Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
dauke da wani dogon riga baki mai kyau da kuma rigar barci irin ta matan turawa,
Wanda da kasa zai iya baiyanawa mace tsiraicin ta,
Turare kusa kala biyar sai kuma wani dan kit mai dauke da dankune da sarka,
Sai kuma kudi dollar's na America, sabbi ful da su suka zubu a cikin wani dan takarda,
Duk kan su mamakine ya cika su don ganin wanan irin kyautar na bajinta da Sonny yai masu,
Duk kan su sun rasa bakin magana saboda yawan kayan da tsadan su,
Anty Dije ce ta numfasa tace a karo na farko tunda suka bude kayan kwasa ki samin a leda safiya har Yusuf ya shigo,
Daga haka suka,watse kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi,
Gurin mahaifin Yusuf din suka fara zuwa wanda yai mamaki kwarai daganin Sonny din a gatin su,
Saboda sanin da yayi ko waye mahaifin Sonny din dakuma sani shi kan shi Sonny din,
Sosai yaji dadi yai kuma alfahari da ganin su atare da dan nashi,
Abin sha yasa aka kawo masu amma sam Yusuf ko ruwan su bai taba ba,
Sai mai faman danne dannen wayan da yake yi abin shi,
Shi dai Sonny din ne ya tatuli giyan shi sosai ba tare da wani buguwa ba,
Bayan sun dan dauki lokaci a tare da tsohon ne inda yake bukatan Sonny da yadan ziyar ci church din su don special prayer,
Ba wani mussu Sonny din yace zai yi kokari yazo kafin ya koma,
Da haka sukayi mai sallama inda yake tajin dadin a cikin rayuwar shi,
Zaune suke su biyu a falon shi Yusuf din sai TV dake ta kara shi kadai,
Kowan su da abinda yake faman yi a cikin systems din shi,
Sonny wanda ya kasa shakat da,samun sukuni a cikkin zuciyar shi tun ganin da yaiwa maryam ya dan yi gyaran murya,
Wanda hakan yasa Yusuf dan dagowa daga abinda yakeyi ,
Ya dan wani marai,raice muryan shi yace pls, Joseph ,
Ina son ka taimaka min duk da nasan cewa abune mai wuya agare ka yanzu,
Don nasan muna da bambancin addini, but idan har ka iya la,akari da cewa wanan ba komai bane Just life ne,
Nasan cewa zaka iya taimaka min, for a few times,
Yusuf wanda ya tattaro hankalinshi yana sauraron Sonny din don jin ko may yake da bukaya agurin shi har yake mai haka,
Don shi azaton shi Sonny yafi karfin ya bukaci abu agurin shi bai samu ba
Tambayan shi yayi cikin karaji da cewa just go a head tell me whay you want,
Saida yadan lashe bakin shi sannan yakai kallon shiga kwaya Idon yusuf da idon shi da suka kada sukayi jawur,
Yace I just want you to barrow me that your fiancée,,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
8⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Cikin wani irin zafin nama, Yusuf ya dago kan shi yakai wa Sonny kallo,
Idon shi sunkada sunyi jawur kamar garwashin wuta,
Sai kalman Innalillahi ya ke iya mamaitawa,a cikin zuciyar shi a lokacin,
Ji ya,keyi tankar, yai tako guda ya,shake Sonny din har lahira,
Kirjin Yusuf har wani irin bugawa yakeyi ya rasa ma awani duniya yake duk idon shi ya rufe a lokaci guda bai ganin komai,
Kalman nan ta Innalillahi da ta zauna mai a baki, itace yake ta nanatawa a cikin zuciyar shi,
Sonny wanda sam bai kula da irin halin da Yusuf din ya shiga ba alokaci guda,
Yusuf yadago kai da niyar yiwa Sonny din wani irin mugun zagi,
Amma sai Sonny din yace "Yes, cikin irin nuna ko in kula din nan,
Yusuf yakara jin wani irin tukukin zafin rai ya taso mai tankar ya make bakon nashi mai halin Dan Akuya,
A hankali Sonny ya,furta I really want to meet her again,
I want to ask her some question a bout her religion,,
Yaci gaba da ce tace gaisuwa da shi addinin ta ya hana don haka yake son jin karin bayani,
Saboda yasha gani others Muslims girls suna sharking din hannu da su,
Sai a wanan lokacin Yusuf da ke jin kan shi tankar wani namijin zaki yadan ji sassauci a zuciyar shi,
Kan shi ya dukar kasa tankar badashi Sonny din ke magana ba a lokacin da irin yadda yake ji,
Sai zuwa yan mintuna,masu yawa Yusuf yace cikin dasasshiyar murya,
Aiko da baka gan ta ba ni zan iya yi maka bayanin abinda kake nufi,,
Sonny wanda bai so jin hakan ba don shi maryam din ce yaso taimai wanan bayanin da bakin ta,
Sai da ya dauki cup din ruwan sanyin dake gaban shi yadan kurba a hankali,
Sai ya dan ja numfashin shi kadan yace wa Sonny kamar yadda kasa ni cewa duk wani addini bai yarda mata da maza su dinga cudan ya guri guda ba,
Sonny din yadan ce Ok,
Yusuf yaci gaba da bayani ya ce mai Allah ubangiji ya umurci, Annabin rahama, da ya hani mata akan cudanya acikin maza,
Su zauna a dakunan su su yi ibadan su,
Sannan su boye tsiraicin jikin su ga kowani irin namiji,
Hat ta muharramin su ba ayarda yaga wasu sassan jikin su ba idan bada wani dalili ba,
Sonny yana kada kai yace, Ok,
Yusuf yaci gaba da maganar shi yana cewa don haka kaga ashe duk macen da kaga tana hurda a cikin mazaje, ta kaucewa addinin ta, ne, tana bin ra,ayin son zuciyar ta,
Yakara da cewa duk diyan musulmuz jai mata ana haihuwan su tare da wanan sunnan a cikin zuciyar ta,
Sonny wanda ke ta sauraren shi tunda yafara bayani,
Yai wani irin numfasawa, saboda sharhin da Yusuf ke mai akan kamun kai na "ya mace,,
Yace to duk mata daga mata har har tsofaffi da yan mata,
Yusuf wanda yakara kai cup din ruwa a bakin shi ya kada mai kai yace eh, hakane,
Wow inji Sonny din wanda ke wani lumshe idon shi don jin abin mamaki daga gurin abokin shi,
Gani yakeyi Yusuf din ya jefa kanshi cikin addinin da babu freedom ko kadan,
Don may za,a ce har yara kanana irin su maryam basu da freedom din rayuwar su,
Baiko karasa,saurare ba wayan shi tai kara hakan yasa suka watse daga hiran da suke yi,
Wanka yafito yana daure da dan karamin towel,, a jikin shi sai dan karami da yake goge ruwan da ya kwanta mai a suman kan shi yake dan tajewa a hankali,
Kamar wanda aka sawa tunane a cikin rayuwar ta,
A yadda yake ji yanzu, ko da zai rasa rayuwan shi akan taimakon a addinin shi zai yiwa musulunci hidima so sai,
Dan haka ya karkare shirin shi yana mai aiyana abubuwa da dama,
Wasu dinki ne irin zalekar nan wando da riga masu laushi, da santsi,
Falon gidan ya fito inda yasamu har ankawo masu abinci daga gidan Anty shi,
Shima Sonny din a cikin shigar kanan kaya yafito daga dakin da yake yana saye, da, wani dan farin glass a idon shi,
Gaba daya saman dining table suka nufa don su ci abinci sun fara bada wani dadewa ba sai sukaji,
Sallama a bayan su, koda Yusuf bai juya ba yagane cewa Aisha ce da kawar ta,
Cikin wani dinkin buje da riga na shadda kowacen su take,
Dinkin ya wani matse masu jiki duk ya fitar masu da suran jikin su,
Nonon su duk ya wani turo kamar a fili a gaban rigar, da suke saye dashi,
Sonny wanda don burgewa baiko iya kauda idon shi a kan su,
Har zuwa lokacin da suka karaso gurin da su ke zaune,
Aisha ta taso gadan gadan da niyar zuwa ta rungumi Yusuf,
Cikjn wani murya mai kama da ta tsohon soja ya daka mata tsawa,
Cak ta tsaya guri guda tana mai wani shu,umin kallon,
Cikin muryan shagwaba tace mai haba Joe, may ye haka dan Allah,
Yaushe rabon da in gan ka ne wai pls ?
Da har zaka hanani hugging naka,
Takara she maganar kamar wata yar karamar yarinya,
Hey, girls' inji Sonny inda yake kokarin nuna masu seat, don su zauna,
Wani irin mugun zama suka yi sun wani turo boom din su baya yai wani tare kaman kayan wanki,
Nonuwan su ya wani turo gaban riga kamar yan matan clubs,
Yusuf wanda sam bai kaunar ya kara daga kai ya kalle su saboda sun bala,in zube mai a fuska har zuciyar shi,
Suna wanan betsere, betseren suna wani jan ra,ayin maza,
A gaban su Sonny yake tambayar Yusuf cewa su wayan nan yan matan addinin su daban ne da na su maryam ko ?
Yace cikin rashin fahinta yana nuna hakan da hannun shi,
Duk da sundan fahinci may yake nufi hakan bai hana su ci gaba da shakiyancin duniyan da suka sa gaba ba,,,
Nan suka kare, watsewan su inda Yusuf yagaji yai masu kora da hali sosai amma sai Sonny wanda yaji dadin kasan cewa dasu yai masu alheri irin ta bajin ta, din nan,
Fita sukayi inda suka fara nunawa Sonny cikin gari,
Jibrin kusan shine mai yiwa Sonny bayani akan irin al,adun kowani culture da yake tambayan su akai idan ya gani,
A gajiye suka dawo gida don haka sallah kawai Yusuf yayi ya haye gadon shi daniyar ya kwanta ya huta amma sai yaji sam ba zai iya ba,
Batare da yaji muryan maryam din ba,
Hello little mummy, yawani shake muryan shi tankar dan yaro,
Maryam wace a lokacin tana zaune gaban mirrow dake dakin nata tana dan shafa mai a jikin ta,
Ta sauke wani lalausar murmushi wanda har Yusuf din yaji shi daga inda yake,
Sai da hakan shima yasa shi yadan lumshe nashi idanuwan a hankali,
Ya gajiya uncle maryam din ce take tambayar shi a hankali cikin nuna kulawa,
Bari kawai maryam wanan bakon nawa duk yasa ni gajiya wallahi,
Komai sai ya kwankwance shi kamar tsohon bature, ko likita,
Tausayin shi maryam taji a irin yadda yai magana,
A hankali tace mai kasan ance bakon ka Annabinka so kayi hakkuri dashi har lokacin da zai koma,
Jikin shine yai sanyi a irin yadda maryam din tai bayani kuma gaskiyane zancen ta,
Sai a lokacin yake tambayan ta Anty Dije, wace, ke ta faman tambayar shi tun safe,
Tadan lumshe ido kamar yana ganin ta a fili tace,
Tunjiya da muka dawo take ta tambayar ko yaushe zaka shigo ,
Yanzu haka tana falo a zaune nasan kuwa kila kai take dan jira agurin,
Ya Sallam yace wallahi maryam har na kwanta saboda gajiya,
Gashi kuma naji ido na kekas don rashin barci, saboda gajiya,
Gabobin jikina sai ciwo suke min kamar nayi wani aiki mai yawa
Cikin wani irin kararan murya tace Allah sarki, idon ta nan da nan yai kamar ya kawo kwalla,
Tace cikin kariyar murya kamar ta mai kuka uncle kasha magani ko?
Bawai magani zan shaba ai da ace zan samu wanda zai mun dan taushe a hankali , a hankali da kila bazan kara ko minti biyu ba zanyi barci,
Kai uncle inji maryam cikin wani irin murya mai nuna tausayi maryam tace,
Kasha magani za ka rage jin pain din da zaran ka sha,
Maryam yakira sunan ta cikin wani irin murya yace,
Nidai fatana Allah yasa baba ya idda nufin shi akan mu batare da ya canza shawara ba,
Runtse idon ta tayi daga i nda take tana maijin kunyar abinda yafadi yanzu din,
Kamar yasan abinda takeyi yace, Yes, ina son duniya ta sheda cewa ke din ce mata, ta halas,
Sai kuma yadan ma rai,raice muryanshi ya ce maryam kiyi hakkuri ki rike Yusuf dinki amma,
Ki gwadawa duniya cewa Furen Juji dane kamar kowa,
Addini bai ce a kyamace shi ba kamar yadda wasu ke ikirarin hure maki kunne akaina,
Hawaye ne masu dumi suka zubo a idon maryam din,
Nan da na ta ringa she,shekan kuka kamar ya fada mata wani magana na daban,
Dif ya kashe wayan shi saboda ba zai iya sauraron wanan kukan da maryam din shi ke yi ba a yanzu,
Cak ya kashe wayan ya wurgata gefen filon dake saman gadon shi, sai kawai yashiga cikin damuwa,
Tausayin rayuwar su yaji da shi da ita maryam din ,don yasan cewa tayi hakkuri sosai tayi biyayya ga mahaifinta,
Rayuwa abin tausayi ce gare su shi da maryam sam bai taba tunanen cewa zai so wata mace irin yadda son maryam din yashige shi haka a lokaci guda,
Tafe a motocin su sun fito wani kauye kallon wasu irin shanaye da Sonny din ke so,
Yusuf sai sauri yakeyi don su karasa wani kauye mafi kusa don su samu sallah jumma,a,
A wani massalacin kauye da yacika makil da jama,an musulmi suka parker motocin su,
Don su samu gabatar da sallah su ta jumma,a a garin,
Sonny kawai suka bari a motar inda yake kallo yadda kowa ke sauri don kada a wuce shi,
Abinda ya kara bashi mamaki shine da mai, arziki da talalka duk guri guda suke tsayawa su hada kafadar su,
Har zuwa lokacin da suka idar yana kallo yadda mutane kebawa juna hannu suna musabi,a,
Sai bayan sun shiga motocin su har sun yi nisa ga tafiyan su ne Sonny ya jefowa Yusuf tambaya, cewa,
Yaga duk guri guda suka tsaya sai mutun guda dake a gaban su,
Tokin motar shi yake yi a hankali batare da yace mai uffan ba,
Sai da suka danyi nisa kadan kamar ba zai yi magana ba sai yace wa Sonny din batare da ya kalle shi ba,
Addinin mu addini ne mai bawa kowa yancin shi batare da nuna bambanci ba ga komai,
Sonny din yace O, I See,
Harzuwa lokacin da suka kai cikin gari a gajiye daboda nisan kauyen da suka tafi,
Inda Sonny din yai ta hotuna da shanaye da fulanin rugan
An kai shi gurin wasan dawakai inda Sunny din duk yarude saboda yadda yaga dawakai lafiyayyu sun koshi sai harbin iska suke yi,
Washe gari ranan Sunday aka kaishi Church inda mahaifin Yusuf tare da, sauran members suka ji dadin zuwan shi gurin su,
Yai masu kyauta ta bajinta inda sukai ta ihu suna cewa praise the Lord,
Tare da,shi suka kwashi rawan su a wanan satin inda shi bawai abinda sukeyi ya damay shi bane,
Sai Sonny yafidda rayuwan cewa zai kara ganin maryam kafin yabar garin ,
Don ya fahinci Yusuf bai ra,ayin haka a rayuwan shi sam, hakan yasa shi fita zancen kwata kwata,
Duk da yaso ace sun wuce batare da ya kai bakon nashi gurin Anty nashi ba amma sai yaga rashin dacewan hakan,
Hakan yasa shi biyawa dashigidan bayan sun dawo wani kauye wurin kallin yadda suke noman su a,local, way ,
A kofan gidan suka dan tsaya inda yusuf yai ta rafka sallama sai zuwa can yaji muryan matar gidan ta karba mai,
Kusan a tare suka shigo su uku gidan shi da Sonny da Jibrin,
Anty ce ta tare su cikin kwaliyan wasu shadda kamfala dake ajikin ta,
Sam maryam bata,san da shigowar su ba tana saye cikin dinki atamfa buje da riga da,sukai mata dagwas a jiki,
Yusuf naganin ta ahaka wani irin kishi ya ziyarci zuciyar shi ya rufe mai idon shi,
Saidai bai bari sun fahinci halin da ya ke viki ba saiyadan basar da hira da antyn shi,
Shiko Sonny yana ganin maryam sai ya shiga washe baki yana mai kokarin jan ta da hira,
Sanin halinta ya dan sa Yusuf sake dan jikin shi don yasan irin hanlin miskilancin maryam din,
Dan wake da mai da yaji sukayi don suci don haka,shima Sonny ya zauna ya kwashi wanan girkin har yana akaro mai,
Sai kuma daga baya hira so sai sukayi indayake tambayar su akan musulunci su dan bashi bayani,
Banda Yusuf wanda ke charting da maryan a lokacin,
Yana fada mata irin yadda yaji lokacin da suka shigo gidan,
Sonny ya koma bayan irin dibin alherin da yaiwa mutane taban mamaki,
Bayan yakoma sauth korea ne Yusuf yai mai waya don yaji ko ya sauka lafiya,
Anan suka dinga hira sai kusan karshe ne Sonny yake cewa Yusuf ai tun da yadawo zancen da sukaui na cewa ya canza addini zuwa ta islama gaskiya yashiga zuciyar shi,
Yaji kuma zai koma din amma on one condition zai koma,
Yusuf cikin jin dadi dafarin cikin jin cewa Sonny zai shigo Islama yace ,
Yace cikin karagi ya fada mai ko manene wan condition din,
Sonny yace yana rokon shi alfarma da yabar mashi maryam ya aura, don ta taimaka mai gurin fadakar da addinin shi,,,,