Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
kidar da ke tashi a motar na siliado,
Sun kusa shiga gari ne yadan joyo inda take yana cewa,
Wani unguwa zamu tafi ne, ?
A hankali Maryam tace furta da ka sauke ni a round about kawai sai in karasa,
Batare da bata amsa ba ko tsaya yace wani unguwa pls, ?
Cikin ,ciki ta furta kwanar kuka,
Kwanar da zai sada shi da unguwar ya karya, daidai kusan uguwar ya ce gidan wa,
Illiyasu costume, kallon ta yakarayi da kyau don jin gidan da take,
Yace ke kaunar matar shine ko, kai ta gyada mai a hankali,
Daidai kofar gidan ya aje ta,
Ya ce toh nagode, maryam da taimakon da kikai min,yau,
In sha Allah zan gyara ga dalibai zaku samay ni masauki da rangwamay,
Kan ta na kasa cike da jin nauyi,
A hankali tace nima nagode malam da fahintar gaskiya da kayi,
Murya cike sa cike da amon murna yace ai ni ban san may zan kara fada kuma,
Ta bude gambun motae a hankali tafita shi kuma a hankali ya fara ribas da motar shi,
A nutse ta rika takawa har zuwa kofar gidan su, inda taga wasu a zaune, saida sun bada baya,
Kallonta yayi a glass din motar har tashige shi kuma ya harba yabar shi yan,
Zuciyar shi fam da tunanen kalaman yarinyar,
Har ta shige gida batare da ta lura da wanda ke wajen gidan nasu ba alokacin,
Shigewar ta yabi bayanta da kallon mamaki a ran shi yana mamakin yau she tagirma haka,
Maryam na shiga gida tasamu Anty Dije, tana aiki, taimata sannu da gida tafada Wanka don ta dan ji dadin jikin ta,
A marairaice maryam ta ke cewa Anty Dije, kamar mai shirin yin kuka
Anty tunda safe banci komai ba tun da na fita gida,
Yar karamar harara Anty ta sakar mata tana cewa, ,oho maki, danace ki tsaya ki karya ba ki ,kikayi ba waike kina dokin zuwa makaranta,
Yar guntuwa tsuki tayi tace kuma wallahi duk sakkon danayi ban samu lecture din ba anty,
Baki Anty ta tabe mata tace anfada maki ana samu cikin zafi ne,
Aikomay zakayi kayishi a cikin hankali, don rashin cin abinci na iya jawo maki ciwon ulcer,
Falo tadosa don ta zauna ciki ta ci abincin ta tana kallo,
Ganin mutum tayi a zaune yana cin abinci shi a hankali,
Juyawa tayi da sauri da niyar barin falon a lokacin, sai kuma tatuna cewa ba su gaisa ba don haka ta tsaya cikin ladabi tace mai ina wuni,
Da wata irin dasashiyar murya ya amsa mata, a hankali,
Sai ta juya kawai tabar falon ,shiko mamaki yaji kwarai da gaisuwar da yasamu cikin mutunci gare ta yau,,,
Wanan shigowan da su Joseph sukayi tare da abokan ahi shigowa ce ta musam man sukayi
Don bukin sallah da za,ayi inda matasa ke bukatar a bukin hawan dawakai wato Dubba,
Don haka basu samu wani zama ba sosai kamar yadda suka saba,
Don yawan zirga,zirgan da suke yi tsakanin birni da kauye gurin ganin cewa komai ya kammala,
Yau ma kamar kullun sun dauke shi zuwa wani kauye duk da shi kauwaici yake masu don ganin cewa suna kokarin sashi cikin al,umurorin su,
Amma shi gaskiya duk irin wanan abin bawai yadamay shi bane shi harkokin business din shi kawai ke gaban shi,
Amma a zuwa yanzu abin da yake gani gurin su jibrin da KB dama sauran abokan su yana bashi sha,awa sosai ,
Duk masifan da mahaifin shi zaiyi yayi mai sunyi mai preaching kala kala akan ya daina bin diyan musulumai,
Kawo yanzu, Yasa an gyara mai gidan mahaifin shi amayar mai dashi hawa biyu sai kuma katon parking space mai girma da saura guraren da ake samu masu kawata gida,
Amma duk wanan baisa Mr Ema kyale dan nashi ba, da fitinar ya daina tallafawa mutane musanman musullumai,
Yasa ma Joseph din ido ne kawai don yasan cewa Joseph din yanzu ya wuce sanin shi,
Wanan hurda da kuma al,adun da Joseph keyi na hausa baima ma Mr Ema dadi sam,
Yau ma kamar kullun cikin fushi yake wa dan nashi fadan cewa yaran hausawa sun asirce shi ne,
Saboda labarin dayazo mai cewa da gudun mawan Joseph acikin wanan gagarumin bukin da matasa ke ta kokarin hadawa don cigaban masarautar su,,
A fuce yace baya son Joseph ya kara zuwa garin yafi bukatar ya daina zuwa da ace yazo yana hurda dasu haka,
Wanan maganar harta kai Joseph yai yun kurin gina gidan shi inda zai dinga sauka inda yazo,
Sai da baban yaga cewa zaiyi hara sosai ya kuma kara bidan dan nashi sulhu,
Inda ya ke sheda mai cewa hausawa shu,uman mutane ne yana gudun nan gaba ne kada su ja,ra,ayin shi akan wani abu can,
Maryam wace yanzu, haduwar ta, da A,A MASUGA, yazama mata, wani sanadin alheri,
Don kwana biyun nan shi ke, zuwa da kanshi ya diba yagani ko ya karatun ta ke tafiya,
Tun maryam na dari,dari har ta fara dan sake jikin ta dashi suka dan fara sabawa,
Duk wanda yasan Maryam ada yanzu in ya ganta bazai sheda cewa ita bace saboda,
Tazama cikakiyar yar jami,a saidai har yanzu wanan hali nata yana, nan kamar da ba ta yawan kula samari kamar sauran yan mata,
Mutana suna zaton cewa ita, sister din A,A masuga ne,
Saboda yawan ganin da ake masu tare ko kuma yawan kulata da yake yi,,
Kwanan nan gidan Anty Dije cika yake yi sosai sasboda gab suke da fara program din su
Duk may neman Joseph indai yana cikin garin kwantagora a gidan anty dije zai samay shi saboda bai son su samay shi a gidan baban shi don gudun fitina,
Tafe suke tare da A,A masuga,,,,da wani abokin shi,, acikin motar shi sai faman waya yake, yi da alamar da mutanen gidan su yake waya don yadda taji yana bada ansa yasa tagane hakan
Yana gama wayan yai yar ajiyar zuciya tare da shafo sumar kan shi tundaga, fuska, zuwa baya,har kusan wuyan shi,,
Sai a lokacin yadan waiga inda maryam ke zaune hankalinta a titi, tana kallon yadda abin hawa suke ta zirga zirga kasan cewar yamma tayi a lokacin,
Maryam ya furta a kasalance kamar yadda yake kiranta kullun,,
Wanan, kiran shi ya,katse mata kallon titin da take yi tun dazu,
May yafaru naji kin yi shiru, ko , yadan kalle ta na minti guda,
Cikin nuna kulawar sa yace kan ki na ciwo ne, naga kin yi shiru,
Kanta ta girgiza tace a,a babu wani ciwon kai ,
Illa masu son yin bukin nan dake son takurawa rayuwan mu,
Ace bamu da hutu sam a gidan mu in har wanan dan Christian din yana gari,
Baki makam A,A masuga ya tabe yace lalai kam ku samu aiki,
Yace wai may ye alakar shi da ku ne, ma wai da naga ya na zuwa gidan ku duk lokacin da yake gari, gashi shiba musulmi ba ba bahaushe ba,
Batare da tai magana ba tai dan guntun murmushi irin na iya fuska, kawai,
Aiko kamar kar su karasa kofan sai ganin jama,a fam sukayi ana t hayaniya kamar ana wani buki,
Da kyat malam masuga yadan samu ind ya Parker motar shi a gefe don tafita,
Aiko idon jama,an dake gurin ca,aaa akan motar don suga ko waye zai fito cikin motae,
A hankali ta bude marfin motar tare da yin yar guntuwar tsuki wanda duk inda kake zaka ji,ta,,,,
Dan harara malam ya watso mata daga inda yake yana cewa
In bake ba wake gudun taron mutane ?
Batare da tace mai komai ba ta,kauda kai zuwa inda taga su Joseph zaune suna diban wasu takardu a hannayen su,
Diba guda tai masu takauda kai gefe guda cike da jin haushi, don wani iri taji a ranta,ganin yadda yake kokarin shige masu,
Koda A,A masuga ya tsaida mota tafita , ko kallon inda suke bayi ba nan tabi ta gaban su ta wuce kawai abinta batare da ta tsaya gaidasu ba,
Kamar may rada taji ya furta sunan ta a karo na farko ke nan tun sanin tada shi,
Wasu takardu yamika mata na cewa don Allah taba Anty Dije ta aje mai akwai wanda zaizo ya karba a gurin ta,
Kamar ta wuce don ita aganin ta yama raina mata wayo ,
A matsayin shi na kafiri, Arne, zaice zai ai,keta sai kuma fadan Anty ya fado mata a rai
Dole ta tsaya ta mika hannu ya miko mata, cikin rashin ko inkula,
Tana shiga rai a bace ta yi kokarin mikawa anty takardan tai shigewar ciki,
Ana cikin wanan hada,hadar shirin hawan dabar da suke yi wanda mutane sun hana Joseph din tare da mabiyan shi shakat,
Har su maryam dake tare dashi a gida koyau she zakaji ance ana wai sallama da Joseph din,
Ita dai maryam mamaki taje ji na wanan halin da ga mutane na kokari zubar da mutuncin su da Allah yai masu akan kwadai,
Don haka ko tana gida bata yawan zama a waje don gudun damuwar jama,,a
Yau malam A,A bai zo school ba yai tafiya zuwa wurin wani seminar da zasu a kwara state,
Mashi ta tare don komawa gida duk A,A din yace ya hada ta da wani friend nashi ya dinga taimaka mata, zuwa gida,
Amma ita maryam din sai taga cewa bazata iya bin wanan mutumin ba don kawai kariyar mutuncin ta,
Mai,mashin tatara ta hau, duk da tace mai kada,yai gudu da ita, amma kamar zuga shi tayi a lokacin
Haka yakw kokarin wuce motoci da ita a baya makale,
Daidai kwanar sabuwar junction suka hadu da motar yan matasan masu tashe agari,
Cikin wata jar mota haka kallo guda mai jan motar yai mata,ta kauda kai duk ita ma dai taji kunyar yadda take dane bayan mashi, mai mashi nata,gudu da ita,
Kallo mai kamar harara ya watso mata, wanda ita ma din kusan irin kallon ta watsa mai a lokacin, ta mayar mai da martani,
Kai Joseph ta girgiza don in a kwai abin da yai hating she yaga mace a saman mashin ana gudu da ita kamar bata san zafin ta ba,
Bai san har lokacin da yafurta a fili ba yace nonsense,kawai,
A rashi yake tunanen ya furta sai gashi ashe afili ya fadi hakan,
Jibrin dake gefen shi ya kyalkyale da dariya yace kaganeta ashe,
Kai kawai ya gyada mai alamar eh, a hankali ya furta may ye amfanin hawar mashi a diya mace pls,
Maryam ko rana isa gida ta samu anty tasayo zogala, ai cikin murna ta shiga sallah kawai ta idar tafito waje don ta gyara masu zogalar,
Bayan ta yanka su albasa, da attarudu da tatasai sai man kulikuli da ta lema masu asaman takawo garin kulikulin ta cakude wuri guda sai ruwa mai sanyi da ta dauko,
Da shikafa tai niyar zubawa taci bayan ta debi daidai zamar ta asaman wani tabarma da ta shimfida don ta ci gwaben ganyen, da tayi,
Shigowar su ,suma ke nan a gidan, inda, jibrin ke gaba, wani lawal na binsa, sai Joseph tare da wani tajudeen a baya,
Shigowar ya fara rage mata dokin da takeyi nashirin cin ganyen da tayi,
Jibrin ne da shigowar su , yadan kalli inda maryam take zaune yace mata,
Ke ashe har dadi kuke ji indan kun hau irin wanan mashin din dake kusan tashi sama da ku,,,
Baki kawai maryam ta hangame cikin mamaki da maganar jibrin,
Saidai taso ta furta cewa wani abu amma sai ta kasa, cewa komai don wani irin al,ajibi jin maganar da tayi,
Don dai ita tasan cewa ba gwanar hawa mashin bace ko banza
Yau ne kawai da take kokarin ganin cewa ta iso gida da,wuri don ranan da yai yawa a garin,
Ji tayi wasu hawaye masu dumi sun gangaro mata a fuskan ta, ga wani malolon bakin ciki da ya tokare mata makogoronta,
Takai wani dan lokaci a gurin zaune takasa tashi,
Saidai tana kiyasta irin daukar da sukai mata a matsayin yar iska kenan ko,
Bataji zuwan Joseph da Assalam inda take zaune tana hawaye ba,, sai ganin shi tayi gaban ta,
A hankali ya sauka bisa gwiwowinsa, yace little mummy kiyi hakuri amma gaskiya jibrin ya fada maki,
Banza tayi da shi sai kuma wani wawan harara da ta sakar mai, har Assalam saida ya dan ji tsoro ya dan shige jikin Joseph,,
A raunane ya kara cewa kiyi hakkuri wanan ba abin bata rai bane,
Kala batace mai ba sai mikewa da tayi tsam ta nufi kofar da sauri,,,,
Ido yabita, da shi don dai shi baiga abin bata rai aciki ba,,,,,,,,,
ZEEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
Buki sosai akayi a wanan bukin hawan Dabar da akayi don matasa masu ji da lokacin su sun halarci wanan bukin nadaukaka masarautar kasa kwantagora
Wanda ke tatare,da tsohon tarihi acikin ta kamar sauran manyar masauratar da ke a kasa shen hausa,
Anbuga a jaridu da kuma sauran kafafen yada labarai, na kasa,,
Inda bukin yasamu karbuwa fiye da zaton may karatu,
Ana gama wanan bukin da kwana biyu Joseph yabar garin kwantagora , saboda gudun fushin mahaifin shi da yasan cewa yana hake dashi,
Duk irin abubuwan da ya wakana agurin duk Mr Emanuel nada labarin komai tankar a gaban shi akayi, duk shagallalikukan
Don haka joseph ko kasan bai tsaya ba ketarawa yayi zuwa kasashen waje da niyar yatafi, yadan huta a can,
Tun bayan wanan abubuwar, maryam babu ruwanta da zancen, wani wasan da akayi
Wanda ita take gani kamar duk wanan abin bai cikin irin tsarin rayuwar ta,,
Ita bata masan cewa masu takura masu a gida, basu garin ba tun bayan bukin da gari yayi kamar zai tsage, don cinkoson jama,a
Don ganin da su tun zancen da suka ce ta hau mashi a na gudu da ita kamar wace bata san zafin kanta ,
Ita ko a nata zaton gani takeyi kamar suna ganin cewa bata san darajan kanta ba ne tunda har take hawan mashin da na miji,
Idan har ta tuna da wanan kalamin sai taji duk yanayin ta ya sauya,,
Saboda ba karamin ci mata fuska take ganun sun yi ba,
Takan yi tsuki tace wai gwano baya jin warin sa, su da suke hurda da yan iskan yan mata
Shine har zasu samata kazafi akan hawa mashi, idan bata hau mashin ba da may zatai tafiya to,,,
Wata rana da la,asar bayan Maryam ta dawo daga wani gida da anty ta aiketa karbo, mata sakon wasu kaya da aka turo mata ta daga kano,gurin wata mata,,
Don yanzu Anty tana dan taba business irin da matan gida ke dan yi,
Domin kariyar mutuncin su saboda hana, bani bani gurin maigida,
Wani mutum tagani dattijo zaune a kofar gidan su, tun daga nesa take kallon mutumin a cikin mamaki, saboda ganin shi da tayi gab da kofar gidan su,,
Saboda a gaskiya bata taba sanin shi acikin masu zuwa gidan su ba,
Koda kuwa gurin mijin yar ta ne, bai daga cikin masu zuwa gidan,,, sam,
Gashi kuma kaman nin sa sun nuna cewa kamar yana tare da lalura,,,
Tafiya take yi a hankali, cikin dan shakku,kamar za,a kamata,
Tana karasowa gab inda mutumin ke zaune sai mutumin ya mike tsaye da sauri ganin cewa gidan maryam ta dosa a lokacin,
Cikin dan tsoro da kuma ladabi maryam ta dan duka kadan tace Baba ina wuni, ?
Yace yauwa "ya ta lafiya kalau,
Dan Allah ko gidan nan kike yan mata, ?
Maryam dake dan ja baya baya kadan da kamar tace mai a,a sai dai ta daure tace mai eh a nan take,
Hausar shi na nuna mata cewa mutumin ba pure hausa ba ne,
Ya ce dan Allah yan mata ina son ki min iso a gurin mai gidan nan,
Cikin mamaki Maryam ke kallon shi tace mai baya gari,
Shiru taga mutumin yayi cikin damuwa yana mai dan ya mutse fuskan shi,,sai kuma taji duk yaba ta tausayi,
Ita a zaton ta ko yazo maula ne irin yadda wasu masu kararen zuciya ke yi a wanan zamanin,
Kaga mutum majiyi karfi amma sai