Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
gwanin ban sha,awa,
Sonny wanda sai yanzu yadan gyara zama don yai magana yace very interests,
How i wish to be there ,
Yusuf wanda tun fara hiran tsakanin Jibrin da Sonny bai ce kala ba,
Sai yanzu yadan gyara zaman shi ya daina rubutun da yake yi a cikin system din shi,
Yadago kai yace wa Sonny din ai sai ya gasu da, idon shi zaigane abin da shi Jibrin din ke nufin da kyau,
Sonny wanda da farko yaso yai magana akai amma kuma sai ya ga cewan hakan, shi ya fi don yagani da idon shi,,,
Sai dai kuma matsala guda ce a gurin shi ba komai ba,
Saboda jin da,yayi cewa da mota zasuyi wanan doguwan tafiyan,,
Shiko tafiya ko a cikin jirgi,ne bai son mai tsawo sosai, don baya son zama da yawa guri guda,
Ga shi kuma, yana jin dadin labarin da Jibrin ke mai na al,adun mutanen kasan Kwantagora,
Don haka yaji kawai zuciyar shi na bashi shawaran akan ya tafi yaganowa idon shi komai,
Sai muryan shi suka ji kawai yana cewa
When are we going there ?
Ba Yusuf ba har Jibrin wanda ba wai ya san Sonny din bane da farko
Sai da yai mamakin jin maganan da ya fito a bakin Sonny,
Yadan daga masu gira irin na gogagun yan duniya yace Yes of,course i want to be there,
Yusuf wanda ke sauraren su duk zancen da suke yi murmushi yayi kawai,
Tun safe take, expecting din wayan shi, amma sai taji shiru,
Tuna ne kiran shi takiyi amma kuma sai tana jin nauyin hakan
Amma kuma maganar da Safiya tai mata akan tayi kokarin cusha kan ta gare ko da bata ra,ayin yin hakan,
Don haka taji wani kwarin gwiwa yazo mata a lokaci guda, na takirashi, kawai,
Bata lokaci tadauko wayan ta dake saman gadon ta,
Dialing din nobar shi hannunta, yayi a lokaci guda taji kiran ya shiga,
Har zuwa lokacin da kiran ya katse batare da an,daga wayan ba,,
Tana kokarin aje wayan ne taji kira ya shigo a na ta wayan,
Sai da tai wani dan murmushi irin da ke makalewa a can karkashin zuciya ,
Receiving ta dan,na bayan dan jan ajin da tayi bata dauka ba,
Assalamu Alaikum ta fadi a cikin wani yanayin murya wanda zaka dauka yar larabawa ce ,
Sai da yadan rausaya kan shi daga gurin da yake kadan , sanan ya ansa mata, sallamar ta,
Idanu a a runste tana jin wani abu na fisganta a zuciyar ta wanda bazata iya fassarawa ba,
Muryan shi takara ji kamar mai mata rada a cikin kunen ta yana cewa,
Hajiya maryam barka da warhaka, ya kuke ya yau ya su anty da Family ta ?
Duk sai taji ta wani rude daga kawai jin muryan shi, da ta yi,
Ya fahinci hakan daga inda yake don haka cikin lumshe ido shi, sai ya kawar da zancen da cewa,,
Kin san kuwa cewa dama ke ce nake jira ki, kirani don in tabatar da zargin da nakeyi a kan ki,
Sai dai kashhii, gaskiya zatona ashr ba gaskiya bane a kan ki,
Muryan maryam cikin mamaki take tambayar shi ko wani zargine yake a kan ta, ?
Cikin kashe murya tankar maryqm din tana agaban shi yace
Ina Zargin Maryam, ce da rashin so na sai dai akan tursasawan mahaifin ta da yarta,
A take taji wani irin nauyi da kuma kunya sun lulube ta saboda abinda yace,
Zubewa tayi akan gadon ta sannan ta lumshe idon ta
Bugawar ta zuciyar tana yi don haka tadan sa hannu tadafe gurin a hankali,
Zuciyar nata kawai take iya sauraron bugawan nashi yadda yake karuwa
Tambayar kan ta tayi may zatace mai daidai da ansar da ya dace da maganar shi ?
Cikin wani irin murya taji bakin ta na ce mai amma ai ance zato zunubi ko ?
Cikin yar dariya irin ta kasai,ta Yusuf yace kenan zaton ki nakeyi da hakan ?
Yafada cikin wani irin murya kamar ba tashi ba saboda taushin ta,
A cikin dabara maryam kau da zance don bata san may zatace a irin yadda take ji, ajikin ta,
Ganin zata kawar da zancen yace a hankali cikin muryan nan nashi,
Baki bani amsata ba maryam zaki kawo wani maganar ta daban,
Murmushi tayi wanda har ya ji shi a cikin zuciyar shi,
Wanda har saida ya lumshe idon shi don jin dadin hiran da su ke yi,
Yace to shike nan tunda bazaki fada min ba amma fa ki sani dole sai kin ansa min tambaya na ,
Maryam wace ta sadad da kai kasa cikin jin kuyan tankar a fili suke hiran,
Tambayar ta yakara yi da cewa "Kin amince ?
Da cewa zaki bani ansar tambaya ta ko,
Kai maryam ta daga gami da cewa "eh, tankar yana ganin ta ,
A cikin wani muryan farin ciki taji yadaki wani abu a gurin dayake ,
Ya ce "Great, maryam ko a haka na gamsu da ansar da zaki bani nan gaba,
Nagode taji yace,
Ba za ki taba regrets a kaina ba insha Allah,
A zuciyar ta karba mai da cewa Ameen ya Allah, tana mai dan lumshe idanuwar ta,
Muryan shi taji kamar a mafarki yana cewa Ina son ki maryam,
Son da ban san lokacin da har haka ya shigeni ba a rayuwata,?
Murmushi maryam tayi cikin jin kunya take cewa ai shi so ba sai an san lokacin shigar shi ba,
Idanun shi yadan kara lumshewa yace Really ? Cikin alamar tambaya,
Tagyda kai ta ce kwarai kuwa,,
Cikin wani irin nishadi da jin dadi suka kasance tare a wayan har zuwa wani lokaci,
Ganin lokaci yaja basu sani ba yasa shi cewa maryam har naji bana son ki ajewa yau,
Dariya tayi mai sauti har saida yaji sh a ranshi yai mamaki kwarai yadda akayi yau tai hira dashi haka cikin sakin jiki
Yau zuciyar shi ya tabbatar mai da cewa ya samu karbuwa agurin maryam, fiye da tsan manin shi,,
Dan Allah kuyi managed da wanan nagaji sosai wallahi jiya nadawo daga gurin seminar,๐๐๐
[4/21, 22:08] Anty Lantana: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
FUREN JUJI
๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
7โฃ8โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Zaune yake bayan sun gama waya hannun shi duk biyu a dukule saman habar shi,
Tunane yakeyi na yadda yau maryam har ta sake jiki dashi suka dan dauki lokaci suna online,
Gaskiya har zuwa yanzu zuciyar shi na bashi cewa akwai dai,
Can kuma sai wata zuciya take tambayan shi a kan may zai damu da ko ma may ye, ma dai oho,,
Don haka kawai sai ya ja wani dogon ajiyar zuciya ya furzar da iska daga bakin shi,,,
Duk wanan abinda yake yi Sonny wanda yazo da niyar ti mai magana ya na tsaye daga kofan office din yana kallon shi,
Karasowa yayi inda Yusuf din yake zaune yadan zagayo ta bayan shi,
Sai da yadan dafa shi sanan yake cewa, Yusuf din,
Ina mamaki irin yadda wanan Baby din ta samu sa,an ka haka,
Idon shi yadan lumshe yai, rau da idanun shi cikin rausayawa,
Ya ce, I really love the girl,
Inji Yusuf yafada cikin lumshe idon shi,
Sai kuma yai wani firgigit ya,dago kai yakali Sonny, ya ce,
But she she is a small girl not More than 20 years now,
What inji Sonny cikin wani irin mamaki ya tambayi Yusuf,
Yusuf yadan gyda mai kai alamar abinda yaji ya fadi gaskiya,
What a surprise, ?
A small girl like dis charming your heart ?
Sonny ya tambaya a cikin mamaki yace, kuma tasan yadda zatai handling din ka,
Dariya kawai Yusuf yai mai ya mike tsaye daga inda yake
Sai da yakai wurin window dake manne da office din yadan tsaya yana kallon motocin da ke sintiri a saman titin dake layin,
Cikin wani irin murya mai amon wani sauti na fahinta yace,
That is good characters in my religion, sai kuma ya juyo gurin da, Sonny yake tsaye yana kallon shi cikin mamaki,
Har gaban shi ya karaso gab da shi har suna iya jin numfashin junar su, kamar zasu yi fada,
Yace she is gift for me from Allah,,,,
Naimat ce tashigo gidan Anty Dije da murnan su kowa ya tare, wanda hakan da akai mata yasa ta jin wani irin dadi a rayuwan ta,
Maryam wace a lokacin tana, ciki bata san da zuwan Naimat gidan ba,
Sai ganin Na,imat, ta tayi kawai gaban ta a tsakar gida,
Itama dai da dan gudun ta ta tare ta suka rungumay junan su cikin jin dadin ganin juna
Naimat din ce ta ture maryam din baya cikin batare tace wallahi maryam nayi fushi da ke,
Kin sani sarai ni ka,daice a gidana Ibrahim baya gari amma ko ki kawo min ziyar haba maryam , banji dadin haka ba gaskiya,
Cikin dan marai,raice murya maryam tace haba dai Naimat keep n fasan cewa ni kewa anty aiki yau she nake da time din fita, unguwa,
Harara Naimat takai mata cikin wasa tace ke dai ba wani kawai dai ba ki so zuwa bane,,
Dakin maryam din suga shige gaba dayan su a lokaci guda,
Dan abin tabawa maryam takawo masu amma sai taga cewa Naimat, din bata ci komai daga cikin abinda ta aje mata a gaban ta,
Don haka sai maryam take fadawa Anty cewa Naimat bataci komai daga abincin su ba,
Bayan kamar yan mintina sai ga รnty Dije ta shigo dakin
Fuskanta dauke da fara,a ta samu guri kusa da Naimat din ta zauna, suna mai dan fuskantar junar su,
Kallo guda Anty dije tai mata sai tai murmushi tace,
May kike son cine Naimat, ?
Naimat wace fuskanta ke dauke da murmushi ta dan dukar da kai cikin dan jin kunya ta ce ,
Anty ba ko,mai a barshi kawai , kamar ya za,a barshi haka zaki zauna da yunwa,
A hankali tace inda zan samu shinkafa da wake da mai da yaji zanci,
Inda maryam take anty ta kalla tace, muna da sauran wake ne ,
Maryam ta mike da niyar zuwa duba wake sai Naimat tace bani wayar ki maryam,
Ba wani mussu maryam tamika mata wayan ta wuce abinta, zuwa kitchen,
Ita ma Naimat din kwance takai ga wayan a hannun ta ta shiga gurare,
Busy maryam take a cikin kitchen tana kokarin dafa abincin don kada Naimat ta matsu,
Sako taji ya shigo a cikin wayan na maryam dake a hannun ta don haka sai tai kokarin zuwa diba sakon,
A nan taci karo da sakon da A,A ya aikowa Maryam dashi,
Tsab ta karanta sakon cikin tashin hakali da damuwa,
Nobar Yusuf ta bida ta tura mai sakon ,
Sai kuma ta jawo nata wayan takirashi take sheda mai cewa itace ta tura mai sakon ,
Tagani ne acikin wayan maryam shine ta ce bari ta turo mai,
Da sauri kuma tagoge kada maryam ta fahinci cewa, tayi amfani da wayan,
Ba,a dauki wani lokaci ba da maryam tadawo dakin dauke da kulolin abinci a hannun ta, ta dire su a gaban Naimat,
Sosai Naimat taci abincin don abincin yai mata dadi a baki,
Ta dade rabon da taci wani abinci irin haka kamar yadda ta ci shimkafa da waken,
Tana ci suna zuba hira da maryam kamar a bin hadin baki saiga, Safiya ta shigo gidan,
Gaba dayan su suka sa ihun murna a lokaci guda ,
Maryam wace tasan da,zancen korafi a kanta a bakin safiya ,
Ta,sheko da guda ta,rugumay ta ta baya itama dai ture ta tayi tana cewa anya kuwa maryam idan kin yi aure zakiyi zumunci, kuwa?
Bari har inyi auren kiga yadda zanyi ta zumunci da ku sai kun ce na i,she ku,
A lokaci guda suka sa tsaki a tsakanin su don jin abinda maryam tace,
Au to ku bari ku gani sai kun sha mamaki na tafada cikin tsigar zolaya,
Safiyace bayan ta zauna take cewa tare da daga kai takalli maryam,
A,A ya bugo maki waya ne maryam,?
A lokaci guda fuskan Maryam ya sauya daga fara,a zuwa bakin ciki
Batare da ta iya bada ansa ba tace, idon ta sun dan ciciko da hawaye kamar za su zubo, tace,
Safiya pls kada ki kawo min zancen wanan mara mutuncin pls,
Cikin mamaki suke kallon ta don jin cewa yau maryam ce da bakin ta take kiran A,A da wanan sunar,
Safiya tadan gyara zama daga kan kushin din da take tace hmmm,
Ji min ,fa A,A din nan dan wullakancin mutum kawai jiya yakirani da waya
Yadinga surfa min zagi ta inda yake shiga ba nan yake fita ba,
Wai mu makwadaita, macuta munyi mai butulci a kan kudi,
Ba son Allah da Annabi kike mai ba tun farko don da,son gaskiya ne da baki canza ra,ayinki ba akan shi,
Ke tun ina cewa ya tsaya in mai bayanin yadda zancen yake y
Fam yaki yarda da zance na in fada maki har takai ni ma nafara mayar mai da bakaken maganganu,
Naimat ce tace may ki,kacewa dan iska ke kuma,?
Ta tambaya a cikin fushi da harshen hausan ta dake da surki da na kabila,
Safiya tace haba ke ko nice fa,
Har zaki tambayeni may nace mai,
Ai saida ya shiga cewa kin gane ne safiya ki tsaya ki saurare ni ma wallahi,,,
Tace kawai sai na kashe waya din ban son jin komai daga bakin dan iska kawai,
Kawai ba,su ankara ba sai she,shekan kukan Maryam wace ke gefen su suka ji,
Lokaci guda duk suka kai mata kallo a cikin mamaki,
Da farko safiya tana zaton don tayi wa A,A cin mutunci maryam ke kuka,
Amma sai suka ji muryan ta a cikin kuka tana cewa,
Ban taba zaton cewa malam zai iya min irin wanan cin fuskan ba,
Ida da har ina kwadayin dukiya ne ai da shine mutun na farko da zai fara shedan haka,
Amma yafadi mana duk zamana dashi na taba rokon shi ya bani koda kwandala ne,,
Nan dai suka shiga bata mussalai, masu ma,ana har ta dan kwantar da hankalin ta,,,,
Zaune yake saman kujera yana karanta text din sai kawai yaji cewa bazai iya karasawa,ba,
Don haka ya aje wayan saman table din glass din da ke a gaban shi cikin bacin rai,
Wani irin abu yake ji a zuciyar shi takar idon shi zai rufe, alokacin,
Ji Yusuf yi bai ma san may ya ke ciki ba a lokacin,
Don haka sai ya ji tankar numfashin shi yana shirin daukewa a lokacin,
Da kyar ya iya nemo natsuwa ya ya furta a hankali yayin da yake dafe da kan shi dake mai ciwo tankar ya tsage,
Yace,
Innalillahi Wa, Inna, Ilaihim, Raji,un
Ya jima shiru dafe da hoshin shi da hannun shi guda a hakan yana nanata wanan addu,an,
Sannu a hankalo yadan dinga jin zuciyar shi na walwalewa a hankali daga kuncin da yake a ciki da farko,
Mikewa yayi zuwa bakin window falon shi,,yadan furzar da iskan kamar yadda yake yi, idan yana cikin yanayi,
A,A ya ambata a hankali insha Allah zan gwada, maka cewa wani dan furen jujin yafi dan furen gida mutunci,
Zan gwada maka cewa imani da biyayya suna da amfani ga dam adam ,
Daga haka yaji wani irin tukuki ya taso mai don haka bai iya cewa komai sai kalman innalillahi da yake ta nanatawa a cikin ranshi,
A hankali ya tako zuwa dakin shi yana mai tunan cewa lalai A, A zan gwada maka cewa,
Ni Yusuf nagaji sunan kwarai da ga mai sunan ,, ni Namijin Gwarozo ne acikin mazaje,
Ba dan akuya ma ciyi amanan diyan mutane da abokan azarki ba,
Daga haka yaja kafar shi da kyat har ya isa bedroom din shi,,
A rigingine yakwanta yadinga tasbihi ga Allah ubangijin shi, tare da neman a fuwan shi,
Yasan cewa wanan irin gorin shigar shi cikin addinin, musulunci da mutane ke masa,
Ya ringa yin addua akan Allah ya bashi ikon cin wanan jerabawan da ya ke acikin sa, daga kuma neman rinjaye akan masifun da yake fuskanta,
A haka ya dinga juyi a kan gadon shi yana tuna irin kalaman da ya ke fuskanta daga mutane da dama akan musuluntar shi,
Jikin shi yana jin shi tankar anyi mai duka idon shi sun kada sunyi jajir, rayuwa gaba daya yafita ran shi,
Allah gafurur Rahimun, yana, nan cikin wanan halin, ne barcci ya dauko shi,
Ya jima sosai yana barcin bai farka ba har zuwa lokacin da nauran da ya saita masu tayar dashi daidai lokacin sallah,
Tabbas yaji