Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
kula mai da yar shi da,sukeyi tsakani da Allah,
Maryam wandda yanzu girma da wayo yazo mata ta roki Anty ta barta taje gurin mamanta, acan Bobi kafin ta fara karatu,
Anty bata kiya ba saida tace sai ta fadawa baba don kada, yazo yaji daga baya yai fada
Baba bai,yi fada sai fatan adawo lafiya da yai mata yabata dubu daya yace tasai masu tsaraban man shafi da sabulun, wanka,
Cikin kwana biyu akai mata yan shirye,shiryen tafiya,
Duk da bawai maryan ta saba da mamanta bane amma dai tai ta zumudin zuwa kauyen,don tagane su,,,
Ranan da zata tafi tunda safe ta hana idon ta barci don zumudi,
Har saida Anty ta kasa kan,newa tai mata, magana
Maryam wai,dama dai ashe kin dade kina son yin wanan tafin ne ko,
Yar kunya taji da kuma nauyin Anty nata, saita dan sune kanta tace ,aa anty kawai dai ina son zuwa ne inga yadda garin yake wallahi,
Har inda zata shiga mota Anty ta rakata tare da yaran su,,
Inda yaran ke kuka sai sun bi little mummy su inda zata,
Shiru take zaune cikin mota sai tunane takeyi yadda zata riski mahaifiyar ta ,
Don dai tasan cewa zaman kauye na maida mutum iri, sai tausayin mahaifiyar ta ya,kamata
Tace Allah sarki mama ita kuma nan Allah yai nufin zaman rayuwan ta,
Haka tai ta tunane azuciyar ta har suka isa garin kamfanin,Bobi, saidai tai mamakin ganin garin a saman babban titin zuwa minna da kwantagora,
Tana sauka idon wa yanda ke zaune a bakin titi yayo kanta caaaaa
Wani yaro tagani ya tafiya sai,tai mai sallama nan take tambayar shi gidan liman hamza,nan yaron yai mata kwatace akan tabi wani dan lungu, zata ga wani gida mai katon icce a kofar gidan tashiga nan ne gidan, tana bi kuwa sai gata a kofar gidan,,
Da sallamar ta tashiga mata uku tafara gani su guda tana daka guda kuma tana duke tana wanki dayar kuma tana wanke wanken kwanoni,
Duk kan su daurin zani agaba, ga yara manya da kanani nan jagwal da su, wasu majina ahanci wasu kuma kunu ya bushe masu a baki har hanci,,,
Sun karba mata sallama cikin mamare ki wace don ganin tada sukayi da kaya a tare da ita,
A cikin ladabi ta durkusa har kasa tana gaishe su ,
Abin mamaki sai ganin mata takeyi suna bulowa daga wani dan lungu, ashe ganin tsoro taiwa gidan matane, ciki fam kusan su goma,
A cikin sanyi muryan nan nata take cewa, don Allah mama Rukaiyan saleh nake nema,
Wata mata wace ke daure da wani zani blue mai photo barewa ce tace taufa gani nan,
Sai wata wace ke gefe tsaye tun shigowar shin kodai Mamuce,,
Maryam tace maryam ce sai salati suka hau alokaci guda,
Suna murna da farin cikin ganin ta, cikin sauri suka fara kwasan kayan ta zuwa ciki dashi,
Maman ta tace a kai ta, dakin abokiyar zaman ta, wace suke cewa Ladi,
Anan akai mata masauki ita, da kayanta, kafin wani lokaci har an kewaye ta da abinci kala kala,
Da yake kauye ne duk sunyi abin sanar su tasayarwa,
Kwarai mahaifiyar Maryam taji dadin ganin Maryam, da kuma wanan ziyarar da takawo masu,
Bayan kowa ya watse akabar Maryam da mahaifiyar ta, a hankali maryam ta dago kan ta takalli mahaifiyar ta wace ke tsugunne a gefen dan gadon ta,,
Tace mun samay ku lafiya mama, cikin kariyar murya take maganar kamar wacce zatai kuka alokacin,
Mahaifiyar tace takauda kukan da cewa yasu wajen yayan naki ina fatan duk kuna lafiya ?
Kikara rike yar uwar ki da amana kin daiga yadda itama tarike ki amana,
Ba maicewa ga yadda kuke da ita ,don ko da nake nan ina jin irin zaman da kukeyi da ita
Duk wani abinda ta hore ki dashi kiyi kokarin rike shi,
Allah ne kawai zai iya saka mata da alherin sa,,
Saidan hiran sauran jamar su da sukayi inda take tambayar ta ko kwana nawa zatai masu ta sheda mata sati guda zatayi ta koma,
Daga karshe ta gabatar mata da tsaraban da tazo masu dashi
Nan mama tai filla,filka da kayan saida ta,tabatar dakowa na gidan yasamu tsaraban,
Maryam taji dadin zama tare da mahaifiyar ta duk da a kauye suke sam bata nuna masu kyama ko nuna wayewa,
Dan zamanta har da karatun addini suka dan samu daga gareta,
Duk safe za,a kawo mata abin kari daga ko wani shiya nagidan hakama da rana ko dare kowa da kwanon shi da zai aiko mata,
Ana gobe zata koma har daga makwabta aka dinga kawo mata tsaraba irin na kauye,
Badon sun so ba washegari tabar su takamo hanya dawowa ita kadai,
Tunda motar ta tashi sai taji zuciyar ta duk ba dadi ya cushe mata guri guda ji take kamar kada su rabu da su,,
Hannu tas tadan share hawayen ta da taji yadan gangaro mata,
Sannu a hankali sai gasu Allah ya kawo su cikin gari lafiya,
Zaune yake a kofar gidan su Anty dije Assalam na rike a hannu shi yana yar wasan lilo da hannu Joseph din,
Mai mashin din da ta hau ne yazo har kusa da inda suke zaune,
Ido yabita dashi har lokacin da ta sauka ta mikawa mai mashin kudi,
A,lokacin mai mashin din ya sauke mata wani buhu,da ke shake da kayan tsaraba da tazo dashi,,,
Joseph ya sauke hannun Assalam a hankali shiko Assalam naganin ta yaje ya kankamay ta ya,na, ihun da murnan ganin ta,
Suna can suna murna basu san lokacin da Joseph ya dauki buhun kayan da kuma yar trolley din ta zuwa cikin gida,
Saida suka gama ihun su koda zasu diba basuga kayanta ba ,kuma basuga Joseph ba
Sai ganin shi sukayi ya na fitowa da ga cikin gida, yana kakabe hannun shi, da handcarchef, din shi,,
Da mamaki take kallon shi don sam,batai tsanmanin cewa zai iya daukar mata kaya dakamshi zuwa cikin gida
Juyawa tayi daidai lokacin da ya iso inda suke tsaye, cikin yar karamar murya tace ta gode duk da tasan cewa bawai dole bane ya amsa masu,
Tadawo da sati tafara shiga makaranta daukan lectures,
Maryam yarinyace mai hazaka ga karatu dama duk kowani famni ba,abarta a baya ba, tana kokartawa,
San,nu,a hankali kanta yafara wayewa kamar kowace budurwa da ke makarantar,
Yau ma kamar kullun shiri takeyi don gudun makara,,saboda tasan cewa suna da lecture din wani bakon malami da zai dauke su,
Gashi sun samu labarin cewa baida wasa ga aikin shi duk wanda yazo bayan shi bazai shiga ma aji ba alokacin kuma, dole kowa yasai handout din shi,
Yau har da break fast anty tayi da ita ta tsaya tasha amma maryam sauri take yi tace idan taje can zata samu dan abinda taci,
Ta dade a bakin titi kafin ta samu abin hawan da zai kaita amma sai suce bazasu je har can ba yanzu da safen nan, sai da kyat tasamu wani yace zai kaita a dari biyu tace ba komai,su tafi,,
Hakan ya jawo mata makar har time din da za,a fara lecture din yadan gwauta da minti biyu kacal,
Amma jin cewa da tayi ance baida sauki lecturer din wurin rashin nasiha,
Yasa taja baya kawai tasamu wani mota ta dan kwanta saman motar, kadan
Rayuwar ta yai matukar baci sosai da rashin samun wanan lecture din da batayi,
Tana tir da halin rashin imani,ko, nasiha nawa su, mutane,
Tsaye yake kanta yana magana amma Maryam batasan cewa, da mutum yana mata magana ba, alokacin,
Motsin da taji ne kamar kusa da ita shi yasanya ta dago kai da sauri don gani kowaye gurin,
Wani black, handsome guy ne tsaye agaban ta,sajen fuskan shi yah karawa fuskan shi wani daraje,da girmamawa,
Cikin shigar dinkin shadda yake,dinkin wanda ya tsaya mai,daidai ciyar shi sai guntun hannu, da a,kaiwa dinkin,
Yana saye da wani farin glass wanda bazata iya tamtace, ko na magani ne ko fashion ne kawai,
Duk da indon shi nada glass bai hanata,gani kwayar idon shi ba da kuma kallon mamakin da yake mata,
Batasan lokacin da taisauri ta mike ba daga kwanciyar da tai, a saman motar mutane,
Yana tsaye hannayen shi rungumay a kirjin rungumay
Ganin ta tashi yasa yai saurin kokarin wuce wa,
Saida kuma yaji ta saki wani dogon tsaki, tare da yin kwafa,
Dawowa yayi yana ce mata lafiya dai ko naganki a haka, ko kina son wani taimako ne,
Dan tsaki taja tana kokari gyara jarkar dake rataye a kafadar ta,
Wani mugun malami ne yabata min rai don yaga Allah yabashi baiwa ya,manta cewa wani dama ne ubangiji yabashi
Saiga shi ,shi yana amfani da damar yana cutawa diyan mutane, da, damar ta shi
Tadan daga kai a karo na faron tunda tafara mai magana cikin bacin rai, tace ,,
Wai ace duk samakon danayi don kada in makara, shiga,lecture din shi, saboda ance shi mugune in,,, in an, makara bai bari mutun yashiga,
Sai ga shi,,abin hawa yabani matsala wallahi,
Amma abin haushi wai minti biyu kacal na dora a saman lokacin da ya,fara lecture,
Sai,gashi wai ya rufe ba mai shiga kuma,,Abin haushi ance bai yiwa Allah don mugganci, shi,
Tun da tafara fuskan shi na a,kanta,
Fuskanshi dauke da murmushi yace too bad,
Is alright, may sunan guy din ne wai,,,
Ido ta,dan zaro waje tace kai may ye, zakai mai wa yanda ma suka dade tare dashi sun yaba shi da mugun hali ,,,
Fadamin sunan shi kawai ko zan iya taimaka maki akai,
Taidan wani far da ido taba alamar tunane, can tace,
Hmmm wai,ko A,A, MASUGA suke ce mashi ba, ko wa ma something like dat dai,
Ya na kokarin bude motar shi, yakalle ta ido cikin ido, yace mata,,
Ok ki,samay ni a block C idan kin,je office na uku daga daman ki, ,ki shi ga zaki samay ni, ciki,zan yi kokari in gani, may za,ayi akai,
Bawani jin darrr ko kuma tunane, wani abu dakaje yadawo, gareta, sai cewa tayi, to kawai ta amsa mashi alokacin, har yashiga motarshi yana kokarin tayar wa,
Sai bayan ya wuce ne tai dan ajiyan zuciya cikin bacin rai tace shikuma wanan din ma kowa ye a makarantar da zaice, zai tunkari, AA Masuga,
Tunda duk sakkon datayi tun da farar safiya ya hana yashiga ciki,
Next lecture tashige abinta batare da ta damu da zuwa gurin da ake jiranta ba,,,
Don ita a ganin ta mugun malamin ya riga ya cuce ta ko,,
Zaune yake yana aikin tura sako a cikin system din shi yanayi yana gyaran dan farin glass din da ke man,ne a fuskan shi,
Saidai a cikin zuciyar shi maganganun yariyar dazu ke mai yawo a kwakwalwan shi, yana jin muryanta tana fadin ,,,,
Allah yabashi dama saidai shi yana amfani da wanan baiwar yana cutar, da,diyan mutane dashi,
Yau ko karyawa ban tsaya nayi ba saboda kawai in,samu shiga kafin time din shi yayi sai,dai abin hawa yaban matsala saboda, minti biyu, kawai kacal, na kara
Shine ka gan,ni ana ya hanani shiga, saboda daukar alhaki
A cewar wanan yarinyar da ke ta fadamai magana tsakani da Allah
Kai ya girgiza da yakai nan yana mai furzar da wani irin iska daga bakin shi,
A gaskiya wanan maganan ta soki zuciyar shi don dan abu kadan kejawa mutun matsalal rayuwa,
Shi baiyiwa mutane uzurin matsalal suba taya shi Allah zai sa wani yai mai nashi watarana,
Idan ma har bai yi nasiha ba sai wani yazo yayi don komai dadewan ka a wuri dole watara bakai, bane a gurin,,,
Ire,iren wanan tunanen yadinga yi a zuciyar shi yanayi yana kallon agogon dake daure a dogon hannun shi,
Dan tsaki yaja don rashin ganin yarinyar batazo ba balle ya karasa jin korafin jama,a akan shi,,,
Maryam ko wace sai kusan uku na rana tasamu kan ta sai a lokacin ta tuna cewa ,wani yabata appointment dazu da safe,
Bashiri cikin sauri tajuya zuwa block din da aikai mata kwatance,
A hankali ta kwankwasa kofar office din yana zaune hankalishi naga aikin da yake idon kafe da farin glass din dake idon shi,
Batare da yadago kai ba yake cewa mai kwan kwasawar come, in, batare da yadaga kai ba still
Da sallama abakinta ta shigo office din wani irin sanyi da kuma kamshi, turaren maza na Minkaeel, ne , ya,daki hancin
Sai da yaji muryan mace ce yadan dago kai yaga kowace,ce har zai maida kanshi ga abinda yakeyi
Ido biyu sukayi da maryam wace ke cikin shigar doguwar jallabiya sai dankwalin da ta yane fuskanta da shi,
Wanda iya round din fuskantà kawai zaka iya gani ,duk sauran jikin ta a rufe yake lif,
A hankali cikin dishasshiyar murya take gaishe shi cikin ladabi,
System din dake gaban shi yadan rufe kadan ya na mai fuskantar ta,
Cikin kujeru biyu dake office din suna fuskantar wanda yake zaune ya nuna mata,
Malam kayi hakkuri pls sai yanzu muka , fito, daga lectures,
Cak taji numfashin ta ya tsaya daidai lokacin da tai tozali da wani dan prem dake kafe a gaban tebur din shi
An rubuta da wani ruwan gold cikin wani sallo A,A MASUGA,,,,
ZEEE MAKAWA,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
1⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
A,A masuga ido ya kura mata batare da ya dauke kan shi ba don ganin irin re,action din da tayi lokacin da idon ta yakai ga prem din,
Murmushi yayi yadan gyara zaman glass din dake idon shi, dai dai lokacin yake ce mata,
A nutse, ya,ce,ya, sunan ki malama,, cikin wata irin tsadadar murya yake magana kamar bai son yi,
Kusan minti uku bata iya cewa komai ba har lokacin
Murmushi yayi shi ya fargar da ita daga dogon tunanen da tafarayi naganin gata a gaban hukumar makarantar an gurfanar davita akan sai takawo shedan cewa A,A masuga mugune,
Kara tambayar ta yqi yana mai cewa ,cewa nayi ya sunan ki ne, ?
Murya kasa,kasa ta furta cewa Maryam Abdullahi, Bobbi,
Jin yayi shiru tadan dago kai ta kalli inda yake cikin sauri ta dukar da kanta,
Don shima din ita yake kallo a lokacin,
A,dan kunyace ta furta don Allah kayi hakkuri ban san,,,,,
Hanni yadaga mata yana mai gyaran murya yace
Naji duk bayanin da kikai min dazu akan AA masuga
Maryam wace kan ta ke duke sai a lokacin tadan dago kai takara kallon shi a karo na biyu don jin da tayi tace A,A masuga,
Azuci kuma cewa tayi jidan rainin wayo ko har yanzu yadauka ban gane shine ba yaci gaba da shanmata na ,,
Kamar daga sama taji ya kira sunan ta in full,
Adan tsorace, ta dago kanta, saidai wanan karon fuskan shi a daure take tamau, bakamar dazun ba, daya dan sake ta,
Kai ta mayar kasa don ji takeyi gaban ta yana ba da dammmm,
Yace, naji dadin wanan maganar da kika fada min da don tun da nake ba wanda ya taba fada min cewa abin baidace,ba,
Nikuma azato na hakan taimaka wane ga dalibai, ban yi la,akarin cewa zai iya illikanta rayuwan wasu ba,
Kokuma in ci hakkin wani ta irin hakan da nakeyi ,
Yace kin san may ?
Kai ta dake kasa, ta girgiza mai,,
A hankali yaci gaba da mata yan tambayoyi , saidai wanan karon a kunyace take bashi ansa,
Sallama tai mai gami da bashi hakuri,
Yace haba dai ita taimakon shi, ta tayi tunda har ta iya fada mai gaskiya,,,,
Shiru yadan biyo baya sai shi A,A din ne ya ita cewa muje in kaiki gida don time yayi ko ,
Don kada ki rasa abin hawa,
A ranta tace wake kai ta gida da, da bata dare,
Amma a fili dan murmushi tayi, tana mai cewa da kabar shi ai zan samu bus,
Batare da yai magana ba ya mike tsaye, yana mai hada yan tarkacen shi a cikin yar briefcase din shi,
Maryam tarigashi fitowa yana biye da ita a baya don sai da ya tsaya yadan rufe office din shi,
Amma may suna fita fafir Maryam tace yabar shi kawai bazata shiga ba,
Saida ya nuna mata cewa bai son jayayya, sanan ta daure suka tafi, a cikin motar shi, kirar Peugeot NEW MODEL,,,
Tafe suke ba mai magana acikin su sai dai