Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 84

21K to 24K   out of 251.8K words

su zuwa yanzu,
Amma shi in har yana gari yana attending din Church tare da su,,,
Shi a ganin shi rayuwar shi ce hakana ta taimako mutane,
Saboda in sun diba ai yanuna wa yanda ke zaune saman benci tare da su da hannu yace,
Joseph na nin su har gida ya tai maka masu time to time,
Yace ko ba haka bane, sukace gaskiya ne, hakane,
Yace to shi yana ganin cewa wanan halin nashi haka take duk wanda yake tare da shi yana taimaka mai,
Mr Ema dake gefe yatokare hannun shi da sanda hular shi ta gwalmade gefe guda sai kafa kawai yake buga wa a kasa,
Jin jawabin na Mr Okarpo yasa gurin ya kara daukar hayaniya, so sai wanan karon,
Mutane da yawa daga cikin su suka kawo shawaran cewa Joseph yaron kirkine,
Shi yasa yake tare da duk wani wanda tunda suns tare ,,
Don ya na taimakawa hausawa ba shine zai sa a ce yana son yin wani abinda ba daidai ba,
Amma duk da haka su elders zasu kirashi su tsawata mai akan hakan,
Da wanan shawaran taron ya watse kowa na fadar albarkacin bakinshi,,,
Tunda Mr Emanuel yadawo daga gurin meeting din rayuwar shi take bace saboda shi a ganin shi an wa dan shi kullin sheri
Saboda kawai cigaban da ake ganin ya samu,
In bashi ba taya zasu dangata shi da wani akida cen,
Yan uwan shi kaf ba musulumi ko wani akida ta daban,
In ma hakane zaiwa Joseph din fada ya daina shigowa kwantagora gaba daya,
Yana yi yana tula giya a cup yana shan ye wa kamar wanda bai da kimar ciki,,,

Duk wani abinda zata bukata ta shirya shi a cikin dan kit din da tadauka don tafiya,
Batare da ta fadawa koda Amina ba zatai wanan tafiyar da zatayi yau,
Saida ta gama shirin ta tsab sanan ta fita tsakar gida inda, inda inna ke zaune bakin murhun ta na kasa tana gyara wuta ga koko a cikin wani dan roba mai marfi wanda ke nuna abinda ke a robar fili,
Ganin Aisha waje da safen nan yasa inna cewa, wa azubo maki kokon ne ?
Tawani ya mutsa fuska kamar wace akaiwa tayin kashi tace kai haba inna da safen nan haka,
Kujera ta jawo gefen inna ta zauna tana fada ma inna cewa zata kauye gurin kakar su ta dibo ta,
Shiru inna tayi cikin zargi take kallon yar nata wace ke magana cikin matse fuska sai kace aiba uwar ta take zance da ita ba,
Har ta mike uwar tace kwana nawa zakiyi saida takai kofan dakin ta ce batare da ta waigo ba,
Sai lokacin da kuka ganni kawai inna,
Daga haka tashige tadauko dan kit troler din da ta shirya kayan ta aciki,,
Tashan hanyar BCG ta nufa tana zuwa ana cewa Minna Abuja kaduna,
Abuja tace kawai kai tsaye aka karbi dan troler kit din ta a ka nufin motar dake kan layi,,,,
Musalin karfe ukun rana ta isa Abuja, wayar ta taciro takira layin shi,
Kira nabiyu yadaga layin yana mai cewa hlo, cikin wata irin murya ta ke magana kamar ta mai shagwaba,
Joe gani a Dikko fa,
Cikon mamaki yace mata Dikko fa Aisha tace mai eh ,
Kwatancen inda zata sauka, ta, tsaya yai mata, yace zai turo azo adauke ta,
Joseph yayi maki kwarai da jin cewa wai gata a dikko, bayan jiya sukai waya yake ce mata yana Abuja yazo yin wani dan aiki ne ,
Sai gashi kawai yana fitowa daga gurin meeting kiranta ya shigo mai,
Wata mota mai kama da, Box ta faka a gaban ta kau da kai tayi kamar bata gasu ba,
Sai hon da taji yai yawa yadan sata waigawa, driver motar ke ce mata itace Aisha ko ta karba mai ya nuna mata complement card din Joseph
Hskan yasa ta yarda da shi ta shiga motar bayan ya bude bayan motar yasa mata kayan ta ciki,,,
Wani gida mai hawa biyu suka shiga gidan bawani fadin fili ke gare shi ba amma ko kafin ka shiga kaima kasan cewa hadaden gida ne,
Da,sallamar ta ta shiga don duk ta rude da gani daular duniya da ta gani,
Jin da tayi yana ce mata hy Aisha,,u are, wel,come,
Daidai lokacin da yake saukowa daga steps din gidan,
Yar murmushi ta sakar mai tana wani nuna kamar alamar jin kunya,
Zuwa yayi inda take tsaye yai dan hugging din ta yana mai ce mata bukin surprise ke nan,
Kujera ya nuna mata ta zauna daidai lokacin mai aikin shi yashigo dauke da trey da drinks a ciki, sai cups guda biyu, a sama,,,
Shi da kan shi Joseph din ya zuba mata drink din a cikin cup dai dai lokacin kuma yake tambayar ta ina kawar ta wanan karon,
Tana karban cup din da yake miko mata ta ce, ba wanda yasan cewa nazo gurin ka fa,
Cikin nuna mamaki yafada cikin yar muryan nan tashi, yace saboda may,
Ta dan daga kafadar ta tace Just,
Tace ban son kowa yasan cewa nazo gurin ka, shi yasa tadan kare zancen acikin yar shagwaba,,,,
Bayan tai wanka ta kimtsa jikin ta wani dan kwalba ta dauko a can kasar handbag din ta,
Wani dan ruwa ne aciki blue kamar ruwan turare ta dan shafa kadan a saman maranta,
Sai kuma saman goshin ta daidai tsakiya ta man,na kadan,
Body spray ta feshe jikin ta da shi mai mugun kam shi na ,
Wani ribon ta dauko daga cikin handbag dinta, tadan feshe shi da kamshi ta daure kanta da shi,,,
Duk da tana da gajiyar tafiya a tare da ita, hakan bai hanata binshi zuwa cikin gari ba,
Sahad store ya nufa da ita inda ya bata damar daukar duk wani abinda take bukata yakuma ce mata kada taji komai,,
Cikin yar kunya take zabar yan abubuwa kamar wace bata so, Joseph na tsaye gefe yana kallon ta,
Ganin zata bata mai lokaci yasa shi kwasan mata abubuwar da mata ke yawan amfani da su,
Kamar su manshafi turare, kayan makeup, sai kuma ya juya yanufi fannin sutura,
Sayayyan alfarma yai mata,a wurin sai turamen zannuwa da ya jido kamar mai hada kayan lefe,
Jin bills din kudin saida ya sa Aisha dan kaduwa amma sai taga kawai ya biya batare da jin darrr ba,
Mamaki fal a zuciyar ta don bata taba zaton koda quarter haka ba, daga kowani irin mutum,
Sai wurin kayan kwalama da suka nufa inda nan ma ba karamin kudi ya kashe mata ba,
Wani Guy dake gefe ya ya matso kusa da inda suke tsaye yana cewa sannun ku da,zuwa ya hanya,
Idan kuna son dinki express ga shagon mu nan zaku samu zuwa gobe insha Allah,
Joseph ya dan kalli inda Aisha taja tai tsaye yana mai tambayar ta tana bukatar dinki, ne, kai ta gyada mai alamar eh
Cikin turamay da suka sayo suka bada guda biyar, dinki, akan dubu Ashirin,
Babata lokaci ya biya guy din sai yabasu nobar da kuma, card wanda zasu zo karba,
Daga haka suka wuce zuwa gida da kaya niki niki,
A,falo suka zube nan mai aikin gidan yakawo masu plate, tare da drinks da su, cultularies,
A hankali take komai don abinda take gani ya wuce tsanmanin ta,,,
A daki guda suka kwanta ita, da Joseph duk yadda Aisha take ganin ita yar bariki ce ta katsewa wa Joseph,
Saida ta kwana da dimbin mamakin irin halin Joseph ,
Duk yadda taso tambayar shi ba fuska saboda bala,in kwarji da yake mata, a idon ta,
Kwanan ta hudu Abuja tare da Joseph iyakar shi da ita romance kawai da nuna concern a kanta,
Kamar yadda ba ta fadawa Amina cewa ta na, Abuja ba shima Joseph, din bai fadawa kowa zancen zuwar ta ba, gurin shi,,,
Mota ya bayar aka,dawo da ita har kwantagora, tare da kaya da ya saya mata, niki niki, ,,,
Wa,iyazu billah yar musulumai zamani ke nan babu ruwan da dataraiya da kowani irin mutum ita dai kawai ta samu kudi shine gurin ta,
Yadda ta canza kawai yasa Amina gane cewa gurin Joseph ta tafi,
Cike da mamakinta take kallon ta don ganin irin abinda take fitar wa,
Cikin dan rada take, cewa Aisha mutumiyar har kin fara bani tsoro wallahi don kin wuce sani na,
Tana kokarin jera, kayan makeup din ta a mirrow dakinta ne tai yar dariya, tace da nai may fa,?
Haba haba inji Amina Aisha ace har kuma Royce din mu ya wuce ga hausawa musulumai yan uwan mu ya koma ga Christian, haba dai haba gaskiya hakan baiyi ba,
Wani irin kallo ta watso ma Amina daidai lokacin da ta bude akwantin da tashigo dashi,
Kayan da Amina tagani ciki fam shi yasa ta kara zare ido waje,
Tace, shin Aisha kina nufin ,,,,,, nuna kayan tayi da dan yatsanta don tama kasa furta ko a,
Kwarai kuwa inji Aisha tana mai gyada ma Amina kai, tace
Uban wa zai bani wanan koda kuwa sau nawa ina bin mutum motar shi ko wani mafaka
Amma kinga wanan tana nuna kayan da hannun ta tace a free wallahi na,samay su Amina,,,,
Ido waje Aminat ke kallonta cikin mamaki tace a free fa ?
tace wallahi ko,
Amma dai gaskiya mutane ba zasu gane cewa babu wani alaka atsakanin ku mai zurfi,
Ina ruwana da mutane inji, Aisha, duk abinda zasu fada suyi ta fada mana,
Manja da doyan da Irish da, tazo dashi ta dibar ma Amina mai yawa,
Ita dai Amina sai mamakin kawar nata takeyi kawai,
Ace yanzu har da arna suke mu,amula, kai gaskiya Aisha tayi nisa wallahi,,,
Don haka, taja bakinta tai shiru kawai batare da tafadawa kowa,ba ita dai tasan cewa duniya ce zata fada ,,,,,

Tsaye yake yana waya da kanin shi, Samuel wanda ke zaune tare da baban su a kwantagora inda Samuel ke fada ma Joseph meeting din da elders sukayi a kan shi,
Yai mamaki matuka da jin zancen Samuel din don yasan cewa yana ikar kokarin shigurin ganin cewa ya kyautata wa Church din na su,
Badon komai ba saidon kawai ya kare martaban gidan su daga alumar su,
Cike da mamaki yasake tambayar Samuel labarin mahaifin su,
Dan shiru Samuel din yayi kadan kafin can,yace yana nan saidai gaskiya maganar tadan tayar mai da hankali,shi,
Kai kawai ya girgiza yana mai shafan fusakan shi in akwai abinda ya tsana yanzu shine yaga bacin ran mahaifin shi,,
Sallama yayi wa Samuel din yana mai jin haushi elders din na su, akan jefa mai mahaifi cikin damuwa,
Shin ina ma ruwan su dashi dazasu sa mai ido a harkokin shi,
Yasan cewa koda ya kira mahaifin shi ba wani maganar da zai ji a gamay da elders din,
A karshe ma yana iya ganin laifin Samuel da ya fada mai, zancen,
Tun yana tuna zancen har ya share maganar, gurin fridge ya nufa yadauko goran ruwa, ya tutula ma cikin shi,har saida ya zuke gora guda gaba daya ya wurgat da rubo, a dustbin,
Kiran wani Michael ne ya shigo mai a lokacin inda yake sheda mai cewa yason su hadu saboda maganar man Gas dayake son suyi a lokacin,
Michael mutum ne mai iyali shi duk da bawani babban mutum bane sosai,
Yasamu Michael da yaran shi suna wasan basketball, agidan shi
Yaran naganin shi sukayo wajen shida gudu suna mai oyoyo,
Rungumay su yai cikin jikin shi ya na dan shafa masu kumatun su,
Sun san zuwan shi gidan su alherine don haka ledar Sweet din da ya riko masu ya mika masu,
Murna da ihu suka hau yi suka shige cikin gidanan su binsu yayi da kallo
Nan take alkawarin da yaiwa Assalam ya fado mai arai,
Don yasan cewa yaro baya man,ta alkawari duk lokacin da yaga wanda yai mai alkawari bai cika ba sai ya tuna,,
Don haka ya kudurta a ranshi cewa da yabar gidan mic zai wuce yaiwa Assalam sayayan shi ne,,,,,,



ZEEE. MAKAW
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Yau gidan Anty Dije baka jin komai sai kamshin girke, girke ke tashi kala,kala,
Duk wanan kamshin anayin shi a kan maigidan da zaidawo yau daga gurin aikin shi can garin Lagos,
Tun jiya ya bugo masu waya yana mai sheda masu cewa yau zai iso, sanin da sukayi cewa ysna saman hanya,
Yasa su wanan girke girke da kara gyara gida duk da dai gidan nasu ko yau she fes yake,bazakace akwai yara agidan ba,
Bayan sun kammala aiyuman su ne sun gyara guri sai kuma,suka shiga gyaran jikin su,
Duk da zaman Iliyasu ma,aikacin custom ne hakan bai sa ya wadatar da matar shi da komai ba,
Don dai da ka ganta kasan cewa zaman hakkuri takeyi kawai, don babu wani kama na nuna wadata atare da ita,
Allah yasa mata hakkuri da dauri sosai don sam baka taba gane halin da take ciki,
Cikin wanan halin hakkurin da takeyi bai hana yan uwan mijin ta,sata gaba ba da fitina
Don su gani sukeyi ai duk wani bida na Iliyasu yana gurin Anty Dije da yan uwanta,
Idan suna wanan zancen bata bata ranta saidai tayi murmushi kawai,
Don takan ji dafin rashin gane sirinta da basuyi ba har suke ganin cewa komai na hannunta,
Basu san cewa dan uwan su ne mai laifi ba,
Harkokin shi kawai yake yi a can bariki abin shi,

Maryan zaune tana kwalliya a gaban madubi da ke kuryan dakin anty Dije
Wanda har in tana son yin kwalliya mai tsayi dole sai ta shiga har kuryan dakin na anty Dije,
Sauri take yi ta tafi karbo ma anty Dije dinkun nan ta a uguwar Rimaye,
Waje wata yar uwar maman su Anty Dije din don matar ta iya dinkin zamani sosai,
Atamfar code,viore ne mai ruwan makuba da milk, ajikin ta,
Dinkin riga da zani ce tai daurin baya ta kulle shi a tsakiyar baya,
Turaren Anty Dije tadan fesa kadan
, Saida tagama hada komai tadauko dan wani karamin hijabin ta, ta sa sai takalman Bella, da tasa, a kafar ta,
Cikin yar muryan nan nata take sallamar Anty Dije a hankali don gudun Issalam kada taji ta tace zata bita,
Don ance tayi sauri ta dawo, dawuri saboda kila dasu anty zatayi amfani
A gidan mama Asabe tasa mu bata karasa hada dinkin ba don haka tabukaci mama Asabe ta bugawa Anty Dije ways ta sanar mata cewa da dan saura kadan kafin a karasa,
Tana zaune tana jiran dinkin saiga wata budurwa yar gayu ta shigo gidan
Daganin yadda sukeyi da mama Asabe kasan sun saba sosai,
Inda maryam take zaune budurwar takalla tace ma mama Asabe
Asabe ina kika samo wanan yar budurwan mai kyauwo haka,
Saida mama Asabe tadan kalli gefen da maryan take zaune tana mai ci gaba da dinkinta tace,
Diya tace, tazo karban dinkin su ne
Kanyan anty da ake dinkawa tadan taba sanan ta kai zaune saman kujerar roba fara dake dakin da mama Asaben take dinki a ciki,
Turamay zani tafitar guda biyu masu ba,lain kyau daga cikin bakar ledar da tashigo da shi a hannu,
Kai inji mama Asabe amma dai wanan zanin akwai kyau wallahi kamar su sukayi kan su,
Budurwan tana wani ya mutse fuska tace niko kinga Asabe zanin bai suyi min kyau ba
Kodon bani kawai akayi shiyasa ban ga kyaun shi ba,
Mama tana dinki ta ce kedai yar rainin wayo ce taya za,a baki abu kice kin raina,
Amina halinki sai ke wallahi,
Ai ma, mutum abin arziki irin wanan zukakan zanuwar haka ki ce wai ke basuyi maki ba,
Gyalen da ta yafa ta kwabe, ta koma, daga ita sai wata yar rigar t,shirt ajikin ta,
Ta mike ta bude fridge din mama Asabe ta dauko roban ruwan Goje water tadan fara kwakwada,
Maryam dake zaune gefe tana mamaki da kallon ikon Allah,
A, ranta tace wanan duk cikin wayewa ne haka kuma,
Ka cire hijab a gidan mutane, idan maigidan yafado fa ya zatayi,
Muryan Amina yadawo da ita daga tunanen da takeyi
Amina ke cewa mama Asabe bayan ta gama shan ruwan da tadauko a fridge,
Tsaraban Aisha ne fa Aisha mama Asabe, ta tambaya da mamaki,
Ita fa inji Amina

8 / 84