ki duba kiga abinda ke cikki,
Idan da akwai abin da za,a saye akara sai ki fada min akaro,
Maryam najin sun fara zancen akan akwatinan tai saurin mikewa daga gurin da take cikin niyae wuce wa ciki,
Amma sai ji tayi anty na cewa maryam zo ki bude ke da Na,imat ku diba min pls,
Ai bata san lokacin da ta dago kai ta kallo yae ta tace wa ni Anty,?
A kwai wata maryam ce agidan bayan ke maryam, inji Anty,
Kala batace ba sai wucewa da tayi direct gurin akwatinar,
Da babban nasu daga ciki ta soma budewa don yafi tare guri,
Zannuwa atamfa zube a ciki tankar shago, saida su kala,kala,
Sai da gaban maryam ya fadi saboda irin kayan da aka jibga acikin akwatin
Da aduke take sai takai tsugun ne saboda kafar ta ba zai iya daukanta ba,
Haka tai ta daga kayan daya bayan daya har su ka kai karshe yana zaune bai ko kula da abinda sukeyi ba,
Γnty angama inji maryam wace duk tagaji da dagawa,
Wanan ai ba wanin abin da zamu kara aciki a kai masu haka kawai Allah dai yasa albar ka,
Sai alokacin yadago yana kallon anty yace cikkn gyaran murya,
Anty wanan kayan kayan auren Na,imat ce da Ibrahim,
Wani ajiyan zuciya maryam tayi ta yadda ba wanda zai jita,
Amma da fada takeyi don may zasu zageshi haka kuma ya wani zage ya kashe masu dukiya haka ,
Muryan shi ce taji yana cewa anty a,gaskiya
, bana son Ibrahim yai komai anty, saboda ba wai yadade da fara aiki bane,
Kayan daki nake son ki samu time sai aje azaba mata duk inda kikaga yafi,
Cikin watan azumin nan nake son ko da an fara ne ayi auren pls,
Saosai kowa ke kallon shi da mamaki yanzu duk wanan kayan ba akan shi ya sawa ba,
Kawai don jin dadin wasu yayi shi,
Shin anya kuwa ba zancen mutane gaskiya bane da suke cewa Yusuf wai furen kan juji,
Don dai sam halaiyar shi duk abin ayabane baka taba ganin yayi wani abin assha,
Bayan kuma mhaifin shi yana can a matsayin shi na kursungumin kafiri wanda ko da,wasa bsi kaunar yaji kalman musulunci,
Sallamar wani yaron makwabtar su ne ya sa kowa shi,
Yaron yace Assalamu Alaikum wai ance maryam ta zo ga A,A a waje gida,
Wani irin fesar da iska Yusuf yayi da bakin shi don abin da yaji,
Shi a,zaton shi Maryam basu tare da wanan guy din,
Kanta ta maryam gefe cike da jin nauyi yadda yaron yai magana,
Sai yanzu ta tuna cew tabar wayan ta a daki tun dazu tasan yakira lalayin ta bai shiga ba,
Yaron zai kara sallama Anty Dije tai tsuki cikin tsawa tace wa yaro kai katafi dan Allah taji pls,
Kamar may rada yadan kalli inda take yana nu mata kayan da yaci abinci
Wani irin haushin maganar shi taji don tasan zai jagula mata al,amarin ta,
Dakin tatakoma ta gyara kimtsawa alokacin yana zaune da Anty suna zancen uren,
Cikkin shigar wani jan dogon riga ta material, anyi mata wani dinki mai shara,shara,
Sai kamshi ke tashi a duk inda ta gilma saboda yadda ta daba shi a jikkn ta kamar da gaiyya
Fitar maryam ba ai wani dade ba Yusuf yafito a kasalance,
Hango su yayi zaune a cikin mota saida maryam kamar kullun kafar ta a waje yake ganganjikin ta aciki,wani irin haushi guy din ya bashi yau amma bai san ko may yasa ba,
Maryam dake a cikin mota ta hango fitowar Yusuf din daga cikin gidan
Full light ya sakar masu yana kallon yadda maryam take kokarin kare hasken motar da hannun ta
Wani irin ashar A,A ya afka mai da ita wanda har sai da maryam tace, haba malam wanan zagi haka kamar yaro,
Kallon ta yayi cikin nuna zargi yace,
Maryam ku, kuka dauki wanan dan IBO da wani muhinmanci,
IBO ne fa ba wata tsiya ba, ni wallahi zanyi maganin shi idan har ya shiga gona ta,
Hannu Maryam tadaga mai abin da bata taba yi mai ba
Tace shi IBO ba musulumi ba ne?
Damay mutun ke nunawa agurin Allah da al,umma ban da Islama,
Shi wanan da kake nu cewa IBO ne naga yafi wasu dubun hauwa( tauhidi)
Ashe ke nan da ibo da bahaushe da bayerabe kai dama kowani irin kabila
Mafi karfin imani shine mai rin jaye ga alumma bawai yare ba,
Yadda kake ganin shi IBO anan haka acan kasar su suke ganin ka bahaushe kai ma
Kallon ta kawai yake galala don yadda ta zake take kare Yusuf yau a gaban shi abin ya bashi mamaki,
Sai dai duk maganar da ta fada babu wanda ba gaskiya ba daga cikki
Hiran nasu daga karshe haka suka watse ba wani kwakawaran zance sai debet akan IBO da hausawa
Ida ita maryam ta dage da cewa kabila bashine abin suka ga mutun wanda yake musullumi ba,
Dane a lokacin da ake da karancin addini ake irin wanan maganar,
Washe gari Yusuf bai shigo gidan ba sai kusan shadayan rana,
Sanin yana gari maryam bata zama da kananin kaya agida kamar yadda idan mijin Antyn idan yana gari bata wani damuwa da gyaran jikinta,
Yauma dai wasu zanin tamfane masu ruwan powder sai wa su flowers da akai masu masu ruwan milk,
Zaune take a gaban tebur tana cin abinci a cikin natsuwa kamar ko , yaushe,
Yakai wani lokaci agurin tsaye yana kallon yadda take komai nata a natse
Sam bata da hayani ko wani rawan kai irin na yan matan da yake yawan gani,
Ita dai gatan ako da yaushe sai umurnin da akaba ta arayuwan ta duk, da irin, halin miskilancin da ke gare ta kafin a saba da ita,
Alamar tsayuwar mutum a kanta taji da kuma kamshi da bawai na irin turaren da yasaba sawa bane yau a jukin shi,
Saye yake da wata yar farar tee-shirt, mai wani dan flower ja agaban rigar daidai saman aljihun gaba,
Wani wando ne baki kamar Jens a wanan yadi yana wani dan walkiya,
Cikin dan rudewa ko razana da ganin shi a tsaye tayi
Saboda azaton ta har yazo ya karya ya wuce ko
Sai idon ta ya hango mata abin karin sa a gefe aje,
Don sam yau kin fitowa tayi tai kwanciyar ta kawai, abinta, adaki sai da ta ga cewa rana yayi shine ta fito,
Da yar murmushin shi ya karaso har inda take zaune,
Ina kwana ta tare shi dashi yayin da yazo gab da ita,
Dukawa yayi gab da ita batare da ya amsa gaisuwar ta ba yace
Saurayinki maryam baida kirki ga fahinta na bai dace yazo har kofan gidan ku ya saki a mota ba, mutane shiya suna ganin ku,
Gaba kura baya karen daji,
Jiya ta yi da A,A yau kuma Yusuf ya,tare ta da zancen A, A din,
Ki kula maryam ke mace ce kada ya bata maki record din ki pls,
Bata son nuna mai maganganun da yai mata sunyi mata tasiri a zuciya ,
Amma afili sai ta dake tace ban ga abin sa ido irin haka ba har zargi na son ya shiga,
Yan mata nawa suke hira a mota wasu ma har gida suke bin namiji amma sai mu da muka zauna akofa za a wani sa muna ido,
Wani ajiyar zuciya ya sauke gami da dan kura mata ido kamar zuwa second minutes,
Mikewa yayi daniyar wucewa amma sai yaji muryan ta a rau,nane tana cewa "Na, Gode"
Da dan mamaki ya waigo ta saidai kanta na kasa tana wasa da spoon din dake a hannun ta,
Dan nazarin ta yayi sai yaji wani irin tausayin ta ya kamashi a take ya juya da niyar barin falon,
Ga abincin ka can fa inji Naimat wace duk basu san cewa ta na gurin ba ashe,
Hannu yadaga mata alamar yagode kawai ya juya yabar falon,
Kallon mamaki da al,ajabi kawai maryam kewa yusuf din
Ita ko Na,imat saida ya fita tasa hannu ta toshe bakin ta tana darita cikki,cikki tace
Wa maryam da gani nasan cewa kin tabo big brother yau,
Maryam tace kawai dai yaso yasa wa kanshi abin da bai shafe shi bane,
Nan dai maryam ke fadawa Na,imat yadda sukayi da shi,
Na,imat tace gaskiya sister ba karya bane don mu yaren mu bamu irin wanan sam,
Kinga kuwa tunda yanzu anzama daya dole ya fada maki gaskiya, saboda yasan cewa zubar da mutunci ne irin haka,
Mamakin jin abinda Naimat tafadi maryam tayi,
Yanzu a she har akwai abi da bahaushe zaiyi ace wai IBO naganin shi a cikin rashi tarbiya,,,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA
[3/25, 06:08] Anty Lantana: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
6β£0β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
Kaunar da kuke nu na min yasa har na kasa bakin godiya agare ku,
Fatan Alheri ga duk wance ta fahinci ma,anar wanan sakon da nake isarwa,
Ubangiji Allah ya kara maki ke mai karatawa daraja da,dauka,
Allah yasa mu gama da duniya lafiya baki dayan mu
Allah ubangiji ya taimaki addini musulunci da ma musulman baki daya
Ya Allah karawa Annabi Daraja,πππππ
Gudu yake shararawa acikin motar shi hannu shi guda yana, dan shafo fuskan shi dashi a hankali,
Tunane yakeyi wai may ke sa shi damuwa da al,amarin wanan yatiyar ne,
Har