Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
ZEEE MAKAWA YELWA
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
8β£1β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Ina, rokon Allah Ya saukar da Albarka, Alkhairi,Falala, Wadata, Ni'ima, Gafara, Rahama, Lafiya mai amfani, Kwanciyar Hankali a garemu da Zuri'armu, da Musulmai Baki dayan mu Masoya FUREN JUJI,,,
Yusuf wanda ya kai wani lokaci agurin da yake zaune ba tare da ya motsa ba
Saboda mamakin maganar da Sonny din yai mai yan mintituna kadan da suka wuce,
Hamdala yai ga Allah ubangiji subbahanahu, Wata,allah,
Da ya kaddarace shi da ansa kalman shahada yafitar dashi daga cikin kafirci,
Idan ba halin rashin imani a zuciya ba may zai sa Sonny ya tunkare shi da wanan zancen,,
Na jahilci watau badan Allah zai musulunta ba ke nan don biyan bukatar shi ce kawai,,
Wanan maganar yasa tunawa da wani Christian dan church din su wanda,
Yai ridda har sau uku saboda jahilci inda ya zama Christian sai ciwo ya wuce daga jikin shi,
Idan ya koma musulmin shi sai ciwon yadawo mai sosai fiye da farko,,
Sai in har ya koma Christian zai samu sauki acewan shi wai a church ne saukin nashi yake,
A haka har ya mutu cikin Christiatanci, batare da ya farga da cewa taimo yaje samu daga yan churches da kulawa fiye da zaman shi a cikin musulmi,
Wani irin ajiyar zuciya Sadiya tayi bayan tagama jin labarin da fauziya ke fada mata,
Akan irin alherin da Yusuf tare da abokin shi sukayiwa mutane a ziyaran da suka kawo,
May Yusuf ke nufi da ita ne yanzu, sam babu ita ke nan acikin tarihin rayuwar shi,
Wanan abin yai mata ciwo duk da tasan cewa kanin mahaifinta ne yai mata silar wanan sherin,
Tabas yazama dole tamike tsaye ta san abin yi kafin wankin hula ya kai ta dare,
Tamike tsaye tana gyara gyalen da ta sabalo a wuyar ta,
Tana cewa kwanan nan zai dawo gare ta don ba laifin ta bane ai da zai dauki tsana ya sa mata
Ita har gobe tana so shi don haka bazata iya hakkurewa da shi ba, a rayuwan ta,
Ta,dan ce a hankali tabbas sai ka dawo da kafan ka, nice dai matar taka, don ka sani,,
A hankali gudu yake shararawa saboda yana sauri kada rana tai mai bai isa da guri ba,
Ganin ya fara hangen garin Kano' din yasa shi dan rage gudun da yake yi,
Next kauyen da zai iya sada shi dagarin kano din yaga dan dan,dazon mutane a bakin titi ga wani mutun tallabe a jikin wasu matasa, su biyu,
Duk motocin dake gaban shi sun wuce batare da sun tsaya ba,
Tun daga nesa idon shi yahango mai abinda ke faruwa sai dai zuciyar shi tabashi ce inda muggan mutane ne baizaiga wanan taron ba acikin gari haka,
Yusuf, wanda ke cikin motar shi yana tafiya a hankali, yazo gab dasu ya tsaya,
Baka jin komai sai kiran da ke tashi a motar da kamshi da sanyin A,C,
Kafin ya sauke glass sai,ga wani dattijo mai farin gashi jefi,jefi akai yadan leko shi,
Yace dan Allah malam ka taimaka muna da wanan bawan Allah zuwa cikin gari asibiti za a kai shi,
Ba musu ya bude masu security din motar sai motar ta bude,
Har zasu shiga sai yaji muryan wani daga waje gurin mutanen yana cewa kai amma dai ku baku da hankali,
Kuga mutum haka cikin wanan irin motar shine har zaku tare shi batare da,kun san kowaye ba,
Kudibafa ku gani lafiyayen mutun yafito neman kai kamar makafi kun wani fadawa har kai uku,
Murmushi Yusuf din yayi kawai sai,da yaga alamar cewa sauran mutanen sun dan tsurata da zancen mutumin,
Saida ya lumshe idanun shi sanan yace masu , duk da ba,a gane macuci a fuska,
Ni saboda Allah da Annabi zan taimaka maku amma fa idan kun yarda,
Tsakanin su aka dan yi jimm sai wani daga cikin diyan mara lafiyan yace Allah ya tsare ku gyara mu shiga kawai,
Tafiya yake yi dasu a hankali yadan yi yana waigen tsohon dake ta Nishi sama, sama,
Tambayar su ya yi wani asibiti ne zaku kai shi, ?
Nan suka fara muhawaran asibitin da ya fi saukin ganin likita, da kuma saukin kudi,
Don haka, Yusuf yace may ke damun baba din ne. ?
Yaron nashi wanda alama ya nuna cewa shine babba daga cikin su yace,
Yau kwana biyu bai fitsari bai bahaya,
Subbahanallahi inji Yusuf din cikin dan rudewa,,
Yace akwai wani asibiti ne da kuke ganin ya na da kyau mu tafi can,?
Ganin cewa mutanen kauyawa ne yasa shi dauko wayan shi,
Noban Alhaji sambo ya kira yana bincikan shi ba bata lokaci yai mashi kwatance,
Basu wani shawuya ba ga kwatancen da akai masu,
Yusuf wanda yazo kano harkan business din shi sai gashi ya buge ga zirga,zirgan asibiti,
Dashi akai komai, har zuwa lokavin da likita ya zo yadiba tsohon dake ta kugin wahala saboda azaban da yake sha,
Dubu sittin da yan kai likita yace su fara bayarwa tukun ,
Zasu tsaya inda,inda Yusuf ya jawo yan dubu, dubu daga aljihun rigar shi ya mikawa likitan,
Ba a fi wasu yan mintoci ba aka jaye mai komai yasamu sa, ida,
Gado a,kabashi don haka Yusuf din ne yakara biyan sauran kudaden da ake bukata,
Tun safe sai zuwa bayan sallah azahar ya samu kan shi,
Sai, a lokavin yashigo dakin dakin bayan ya gaishe su a mutunce sanna ya gusa gurin tsohon da yaji suna kira da malam yai mai sannu ya jikin, ?
Malam din yadan dago kai, zuwa gurin da Yusuf yake tsaye daga gefen shi,
Hannun shi yadago a hannkali ganin may yake nufi ne yasa Yusuf din saurin mika mai nashi hannun,
Yarike hannun jimmmm har zuwa wani dan lokaci bakin shi kawai zaka ga yana motsi,
Sunan shi ya tambaya yace mai Yusuf yake, sai tsohon ya dan gyada kai alamar gamsuwa,,
Kokarin wucewa yayi bayan yai masu sallama, daya daga cikin su ne yai a,zancin karban nomba Yusuf din da sunan zasu kirashi suyi mai godiya daga haka yai masu sallama, ya nufi gurin da zai sauka,,,,,
Kwance take saman gadon ta tana barci amma sai juye juye takiyi daga kwancen, da take din,
Gudu take tayi a,wani bakin daji mai duhu da kuma, sarkekiya,
Rigar barcin dake saye a jikinta shine saye gareta a cikin mafarki,
Gudu kawai takeyi sai wasu halittan da bata taba ganin irin su ba ke bin ta a guje,
Hakin da takeyi agudun shine ya baiyyana afili tana ta juye juye,
Tana gudun tana cire wanan yagwagen dake sarke mata hanya da jikin ta,
Bakin wani rami suka kawo ta inda taja ta tsaya guri guda,
Gani cewa wa, yanan halittun sunyo kanta gadan gadan yasa maryam din kara hannayen ta biyu ta rufe jikin ta zuwa fuskan ta,
Tare da furta Innalillahi cikin wani irin murya mai karfi,
Wanda har mueyan yakai dakin da Anty dije take tare da dan ta Abubakar da maigidan ta, da yazo kwana biyu da suka shige,
Wanan sautin da Anty Dije da maigidan tasuka ji na maryam shi yasa su taso cikin sauri zuwa dakin da maryam din take kwance,
Jikin ta ya jike kamar wace akaiwa yayafin ruwa akai,
Jin karan bude kofan su anty yai daidai da saukowan ta saman gado da karfi ,
Inda tayo kan Anty nata cikin kaduwa tana kokarin shigewa jikin ta a tsorace,
Hakalin Anty Dije ya tashi matuka saboda irin halin da, ta ga kaunar nata a ciki,
Don haka sai ta rugumay maryam din a jikin ta inda take ta maida numfashi guda guda a tsorace,
Dakin suka fito da ita zuwa falo inda sukabar mijin na Anty yana yan dube dube a dakin kamar wanda ke bidan wani abu, a dakin,
Kusan a nan suka karasa kwana falon inda har da yaran suka kwaso zuwa falon,
Dakyat suka ga safiya da maryam din saboda irin halin firgicin da ta shiga ciki a lokacin,
Tun a massalaci gurin sallah Asubah mijin Anty ya shedawa baba abinda yafaru da maryam din a daren jiya,
Gida baba ya koma ya gyara shiryawa ta re da zuwa gurin, wani aminin shi malami ne,
Malam na, Ngaski, inda yai yan abubuwan su na malamai,
Daga karshe ya danyi rubutu yasa a cikin wani leda yace abata tasha zata samu barci,
Hakan akayi kuwa don dai maryam din ta samu barci sosai har da kuma zafin da jikin ta yayi duk ya rage,
Sai zuwa kusan la,asar tasamu tadan mike, ruwa ta watso a jikin don takara jin karfin jikin ta,
Bayan ta dawo tasamu anty ta hada mata abincin ta ,
Saida tai sallah sanan ta samu guri ta zauna tafara dan tsankwaran abincin a hankali,
Mafarkin da tayi ne yafado mata a rai irin yadda tai ta gudu acikin wanan bakin daji,
Siffofin wa yan nan miyagun namun dajin da tagani su yo kanta yasa ta saurin zabura da karfi tankar a lokacin ne abin ke faruwa,
Anty ce cikin fadar Wa,iyazu Billah, maryam ki dinga karanto addu,a a bakin ki pls,
Hakan yai daidai da shigowan baba gidan wanda yake dauke da wani bakin leda a hannun shi,
Anan ne yadan murmusa yace Allahu Akbar watau duniya abin tsoro ne Dije,
May Maryam ta tarewa mutun da har zai sata gaba haka yarinyar da naga bama fita takeyi ba,
Karbi wanan maza bata tashanye kuli guda gaba daya yanzu ta, shafa sauran ajikin ta,
Dayan kuma da dare idan zaku kwanta sai ki bata Allah ya kyauta,
Duk sukace amin alokaci guda tare da karban kullin suna budewa
Mahaifin nasu ya dan kalli yar tashi wace take hankali a tashe duk ta wani ramaywa a lokaci guda,
Yadan gyada kan shi alamar takai ci acikin zuviyar shi fam,
Addu,oin tsari ne ya kara nanata mata idan zata kwanta tare da cewa insha Allah zata daina ganin abinda take gani, kuma Allah zai kare ta daga duk wani maisheri,
Daga haka ya mike zuwa yai madu sai da safe,
Yusuf wanda yake masaukin shi zaune ga abincin da aka kawo mai ya sa agaban shi amma yakasa cin komai,
Tunane duk ya addabi zuciyar shi kamar yai ihu ko zai samu relief a lokacin,
Sakon da Sonny ya kara turo maine akan zancen yana son musulunta am.a sai idan Yusuf zai bar mai maryam a matsayin gift din shi na shiga musulunci,
Wani irin nisawa yayi tare da runtse idon shi da suka kada mai sukayi jajir alokacin,
Kara bude su yayi inda ya kurawa labulen dakin ido kamar mai son gano wani abu a cikin dakin,
A gaskiya yana son musuluntar Sonny do min wani babban jahadi ne a gare shi,
To kuma ya zaiyi da dakon son maryam da yakeji tun tana yar ficiciyar ta,,
Wanda sai a yanzu ne ya gane cewa So ne yake mata shi yasa yake kin duk wani al,amari na,ta a wancan lokacin,,
Idon shi yadago ya bude inda yaci gaba da nazarin shi akan abinda ke damun shi,
Ya san halin Sonny sosai yana daga cikkin ire iren mutane yan son rayuwa wa yanda sam sukan manta da akwai mutuwa,
Gashi kuma matashi ajin farko masu fada aji a kowani, kasa,
Duk inda suka kyalla ido suka ga mace har sukaji suna son ta tofa sai sun lasa suke iya kyale ta,
Wani irin kishi ne mai karfi ya tukako zuciyar Yusuf saboda tuna kowa ye Sonny din da yayi,
Maryam din ce ta bashi tausayi a yadda yake ganin cewa duk laifin shine da ya kawo shi inda take,
Inda zuciyae shi tai dan sayi shine tunawa da yayi da kowace ce maryam din,
Shi kadai ya murmusa don sanin kowace maryam din dayayi da sanin halaiyanta,
Maryam yarinya ce da tasan ciwon kanta, wace abin duniya bai taba tsone mata ido,
Ga tada kau da kai ga abin mutum don shi duk iya sanin da yai mata bata taba cewa tana son wani abu agurin shi ba,
Ire iren wanan tunanen yai tayi kala kala inda daga karshe ya yanke shawaran, abinda ya dace yayi akai,
Jiki ba kwari haka ya mike daga gurin da yake zaune saboda shawaran da ya ke ganin itace kawai mashi mafita,
Ya hana shi sukuni a zuciyar shi don haka wanka ya fada ko da zai ji sanyi a zuciyar shi,
Ga abinci a gaban shi amma sam yakasa koda spoon guda, ne saboda irin yadda yake ji, a zuciyar shi,
Dan tsohon da ya taimakane ya fado mai a rai saboda yana da bukatan yayi ko ya jikin nashi
Kira na biyu aka daga wayan da sallama bayan ya karba ne,
Yagabatar da kan shi a gare su nan da nan suka sheda shi,.
Godiya suke mai shikuma yana kokarin tambayar su lafiyan tsohon su,
Nan dai yai masu alkawarin cewa zai dawo ya ziyarce su zuwa gobe idan ya rarage abinda yakeyi,
Maryam tana zaune duk tunanen rashin jin muryan Yusuf kwana biyu da batayi yana daga cikin abinda ke dan damun ta,
Bata san may yasa ba yanzu take yawan jin shi a jikin ta fiye da tsan manin ta,
Muryan Anty Dije ce taji a kan ya tana tambayar ta Maryam lafiya dai ko ?
Bakomai tace wa yar nata,
Bakomai nagan ki haka a zaune cikin damuwa maryam,?
Yar mursmuhin mai kama da yake ta sake kawai,
Kodai Yusuf kike tunane tunda naga jikin ki dai kin ji sauki yau,
Mamaki ya cika maryam din don jin abinda yar nata tafadi,
Kai tagirgiza tace haba dai Anty may zan yi tunane gare shi,
Anty dije wace bawai ta yarda bane tace bam san may yasa wayoyin shi suke a rufe ba,
Duk layin shi nakira akashe suke tun jiya da safe,
Don haka nima ina tunanen ko lafiya yake amma barin kira Jibrin muji,
Jibrin din ne ke sheda ma su cewa yatafi kano gurin wani meeting ne amna zuwa gobe zai dawo Insha Allah,,
Sai alokacin maryam tai dan ajiyan zuciya har yar nata taji,
Amma sai bata ce mata komai ba wucewa kawai tayi zuwa cikin gida abin ta,
Gurin da take zaune tadan kai kwance anan barci ya dan kwashe ta, batare da tasani ba,
Anty Dije wace ke kitchen tana tuka tuwo muryan maryam dake barci a falon ya katse ta daga tukin tuwon da takeyi,
Wani irin kakakari da shure, shure takeyi kamar wace ake zarewa rayuwar ta,
Sosai Anty Dije ta razana saboda ganin yanayin maryam din, a lokacim,,,
ZEEE MAKAWA YELW@
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
8β£2β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Ina rokon Allah ya nuna mu na, wanan Watan mai Albarka da Darajja, Ni,ima Gafara da Rahama,
Ya Allah ka sa damu da Albarkokinan na shi, lafiya RAMADAN KAREEMπππππ
AMEEN YA ALLAHπππππππππ
A gajiye yake taka matakal ginan ya na saye da rigar shadda mai ruwan makuba
Dinki rigar iya cinyar shi kawai da yar gutunwar hannu daidai gwiwar hannu,
Saboda zaman da yasha gurin meeting din starching rigan yadan takure , takure,
Kan shi babu hula sai sheki da yakeyi yaji oil ga kamshi,
Hannun shi guda yana a cikin aljihun shi da sauri sauri yanzu yake tafiya don ya isa gurin motar shi,
Tundaga nesa ya bude motar yana isowa yashiga,
Fuskan shi ya shafo da hannushi yakara mayar wa har zuwa wuyar shi wani iska yafurza tare da fadin Ya Allah,
Yana daukar waya kiran anty dije yana shigowa mashi,
Sai a lokacin ya dan yi ajiyar zuciya a irin yadda yake ji, a zuciyar shi,
Sallamu Alaikum Anty Sorry zan kira ki dan anjima kadan pls, ina saman hanya ne,
Bata aje wayan sai fada data haushi dashi cewa zai kashe waya haka har kwana biyu,
Murmush mai sauti ne yadan sake saboda yasan cewa shi mai laifi ne sosai,
Don haka yace gwiwa na a kasa Anty aimin afuwan pls,
Kwanar asibitin da yanufa don diba tsoho ya karya batare da wani dogon tafiya ba ya isa asibitin,
Tsohon yana kwance saida hannun shi guda yana daure da ruwa ana mai kari,
Dan tsohon najin muryan Yusuf ya yunkura da niyar tashi,
Gaba daya har Yusuf din suna hada baki gurin cewa ,a, a, a baba ka kwanta da ruwa a hannun ka,
Tsohon yakoma ya kwanta yana cewa to, to, yana mai gyara