Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
Ba zai iya rike ta da kyau kamar yadda yakeyi a yanzu ba,
Karan wayan shi ce ta tashe shi daga barcin da ya samu mai dadi barcin safe ke nan,
Idon shi a rufe saboda dadin barcin ya mika hannu dai,dai inda karar wayan nashi yake fitowa, ya dauko ta cikin kasala,
Antonia ya gani rubuce, zubur ya mike don kiran da yagani daga NANI ANTONIA,
Hlo, how you na dey,
Batare da ta ansa mai ba,take cewa Oga Pipkin dey sick since yesterday,
E no even go to school woo,
Mikewa yayi zubur yace subbahanallah, gami da furta sunan dan yaron,
Abdulraham a fili, tare da kokarin mikewa tsaye, daga gurin da yake kwancen,,
Hlo,
Antonia yace cikin harshen turancin yan kudu,
Ki shirya, shi kun ji zan kira doctor yazo ya diba min shi yanzun nan pls,
Yana kashewa ya shiga neman nobar doctor chukuma,,
Doctor chukuma wani likitan yarane da yake yawan kai yaron gurin shi tun bayan dawowar su Abuja,
Ba wani bata lokaci ya kira doctor din ,wanda a kira na farko ya, samu nobar doctor din a gurguje yai mai bayani cewa ya je gidan shi ya diba mai boy bai,da lafiya,,
Wanka yafada saboda ya samu ya isa Abuja da wuri ranan
Sai alokacin yake mamakin irin wanan gwaunatin ta Nigeria,
Ace babban gari mai tsohon tarihi kamar garin kwantagora ,
Wacce ta tara din,bin al,umma iri,iri wai har yanzu ba ai mata wani abin cigaban al,umma kasar ba,
Ya kamata ace yadda take business center tana da hanyoyin masu sauki daga railway ,zuwa airport, da sauran su,
Amma saboda handama manyan kasar mu da basu da kishin zuci har yanzu an rasa wanda zai yiwa wanan kasar irin wanan aikin cigaban, na al,umma,
A cikin barci da sukeyi na safe mai dadi da shiga rai suke jin muryan Yusuf din sama, sama,
A hankali ta bude idon ta a dai,dai lokacin da takejin yana cewa anty yanzu zan tafi Abuja don an bugo min waya yau da safe cewa, Pipkin bai da lafiya,,
Kuma yaron bawai ya wani saba da sabuwar nani din shi ba,ne,
Don kusan zuwan Naimat, nan ne na dauko matar daga kauyen mu,daga haka sai,
A hankali kuma taji dan she,shekar kukan Naimat a bayan ta,
Cikin idon barci maryam ke kallon Naimat din inda a hankali tadan mike zaune,
Inda Naimat take zaune take kallon ta, wacce ke kokarin goge hawayen dake sin,tiri a idon ta,
Ganin maryam din ta farka,ne yasa ta juyowa inda take zaune suna fuskantar junan su,
Hannun maryam tariki a cikin kuka ta nace wa maryam din,
Maryam ina son yaron nan, bana son ya mutu wallahi,
Saboda na,sha wahala sosai akan shi zaman da, da ,ni akwai wasu muhinman abubuwa da nake tunawa, akai,
Maryam wace ido kwai ta kura mata a cikkin mamaki, take kallon, Naimat din don sam bata fahinci inda maganar ta ya dosa ba,
Sai kuma hankalin ta ya,koma falo su, inda taji Anty Dije na cewa bazan bari kabi hanya baka karya ba Yusuf kabari ko cooker,oth ne a, dan dama ma,ka
Daga Saman gadon tai ko,karin saukowa a lokacin kafin ta idda sauka taji muryan Anty cikin daga murya tana kiran ta,
Sam ta mance cewa kayan barci ne ajikin ta don haka ta nufo falon da sauri,
Riga da wandon kayan barci sabon kitson da akai mata na wevin "yan ritsi,ritsi, sunyi lub, lub a kanta , gwanin sha,awa,
Da sauri ta iso inda anty ke tsaye dauke da yaron ta,
Shi ko sarkin lakewa a jikin uwar shi, a hannnu, ta yake dauke yana son shan nono, yanzu
Itama Anty sai yanzu tasan cewa kiran da tai,ta kwadawa Maryam din yasa ta rudewa cikin barci ta fito a haka,
Zanin da ta jawo don ta dan daura a sama take kokarin daurawa akai tana fadin gani Anty,
Da sauri ya kara waro idon shi waje don sak kalan kayan da yaga mai cikin da yai mafarki ne dasu da asuba,
Don Allah hada heater ki dama wa Yusuf cookeroth da,sauri pls, inji Anty Dije,
Sai a lokacin maryam wace tagama daura zani saman kayan barci ta, ta kai kallon ta inda yake tsaye tace ,
Ina kwana a hankali,
Shima dai ansa mata yayi cikin rashin walwala da sauri maryam ta nufi hanyar zuwa kitchen, din
Wani irin mugun bugun zuciya yaji mafarkin ne ya fado mai a ran shi,
Kafin yan mintina har ta hado mai cikin wani bowl mai dan fadi tazubo mai saboda yai saurin shan iska,
Anty Dije ce tace dan juya mai ya sha iska don Allah kada ya makara,,
Fuskan shi a hade kamar wanda bai taba dariya ba a rayuwan shi,
Wai waye Pipkin din nan ta ke tambaya a cikin zuciyar ta,
Dukawa tayi daniyar tafara motsawa mai orth din,
Wani kamshi ya daki hancin shi wanda saida yadan kara kallon ta ta wutsiyar ido,
Mamaki yaji don yasan daga barci ta tashi tafito amma kuma take wanan kamshin haka ?
Kai wanan yariyar akwai tsabta da yawa idon shi ne ke kallon yadda har an gyara ko ina na gidan ko kamar ba,a bata ba,
Muryan maryan ce mai magana cikin sanyi take cewa
Ya Yusuf addu,an samun lafiya za ai mai kasan ciwo bautan Allah ne both babba da yaro,
Amma duk da haka akwai wasu magani da mukewa yara amfani da su sai ka tafi mai dasu adinga mai amfani dashi a gani,
Mikewa tayi don ganin kunun yai dan sanyi saboda tasan cewa baya shan abu mai sanyi shi,
Dakin Anty ta shiga sai gata tafito da kwalaben magani a hannun ta,
Kara durkusawa tayi gaban shi tana mai bayani guda guda yana dan kurba kunun dake a hannun shi vikin cup a hankali,
Idon shine suka sauka a gaban rigar barcin ta waiyazu ;billah
Da sauri yakau da kan shi gefe har takare mai bayanin cewa wanan man
Habbatussauda ce, wanan, Zaitun ne, sai kuma man Albasa a dinga hadawa da pure zuma,
Takare maganar nata da ce wa a hankali Allah ya bashi lafiya,
Ameen ya ce cikin jin dadi da irin nuna kulawar da tai mai,
Sai alokacin ta juya gurin da Anty Dije take zaune tana shayar da danta tace
Anty idan zan fita atuna min in sayo wasu a aje dan Allah,
Mamaki yaji cewa sayen maganin ma sukayi ashe,
Bai wani dauki lokaci ba ya mike yana kokarin gyara jikin shi inda yadan takure,
Naimat ce tafito, cikin damuwa duk da tayi na mijin kokari gurin saita kan ta saboda kada agane cewa tayi kuka,
Maryam wace ke tambayar Naimat a cikin kashe murya,
Pipkin din yaron waye shi ?
Murmushi kawai Naimat tai mata, batare da taba ta ansa ba,
Ànty Dije ce tace ke baki san yaron Naimat ba Abdulrahaman,
Wani irin kallon mamaki maryam kewa Naimat daga haka Yusuf yai masu sallama ya tafi,
Yusuf tuki yakeyi shi kadai a cikin mota sai sharara gudu ya ke yi,
A cikin nishadi yake tukin shi hankali kwance sai dai kuma zuciyar shi tana gurin da yake, tunane
Sai,dai a kai, akai, yana dan duba agogon hannun shi, sai kuma ya daga kai yadubi, hanya,
A gaskiya a yadda ya samu yaron yana jin jiki sosai,
Saboda duk da ya samu yana barci amma jikin shi gadau yake da zafi,
A hankali ya duka a gaban yaron yana mai dan taba mai jiki a hankali,,
Wayar shi ce tai kara alamar kira ya shigo mai, a lokacin,
Batare da ya mike ba daga inda yake yadauki wayan
MARYAM BLACK yagani a rubuce wani irin murmushi ne yadan subuce mai,
Assalamu Alaikum, tace cikin yar siririyar muryan ta,
Ansa mata yayi da wa,alaikissalam ,
Maryam na barku lafiya,
Ya Yusuf ya hanya ka kusa isa ko,
Ina gida Maryam,
Yana jin ta tana cewa yai har ya isa fa,?
Muryan anty yaji tana cewa Yusuf wallahi ka rage wanan yawan gudun naka fa,
Maryam ya ambaci sunan ta, cikin wani irin murya,
Naam ta ansa mai itama cikin rudewa da jin irin kiran da yai mata,
Ya maijikin tace mai cikin sanyin murya,
Nasamu yana barci, amma dai jikin shi da zafi sosai wallahi,
Ya Yusuf kasamu kyale ko towel, kasa a ruwa ka din ga tai maka mai, dashi kana dan goge mai jiki dashi,
Jikin zai mai sauki idan an gama saika bashi wanan man albasan da sauran su ya sha,
Sai kuma tai shiru bata kara cewa komai ba daga hakan jun shirun nasu yai yawa shiyasa yakatse da,cewa abashi Anty,
Zaune yake a bakin gadon da ruwa da wani farin towel,
A hankali ya ke matse ruwan da towel din ya kwaso,
Yana dan mannawa a jikin yaron dake kwance a saman gadon shi,
Nani Antonia ta na tsaye gefe guda ta dan rakube a bango tana kallon abin da yadace ace itace tayi amma sam rudewa ya hana ta yi tun farko, don da ace tayi da jikin yaron bai kai haka ba,
Sannu a hankalo ya bude idon shi ,ba su sauka ko ina ba sai a,saman fuskan Uncle din shi,
A hankali ya ce uncle, sai kuma yai dan murmushi,
Wani irin tausayin yaron nen ya kama shi yaro mai kyau ga wayo amma ace wai ya tashi babu uba,
Kai mutane ba su da tsoron Allah sam, ka haifi yaro sai kuma kaki shi,
Yanzu badon Allah ya nufi yaron da,zama gurin shi ba da haka zai tashi acikin addinin Christian,
Uncle yaron yace a lokacin da yake kokarin ganin cewa ya kai zaune,
Da sauri Yusuf yatare da hannun a haka yadan mike zaune yana dogare da bayan hannun Yusuf,din
Rugumay shi yayi a lokacin maman Choima ta shigo dakin da cikin tafiya irin na tsofi
Da harshen IBO take mai yadawo lafiya ya hanya,saboda bata san inda ya tafi ba,,
Nan take ce mai wai yaushe ne Ejoma zata dawo garin su da ta tafi,
Ita fa shiya sa tace, tun farko Ejoma taje da dan ta,
Gashi yanzun ta wuce tabar mutane da yaro ana mata wahala,
Kan shi na duke yana sauraren ta yana makale da yaron a jikin shi,
Yace Mama,aaa,,,,,mamaaaa will stop dis,
Abdul is my son pls,
Lokacin yaji dan yaron ya kara shige mai a jikin shi ,shima dai din kara rungumay yaron ya yi cikin jikin shi,
Sai da ya tab batar da cewa yaron yaci abinci ya koshi san nan yasa akai mai wanka ya kara bashi magani,
Zaune a bakin gadon shi yana kallon wayar shisai dai ji yakeyi kamar ya kira maryam a lokacin,
Saboda irin yadda yake jin kewar ganin ta a yau din,
A hankali ya maida idon shi ya lumshe ya fadi a fili she is beautiful,
And her skin is natural,
Kwance yakai ta baya saman mamakeken gadon shi yace
And very religious, wayan shi ce tai kara azaton shi maryam ce amma sai yaga Aisha, ce, ke kiran shi,
Aisha ya kara furtawa yau rabon da ta kira ahi tun lokacin da sukayi sa,in sa da ita akan sadiya,
Baikara kula ta ba ko yanzu kamar kada ya dauka amma sai ya daure yadauka,,
Sun yi gaisuwa na mutunci da shi sai kuma ta fara mai korafin wai ya shigo KG yaki neman ta har yadawo,
Zata ci gaba da magana yadakatar da ita da cewa Aisha na fada maki ba yauba cewa baza mu shirya ba,
Saboda duk halaiyan ki basuyi min ba san kwata,kwata bana son inga mace bata kamun kan ta,
Nayi dake ki daina amma kin kiya,,,,,,,,,,
SEENABU ZEEE MAKAWA
.🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
IYA,KA, NA,ABBUD, WA IYA,KA,NAS,TA,INN
Zaune take tana kokarin shiga barci amma hankalin ga na gurin dan yaron da taji an kira,sunan shi da Pipkin, din,
Duk da ba sanin shi tayi ba amma tausayin shi ya, kama ta a cikin ran ta,,
Kamar kullun yadda ta,saba kafin ta kwanta, barci al,adan tane ta zauna ta shafe jikin ta da kayan kamshi duk da ba,wasu masu tsada bane,
Sai kuma takan zauna ta dinga jero adduoi da duk ya dace tayi kafin ta,kwanta, barcin,
A hankali ta,shafa adduan karshe da tayi ta,juya dai,dai gefen daman ta, ta,kai kwance,
Hannun ta ne ya sauka saman kan wayar ta kamar ta share sai kuma ta dauko wanyan,
Nobar A, A din ta ne last call din ta na yau, sunyi magana da shi akan cewa zai yi tafiya na yan kwana ki
Zai tafi su gana da mahaifiyar shi wace ke zaune Abuja da mijin ta da take aure yanzu yana aiki a,Agric Bank,
Kamar ta aje ga kuma idon ta na kallo nobar Yusuf din,
Inda Naimat take kwance takure saman kujerar three seaters wani irin tausayin Naimat din ne taji yakama ta,
Don tun da labarin rashin lafiyan yaron yazo musu tun wanan lokacin
Bata da wani kuzari ajikin ta duk ta wani su,su ce a yinin ranan,
Direct takai hannun ta ta dan na kiran layin shi batare da wani tunane ba,,
Yana a kwance idon shi a lumshe yana tunanen bari ya, shiga wanka ko zai samu natsuwa,
Firgigit ya na kallon gurin da,wayar yake saboda tun gama wayar su da Aishan shi wace taita mai masifa akan rashin kulata da ya daina yi yan zu,
Maryam Black yagani maryam again ? da sallaman shi ya ansa kiran nata,
Cikin wata irin dasasshiyar murya yace maryam ya kuke ya su Anty da yara,
Ta ansa mai cikin yar muryan nan nata da cewa lafiya, lau,
Uncle ya yaro mai jiki yaji sauki ko,?
Murmushi ya sake saboda jin yau ta tuna da tsohon sunan da suke kiran shi kafin ya musulun ta,
Alhamdullahi don har ya ci abinci ,
Masha Allah maryam tace,
Sai kuma tai shiru,
Shima dai din shirun yayi a lokacin
To Allah ya sauwaka, tana batun kashe wayan,
Au maryam har zaki kashe wayan ke nan ban ko gama magana ta ba,
Murmushi tayi tace kawai dai dama don muji cewa ya jikin yaron ne yasa na bugo ma,
Ina Assalam ?
Ta karba mai da cewa gashi nan yayi barci, tun dazun
Cikin hikima ya rika dan janta da hira kadan kadan,, yana mata yan tambayoyi
Sai kuma ya fada zancen Assalam da isalam,
Duk dao don ta saki jikin ta da shi ,
Har zuwa wani dan lokaci mai tsawo maryam a zuviyar ta duk ta matsu ta aje wayan saboda duk a matse take tankar a gaban shi take magana,
Duk da Yusuf ya fahinci cewa tana son anje wayan hakan bai sa ya kyale ta ba,
Sai cewa da ya yi idan yaron yaji sauki zan dawo don ban gama abin da nake yi ba nadawo,
Batare da tasan may yafito daga bakin ta ba sai cewa tayi,
To ya Yusuf ka,zo, dashi mana nan gurin mu tunda mahaifiyar shi tana tare da mu,
Idan nazo dashi may zaki iya yi mai, ?
Yar dariya gun,tuwa tayi tace ni , ?
Haba dai yaya Yusuf sai kace ni ba mace ba ce ,
"Masha, Allah" yace "
Aishe mijinki ya huta ke nan tun da kin iya reno,
Kar ki damu ai nan ma akwai, wace ke kula dashi sosai tankar uwar shi na kusa,
Amma dai ai zaman shi a kusa da uwar shi ina ga zai fi mai ya sake ko,?
Murmushin maganar da tayi yayi kawai saboda yadda tai maganar nata tankar, wata babban mace, da tasan yadda ake kula da yara,
Kaga sai ka sallami Nani din nashi ko ?
Wani sabon dariya yasa mata wanda dariyan yaba maryam mamaki so sai,
Tambayar ta yayi, don ya ji a kage take da ta kashe wayan
May yas naga kin damu da zancen ciwon Abdulrahaman, ne,
Cike da jin kunya maryam tai yar murmushi tankar yana a gaban ta,
A kunyace ta ansa mai da cewa saboda nasan cewa yaron na da muhin manci a gurin ku,
Kuma dai ai yaro na kowane ko ?
Murmushin da yayi har cikin dodon kunnen ta, taji shi a lokacin,
Sallama sukayi inda yake mata godiya da kuma yimata sai da safe,
Barci mai nauyi yai gaba da ita, bayan ta kashe wayan,
Na imat wace ke lafe tankar wance tai nisa a cikin barci
Tai wani irin ajiyar zuciya bayan ta gama sauraren duk yadda sukayi,