Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
daga cikin su don yana son suyi wani yar shawara, nobar wayan babban ya basu, wanda uban yace yana koyon sanar Carpenter ne yanzu,,,
Kudi yabashi dubu hamsi yace mai nada wani sati zaiga sako in ya koma,
Sundanyi hira kadan sannan sukayi sallama, dashi suka barshi, cikin tausayawa da irin halin da yake ciki a yanzu,
Ganin wana bawan Allah yasa zuciyar Joseph a cikin wani irin
yanayi, wanda ya hanashi sukuni,
Kasancewar yau jumma,a ne mutane sai haraman zuwa massalaci sukeyi gungu,gungu mata kuma suna gida sun chaba ado kamar sallah,
Gidan รnty Dije ma ba,abarsu a baya ba don daga manyan har yaran cikin kwalliya suke suma,
A,wasu gije har abinci akeyi ta musanman don farincikin da darajan wanan ranan,
A wasu giden masu dan hali kuma zakuga ana ta rabawa yara dan abin sadaka wasu da safe wasu kuma sai bayan ansauko daga jumma,a,
A lokacin da kowa ke ta haraman zuwa sallah jumma,a daidai lokacin ya shigo gidan na Anty,
Wanda a yanzu duk sun saba da irin zuwan shi sun,san cewa inhar yana gari to baida gurin hutu sai guri su
Saboda har cikin ranshi yana son yananyi irin na antyy Dije
Don mace ce wadda tasan kanta dama duk wani wanda yake tare da ita,
Alwala maryan keyi da buta a yar tsakar gidan su inda Assalam ke tsaye wai yana jiran tayi tabashi,
Muryan Maryam din ne ke cewa kai Assalam wazai kaika masallacine wai tunda Daddy baya gari
Joseph yanuna da hannu shi yace da Uncle zamu tafi ma na, ko uncle,?
Yana mai tambayar shi, cikin azama,
Yace mai eh Assalam, tare zamu,
Maryam wace ke kokarin wanke kafar ta ta waiga da sauri takalli inda Joseph din yake,
Muryan Anty Dije ne ke cewa, kai Assalam kabar uncle ya huta pls, kabari har Daddy ya dawo sai ya kaika,
Kuka yaron ke kokarin yi alokacin ciki sauri Joseph yace No, bar shi inkaishi mana anty,
Buta yaron yadauka yafara alwala kamar yadda manya keyi,
Ba abinda ya fadowa Joseph a rai sai zuwan su jereselem, da kakar shi,
Inda sai kayi kusan duk wasu abu da musullumai keyi na ibada,
Gashi Assalam karamin yaro wai har yasan cewa zai gana da ubangiji yayi tsarki,
Muryam Assalam ce takatse shi yana cewa nagama uncle, mutafi,
Ga mamakin kowa mikewa Joseph din yayi yakama hannun yaro
A hanya yaga wasu idon sani yafarka motanisa yabasu yaron yace suje dashi
Ana tasowa suka kawo mai shi yatada mota yajuyo tun ba,a tashi ba,
Kayan su fruit yadan tsaya suka saye a hanya sanan suka karaso gida
Daga Anty har maryam sun matsu suji ya akayi da suka fita, tare zuwa masallaci da,Assalam,
Kayan fruit din suka shigo dashi nikiniki a cikin ledoji ,,
Maryam wace tafito cikin kwaliyar ta ko kallon su batayi a da suka shigo gidan,
Da kanshi ya nufi har gurin fridge ya aje kayan a hankali daidai lokacin Anty Dije ta sallamay tafito, daga daki
Yadda taga Maryam tayi mai sai kawai bataji dadin hakan ba,
Daki ta shige abinta don makada asata wani aikin,
Dakun Anty ta fado rai bace sanan tahau surfanta da sababi,
Maryam ta bude baki da zumar yin magana hannu Anty tadaga mata alamar batason jin komai daga gareta,
Tace baki da hankali ko wayo zance inba wqutaba yazaki nunawa mutumin da ake fatan shiryuwan shi haka a fili,??
Gaskiya ki gyara hali Maryam don kowa ma haka kike masu,
Kada ki kore min jama,a pls,
Maryam batace komai ba don tasan cewa yau ta batawa รnty Dije rai sosai don batai mata fada haka gaskiya,
Murya na rawa tace don Allah kiyi hakkuri anty bazan karaba insha Allah,,,,,,
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
FUREN JUJI
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
1โฃ6โฃ
ZAINAIB IDRIS MAKAWA
Zaune take a bakin gadon da ke cikin dakin su tai tagumi da hannu guda,shiru tayi sai tunane takeyi
Don tunda take da anty bata taba ganin fushinta ba sai yau,
Yau din ma akan wani bare kafiri , wanda ba musulmi ba ma,
Wai may yasa za,a dinga takurawa rayuwan tane haka akan sai ta yi abinda zuciyar ta bai son aikatawa,
Motsin da taji shi ya sanya ta dago kai da sauri don ganin ko waye shigowa, dakin,
Anty Dije ce tashigo dakin tana rike da wani dan ledar mai nuna tambarin shago ajikin shi,
Yar kujerar dake dakin ta zauna a hankali, tana fuskantar yar kaunar nata wanda tun dara bata fito ba,
A hankali Maryam din ta dago kai karo nabiyu takara kallon antyn nata, sai kuma ta sunkuyar da kanta kasa tana kallon kasa,
Cikim natsuwa Anty Dije ta fara magana maryam don nai maki fada yau shine kike fushi,
Kinfi son in barki ki dinga yin abinda bai dace ba ko yau she, ?
Dago kai maryam tayi da niyar yin magana suna hada ido dayar nata,sai kuma ta kasa fadin abin da tai niya,
Indan har kinga cewa wullakanta dan adam na da kyau sai kici gaba,
Tanafadar haka tamike tana cewa sai kizo ki ci abinci in kinga dama,
Dago fuska tayi caba caba da hawaye, ta dubi yar nata tace,
Murya kasa kasa tace nifa ba fushi nakeyi ba anty,
Fuskan Anty kumshe da murmushi tace Allah ya kyauta amma dai gaskiya ki gyara hali duk wanda zo gidan nan sai yai min korafi akan halin nakasa irin naki maryam,
A dan tsorace ko mamaki tadago fuska, takalli yar uwan,
Kuka tajeyi a hankali irin na bantausayin nan tace yanzu anty nice mutane kewa korafi,
A ranan wuni zungur maryam tayi a daki tana ta faman fushi da kowa don har Issalam mutumiyar ta bataga fuska ba,,,
Tunda safe tafito itace farkon fitowa tsakar gida tafara shara da kokarin dora masu abin kari kamar kullum,
Saida anty Dije tagama duk abinda takeyi san nan ta fito waje tasamu yar uwar ta tana
Sun gaisa kamar wani abu bai faru ba a tsakanin su,
A tare suka kara aikin sanan maryam tai wa yara wanka kamar yadda ta saba yi,
Tuki yakeyi akan hanyar shi ta zuwa Lagos gaba daya hankalin shi naga tunanen Assalam
Yaro karami ya iya yin alwala batare da ankoya mashi ba,
A hanya ya tsaya yaiwa kakar shi da Ejoma da suke zaune tare da shi a gidan shi na Lagos,
Tsaraba, a wani dan kauye da ake tsayawa kafin ashiga garin, lagos,
Tunane ya cigaba da yi na yadda zai, yi da mahaifin shi,
Don kwata,kwata baya son zancen kakar su a rayuwan shi,
Wanda shidai a iya zaman su yasan cewa mutumiyar kirki ce ita,
Ya iso gari lafiya saidai yasamu G/ma bata jin dadin jikin ta,
A yadda Ejoma ke fada mai tun wucewar shi kusan sati ke nan G/ma bata jin dadi amma ta hana a fada mai, wai don kada yadamu,
Wanka yayi ko abinci bai tsaya yaci ba tashiryo cikin waso kananin kaya sai kamshin turare ke tashi
Mama dake zaune saman kujera two siter yazo inda take ya zauna asaman hannu kujerar da take yadan rankafo kanshi saman kafadar ta kadan
Yana tambayar ta a hankali ki may ke damun ta sai ce mai tayi batajin komai ita,
Cikin dabara Joseph ya lalaba yar tsohuwar suka tafi asibitin da yake zuwa,
Likita ya dibata da kyau inda yace ba wani abu damuwace ke da munta kawai sai dai yadan rubuta mata yan magananuwa don tasha,
Bayan sun dawo gida dakanshi ya hada mata tea mai kauri ya hada da maganin ta yakaimata,
Zaunawa yayi gab da ita yana dan bata a hankali har tadan samu tasha,
Alokacin yadan mike tsaye da niyar barin dakin don yaje yadan huta, saboda yana tare da gajiya,
Hannun shi mama ta riko da sauri ya jiyo don yasan cewa da magana kenan,
Komawa yayi ya zauna gab da ita saida suna fuskantar juna a wanan lokacin,
Fuskan yar tsohuwar fam da damuwa tace My child something bad wan happen to you,
Joseph yadan kamo hannuta ya hade cikin nashi yana yar murmushi yace,
Mama nothing will happen to me just cool your mind pls,
Tace it ,will ,my son
I see am in my dream,
Dariya yakari yi mata yana mai rungumota zuwa jikinta,
Kalamai masu kwantar da hankali ya ke mata don yaga cewa ta saje zuciyar ta,
A hankali ya mike ya kamata zuwa kan gado ya kwanatar da ita tare da jawo bargo ya rufa mata,
A,hankali yabar dakin yana mai rufo mata kofar dakin,
Saidai may yana fita daga daki sai kuma maganar mama ya dawo mai sabo a zuciyar shi,
Fridge ya nufa yabude yadauko giran ruwa mai sanyi ya dan kwa kwada,
Hakalinshi a tashe don yasan cewa akwai abinda ke damun mama din saidai ba zai so ji ba don shi bai yarda da camfi ba rayuwan shi sam,,,
Maimakon ya shiga dakin shi kamar yadda yai niya sai kawai yasamu kan shi dazama saman daya daga cikin kujerun dake falon,
Yakai wani lokaci a gurin zaune yana tunane shi kadai bakajin karar komai a falin inbada na,urorin daje ta aiki a cikin falon,
Azuciyar shi yake tunane don yasan cewa maganar irin su mama ,g tasu al,adan ba karamar magana bace,
Da wuya su furta bai faru ba, to amma shi gaskiya har yanzu bai yarda da zance tsafi ko kuma wani believe ba can,
Yakai wani lokaci gurin zaune yana iya na,zarin shi akai,
Daga karshe dai ya mike jiki ba kwari ya shige don ya kwanta,
Abakin gado yake a cikin shigar shi ta kayan barci bayan yagama komai, ga irin al,adan yakeyi kafin ya kwanta,
Bible ne rike a hannu shi gwiwowin shi suna kasa kan shi a saman gado idon shi a rufe yafara jero addau,oin da yasaba yi kafin yashiga kwana
Saidai wanan karon ya dan sauya addua,n shi bakamar yadda yasaba ba,
A hankali ya mike zuwa kwanciya saida a lokacin kuma watan shi tai kara alamar sako ya shigo mai,
Samuel ne ke sanar mai cewa Dad na fada dashi cewa anfada mai wai Joseph din yatafi gurin Abdullsamada
Mamaki yayi so sai dajin haka don haka sai yai alwashin cewa daga wanan karon ba zai kara, daukar zance Dad ba na hana shi yin alheri ga duk wanda yaga dama nan gaba,
Abdulsamad wanda ko ganisa mutum yayi bai san shi ba,a da dole ya tausaya mai,
Balle shi da yagirma a gaban shi
Shi agare shi may,ye amfani samun mutun ace bai iya taimaka wa na kasa da shi,
Gaskiya duk abinda zaiyi wanan karo saidai ayi ta don dai shi yayi niyar tallafawa Abdullmalik din,
Da wanan tunanen a zuciyar shi ya kwanta barci sai juyi yakeyi a tafkeken gadon nashi,
Aisha wace tai shawaran zuwa Lagos gurin Joseph
Don dai tagane cewa idan ta cin mai can tafi samun kudi, bisaga in yazo nan garin
Don anan mutane sunayi mai yawa ga bukatun yau da kullun,,,
Saidai tayi rashin saa yace mata aranan ya wuto zuwa kaduna don halartan wani taro da zasuyi akan karin farashin da,suke son yi
Bata hakkura ba don haka kaduna tasamay shi
Saidai yana gurin meeting a lokacin don haka driver ya tura yadauko daga tasha zuwa inda yai masauki,,
Sai gab da magriba yadawo yace ta shirya su, wuce zuwa Abuja yanada uzuri kala,kala acan don haka ba zai samu damar tsayawa kaduna din ba,,,
Waya yakeyi alokacin don haka sai yaga kawai Aisha tana kokarin har hada kayan ta,
Yana gama wayan yakai kallon shi gareta yace, sai naga kamar lokacin sallah yayi ko,?
Bazakiyi sallah ba kafin mutafi, inafa zai fi maki don sai dare nasan zamu karasa,
Tana wani jan kafa kamar bata son yin sallah a lokacin,
Har ta idar yana zaune sai dan,ne danen wayar shu kawai yakeyi,
Duk da bawai yasan ya ake sallah ba yadai fahinci cewa batai wani dadewa ba a gurin yin sallah,
Don haka da mamaki yake ce mata har kin gama ko,??
Don haka mikewa yayi yadauki duk wani belongings na shi dake daki zuwa waje,
Sai cikin dare suka samu isah don haka masaukin shi ya wuce direct, don KB yasan da zuwan shi,
Yasa an gyara komai duk da dai dama gidan kullun acikin gyara yake,
Shikan Joseph suna isa a cikin daren nan fita yayi zuwa gurin wani mutum da yake son gani,
Aisha tun tana jiran shi tana yar tsuki, har barci ya dauke ta, bada sanin ta ba,
Kodo Joseph yadawo yasamu tayi barci don haja ko take away din da ya zo masu dashi batasamu ci ba,
Kiran sallah da akeyi daga wani unguwa wanda da alama ba nisa daga gidan Joseph din shi yata da Joseph din a lokacin wanda dama al,adanshine haka duk wani Christian mai rikon addini yana tashi daidai wanan lokacin,
Don yin morning prayers din su kullun,
Aisha tana kwace shemay shamay saman gado, tana barcinta abinta,
Yar rigar barcin da tasa don daukar hankalin Joseph, har barci ya kwashe ta yadan kware gefen ciyar ta a fili,
Don haka yana fitowa yin burshe, ya isa har bakin gadon inda ake kwance ko motsawa batayi ba,
Yana mamakin wanan irin barci haka ace mutum bai tashi ya yi morning prayer, haka,
Hannu yakara kaimata yana dan dukar cinyar ta data dan kware wurin barci,
Yana cewa baki tashi kiyi salkah kadafa time ya wuce ki,
Sai wani mika takeyi shiko sai kallon mamaki yake mata alokacin
Yaga cewa ai Assalam yarone amma duk yake tare dasu akai kiran sallah
Zakaga yaron na kokarin tashi zuwa yin sallah,
Amma ita gata da girma ta yaga bata damu da ta tashi yi ba,,,
Kallon inda yake tayi ido tafa da kwana, tace mai kabari kawai inda na tashi ai zanyi,
Wani irin mamaki ya kama shi azuciyar shi yana mai cewa O God help me with dis ,
Aisha sallah ma bazaki tashi kiyi ba sai kinga dama,
Haba kiwa kanki fada mana ai dis is bad wlh, abindan lokaci kadan,,
Tai wani mika badon taso ba ta tashi buguzun,bugunzun zuwa cikin bathroom, ko minti nawa bata kai ba saigata tafito wani dan yalalon gyale ta yafa
Joseph wanda yai daidai da gama addu,an shi ya na kokarin rufe Bible din shi ya kalle ta yana mai kada kai cikin mamaki don ganin gyaken da ta yafa wai zatai sallah, dashi,
Kwanciya ya yi rigingine ya kallon yadda take dangwara goshi kamar wace keda wani uzuri ,a gaban ta,
Ba,afi mintuna ba ta sallamay tafado mai saman gado gaba dayan ta,
Kokari takeyi ta fara romancing din shi sai yai dabara yadan jaye ta daga jikin shi yana nai ce mata zan dan fita jugging ne yanzu kafin gari ya haska,
Yajaye daga jikin shi yana mai kojarin daga wa don ya sauka saman gadon,
Sunan shi takira cikin wani irin muryan yaudara idon ta ya canza kalla a lokacin, tana mai ce mai
Wai may yasa kake min haka ne pls ta ya zan bata time dina zuwa gare ja amma kai kullun sai ka kawo min uzurin da baikai yakawo ba,
Tana kokarin kara jawo shi zuwa gareta yai saurin karasa mikewa daga saman gadon
Yana maice mata ki tambaya kiji ni Joseph ba irin wa yan nan mazan bane da kike tsan mani,
Wanan ma da kikaga ina maki just don kada kiga kamar banda,time dinki ne,
Amma tunda kinga hakan ma bai isheki ba
Ya nakai kofa yace pls ki daina zuwa don hakan ma na itmya jamin matsala,
Mamaki da tsoro kalaman shi suka jefata ita Aisha,da mutum nawa ke kokarin kawa gareta ne yau har wani ke fada mata haka,
Inbadon tasan cewa tana moriya dashi ba ko a haka da yagane cewa tawuce wanan kalamin gareta,,,,
Bayanshi tabi da kalllo har yabar dakin cikin shirin zuwa dan motsa jiki,
Hmmm Aisha bata san waye Joseph ba da batai tunanen hakaba daga gare shi,,,,,,,
ZEEE MAKAW
ZEEEE MAKAWA,,,,,,๐๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
FUREN JUJI
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
1โฃ7โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Alhamdullah jerabawan su maryam yafito yanzu ,yaya I,lliyasu ya samo mata guri bi karatu,a FCE kwantagora, inda zata karanta bio,chemistry,
Maryam taji dadin wanan abin so sai ba maryam ba kawai har baba
Don har gida yazo yai ma Anty Dije da mijin ta godiya akan