Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
I just want be,
Sai kawai ya bude littafin dake agabanshi yaci gaba da karatun shi,
Kara tsiyaya ruwan mayen, cikin kofi yayi yana yi yana mai kallon Yusuf yana dariya yana girgiza kai,
Yusuf yagane nufin shi sarai watau bai san abinda yake yi ba ke nan,
Anabi din dake ire agaban shi ya tsinka ya jefa abakin shi, a hankali,
Sonny dake kallon shi yana ta murmushi ganin yaci diyan Anabi din yace ma Yusuf so is true some food's or drinks are forbidden to Muslim's people,
Sai yar dariya dayayi yacewa Yusuf kagan ni nan shiyasa banyarda da wani addini ba can,,
Nafi son in zauna ahaka batare da wani takurawa ba yafi min, yakafa kofin mayen shi a baki yashiga kwankwada,
Ckin wani sallo ya kira sunan Joseph din yana mai mai kallon serious alokacin,
Stop calling me with dat name pls
Iam YUSUF,
Still Sonny bai yi fushi ba kamar yadda Yusuf ke mai magana a tsatsaye,
Yace woow so a Nice name, Yusuf I love the name,
Do u remember we have a course mate, from, Egypt with dis name,
Sun dauki wani lokaci a gurin Yusuf na ba abokin nashi kuma aminin shi labarin irin halin rayuwar da yake ciki,
Dakuma dalilin shigar shi cikin musulinci,
So u have faith in dat,
Yusuf din yana,mai kada kai yace rely,
Agogon hannun shi da yadan daga yadubu shi ya nuna mai ko karfe nawa,
Ba bata lokaci ya mike zuwa dauro alwala, don ya gabatar da sallah magrib,
Duk a binda yakeyi Sonny yana tsaye a jikin bango ya harde kafa yana kallon Yusuf din, cikin mamaki,
Azuciyar shi yana tunanen har yaushe ya fara islama da zai iya wanan abin dayaga sunayi time to time,
Daidai lokacin da Yusuf yai sallama yadaga hannaye shi sama yana addu,a zai shafa yaji a na taben hannaye a bayan shi,
Cikin mamaki ya juya Sonny ne tsaye, yana mai dariya ya na tafawa,
Yace so Are so serious with dis religion,?
Baima magana yadauke carpet din shi da yake sallah akai, yashige da abinshi, ciki don gudun kada wani najasa ya haukai,
Kwana biyu dayin haka suna zaune suna cin abinci ,rana kira yashigo a wayar Sonny,
Saida yadauki tissue, ya goge bakin shi da kyau sannan yakai hannu ya dauki wayar, dake kara sabon kira,
Sabon noba yagani wanda bai san may shi ba , da mamaki yadauka yana kallo a hankali,
Bayan gaisuwa shiru yayi yana sauraren mai magana daga dayan bangaren cikin natsuwa,
Idon shi suka sauka akan Yusuf wanda shi ma alokacin ya gama cin abinci yana goge bakin shi,
Abinda yaba mai maganar dashi ansa yasa Yusuf saurin dago kai ya kalli Sonny din,
Sonny ke cewa shi canza addinin shi ba matsalar shi bace iyakar haduwar su dama ta friendship ne, yazama masu amin taka
Don haka shi bazai iya sa Yusuf ba yadaina abin da yake so kamar yadda shima Yusuf bai isa ya hana shi irin rayuwar da yake so wa kan shi ba
Wanan is a personal matter not a business or a deals,
Daga haka ya dangware wayar ya na tsaki batare da ya kalli gurin da Yusuf yake ba yatagi fuuu, yabar gurin,
Mamaki kan Yusuf yayi matukar yin shi da wanan bita da kullin da ake mashi,
Bayan fitan Sonny a dining area din Yusuf yakai dan wani lokaci zaune yana tuna
Mikewa ya alokacin yanadan tako acikin dakin yaje ya dawo,
Yana tunanen wanan hali irin na mutanen su da basu da yarda da kaddara,
Sai alokacin yafara tantance tsakanin kafirci da imani,a musulunci
Yanzu yagane cewa,ko dan karamin yaro musulmi yafi katon kafiri imani,
Sannan ga sauki ga musulunci duk dadewan ka wanda bai sallah koda kakai shekara dari, ne
Duk ranan daka ce ka karbi kalmat shahadda duk zunuban ka sun wanke kadawo daidai da musulimi dan shekara dari,
Hannayen shi rungumay abaya yatsaya cak don tuna wani abu da,yayi a zuciyar shi,,,,,,
A gajiye yau maryam tadawo daga makaran ta duk da tasan cewa akwai aiki agaban ta na girkin dare,
Amma bai hata wurgat da jakarta gefen kujera ba tafa saman gadon Anty Dije
Tana mai cewa wash Allah na Anty tun safe banci komai ba wallahi
Ga abinci can ki dauko ki ci mana,
Wayyo ni Allah anty abincin baya wuce wa saboda dadewar danayi banci komai ba,
Saidai dan abu maidan ruwa ruwa pls,?
Takarashe fadi tana mai kashe ma Anty ido guda alamar zo laya,
Tana wani lankwashe kai kamar zatai kuka,
Anty Dije tace, cikin murmushi,, to,gashi maryam banda wani abu mai ruwa bayan tea,
Sai ko drinks din da Yusuf yasiya muna kafin yatafi,
Nako san baki sha, abinda yafito daga gare shi, ke
Tunda Anty ta fara zancen ta maryam wace ke kwance,wai tana exercise din bayan ta,,
Tamike zubar dan jin inda maganar Anty Dije ya dosa,
Anty Dije tana yin shiru,,maryam ta dan langabe kai ce, hai Anty wanan dane fa yana kafiri,
Cikin kwarewa da iya iya shagwaba ta furta zancen kamar wace zatai kukan gaske,
Dallah ja cen kunya bai isheki ba wallahi Maryam, inbashiba wai yau kece da cewa hakan,
Maryam kan mikewa tayi alokacin ayadda takejin son shan drink's komai zata iya,daurewa, akai,,,,
ZEEE. MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,
Yusuf yadan samu natsuwa sosai a zaman shi tare da Sonny saboda shi Sonny ba mutum bane mai son shiga har kan wani,
Wanan damar da yusuf yasamu yasa,shi samun sakin jikin shi har ya manta daduk wani tashin hankali dayaje ciki,
Ganin yau jumma,a ce juma,a biyu kenan bai samu yin sallah jam,i ba
Don haka yasa a ranshi cewa yau zai shiga gari yadan zagaya don yadiba ko zai samu wani guri da musulman garin ke yin sallah jumma, din,
Tun ranan Thursday ya shirya cikin shigar wasu kanan kaya kamar yadda yake yi kulun,
A daida, fita ta wajen gidan, suka hade da Sonny wanda ke shirin shigowa,
Kallon mamaki yaiwa Yusuf din yana mai tambayar shi ko ina zai tafi haka,
Ba boyo ya sheda mai cewa ga inda zashi searching din gurin bautar su na ranan Friday ne,
Haba joe in ji Sonny yakamata ka fada min sai mu fita tare in taya ka dibawa, ai hakan zaifi katafi kai kadai,
Zuciyar yusuf tayi fes jin abinda Sonny yace yasan kuma har cikin ranshi yafada,
Basu sha wani dogon wahala ba sosai don wani abokin hurda Sonny musulimi suka kira shi yai madu kwatancen gurin suka tafi,
A zahiri idan kaga gurin zaka dauka wani, ma,aikatace sai dai in kashi ga,
Sundawo gida Yusuf na cike da farin ciki har bai iya boyewa,
Sonny ya fahinci haka sosai inda ya yake tunanen irin yadda wanan addinin yai tasiri aran Yusuf cikin lokaci guda,
Saboda yasan Yusuf din sosai lokacin da dukkan su suke bearing din Christianity
Baibada wani munhin manci akai ba kamar wanan yadda ya ga time din sallah su five times a day baya wuce joe din,
Shin wai su muslim din nan wasu irin mutane ne masu karfin zuciya haka da taurin rai, akan abinda suka yarda dashi,
Basu dawo gida ba saida suka biya gurare da dama aranan, inda Yusuf yai yan sayayan yan abubuwan bukatun shi indan zai dawo Nigeria,
Washe gari tunda safe,Yusuf ke ta shirin shi na zuwa massalaci batare da bata lokaci ba yafito cikin shiga mai daukar hankali, sai kamshi ke tashi ga carpet din sallah shi da yar karamar tasbaha a hannun shi yarika,
Da mamaki Sonny ke kallon shi don shi har ya manta zancen zuwa mosque yau, da Yusuf zai yi,
Amma sai yaga ashe cewa shi Yusuf din bai manta ba abin na zuciyar shi,
Tausayi sosai abokin nashi yabashi sanin cewa yayi nisa sosai ga wanan akidar,
Al,amarin sai ya burge Sonny kawai, don ya yarda da mutane ke cewa wai islam is a teitorim religion,
Sai ya fahince cewa rayuwa ce ta saukake, aciki babu takurawa juna ko sa ido ga harkan wani,
Don haka shi da,kan shi ya bukaci kai Yusuf din, mosque, aranan,
Motar shi maikyau mafi tsada suka shiga inda tun a kusan haraban gurin zakaga irin yadda maza da mata da yaran su ke ta dandazon zuwa gurin bautar nasu,
Kowa kagani cikin shiga ce ta alfarma ko ina lif a rufe daga mazan har matan su,
Gwanin ban sha,awa gaduk wanda yagan su, kowa kula dan uwa tankar yan ciki daya,
Sai zuwa wani lokaci mai tsawo suka dawo daga, massalacin daka kalli Yusuf kasan cewa yana cikin annuri, aranan,
Saboda yadda yake ji tankar andauke mashi wani nauyi ne arayuwar shi,
Sai yanzu yake tabbatar wakanshi da cewa ba karamin sa,a yayi ba nafitowa daga cikin kafirci cikin duhun kai,
Indan har su wa yanda sukayi zamani da Annabi Isah yan uwanshi da yan yaren shi da akasa su yarda dashi da sakon shi,
Suka kan su sun tabbatar dacewa akwai wani wanda zaizo bayan ahi Isah din kamar yadda yake da magabata agaban shi (watau, annabawan da sukazo kafin shi)
To su yanzu da suke bin akidar Christianity don wa sukeyi tunda an fada masu a littafin su cewa zai zo,
Hannun shi yadaga yashafi sajen shi dake kwance a fuskan shi lif,
Yana mai hamdalah acikin zuciyar ashe afili har da hannuwar shi yadaga sama yashafa,
Sonny wanda ke kallon shi mamaki yakara kamashi sosai sai ti yake yi yana dan satan kallon Yusuf din,
Wanda ahalin yanzu yaga yadda yaimai wani irin kwarjini
Washegari da safe, bayan ya idar da sallah yazauna yayi irin addu,oin da yasaba yi,
Gurin yin exercise yadan fita har zuwa lokacin da gari ya washe sosai,
Sanan ya,shiga wanka yafito ya hau tebur don yin break fast,
Sonny yafito cikin shigar zuwa office yadan zauna tare, Yusuf suka karya nadan wani lokaci,
Yusuf din ne ke fadawa Sonny yana son ya koma gida don ci gaba da harkokin shi don gudun kada su tsaya mai duk da yasan ba abinda zai faru insha Allah,
Sonny mamaki ne yakama shi sosai yace yadawo ya zauna kusa da Yusuf din yana mai ce mai,
May zai sa bazakai zaman ka anan ba, kawai ka share kowa,
Don har na fara maka planing din din abin yi don ka kauda zaman banza,
Amma ni naga kawai gara kabar zancen komawar ka yanxu har zuwa wani lokaci zai fi,
Yadan dafashi yana mai cewa ya daure yaba su, dan time tukun kafin ya koma,
Wanan zance na Sonny abin dibawa ne sosai don hakan zai sa su dan fita zancen shi,
Amma kuma baya son yabar harkokin shi na can gida, sam
Don haka yakira KB da Jibrin tare da,wani babban amin nin shi amanar kulawa da harkokin shi in secret,
Bayan wata guda daga can ya wuce saudiya ya gabatar da aikin umurah,
Yaji dafin wanan tafiyar tashi so sai don yakara yin hamdallah da rayuwar shi,
Sosai suke business kamar a gida Nigeria suke, don Sonny mutum ne wanda bai ma natare da shi keta sam,
Ba karamin riba yasamu ba daga wanan zaman da yayi acan
Gashi ya murje yayi kyau yayi dan jikin jin dadi ba mai muni ba saboda yawan exercises,
Alhamdullah Anty Dije ta sauka lafiya,tasamu Da namiji wanda bayan sati akasawa yaro sunan Abubakar Sadiq,
Wanan sunan yaiwa maryam dadi sosai kasancewa suna A,A dinta ke nan,
Sosai akasha buki sai kace sabon haihuwa ne kamar na farko,
Inda Jibrin da KB suma sun zo har gida sun,wa Anty Dije barka
Shi kanshi maigidan wanan haihuwar ba karamin dadin shi yaji ba don ga haihuwa ga samun girma daya yi agurin aikin su,
Kayan goyo sosai yazo wa maijego da jariri da inda har dangin shi suka dan fara tsegumi akai,
Wai ta tare guri taki bari wata ta shigo itama tadan lakaci arziki,
Sai ita da yan uwanta ke cin abin su, ita dai bata biye masu ba sai harko kinta take yi kawai,
Anci ansha sosai agurin kamar yadda yakamata a duk wani taro,
Sai washegarin suna bayan an watse ne baba yazo da kamshi don ganin jariri
Maryam ce ta dauko mashi shi cikin showel, fari kal,
Bayan an gagaisa ne baba yaiwa yaron addu,a tare da yiwa uwa fatan gama shan ruwan zafi lafiya,
Sai dan shiru yabiyo baya, alokacin ne yadan dago kanshi cikin fuskan damuwa yana cewa anty wace ke tsugune gefe guda saman wani dan karamin kujerar mata,
Ya zancen maryam ne wai yaji shiru, dafarko yaji zancen rigirigi yanzu kuma yaji sakwot,
Dije yakamata ku mai da hankali kinsan dai in badon a gurin ku take ba ba,zan barta har takai haka ba ba wani matsayi
Don ni bokon bandauke shi wani abu mai muhunmanci ba ga diya mace,
Har wasu yan uwa na acan gida suna ganin kamar cewa nine ke ra,ayin tayi karatun bokom
Kinsan yadda nike da yan uwa na duk da bawai wani arziki ke gare ni ba amma ganin ina acikin gari har yanzu akwai hassada a tsakani na dasu,
Anty Dije ta dan gyara zaman ta datayi mai kama da tsugun ni ta fuskanci baba da kyau,
Tace baba gaskiya muma bamu so akai war haka batare da wani matsaya ba akai,
Da farko ya nuna muna agaskiya baizo da wasa ba,
Katseta baba yayi da cewa
To aimu,bamuga alamar hakan ba, saurayi yadade tare da budurwa har tsawon wani lokaci amma babu wani magana mai karfi aciki,
Gaskiya Dije idan har bazai wani motsa ba yakamata kufita zancen shi kada kice zaki biye wason ran yariyar nan,
Kodai ba yanzu za ai auren ba to ya motsa ma na asancewa,yana ciki,
Ya turo da manyan shi su shiga cikin harkan hakan zaisa kiwa yasan matsayin sa,
Daga anty har Maryam kansu na duke akasa don jin maganar da baba keyi acikin bacin rai,
Daga haka yamike yana cewa kunji maganata ke nan nafada maku nagaji da surutun mutane haka,har aciin iyayen ku ke Dije ina shan surutu,
Itama Anty Dije mikewa tayi alokacin tana cewa baba yayi hakkuri insha Alkah komai zai zo karshe badadewa ba,
Har baba ya bargidan kan maryam yana kasa aduke, cikin ladabi,
Daren ranan Maryam bata samu yin wani barcin kirki ba kamar yadda tasaba gatada karatun test nan da kwana biyu,
Saboda maganar tazo mata abazata don bata tsanmaci baba zai yi wanan zancen ba,
Washegari haka ta tashi bawani kuzari atare da ita saida Anty taimata magana sannan tadan sake ranta,
A makaranta duk yadda taso taboye wa safiya abin bai yiyu ba,
Don haka safiya sai taji kawai itama bataji dadin ganin aminiyar cikin damu ko yaushe kan zance guda
Gaskiya yau zata fada mata gaskiya cewa ta rabu dashi kawai takama masu zowa son ta da gaskiya,.
Don ko a kwanaki wani abokin Jibrin yai masa zancan ta,
Zaune suke a cafeteria su na son dan shan, drinks,
Maryam wace ta dade da lulawa duniyar tunane, ko bata ko san ida suke ba a lokacin,
Safiya tadan mata kyatci da hannu a fuska tadanzabura kamar wace taji tsoro,
Dan ajiyar zuciya ta sake tare da kallon safiya din tana kokarin kako murmushi,
Safiya tadan kai mata harara cikin murde fuskanta,
Wai Maryam mayke damun ki hakane pls,?
Tadan gyara zaman ta,tace bari kawai safiya wallahi ina cikin damuwa,
Tun jiya da baba yazo muna barka haihuwa,,
Dakata Maryam, wallahi ki,yiwa kan,ki fada ki danai irin wanan dogon tunanen kadafa ki jawa kanki matsala ina fada maki kullun,
Akan namijin daba ki tabbatar ko zaku zauna tare zaki halaka kanki,
Tadan kara nisawa tace ,baba yazo jiya yaiwa anty Dije tas akaina,
Maganar baba tajiya yasa nakara sanin cewa, A A ba sona da aure yakeyi ba kawai dai,yana son amfani dani, ne ya nunawa duniya,
Don haka maryam da kullun aitawa yar uwata fada akaina,
Gara kawai in rabuda shi in huta Allah yabani wani yafi min safiya,
Subbahanallahi maryam kada kuyi saurin fadar haka mana,
Nan da nan idonta yakawo hawaye, kamar zatai kuka,
Wallahi safiya hakan yafi min don bazan yarda kullun mahaifina yaita bata ranshi akaina ba,,
Dan shiru sukayi a tsakanin su, nadan wani lokaci
Safiya tace kenan kina nufn duk son dakikewa A,A ya tashi abanza kenan,?
Saida ta share kwalar da ya silalo mata tukun sanan tace,
Gaskiya kan safiya rabuwa dashi zaifi min
Yanzu ke maryam bazaki canza shawara,ba akai,
Ki tunkare shi kiji may yake ciki akai, ?
Maryam ta katse Safiya da cewa ,