Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
ba takama hanyar zuwa dakin takawai tana mai share hawaye,
Tukin mota yakeyi amma hankalinshi na ga magganganun da sukayi da safe a gidan Anty Dije,
A hankali ya shafa fuskan shi da tafin hannun shi,
Inda ya hade wasu miyau masu daci da suka tsaya mai a bakin shi,
Har ya isa garin Abuja maganar taki fita mai azuciyar shi,
Bai huta ba ita kuma maman Choima ta haushi da fada akan cewa ya cuce su da ya aurawa Ibrahim da Naimat,
Don may ya musuluntar da ita batare da sanin iyayyen ta ba,
Dukan shi tsohuwar ta shigayi da hannun ta bibiyu tana mai yin kuka da ihu,
Ganin zata iya bata mai lokaci ya sa shi janta a hankali zuwa dakin ta inda ya zaunar da ita a hankali saman gado yana mai ce mata ba gaskiya bane,
Tace mai ai Samuel ya zo bayan baya nan yake sheda mata abinda ke faruwa,
Sai da ya samu yadan lalabata ya wuce zuwa dakin shi,
Rigar dake ajikin shi ya sabule gaba daya tare da jefata saman gadon shi,
Shima fadawa yayi tare da lumshe idon shi yanamai karanto Subbahanallahi, Walhamdullahi Wallahu ,Akbar,
Har zuwa lokacin da yaji zuciyar shi tai mashi sanyi,
Sannan ya mike zuwa bathroom don yadan watsa ruwa, ko zai ji sanyi a rayuwar shi irin yadda yake ji,
Sai bayan ya fito ne yana,saye da wata jallabiya mai ruwan milk, colour,
Yana dan goge ruwa a kan shi wayar shi tafado mai a rai,
Sai a lokacin ya tna cewa yasa ta a silent tun yana hanya,
Da sauri yadauko wayar yana dibawa, kirane kusan talatin da wani abu,
Inda akasarin su duk kurane daga anty Dije sai kuma sauran friend's da abokan aiki,
Kiran karshe dayagani shi ya bashi mamaki don sam bai yi zaton ganin kiranta ba a wanan lokacin,
Ba kowa bace illa maryam da mamaki yake kallon sunan nata yana mai tambayar kan shi ko may take so dashi har takira shi,,
Wayan ya ajiye inda yanufi gurin da sallayar shi take yana kokarin shimfidawa,
Karar wayar shi ce ta katse shi a lokacin don ya mai da ita da karar ta,
Anty yagani rubuce a screen dinwayar tashi alamar itace ke kiran shi,
Dauka yayi amma sai ta haushi da masifa tana mai cewa ina ya shige haka tun da safe take neman shi bata samun shi,
Nan yake sheda mata cew yana Abuja kada ta damu,
Cikin kwantar da murya tace Abuja Yusuf ?
Abuja ka koma baka fada muna ba may yafaru Yusuf kawuce yau ba sallama haka,
Murmushi yai mata a karo nafarko yau tun xa gari ya waye mai,
Yace ba komai Anty tafiyar ce kawai ta riskeni a haka,
Shirune yadan biyo baya batare dakowa yai magana ba daga cikin su,
Kashe wayan yaji tayi abinda bai taba faruwa ba ke nan a tsakanin su,
Yana kashe wayar kamar hadin baki kiran maryam na shigowa
Amma sai ya share kiran nata kawai yatada sallah shi abin shi,
Ya dade a zaune yana lazumi inda yake ta kai kukan shi ga Allah akan Allah yai mai mafita, da kuma zabi na alheri a rayuwar shi,
Ya mike don ya kwanta ko zai dan samu barci yadan huta,
Ya kwanta kamar minti biyar yaji kira ga wayar shi kokarin kashe wayar yakeyi a daidai lokacin da yaga sunan maryam again a saman wayar,
Kamar ya share ta saidai yadaure ya dauka saboda time din da agogo ya nuna mai nadare,
Muryan taji a cikin wani yanayi tana mai ce mai hello,
Inda shima ya karba mata da cew wa,alakissalam,
Sai kuma tai shiru batare da ta furta komai ba,
Idon shi yadan rintse don wani irin abu da yake ji yana taso mai a zuciya,
Yana niyar kashewa ne yaji muryan ta tana cewa Uncle dan Allah ka taimaka min agurin baba ka fada mai gaskiya cewa ba soyayya atsakanin mu ko kadan,
Yanajin tafafi haka yakatse wayar tashi tare da rufe layin nashi yana mai runtse idon shi da suka kada sukayi ja,alokacin,,,,,,, l
SEENABU ZEE MAKAWA YAURI KEBBI STATE,,,
[4/6, 23:05] Anty Lantana: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
6β£8β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
IYYA KA,NA ABBUD WA,IYYAKA NAS,TA, INN,,
Dan Allah dai jama,a kuyi hakkuri dani saboda lokacina ne nake batawa ina faran ta maku rai dashi,
Bawai dole yadda mutun yake so zai samu ba,
Kuyi min Uzuri pls bawai magana daya nake ta fadi ba yadda labarin yake ne na,ke yi,,,,
πππππππ
A,A ne zaune a gaban kanin mahsifin shi suna magana acikin na,tsuwa inda yake sheda mai cewa ya gama kammala duk wani abin da yadace da ake bukata,
Ba musu kanin mahaifin nashi wanda ke shugabancin al,amarin shi.
Sai yaron duk ta bashi tausayi don shi da a ce ya na da hali ne shi da kan shi zai wa yaron alheri, da duk wani harkan auren shi,
Mutumin yace wa A,A din zai yi magana mahaifiyar shi, don ya shawo kan ta,
Da haka sukayi sallama ya bar gidan kanin mahaifin nashi,
Bai wani nisa da tafiya yakira maryam yana sheda mata cewa cikin satin nan za,a kawo lefen insha Allah,
Duk irin yadda tayi kokarin boye farin cikin ta A, A sai da ya gane har yaji tausayin su ya kama saboda irin yadda suke son junan su
Amma ga mahaifiyar shi tana kokarin raba su a lokaci guda saboda son rai,
Maryam batai kasa a gwiwa ba ta sheda ma yar uwar ta abinda ake ciki,
Maganar Anty Dije ta saurara amma tasan cewa ba wai lalai ne hakan ya yuwa ba,
Don haka sai bata dauki zancen da wani mu,hinmanci ba kawai sai ta share zancen, batare da ta fadawa kowa ba,
Kwana kamar biyu da zancen wanan kanin mahaifin na A, A ya samu mahaifin Maryam, tare da wani dan uwan su akan zancen,
Inda baba ya sheda masu cewa subari sai ya ga yarinya tukun,
Daga haka kawai,bai kara wani zamce ba amma sai may kamar sati guda da magana da wani yammaci sai ga mata dauke da akwatina, har guda uku da kit din su,
Abin ya bawa anty dije mamaki kwarai da gaske, a inda ta aika makwabtan su akakira mata wata kawar ta,
Matan sai wani yatsinar fuska suke yi kamar masu jin wari ko ka,zanta,
Da farko ita Anty Dije bata so ta karbi kayan ba don bata da masaniyar komai akai,
Amma sai wanan kawar na ta tace mata su karba ba,a haka, nan, alheri baizo ma a gida ka kore,
Ba wasu kudi masu yawa anty ta bazu tukuici ba saboda rashin sanin zuwan su a lokacin,
Su ma dai ana su bangaren su fita da,sunan Anty Dije a bakin su kan cewa ba masu wani taron arziki ba,
Can suka koma gidan suka samu shi A A din kowace daga cikin su da nata abinda tace mai akan wai bai samu diyar gidan mutunci ba,
Ga su diyan tallaka am.a suna ma mutane kallon rainin hankali,
Duk maganganun da,suka fadi a gamay da maryam din zu zafe shi a zuciyar shi,
Saida bai ce masu komai ba sai sauraren su da ya dinga yi a lokacin,
Amma yana barin gurin su ya sa waya ya kirata sai abinda bakin shi yaraga mata yana cewa wai an wulakanta mai yan uwan shi
Ita ko maryam sai hakkuri take bashi tana cewa gaskiya basu fadi daidai ba saboda tasan cewa ba halin Anty Dije bane haka nan,
Don haka sai ma taga cewa shi ai bai ga laifin nashi ba sai yar ta kawai, kashe wayan tayi tana mai mugun jin haushin matan da sukai masu wanan mugun kazafin,
Tun wanan lokacin sai bata kira A,A din ba shi kuma haka, dakewa tayi dashi,
Bayan wasu kwanaki suna zaune a tsakar gida saman wata katuwar tabarman roba zaune, suna shan iska,
Kasan cewa garin yau babu wutar ne fa zafi yai masu yawa,
Bayan sallah isha,i zaune take tana lazumi inda yaran Γnty ta ke ta faman damunta da surutu,
Muryan Baban su ne su,kaji a cikin wanan daren,
Take gaban maryam ya tsinke ya fadi. Gaisuwan baba suka fara yi suna mai sannu da zuwa,
Maryam wace bata san ko may yakawo mahaifin nasu ba acikin wanan daren,
Da sauri ta mike zuwa shimfida mai tabar don ya zauna,
Har zata wuce gurin da take zaune da farko bayan ta gama mai
Muryam baba taji yana cewa dakata samu guri ki zauna, don tafiyar ki ce wanan
Turus tayi waje guda tana mai za,zare idanun ta a lokacin,
Kanta ta sun kuyar kasa har zuwa lokacin da Anty ta ta karaso gurin,
Da ga can gefe guda ta dan samu ta zauna tana mai addua acikin zuciyar ta
A hankali ta daga kai ta kalli yar ta wace ke kokarin zama a kusa da ita
Kanta ta maryam kasa don ganin canzawan da fuskokin su yayi a lokaci guda,
Gyaran murya baba yayi kamar kullun idan har ,ai yi magana mai muhin manci
Ya,soma da adduan koran sheda da kuma fatan alheri a gare su,
Sannan Baba ya soma da cewa dalilin wanan kiran shine don in fadakar daku in fada maku abinda ba,ku sani ba yau,
A hankali maryam wace kanta ke a duke ta dan dago ta kalli su anty da baba, sai kuma ta mayar da kanta a kasa,
Baba yace maryam ina son ki saurare ni da kyau ki ji may zan fada maki akai,
Yaron nan dan gidan yan masuga da kikaturo min iyayyenshi,
Kwanakin da su ka wuce, nace su dan dakance ni akan wani bincike da nake son yi,
Kawai tun ban ai,watar da komai ba sai ga zance daga yar uwar ki cewa wai sun kawo kayan lefen su,
Sai kuma baba yai shiru hakan yasa gurin yai shiru kamar ba kowa agurin, a lokacin,
Ina son ki san cewa maryam duk da ban da komai "ya ta ba yar babyn roba bace haihuwar ki akayi kamar kowa ce "ya, dake garin nan,
Hawayen da yake bin fuskan tane tai kokarin sharewa a lokacin
Maryam baba ya kira ta da wani kakausar murya yace mata
Ina son kamar yadda kuka tsara kawo kayan ku ke da shi to haka kuma zaki, kara sheda mai cewa ya aiko wa yanda ya turo su kwashe mai,
Wani irin kuka maryam tasa mai tsuma zuciya inda baba ya ce kaiyya,
Ta yaro kyau take bata karko,
Wanan yaron da na zaba maki bawai na fasa zancen shi ba ne don kin ji cewa nayi shiru,
Duk wani bincike da uba yakamata yai wa mai bidan diyar shi nasa an min tun tuni akan wanan yaron dan gidan na masuga,,
Gaskiya ba zan iya bada diyata wanan gidan ba sam,
Saboda wasu dalilai, da nagano akan su da kuma kwata kwata ni dai bai min ba,
Kara dan sautin kukan ta tayi a lokacin saboda jin hukuncin da baba ya yanke a,kan ta,
Sai kuma ya sasauta harshen kadan yace ke maryam in banda abinki, wanan yaron ai abin tausayawa ne, a gare mu,
Dago kai tayi don jin abinda baba yace tadan kalleshi a cikin mamaki,
Taci gaba da cewa, kowa a garin nan yasan cewa baida gidan zuwa wanda yafi nan,
Yau ai abin kunya ne ace muna nan har ake mai gorin mace,
Wanan kawai bai isa mu wani ishara ba aiko da ace banda "ya ta cikina zan zagaya ko a cikin dangi in samo mai,
Balle gani da ku har ku hudu a gida ke ce kawai ko a gidan nawa zan iya bugun gaba da ke batare da raina ya baci ba,
Shiru yayi na dan tsowon lokaci, kadan sai kuma ya goge hawayen shi,
Abinda ya tayar wa maryam har Anty Dije da hankalo ke nan, suma kukan su ka fara yi,
Baba cikin muryan mai kuka yake cewa sam ban tsanmaci haka ba daga gare ki maryam
Sannin cewa da kikayi bazan iya cutar dake ba a matsayina na mahaifinki,
Idan har akwai wani da da nake so da tausayawa a cikin gida maryam bayan ki ne,
Badon komai ba sai kasancewar baki da uwa a cikin gidan Allah ya taimake mu ni da ke yaba mu Dije a matsayin uwar tayarwan ki,
Cikin muryan kuka maryam ta dago kanta tana mai cewa baba ni bance ba zan yi ma biyayya ba,
Amma wanda kake kokarin hada ni da shi shine duk yan uwan shi kafirai ne Arna
Wa yan da ba su sallah basu kuma da niyar yin ta ako da yau she,
Kafin ta kai karshen maganar ta baba yace kin ko ga idan ki shiga gidan shi kun zama ku biyu ke da shi,
Hakan zai sa ya rage kuncin rayuwar da yake ciki na yan uwa da rashi shakikin abokin shawara,
Anty Dije wace sai yanzu ta gane hikimar baba na wanan hadin da zai yi wa maryam da Yusuf,
Baba yace maryam kin san wanan yaron da dadewa kuma kina da masaniya daga wasu daga cikin halaiyar shi,
Kin ga ke nan abin zai zo maki da sauki don saboda sanin abubuwa da dama dakikayi a kan shi,
Yakare da cewa masu, kinga mu, wanan ne kadai gata da mutuncin da zamuyiwa Yusuf maryam, a irin yadda ya rike mu,
Maryam wace ta dago kai acikkn mamakin mahaifin ta wanda ke tausayawa wani bare bisa ga ita da take yar shi ta cikin shi,
Cikin kuka tace baba niko halin da zan shiga fa idan har an min haka,
Haushi ne ya kama baban don jin abin da yar nashi wace yake tinkaho da bugun gaba da ita,
Batare da ya bata ansa ba ya mike tsaye saboda takaici yana wa wanan shi hukuncin da na yan ke akai, bana son in kara jin komai,
Idan Allah ya kai mu lokacin mun dawo sai mu fara zan ce auren insha Allah,
Daga haka ya fita batare da ko ce madu mukwan lafiya ba kamar yadda ya saba ce masu a kullun,
A,zaune ya bar su kowa jikin shi a mace tun dai maryam wace ke ta sharban kuka alokacin,
Don jin cewa yau za,a raba ta da masoyin ta abin kaunar ta A,A,
Shigowar shi gida ke nan a gajiye daga office da kyat yake dan iya cira kafan shi saboda gajiyan da ya kwaso
Don yau su Alhaji sambo sun shigo garin tun da safe suke zaune a na wasu lissafi akan harkokin business din su,
Saman kujera guda ya samu yazube gaba daya maman Choima wace ke zaune daga gefen shi guda ta wani kalleshi a yatsune ta kauda kan ta gefe,
Saboda wani irin matsanacin haushin Yusuf din da takeji a yanzu,
Yamai da kan shi musulumi yakuma mai da diyar mutane dake zaune a karkashin shi,
Pipkin ne ya sheko da gudu daga dakin da ya fito,
Yazo ya fada mai ajiki yana mai oyoyo da dawo wan uncle din shi,
Rugumay yaron yayi tsam a jikin shi yana mai jin wani feeling akan yaron
Shi har kullun wanan yaron tausayi yake bashi a irin yadda zai tashi ya rayuwa babu mahaifi a tare dashi,
Kara rungumay yaron ajikin shi yayi ya dauke shi cak zuwa saman dining table, inda ya dire shi,
Sai,da suka kammala cin abincin su ya kira Nani din shi taje ta kwantar da shi saboda school da safe,
Shima a gajiye ya haura sama don yadan watsa ma jikin shi ruwa,
Wayar shi ce dake rike a hannun shi yaji tana ruri,
Bakuwar noba ce yagani don haka sai bai dauki kiran da wani muhinmanci ba,
Sai bayan fitone daure da alwala don ka,idan shi ce yin hakan,
A lokacin da yake sallah ya dinga jin wayar ta shi kira nata shiga,
Sai da ya idar yadauko wayan misscall goma sha daya yagani duk da noba guda,
Sai da ya zauna yakira mai wanan nobar da bai san ko waye ba,
Bakuwar murya ce yaji wanda bai san kowaye ba, ya karba mai sallamar shi,,
Tambaya yayi ko waye a layin tare da shi don bakuwar noba ce a gare shi,
Ansa aka bashi a dayan bangare da ce wa, hello don Allah da Joseph Emanuel nake magana,
Murmushi yayi kawai inda ya karba mai da cewa eh dashi kake magana,
Ok inji mai wayar yace kana magan da Aminu ne dan gidan, masuga dake a unguwar jankidi,
Look Joseph ina son sanin inda yaron da Ejoma ta taba haihuwa ne yake,?
Shin macce ce ta haifa ko namiji ina kuma yaron