Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   22 / 84

63K to 66K   out of 251.8K words

maryam ta fara walwale wa, daga damuwar da tashiga,
Saidai shawaran anty yai mata amfani, sosai don har yau A,A Masuga, bai nuna mata komai,
Sai kara nuna mata kulawa da ya,shiga yi fiye da, farko,,,,,
Wanan dalilin yasa ta manta zancen mahaifiyar shi a rayuwar ta ,
Don dai tasan cewa bada ita zata zauna ba da shi ne,
Shikuma bai nuna mata gazawan shi ba akanta kullun kara son ta yake ji saboda irin kyawawan halaiyar

Akwana atashi hasarar mai rai, saiga lokacin bukin KB yazo,
Don haka suka fara zama busy da aiyukan buki duk a gidan su KB din ake sha,anin to amma angwanai suna,zamane a falon yaya illiya dake fuskantar baban titin cikin garin,
Wanan bukin yadan sa maryam dan sakin jikin ta da su KB
Don duk wani abin bukata, dasuke so maryam ce zasu kira saboda abokan su da suka,zo daga nisa,
Matar malam suke cewa maryam inda itako abin na mata dadi arai,sosai,
Ilimi, arziki, kyau, wayewa, wani abune, wanda baiwa ce daga Allah,
Shike ba duk wanda yaso ako wani lokaci, ko yanayi,
Wai duk taron nan na buki KB da matasa masu jin kan zu keyi,
Zuwan Joseph a cikin su duk sai ya dakushe sauran, kamar ba,ayi da farko,
Yana isowa buki ya canza sallo, nan take komai aka fara yin shi acikin morewa rayuwa, dakuma wada ta,
Baki sun zo daga nesa saboda wanan bukin na KB wasu daga ban garen sanar shi ta Gas
Wasu kuma abokaine da aka hadu ta wani sha,ani, aka zama daya,
Maryam ta kira safiya don ta taimaka masu da aiki, tare da,wasu makwabtan su yan mata, biyu, sai kan,nen mijin Anty Dije su uku,
Shanu Joseph yasa,aka yan ka anan bangaren ango, da suke ,
Yasa Anty Dije tayo hanyan yan kwatakwali togo, masu aikin girkin abinci,
Nan da,dan guri ya kici may da taron hayaniya, ga raguna uku da yasa a gyaro akawo duk wurin anty inda yace anan za ai masu nadu girke,girken,
Saboda bazai kai gidan su ba don mutane wasu baza su ci ba idan ance acan akayi,
Duk wanan aiyukan da mutanen da akadauko sukeyi bai hana maryam da kawayen ta zakewa ayi shi da su ba hurjanjan suke aikin su tsakani da Allah,
Abincin da akafitawa baki da shi a wani guests house, bai ko isa ba saboda irin haduwar da abincin yayi,
Hakan yaba Joseph da jibrin dadinkar kayan hada hadadaen abinci, don kara yawan shi,
Suna tsaye a filin tsakar gidan Anty shi da jibrin cikin shigar kananin kaya masu tsada,
Dagani basai an fadama irin haduwar su,ba,
Jibrin yace gaskiya anty kin muna abinda ma bamu zata ba zokiji yadda bakin mu ke santin abubuwan da aka kawo masu,
Anty Dije ta nuna masu maryam da su safiya tace kun ga wa, yanda sukai maku can, don ni har fada naso yi da su da farko,
Kallon inda su Maryam suke sukayi gaba dayan su, alokacin suna kokarin yi masu tuwon dare,
Jibrin ne ya tako har gurin su,yakaraso yana ce masu sannu ku fa, yan mata, da kokari,
Suka amsa mai kowace tana kokarin nuna kanta gareshi,
In ka dauke maryam da kawarta dasuke can ta cikin kicin suna hada perpepsoup, din kayan cikin rago,
Ga mamakin maryam sai kawai ganin jibrin din tayi har cikin kitchen inda suke ya biyo su,
Yana ma safiya wace ke kokarin hada jajage a tukunya,
Wani irin kallo wanda ke da ma,ana ga wanda akeyiwa,
Haba Maryam baki bari ta huta hakanan sai ki dinga bata wahala,
Maryam da mamaki take kallon jibrin din yau wanda zata iya cewa bai ma san sunan taba sam,
Don basu maganar komi a tsakanin su sai gaisuwa,
Saigashi yau yakira sunan ta harda ba,a yake mata, akan wata,
Maryam da ta gane nufin shi sai ta ce mai ya jibrin ko ka manta a kitchen kake yau,
Yadan waiga cikin nuna ko oho yace an, hana maza shiga kitchen ne,
Dariyan da maryam ta kumshe saida ta fasa,shi a fili,
So sai take kyalkyallan dariya har dan diplo din ta na lutsawa fararen hakoranta da ke boye ko yaushe yau su,ka haska, a fili,
Ba jibrin dake kusa ba har Anty da Joseph dake ta waje saida hankalin su yakai garesu,
Suna mamakin may jibrin ya cewa maryam haka yau take wanan dariyar,
Basuyi aune ba saiganin jibrin sukayi ya karbi cibin miyar hannun Safiya yana motsa miyar duk gidan kallo yadawo gare shi,
Ba fatima ba harda Joseph saida ya murmusa yau,
Da sauri yafito yana yarfar da hannun shi wai zafi dan ruwa zafi ya dan tsirgo mai a hannun shi,
Dariya aka karasa mai ba shiri ya jawo handcarchef din shi yana goge hannu da zufa,
Hmmm kawai,, Joseph yace daga karshe don ganin irin tabar da jibrin ke yi,
Har ya kai gap da fita waje ya waigo cikin irin tafiyar nan tashi yace, ,
Meet, me outside pls,
Jibrin har ya fara tafiya sai kuma yadan waigo ya kalli inda maryam take tsaye yace,
Kauna ta zan gan ki in ,nadawo, pls,
Aiki sosai suka sha ranan nan, ana gobe daurin aure suka shirya wani irin gagarumin friend's day, wanda abokai da yan,uwa za,su,halarci wanan bukin,
Maryam dai dama bawai ta na zuwa irin wanan bidi,ar bane don haka sam bata sa rai cewa zata,ba,
Amma sai ga anty tashigo da,wasu din kunan wasu indian materials masu kyau da daukan ido guda biyu,
Ita da safiya saidai kowace da kalar nata, dinki daine iri daya, sak,
Sunji dadin wanan kayan sosai sai dai da anty ta,bukaci zuwa gurin bukin duk suka,bata fuska
Jibrin ne shigo dai dai lokacin, yace yauwa Maryam wallahi ina ta sauri don inzo in samay ki,
Don ban da nobar wayan ki da na kiraki tun can in fada ma,ki,
Gefe dan je da ita, inda ba mai jin su, yace yauwa, Maryam dan Allah magana zan yi da ke a kan kawar ki,
Maryam tace wata ciki, yace haba kindai gane mana, wanan da kuke tare koda yaushe,
Wallahi tun ranan da na fara ganin ta naji ina mutuwar son ta, sosai,
Don Allah maryam ki taimaka min kada son ta, kawar ki ya kashe maki yaya maryam,
Maryam tace, a,a a, gaskiya ba ruwa na kasan halin yan matan ku kada,su samin kawa a gaba,
Ke maryam ban don sheri ni kin taba, gani na da wata, wai budurwa,
Kai ya jibrin wa,yan nan yan gayun yan matan naku da suke biyo ku har gida,
Wa,wai su Aisha ai ni wa yan,nan ko kallin arziki badu isheni, ba balle,
Wallah kasan koni kaina har gobe zargina sukeyi don wani kallo, naga suna min,
Kai maryam, idan sukai mata wanan kallon wallahi, sai naci uban su su dukka,
Da mamaki jin yadada ya ke kalamsi akan safiyar ta,
To ya jibrin Safiya fa ba, irin yan matan ku ba ne don ba wata yar gaye bace,
Kaga bazaku dace ba, don kun fi karfin ta gaskiya kabari tasamu,dai,dai ita,
Kai maryam don Allah kada wanan yadamay ki, ai ninr zan haskata sannu a hankali ko,
Wallahi auren ta nake son yi kuma bawai ina son abin yai wani dadewa bane,
Amma yanzu ki, fara hada mu, insamu in kafa kaina agurin ta,
Sanan , don Allah, ko anty kada kibari taji mubar abina tsakanin mu, har ya zama gaskiya,
Shiru maryam tayi tana dan nazarin maganar, shi ,ko gaskiya yake fafi ko kuma yaudara ne,
Can tace shike nan ya jibrin, tunda kace haka yanzu yakake son ayi?
Yauwa maryam kinga, indan zamu tafi gurin friends day,
Sai kiyi kokari ki hadamu a mota guda dag nan zan fara kafa kaina gareta,
Bayan rabuwan su sai maryam taji abin yai mata dadi, saidai tana zullumi kada yazo ya yaudare ta daga baya don su gogagun ne sai manyan yan mata,
Maryam wai may kike yi ne tundazu baki gyara guri,ba balle ki shirya ba,ga,kina da alamar zuwa ba fa,
Anty ina magana ne da yaya jibrin dama yanzu nake son in hada
Ta waiga inda Safiya take tana dan gyaran dakin da suka bata, da tarkace dazu da suka taru,
Tace ma safiya barin dawo musa labule dake safiya, akwai alheri tafe insha Allah,
Safiya ta kama kallon ta, kawai don bata san ko may maryam din zata fada mata ba,
Saida suka gama duk abinda sukeyi acan cikin dakin maryam suna shirin tafiya don har anty ta shirya yara ko,
Safiya ce ta kasa hakkuri ta ce maryam wai may ye kika ce zaki fada min dazu,
Hannunta maryam tadan riko kadan, ta dan kura mata ido na wani dan lokaci,
Sai kuma tai shiru, tace wallahi har na rasa ko ta ina zan fara zancen,
Ikon Allah inji safiya, wace itama maryam din take kallo,
Fada min don Allah kin sani, cikin duhu wallahi,
Maryam tadan nisa sai kuma tace wallahi safiya,duk ma na shiga rudani wallahi,
Dama wanan ya jibrin din ne yace in fada maki wai yana son ki kuma waida aure,,
Kai haba maryam don Allah ki daina wanan zance ina,ni ina wayan nan mutane
Aina fada mai haka safiya amma sai yace min shi wallahi da aure yake son ki,
Hmm maryam amma kin san cewa mu gidan mu talkawane lis,don bamu da komai,
Don haka ba,an sa kaina cikin wahala ba wallahi,
Inda dai talaka ne iri na ba zan ce maki no ba ,
Kai safiya wayasan gobe ban da Allah, balle har ki saurin yankewa kanki hukunci haka,
Ni shawaran da zan baki yanzu shine tun da har shi ya nuna yana sonki to
Sai ki gwada sa,arki mugani ko Allah zai sa shine mijin naki,
Iyaka dai ki kara kama kan ki sosai dashi kin san su sun saba da rayuwar, wayewa,
Maganganun maryam sun sa safiya tadan yi sanyi ,don gaskiya tafada mata,
San ai aure yin Allah ne bawai zabin mutum bane, sai in Allah dama ya nufa,
Maryam ta mike adaidai lokacin da tajawo kayan da zasu sa agaban tace,
Kada ki cuci kanki safiya don nima kinga lokacin haka, nayi amma sai nazo na fadawa Anty,
Don alokacin ina ganin cewa ga yan mata nan wayayyu a cikin FCE amma zai buge da cewa, yana sona sai kawai nadauka yaudarata zaiyi kawai,
Ashe abin ba haka bane,,hadine daga Allah,
Marya tamike tsaye tana kokarin walwale kayan don su diba dinkin tace,
Tace don Allah safiya ki daure yau ku dan gana dashi, don muji ta bakin shi
Kinfa yace min ma wai shi zai tafi dake gurin hall din ajima,
Kinga ko inda bada gaske yakeyi ba da aibazai yi kokarin nuwa duniya ke ba,
Dan siririn ajiyar zuciya, safiya ta sake tace maryam bawai ban son hakan ya kasance bane,
Ina dai gudun abinda zai jawo min fitina ne kin san halin da mahaifiyata take ciki kada in dauko mata magana,
Amma ba komai tunda naga kin yarda dashi don nasan cewa bazaki kaini mugun wuri ba,
Wayar maryam ne yai kara,a,lokacini ko bata dauka ba tasan cewa A,A din tane akan layin,
Cikin kashe murya ta dauki wayan nan yake sheda mata cewa tajirashi zai zo ya kai su gurin bukin,
Duk da dai bata gaiyyace shi ba tun farko,
Maryam tadan kara kwantar da muryan ta tace malam nasan cewa baka wani hurda da sune shi yasa ban fada ma ba,
Yai yar dariya, yace wallahi jibrin ne ya fadamin dazu da muka hadu gidan mai dashi,
So ki bani nan da minti ashirin zan iso, insha Allah,
Kayan da su maryam suka sa yai bala,in fitar dasu sosai,
Saboda bawai samun irin materials din akeyi ba akon,ina don haka sai yazama wani abin kallo, ga jama,a,
Tsab suka fito gaba dayan su a lokacin, Safiya sai faman koda shigar maryam takeyi ita ma maryam din hakane,
Jibrin yazo har ciki da kan shi yana fadawa maryam cewa tafadawa safiya yana waje yana jiran ta,
A,Daidai lokacin A,A ya iso don tafiya dasu kamar yadda yace zaizo yakai su,
A,lokacin wani kanin mijin anty Dije ya zo don yakai su
Sai ya tar da za a kaisu amma Anty dije sai tace ya tsaya ya kai ta ita,
A hankali suka fito saida ga motoci nan gurin zakace ko a gidan ne ake bukin,
Har bakin motar jibrin Maryam ta raka sadiya tadawo,
Ta bude motar A,A, tashiga
A,A din yadan waiga yakalli inda maryam take yace,
Ina ita safiya din, kuma,?
Tana can a motar jibrin tare zasu,
Tafada a takaice,
Wani irin kallo A,A din yai ma ma maryam.
Yace kina da hankali kuwa, yarinya tazo maki buki sai ki bari tabi wani kato,
Maganar yaba Maryam mamaki, tace jibrin fa nace ma malam,
Yai yar tsuki Mtsss, maryam ban zaci har zaki amince da safiya ta bi wa yan nan da kowa yasan yan duniyar yarane, ne ba,
Yaran da duk gari ankasa gane sanar su har zuwa yanzu
Tunda yafara magana maryam kallon shi kawai, takeyi
Tace haba malam nafada ma cewa ba abin,in da zai samu safiyan,
Ya dan daga mata hannu yanu nna mata alamar ya isa hakanan,
Har suka kai gurin bai kara mata magana ba,
Gurin yacika fam da jama,a lokacin har, kujeru sundan kare daga ciki,
Wasu ne sukazo suka yiwa su maryam kwantace da wasu kujeru a can gaba,
A kusa dasu taga harda su anty dije suna nan gab dasu,
Basu wani dade ba akafara program din inda aka r da Amarya da ango,
Kujerun wasu yan mata dake dan nesa dasu kadan,
Taga ana dan nuno su a hankali bada wani jimawa ba taga A,A ya mike zuwa wajen yan matan,,,,

ZEEEE. MAKAWA,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Jinjina gare tare da fatan alheri ko yaushe Anty Nafisat, Aliyu Harzami, UmmuFadleeh safeenat Abuja, Mamam farida,Maman Walid, Maijidda Harzami, Mariya SB, Jamila Sifiyanu,Anty na hafsat Yusuf, da members din Zeee makawa novel, da members na takari novel Ina maku fatan alheri dacewa da Rahaman ubangijin mu, da kuma gamawa da duniya lafiya,
JUMM,AT, MUBBARAK👏👏👏👏👏👏👏👏


Zaune take daga inda A,A yabar ta ko zataga dawo wan shi sai kawai taga tun yana yar kus,kus,da wanan matar da taga yaje gurin ta har sun kwasa sun fita,
Shigowan Joseph tare da,Aisha yasa ta dan daina kallon hanyar dataga A,A din ya bi, yafita,
Joseph da Aisha tare da Amina sun shigo cikin wani irin shiga ta alfarma,
Don dai ko makiyin su dole ya yaba ma shifagar su,
Aisha ba kunya tana make da Joseph gam saboda ta bushe fitilar ta bata kunya kowa agari,
Yan wasan gidan mai Jauje na kwantagora sun fito sun yi wasa,
Sai wani mawaki makwabcin garin kwantara daga KB state garin Yauri Sani Aiyu dan Dawo shima yafito yai nashi wasan
Nan masoyan Joseph da bakin su suka dinga barin kudi ga mawaka,
Daga karshe aka dan yi traditional show na yaren da ke cikin kwantagora,
Toran kawa, kambari, Dukkawa, Dakarkari, pure hausawa, da sauran su,
Wayan Maryam wace takai iya wuya, yai yar tsuwa, alamar sako ya shigo mata,
Budewa tayi sako tagani kamar hàka Ki, yi hakkuri pls Maryam, bazan samu mayar, da ke, gida ba ,
Ku komatare da Anty pls,
Abinda aka rubuta ke nan a sakon , atake maryam ta fahinci, sakon daga, A,A masugane,
Wani iri maryam taji a ran ta, maganar da ya fado mata arai shine, muryan mahaifiyar A,A alokacin da suka je gaida ita,
Daga haka tamike tsaye daga inda take zaune,
Tafiya takama yi cikin tashin hankali take dan takawa,
Sai muryan Safiya taji a gaban ta tana cewa, banga motar A,A ba a waje maryam,
Dan ajiyar zuciya tayi don ta riga tayi nisa gurin tunane ,
Tafe suke a motar jibrin sai hiran wasan nin da akayi akeyi amma ita sam hankalin ta bai tare da ita,
Abinda zuciyar ta ke tambayar ta shine wacece wanan da A A yaje gurin ta,
Har tasa shi fita hall din taron yakuma iya wucewa ya bar maryam din, a gurin,,,
Har suka isa gida ,hankali maryam atashe yake

22 / 84