Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 84

33K to 36K   out of 251.8K words

bukatar hutu a rayuwar ta yanzu,,
Kwantagora suka nufa daga Abuja inda tsohuwa ciyoma bata so hakan ba don dai ita taso ne takoma gida,
Don yanzu bata son wani alaka ya hada ta da mahaifin su Joseph tunda ya iya rabata da 'ya'yan diyar ta,
Inbadon Allah ya bata jika mai albarka ba wanda yasan darajan ta,

Sai bayan tafiyar Joseph Jerusalem ne labari ya iso ga mahaifin shi irin tai makon da yai wa jibrin again,
Abinda takai shi har da hawan jinin shi ya tashi mai dama ko yan uwan Ema IBO sun san shi mutum ne wanda baya son taimakawa na kasa dashi,
Cikin dare suka isa don tun a hanya sukai waya da Samuel nan Samuel yake sheda mai abinda yafaru
A cike da rashin son taimakon da mahaifin shi baison yana yi ya iso fam a zuciyar shi,,,
Murna sosai yan uwan shi sukayi daganin kakar su wace tun suna kanana so sai rabon da su ganta
Mr Ema yana dawo Church gurin service din dare yai arraba wanan tsohuwar duk shi ba wai wani girmuwar shi tayi ba sosai
Nan da nan anurin fuskan shi ta gushe mai sai da kyat ya iya controlling din zuciyar shi,,
A nuse Joseph yafito daga dakin shi don zuwa tariyan baban shi,
A fusace ya ke karba mai inda yafara mai sababi na rashin bin umurnin shi da Joseph din baiyi,
Yace saboda kaga yanzu kana cin gashin kan ka shiyasa ban isa in sa ma doka kabi ba,
Kafada min may hujjan ka na taimakawa yaran hausawa kuma musullumai,
Joseph har in bazaka daina hurda da wa yan, nan mutanen ba ina warning dinka kadaina shigowa kwantagora pls,,,
Joseph wanda kan shi ke duke tunda mahaifin nashi ya fara fada yadago a hankali ya fara magana acikin natsuwar nan tashi yace
Dole in taimaka masu baba saboda sun min abinda yafi haka alokacin da nake bukatar hakan,
Rai bace Mr Ema yadaga kai cikin mamakin kalamin dan nashi yace,
Kana nufin cewa ba,zaka iya rabuwa dasu ba ke nan,
Shiru yayi mai wanan karon yana dai sararon shi kawai,
Barin falon yayi saboda yasan cewa yanzu wani ,zafi ba ,zai lankwasa Joseph din ba,

Aisha tayi farin ciki sosai da jin cewa Joseph yana gari don tun cikin dare ya kirata yake sheda mata cewa ya shigo,
Tasan cewa ita kan kakanta ta yanke saka kenan don ba karamin abu take samu gurin shi ba,
Duk dai iyakar ta dashi kawai yan wasan ni kuma ba wani mai yawa ba,
Sosai ta shirya ma wanan zuwan nashi saboxa gana da yan bukatoci akan shi da yawa,
Shiko tunda safe ya fita zuwa wani kauye shida KB don yana gari,
Basu dawo ba sai zuwa dare marance,su ka , iso, garin ,
Bayan yai wanka ya shirya zuwa ganin little friend din shi,
Wanda kusan ko yaushe yana tuna yaron haka kawai son Assalam ya shiga zuciyar shi,,
Tsaraba sosai yakawo ma Anty Dije da yaranta don gaskya saida Anty ta kasa yin godiya,
Ita kanta Anty wasu materials madu kyau da tsada yasako mata ciki tare da dogayen riguna,
Issalam tana gama ganin kayan tace ina na little mummy din mu,
Da sauri Anty Dije tace mata ai nawa tare da natane zamu raba,
Wani inji Maryam dake kokarin bude fridge a lokacin don ta debo kayan miya,
Kai ta girgi,za wa Anty tace a nutse na yafe nikan gaskiya ban so,,
Issalam tazo har inda take gaban fridge tace kina so mana little mummy bake ki,kace mama tasaya maki anko ba,
Hannun yariyar maryam ta hado guri guda tace Issalam nagode ban so nace maki
Anty ce tace ke kyale zata karba ai wasa take yi,
Cikin mamakin maganar anty dije ta dago kai kalle ta, da niyar magana,sai kuma ta shiru kawai don irin kallon ki shiga taitayin ki da anty tai mata,a lokacin,
Assalam ne yace mama don ba,a sayo mata nata bane wai bata so ko,???
Nace maku bana so kawai simply ta fadi a nutse daidai lokacin da take kojarin barin gurin,
A hankali yabita da kallon mamaki saboda sai yanzu yafara fanin tsana karara a cikin idon wanan yarinyar,
Ya rasa dalilin wanan tsanar da yar karamar yarinyar ke mashi haka,?
Bayan tafiyan shi Anty taima Maryam fada sosai har takai maryam din yin kuka don dai ita gaskiya bata ra,ayin wanan mu,amular da su anty keyi da wanan Arnen sam,
Washe gari maryam na tsakar gida zaune da farantin shinkafa akan cinyar ta, tana gyaranwa tana raira kira,ar ta, ahankali,
Joseph yai sallama suka shigo tare da Aisha
Wacce tai kwalliya cikin wasu irin haddadun buje da riga masu kyau,
Kallo guda tai masu ta kau da kai gefe guda don bata son kara daga kai,
A hankali tace masu bata nan amma tace indan kazo ga abinci a falo,
Daga haka bata kara wani zance ba sai kokarin ci gaba da aikin gabanta tayi kawai,
Aisha ce cikin magana kamar rada tace wanan yarinyar na lura bata da kirki wallahi,
Ji yadda takewa mutane magana wani iri kamar tana jin warin su,
Baice mata komai ba asali ma kamar bai jita ba,
KB ne yai sallama sosai irin ta musulunci duk da bawai ta sake mai fuska bane amma dai ta karba mai cikin girmamawa da nuna kula,
Daga inda take tanajin suna hira akan wani guy wanda cikin su yake saidai yanzu mahaifin shi bai bari yana binsu sosai,
Wai yana zuwa aikin a gonar mahaifin shi ko yaushe ,
Joseph ne ke cewa gaskiya Umar na ban tausayi don ranan da na ganshi bazaka ce yataba rike biro ba arayuwan shi,,
KB yace Umar din ai yace zai zo zuwa anjima don yana son ku hadu dashi,

Cikin dan lokaci jibrin yai suna a cikin gari wurin yan kasuwa da sauran manyan mutane,
Don jibrin mutum ne wanda ya iya business so sai da jama,a,
Ga kuma tausayi da sanin ya kamata, akan harkokin shi,
Musan man dayake yana kara samun taimako daga gurin ubangidan nashi a asarice,
Ta yadda mutane bazasu iyagane cewa business din shi bane,
Saidai su dauka na company ne kawai,
Joseph ya koma gurin wanan matar abokiyar mahaifiyar shi mai manja,
Inda yake sa ana kawo mata kayan masarufi tana sayar wa talkawa cikin sauki,da rahusa,
Ta yadda tallaka ba zai yi mugun wahala ba, sosai wurin samun abinci,
Tuni sunan su ya fara fice ga al,umma tun mutane suna zargin su har aka gane cewa business ne sukeyi tsantsar ta don ci gaban mutane,
Matasa da dama sun samu abin yi yanzu wanda hakan yasa emirate taji dadin zaman Joseph a tare da al,uman su,
Wani abin sha,awa kuma shine idan ya samu labarin cewa a unguwa suna samun matsalar ruwa ko wuta sai yasa sai yasa a tona masu famfon burtsatse ko kuma ya sauke masu transformer,
Ya sayo motoncin noma birjit ya tura kauyo ka mafi kusa don tallafawa,
Dalilin da mutane suka sa mai furen juji ke nan,don dai yanzu yan kwamintin su na chu sunkirashi mitin yafi a kirga amma yaki halarta,,

ZEEEE MAKAWA,,,
ZEEE MAKAW
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Alhamdullah Allah yakawo yau, maryam sun zana jerabar su ta karshe a girls day secondary school, kwantagora,
Fitowar war,ta kofar class din tai wata ajiyar zuciya gami da fesar da watar iska irin na relief din nan,
A hankali take tafiya zuwa bagin get don tafiya zuwa gida jitayi an jawo ta, Assamau musa ce classmate din ta mai photo ta nuna mata tana da bukar suyi photo,
Fara photon nasu ne wasu yan gidan jodda suka shigo akayi da su
Maryam wace kawo yanzu duk ta kagara ta wuce, gida
Don ta huta saboda duk kwanakin nan bata samun barci don mathematics ce zasu zana karshe,
Gani zasu bata mata lokaci da yawan daukar photona ya sai ta, sa kai kawai zuwa fita daga school compound din,
Wata mota tagani tana jiran wata yariyan batai mamakin haka saboda ga abin hawa na birjit a waje suna jiran yan uwansu wasu kuma samarin su,
Tabbas in ba karya idon ta ke mata ba wanda tagani bakin motar KB ne, don ko ina zata gane shi yanzu don yawan zuwa gidan su da sukeyi ko yau she muddin suna gari,
Kai takar kamar bata gan shi ba sai tafiya takeyi cikin sauri don ta isa gida,
Horn takeji a bayanta kamar kada ta waiga fon tasan cewa ba asaman titi take ba ita,
Sai ganin motar KB tayi gaban ta ya Parker dan zuge glass din motar yayi yana mai dan lekowa ta window motar,
Sai a lokacin tawaiga batare da ta daina tafiya ba,
Ta furta a hankali ina wuni,, dan murmushi ya sakar mata ce little mum babu gaisuwa ,
Dan murmushi tayi wanda ya baiyanar mata da fararen hakora ta da suke a jere ras a cikin dan karamin bakinta,
Tace ai na gashe ka ko, ?
Yace zo muje mana mu saukeki a hanya , gani wata classmate din ta zaune a bayan motar yasata dan kara yin murmushi tace ku tafi kawai ai zan hau achaba yanzu,
Ganin zai kara mata magana yasa ta tsaya badon taso ba don dai kada mutane su samasu ido
Don yanzu ba,a raina sa,ido ga dan karamin abu,
Tana kutsa kanta a cikin motar wani irin sanyi da kamshin wanda bata iya tantance ko motar ce ko kuma masu motar ke wanan uban kamshin haka,
Ga sanyin AC ya hade da kamshi wanda zai iya sa mutum acikin wani yanayi, (A,uzu,bikalamatilllah ,tamattah), tace yayin da take kokarin zama a motar,
KB ne ya juyo a hankali yana mai cewa taufa malama ce injin muka dauko,
Maryam da sai yanzu bayan ta samu natsuwa, ta sheda ko wace su KB suka fara dauka a motar
Wata, fatima Indagi ce yar gidan nufawa asalinsu mutanen garin Bidda ne zama yakawo su kwantagora,
Har suka zama yan gari yanzu don sun san kowa kowa yasan yan gidan su,
Bawai wani shiri sukeyi ko a school da ita ba don haka ko kallon inda take,Maryam batayi ba,
Baka jin komai daga cikin motar sai kida ke tashi ta yadda ko na wajen motar zai iya jin kidar daga waje,
Maganar shi yasa maryam gane cewa yana cikin motar wace tun shigowar ta motar kanta na gefen glass tana mai kallon waje,
Dammmm sautin da kirjin ta yabayar ke,nan a lokacin da taji muryan shi a motar yana cewa,idan ka sauke su mu wuce uguwar JANKIDI pls, zanje inga Abdulsamad,,,
A hankali kwance yake maganar batare da ya kalli cikin motar ba gefen KB din,
A,kofar gidan su Maryam, din suka para tsayawa don su sauke ta,
Daidai lokacin Assalam yadan fito ta wajen gidà yà na kallon motocin a ke wuce wa
Kokari takeyi ta balle murfin motar daidai lokacin da Joseph din ya dan dan,na gurin da duk security din motar suke,
A lokacin kuma Maryam ke fadi cikin siririyar murya,
Nagode, ta furta a hankali ta yadda ba wai lalai ne wani yaj abinda tace ba,
Hannu kawai shima yadan dago mata alamar ba matsala,
Da gudu Assalam yazo ya rungumay mata yana oyoyo little mummy, dan jakar hannun ta yake kokarin karba daga hannun ta,
Sai a lokacin yai arba da Joseph wanda ke a gaban mota zaune,
Sake jakar yayi ya sheka da gudu gurin motar yana washe bakin ganin Joseph din,
Juyawa maryam tayi abinta batare da da tasaya koda kallon su ba
UNGUWAR JANKIDI, wani unguwane acikin kwantagora, inda wane abokin sanar mahaifin Joseph yake zaune,
Emeka ake ce mai ,,,kusan tare sukazo neman kudi agarin, tun suna matasa,
Saidai Allah da ikon shi , cikin wani watan Azumi, sai kawai aka wayi gari wurin wani tafsirin marance da ake yi, Emeka ya kawai sai ga Emeka yace yazo ya musulunta ne,
A ranan yakarbi musulunci a hannun babban malamin dake wa maza tafsir, a kusa da gidan sarki,
Ranan duk wani IBO da ma sauran Christies hankalin su ya tashi sani cewa kowaye Emeka da sukayi,
Duk wani hanya dazasubi don suga cewa sufitar dashi a cikin musulunci abin ya faskara garesu,
Har kudi suka hada mai uban yawa suka kaimai wai yadawo cikin su amma sam yaki karba,
Daga baya da sukaga yaki sai suka fara shawaran yadda zasu cuta mai har ya karaya, yadawo masu,
Wuta suka fara sama shagon shi a tsohuwar kasuwa inda shagon ya kone kurmus,
Da sukaga baizo wurin su ba sai kuma wani dare suka turo har gida aka sace duk dan abinda yasaura a hannun shi suka gudu,
Yan kwamitin su sukazo mzi da makuddan kudi suna mashi tayi akan yadawo cikin su,
Amma san Abdullsamad yaki dawowa, yace shi ya shiga kenan,
Maimako yan uwa musullumai su tausaya mai su mai tallafi ko wani gudun mawa sai kawai aka shere shi nan,
Ganin wahala yai yawa yasa matar shi gudu tabar shi ta koma kasar su, inda takoma ma Christian din ta,
Tabarshi nan tare da yaran shi ma,za uku, suna ta buga,buga,
Yanzu har takai ko suturan sawa baida shi dan gidan shi rabi ya zube baida kufin gyara saifai kawai Allah ne ke rufa masu asiri su samu abinci,
A haka ya auri wata musulma ma sanar saida shinkafa a bakin kasuwa,
Yakan je gurin Mr Ema jefi,jefi in abin yadaure mai da yawa,
Saidai duk sanda yatafi zai dawo da tarin bakin ciki a zuciyar saboda irin yadda Mr Ema kan ta sake mai maganganu,kuma duk kyautar, da zai mai bawanda zai amfana dashi bane, daga dari biyar tsanani dubu biyu,
Rigar shi duk ta yage yage a baya, hakana yake sawa yakoma kamar mahaukaci,
( Allahu Akbar munada wanan raunin wallahi musullumai bamu tallafawa wa yanda suka tuba yanzu,,,,,,,)
Mama manja ce ta fadawa Joseph cewa yana bukatar taimako sosai saboda sani da tai ma iyayensu tare a da,can,,,
Yai mamakin jin cewa har yanzu Emeka Abdullsamad yana agari batare da yasani ba,
A hankali suke gangaro da motar su zuwa cikin unguwar wanda akasari duk tsofafin gina ne a gurin,
Zaune suka hango shi saman wani tsohon icce dake kofar gidan shi ,
Cikin wata tsohuwar rigar atamfa duk ta kode ga farin gashi duk ya dan cika mai fuska,
Yana zaune kai dagani kasan cewa yana cikin halin hau ula,i,,,
Har suka faka motar su baidago kai ya kalle su ba,
Saicewa yakeyi a fili Subbahanallahi, Walhadullahi Allahu,Akbar,,
Sallama KB yamai daga inda suke nufo shi ya karba masu tare da daga hannu har saida yakai aya, tukun,
Sam bai gane Joseph ba a lokacin saidaga baya bayan ya mika masu hannu sun gaisa, duk da kallon mamakin da yake masu namay yakawo su gurin shi,
A fuska yadangane Joseph din cikin yare yai mai kirarin gidan su,
Inda Joseph din yadan duka agaban shi yai mai yar gaisuwa irinta al,adansu
Abdullsamad yadan bugi kafadar Joseph din alamar ya karba mai gaisuwa,,
Joseph yace mai baba kana garin nan shine kashige haka shiru, ,,
Murmushi yayi yadan mike ya ciro wata tsohuwa ashirin a aljihun shi yana kokarin zuwa wani shago xuwa sayo masu pure water leda,
Cikin sauri Joseph yace mai a,a yabari kawai ,acikin nuna damuwa da kulawa yace ma Joseph kabari in shayar daga kai daga cikin dan abin da nake dashi pls,
Yanamai daga hannu alamar ban hakkuri agare shi,
Dole badon sun so ba yakarbo masu ledan ruwa, gida biyu yadawo katakata cikin sauri ya mika masu,
Sukaiyi mai godiya Joseph wanda ke ji alokacin kamar ya zubar da hawaye don tuna kowaye Emeka,
Yace mai ina sauran yaran shi suke, nan yake sheda masu cewa, mutum uku suna nan tare dashi,
Saura kuma sunan can garin su tare da maifiyar su,
Dan shiru ya biyo baya duk kan su kowa da abinda yake anyanawa acikin zuciyar shi a lokacin,
Joseph ne kauda shieun take cewa yaso koda zai samu ganin yaran koda mutum guda ne

12 / 84