Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
adinga kyamar ka kamar wani mugun abu,
Karar wayar shi ce ta katse mai tunane Grandma ce ke magana dashi,
Bayan sun gai sun danyi hira kadan take tambayar shi ko yaushe zai dawo saboda wai, tana son suje gida gurin festival,
A fili ce mata yayi zai dawo zuwa weekend insha Allah sai su fara plan din tafiya,
Amna suna gama waya sai yai yar tsuki don in akwai abin da yai hating tun farko shine irin wanan bukin festival din,
Inda mata da maza zasu hadu adinga yin abubuwa tankar tsafi, a gaban wani halitta,
A gurin ake hada wasu aurataiyan inda nan samari da dama suke ganin yan matan da suke so, sai a kulla alakar aure,
Nocking din kofar shigowa yaji ana yi a lokacin abinda ya sa,shi mantawa da komai ke nan
Ya mike don yadiba yaga ko waye, ?
Aisha ce tare da Amina ,ko,wacen su tasha kwalliya cikin material dinkin buje da riga sun dane masu jiki,
Ga gashin kari sun kara sai kace, wasu diyan kafiran da suke cewa,
Hannun su duk an painte shi da ja kumba, ga wani eyelashes sun zuba,
Haka kawai sai yaji wani haushin ganin su a hakan,
Bakaramin godewa Allah yake yi duk ya tuna cewa wani abu bai taba shiga tsakanin shi da Aishan ba,
Kirjin su duk yawani bultso tagaban rigar su kusan duk rabin nonon su a fili yake
Sai dan gyalen da suka yarfa a wuyar su kamar sarka,
Takalmin su ba,a maganar tsinin shi saboda tsawon shi,
Kokarin shigowa da takalma suke yi amma sai ya dakatar da su da cewa,
Haba sai kace wa yanda basu san darajan gidan musulmi ba cewa sallah zata iya riskan ka,ako ina acikin gidan ka,
Ya cew Amina ki daina biyewa wanan pls yana mai nuna Aisha da hannu
Yace ita ta riga ta kuna bata gudun yin kauri sam,
Darita tai mashi a lokacin da take kokarin cire takalman ta, daga kofar,
Kokarin rungumashi takeyi
Amma sai yadan ture ta baya kadan yana mai ce mata baki da kunya fa ke,
Yanzu fa nagane cewa baka son inadan taba ka inji dumin jikin ka
Tafadi tana kokarin zama saman kujera dake fuskantar inda taga yana son zama,
Yaushe rabon da indan yi hugging din ka sai kawai jayewa,?
Cikin mamakin irin bushe fitilar ta yake kallon ta,
Sai dai bai iya ce mata komai ba yadan yi murmushi kawai, kamar yadda ya saba yi,
Mun,zo jiya baka nan na san cewa kana can gidan wanan munafukar sister karyan ka,
Ciki dakewar murya ce mata look bana son wanan halin sam wallahi may tai maki,
Ita warinki ce da zaki dinga yi mata haka,
Jifa maganar ta kawai nayi yanzu amma kana kokarin cimin mutunci akan ta,
Ai nasan duk plan din ta akan ka wallahi so take ta mallake ka ta aura maka wanan kaunar nata mai kama da bafullatanar Niger,
Kai, inji Amina wace maganar kawar nata yasa ta jin kunya a takaice,
Duk kallon inda Aminan take sukayi cikin wani irin magana take cewa aiko yarinyar nan kaunar Dijen Illita costume tana da kyau,
Ba ita bace, A,A ke nema saidai uwar shi ta hana shi, tace zata hada shi da yar uwar shi,
Yusuf wanda ya nuna bai wani damu da hiran da sukeyi ba don wayar shi ya hau latsa
Amma sai maganar cewa ba za,a bar A,A ya auri Maryam ya tsaya mai a rai,
Ba zai aure ta ba to may yake zuwa yi gurin ta ko yaushe
Gaskiya wanan maganar abin bincike ne sosai,
Kwance Aisha take sama kujerar tawani yi dai,daya da kafar ta,
Aisha ya ce cikin murya da tankar a tashi ba yau don yadda ya furta ta,
Look bana son irin wanan dabi,u sam wallahi hakan baida wani amfani a gare ki a matsayin ki na diya mace,
Bana son kina zuwa wanan gidan idan nazo kina min irn wanan rashin kamun kai, pls ?
Da yar mamaki ta mike zaune da niyar yi mai magana amma sai yadakatar da ita da hannu
Alamar bai son jin komai daga gareta again don tun da tazo batwi wani abin alheti ba,
Ganin yadda fuskan shi ta nuna ne yasa Amina cewa Aisha,
Ke ko gaskiya Aisha haka fa baida kyau wallahi,
Ita sister tawa da kike cewa ta karya tafi min ke sau dubu wallahi
Domin zama da ita alheri ne a gare ni sosai ba kadan ba
Ki fada min zama dake abin amfanin da na samu akai,
Tamike zaune da kyau dan yau jin maganar shi takwyi ba taushi,
Tai wani far da ido tace mai laifin waye idan baka samu karuwa daga gare ni ba,
Yawani kada kai ya ce, Allah yai min tsari da irin taimakon ki,
Zance wai za,a hafani fa kaunar anty kuma ki sani cewa zancen aure na ya kawoni wanan garin ganzu haka,
Daga haka bai kara magana ba yasa kai ya bar falon cike da kunar rai,
Kallon mamaki suke mashi don basu taba tunanen cewa zai iya rufe ido haka ba,
Maigadin shi tare da body guard din shi suka shi go falon suna ce masu zamu kulle gida kufita pls,
Ikon Allah inji Amina tace yanzu dan Allah har ma korar mu akeyi haka, ?
Yau kimanin wata biyu ke nan inda zancen Yusuf da Sadiya sai kara girma yakeyi,
Bayan har Aisha ta sa an binciko mata ko wace yarinya ce Yusuf ke shirin aure,
Tayi mamaki kwarai don jin abinda ta tuhuma gurin anty ba gaskiya bace,
Wanan shigowar don shirin azumi dake tafe yayi wa garin ,
Amma sai kuma ya samu cewa mahaifin shi baida lafiya
A gurin makwacin su yake ji wanda kusan ko yaushe yana fada mai abinda gidan suke aciki,
Gidan nasu ya tafi kai tsaye bayan ya iso inda ya samu duk mahaifin nashi ya,ramay tankar wanda ya
Duk yadda yaso yaiwa dan nashi cin fuska sai ya kasa saboda kwar jin da yai mai a idon shi so,sai,
Yusuf din ya murje ya zama wani matashi hamshaki, dagani basai an fada ma ba,
Da kanshi ya kai shi gurin likita don yadiba shi aga ko may ke damun shi,
Tsumu, tsumu ya na rike da hannun Yusuf din har gurin likita
Inda a karshe aka tabbatar masu cewa yana dauke hawan ji, ne,,
Sosai Yusuf yai ta mai magana cewa,ya daina wanan yawan tunanen, da yake yi kada yai mai illa,
Sai da ya tabbatar da cewa yasha duk wani da likita ya bashi kuma yai ma wa yan da ke a tare dashi magana akan su kula dashi, so,sai
Sai bayan tafiyar shi ne yan church din sukazo cikin fada,suna cewa wai may ya kawo shi, gurin mahaifin shi,
A gaskiya su sam ba, su yarda da wanan ba, tunda yace ba ya tare da su,
Don haka wai sai ya daina zuwa gidan nasu,
Maryam wace ke zaune tana, gyaran kumbar kafar ta,
Wayar ta na gefe guda ta sa Kira,a tana dan bi a hankali,
Yusuf din ne yashigo da sallamar shi inda duk ita da yarta suka ansa mai sallamr shi, a lokaci guda,
Wani yaro yana biye da shi a bayan shi dauke da wani leda da ke dauke da ga hannun yaron,
Maryam wace tunda ta daga kan,ta da ta gaishe shi bata kara kallon inda yake ba ,
Muryan Anty da take daga wasu shaddadoji masu tsada da yakawo wa anty,
Don ta tayashi dibawa saboda ya kai a dinkawa Sadiyar shi,
A yadda suke zance da anty sai yana bawa maryam mamaki saboda irin yadda take gani daya fita waje yadda mutane ke wani girmama shi,
Anty Dije ta shiga wani wasa sadiyar tana wani yaba ta ga Yusuf
Tana kokarin kafa gwaunatin ta gare shi shiko sai wani lumshe idon shi yakeyi,
Don dai a gaskiya da farko ba,wai wani son ta yakeyi ba,
Don dai kawai tana yar uwar Jibrin ce yasa ya yardda da zance,
Sai gashi yanzu sannu a hankali yafara jinta ajikin shi,
Daga inda maryam take zaune tai wani dan guntun tsoki,
Yusuf tunda Allah yasa yanzu kun yi nisa ya,kamata ace yanzu zancen ya fi ni girma, saboda iyayye su shiga har kan duk da dai sun san da zancen,
Yusuf dan rau saya kai yana maijin dadin irin kulawar da Anty Dije ke yawan bashi,
Anty Dije tace hankalin ita Sadiyar ma zaifi kwanciya nake gani, da hakan,
Yusuf zai yi magana ke nan sai jin muryan maryam sukayi gabadayan su tana cewa,
Wai Anty ita wanan Sadiyar daki ta zancen ta ako yaushe,
May kika gani a gare tane wai, mace wace ta zubar wa kanta da aji, tace wai tana son namiji,
Har a dinga wani zuzuta zancenta sai kace wata can ,
Gata wata garmakyakiya da ita fuska ba fara,a , takare zancen dayin yar tsuki a karo na biyu,
Daga haka ta duka taci gaba da yankar farcen da takeyi,
Kamar ba ita bace tai wanan maganar da ta barsu suna mata kallin mamaki,
Murmushi Yusuf ya wanda har ya ba da yar sauti,
Hakan yasa maryam dago kai takalle shi don jin irin abinda yayi,
Anty Dije tace wanan kuma wani zance ne kawai na daban maryam a mma ai ko ba tada makusa sadiyar,
Kallo mai kamar harara tawatso gefen da suke kamar za tai magana sai kuma ta dukar da kanta taci gaba da abinda takeyi,
Saida ya gyara zaman shi da kyau yadan kada kafar shi sanan ya kalli inda take yace ma,
Anty ramawa Maryam tayi don na fada mata gaskiya akan samarin ta ranan,
Batai magana ba sai shiru da tai masu sai kace bada ita suke ba,
Anty dije ce tace hummmm maryam halinki sai ke wallahi,
Ba,a sukar aure fa inda ba zaka gyara ba to kayi shiru akai
Sai a,lokacin tai magana tana mai mikewa tana kakabar zanin ta da wani kyale,
Tace ai ni gaskiya na fada anty don sam ba suyi matching ba da ita,
Anty Dije wace taji haushin zancen kaunar nata tace,
Aisai ki samo mashi wace sukai machin dashi ina ga zaifi wanan jayayar taki,
Daki tashige abinta tana turo baki gaba don dai ita tafadi ba kuma yadda za,aiyi da ita,
Duk da dare ne ya,kamata a ce yai barci by now
Amma sam barci yaki zuwa mai sai ma maganar maryam dake kokarin yi mai yawo a kwakwalwan shi,
Maganar maryam din gaskiya ne duk da ya fahinci acikin gatse tai mashi su,
Amma shi kanshi yasan cewa sam basu dace ba tun farko ,
Saboda Jibrin kawai yadaure har haka tafaru a tsakanin su,
Tunda Jibrin din ya nuna yana son wanan abin shikuma bai iya,watsa mai kasa a ido,,
Juyawa yayi dayan ban garen yana mai kara rintse idanun shi stil maganar ce ke mai yawo akai,har yanzu,,,,,,,,,
ππππππππ
Dan Allah kuyi hakkuri masu cewa wai basu gane abinda nake rubutawa, wai bani rubutu da kyau ku yi min afuwan pls banda enough time ne da zantayin editing
ZEEE. MAKAWA
[3/16, 08:01] Anty Lantana: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
5β£2β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
Assalamu A,laikum yan uwa musulmai, fatan alheri agare ku ko dayau she,
Wanan daren Alhamis din son in amfani dashi gurin mika gaisuwata tare da fatan alheri, ga duk masoya wanan novel na furen juji da,nakeyi,
Kaunar novel din ku na nuna kaunar ku zuwa ga addinin mu ta musulunci maidaraja,
Ubangiji Allah ya kara haskaka maku rayuwan ku, Allah yakara rufa asiri nagade,,,,,,
Zaune yake saman table din dake cikin office din shi yana duban wasu takardu,
Sai laptop din shi dake a saman table din gefe guda ajiye,
Yana rike da biru sai ticking din wasu daga cikin abinda yake diba a cikin takardun yake yi,
Kada kanshi cikin mamaki yakeyi don sam bai taba tsamanin cewa abin ya kai haka ba,
Biron dake hannun shi da pepper ya aje saman table din,
Komawa yayi da sauri saman kujerar da yake zaune da farko,cikin sauri ya fara dan,na computer,
Hannun shi guda da sauri yake sarrafa computer din shi don son ya tabbatar da abin da ya ke gani, a rubuce,
Bakomai bane face zunturu tun ribar kudi da company shi ta samu,
Sau uku yana furta Subbahanallah Wallahamdullah Wa,lah,illaha,illah, Allahu Akbar,
Sai kuma yadora da fadar Hamdallah,
Komawa yayi ya dafe kanshi da hannun shi duk biyu kamar mai jin wani ciwo ko tunane,
Zubur ya mike yana mai daukar makulin motar shi,
Yanufi hanyar da zai sada shi elevator, don ya yi saurin sauka,
Tuki yakeyi a hankali sai tune yakeyi yanayi yana kallon gaban sa,
Gidan wani limamin massalacin da yake yawan bi sallah ya tsaya,
Zaune yake gaban malam cikin ladabi yakewa malam bayanin irin riban da ya samu a cikin wanan lokacin,
Saida malam yai gyaran murya sannan ya fara magana acikin kwanciyar hankali yadda Yusuf din zai fahince shi,
Komai na gamay da zakka da kuma sadaka fissabilliha malam yai mai karin haske akai,,
Godiya yaiwa malam yakawo alheri mai yawa yabawa malam din,
Bai koma office ba saboda yana da abubuwan da yake da bukatar yi kafin dare,
Ga fahintar shi ga bayanin da malam yai mai, shine, cewa zaka bayar da ita ga wanda ke a cikin bukata yafi,
Ko kuma ka taimaki wani ta yadda mai,shi zai iya mikewa,
Ba kamar yadda yaga cewa akasarin madu kudi suna rabon zakkah a yanzu ba,
Da za ace sai tallaka yabi layi adinga bawa kowa dari biyar biyar ko yan dubu guda guda,
Inda zaka ga mutane suna ta tururuwa zuwa karban zakkah gidan masu kudi,
Inda har ko kawa akeyi a gurin taron maza da mata akan zakkan naira dari biyar,
Yau kusan kwanan su biyu ba su komai da shi da ibrahim sai kasafi akan yadda ya kamata sukeyi,
Ibrahim yai mamaki kwarai ga yadda ya fahinci cewa Yusuf din yana kokarin ya kawo sallon bada zakkah shi,
Ance yawan tambaya ko sa ido yana kowa zubewar mutunci,
Don hakane Ibrahim ke yawan yin taka tsantsan ga al,amuran Yusuf daya ke gani,
Da marance ya shirya cikin shigar matafiya, inda yadauki jakar shi tankar mai tafiya,
Hanyar garin Suleja ya nufa saida yai ta yawo so sai a garin,
Inda ya kula da unguwar da yaga talkawa sunyi yawa sosai,
Wani massalaci yagani mai irin ginar laka, yadiba da kyau ya dubi yanayin gurin,
Komawa yayi yasamu wani hotel yakama don ya kwana,
Washegari tun da safe yabar wanan gari na Suleja yaiwa garin kwantagora tsinke,
Bayan tafiyar shi waye war gari sai ga jama,a dattawan unguwa sun taru suna, kallon damin kudin da aka aje a, cikin wani katon leda da akai raping din shi ,a cikin massalaci
Da farko tsoro sukaji amma daga baya sai akace kodai kudin wani matafiyi ne ya manta dasu a gurin,
Sai sukace a kirga sai asamu wanda aka ba ya kai koda banki ne ya aje masu har zuwa lokacin da mai shi zai bullo, su bashi abin shi,
Wata yar farar takarda ce tafado daga cikin ledar, da aka fara warwarewa,
ZAKKAH
A,karubuta da manyar haruffa gabadayan su sai wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wancan, gurin yai tsit,
Mutun guda daga cikin sune yace ALLAHU AKBAR da karfi sai sauran suka karba mai,
a lokaci guda gaba dayan su,,,,
Na suka shiga yiwa mai wanan halin adu,an fatan alheri da gamawa da duniya lafiya,
A garin kwantagora ma irin haka yadiga rabawa mutane zakka batare da ansan cewa daga gurin shi bane kudin ke zuwa,
Jama,a sai zancen ake ta yadawa iri,iri, wasu harda kari sukeyi a,kai cewa, wai ai wani ne kuma sukara yawan kudin da mai shi ya samu,
Tunda yaiwa garin shigar dare baya fita ko ina don haka ba kowane yasan cewa yana garin ba,
Sai wa yan da yake sallah jam i tare da su a massalaci, suka sani,
Yau jumma,a acikin shigar farar shadda dikin tazarce, sai wata fular daya sa wa kan shi mai ruwan Assh colour,
Gidan Anty Dije ya nufa musalin sha biyun rana , ba komai ya sa shi ya nufi can ba sai dan ya dauki Assalam su tafi mosque tare,
Anty a gida ita daya sai Abubakar tai mamaki kwarai da fa ganshi a lokacin,
Baiko kai ga zama ba sai ga yaran sun shigo gida da gudun su don ganin motar uncle Yusuf a kofar gida,,
Bayan yagama rungumay yaran dake mai Oyo,yo