Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
dare sukara mai allura, amma dan Allah ku bashi tea ko kunu yasaha, sosai pls,
Daga nan ya juya yabar dakin cikin tafiyar shi ma kama da ta yanga,
Sai a lokacin maryam ta nisa tana mai kara mamaki da irin rayuwar wanan mutunin,
Allah ya sa yagane gaskiya tace daidai lokacin da tamike ta dan fara gyara kayan da suka wawa,tse adakin,,,,
Sallah tai haraman yi don har lokaci yadan gwauta, bata samu yi ba saboda rudewa,,,
Sai zuwa tara na dare Anty Dije tadawo inda tasamu Maryam zaune gab da Assalam ta kura mai ido,
Tunda tashigo dakin hankalin ta, na gurin su don yadda taga Maryam din a lokacin,
Kayan da tashigo dashi a hannunta taje tana tambayar Maryam maynee, halan naga kin wani kura mai ido
Maimakon Maryam tai magana sai kawai tasa kuka wi,wi,wi,
A rane anty ke kara tambarya ta wai may akayi,
Kuka yaci karfinta takasa magana,balle tai mata bayani,
Jin anturo kofan dakin yasa Anty waigawa don taga kowaye yashigo,
Joseph tagani yana sagale da yar jarket din shi a kafadar shi,.
Cikin mamaki Anty Dije kallon shi sai tambayar shi,take tambayar shi yaushe iso,
Yai yar gajerar murmushi yana kojarin karasawa inda Assalam yake kwance,
Saida yakai bakin gadon yadan taba jikin yaron yaji da sanyi babu zafi kamar dazu,,
Sanan yadan juyo yana gaisawa da Anty dijen, sai alokacin ne ya jai kallon shi ga Maryam wace ke ta faman sharar kwalla,,
Ido yadan zuba mata nadan second, sai yakawar da kanshi daga gareta da sauri,
Azuciyar shi yace dazun ma dayaron ya shiga conscious, batai kuka haka basai yanzu,
Gefen gadon da yaron yake yadan samu gefen bakin gafon yadan zauna
Nan suka fara hira yadda abin yafarawa yaron tun farko,
Yace likita yace, harda typhoid, da kuma malaria ke damun shi,
Maryam wace ta dauro alwalar sallah isha,i, tazo tada sallah duk alokacin suna ta maganar assalam din,
Bayan tabidar ne Anty Dije ke cewa ki hada wanan kayan ki sauri ki je maryam kin san cewa issalam bata yarda dakowa in bake tagani ba
Ga Joseph nan sai ya sauke min ke idan zai wuce,
Gaban maryam ne ya fadi a lokacin don ita sam bata son wani alaka da zai hadata da shi,,
Joseph tashi katafi ka huta ka debo gajiyar hanya,
Anty yatafi kawai zan kira a kaini, yanzu, Anty dije tace Maryam ko da na bargida Issalam fa taki zuwa gidan su Salma,
Da dabara nasamu nakai tacan nasan cewa yanzu haka tana can tana masu rigima
Maryam zatai magana anty tace don Allah tashi ya sauke ki kada dare yakara yi,
Wayan maryam din ne yai kara aloacin cikin murya mai shakewa ta ce, Assalamu Alaikum,
Ido Joseph na akan ta don ya nason subar asibitin don yaje gida kafin maihaifin shi yashiga barci,
Cikin shagwaba taje cewa gata nan zatabar asibitin zuwa gida yanzu,
Tunda suka fara hanya ba wanda yai wa dan uwa magana
Sai shine ma yai dan magana cewa ta danyi hakkuri yasai wani abu a kingays super market,
Batare da yaji maitace ba yabude motar yashige abinshi,
Kara kiranta A,A yakarayi a karo na biyu yana maice mata yana son ya wuce don badadewa zaiyi ba,
Gashi Joseph kuma yasa security lock ya kulle motar don kada sanyi A,C ya rage,
Batare da ta ganshi tafe ba. Dan guntun tsuki tayi daidai lokacin da yabude motar zai shigo,,,
Ledoji ne birjit a hannuwar shi yazube su a gefen shi,
Suna karasawa A,A, natada motar shi daniyar zai wuce abin shi,
Ganin su ya sa yadan dakata sai dai bai san kowakeda qanan dirkekiyar motar ba haka,
A hankali ta sauko daga motar daidai lokacin da shi kuma yafara tatara ledojin da yasiyo a super market yana kokarin bude kofar gefen shi,,,,,
Cikin rawan jiki ta take saurin fita don gudun bacin ran A,A din gareta,
Dan ma,kullin gidan da Anty ta bata dazata wuto take kokarin daukowa daga cikin pos din ta,
Joseph yagane cewa hankalinta na gurin mai motar dake tsaye ya kun,na dim,light din motar,
Da kanshi ya je har bakin kofar gidan yakarbi dan makullin daga hannunta ya bude gidan,
Saida yakai duk kayan da suka dawo dashi daga asibiti zuwa cikin gidan,
Maryam wace har lokacin ta gurin mai motar tadan rankwafa suna magana dashi
Ganin cewa ba,ta,daniya barin gurin mai motar yai mata bayani cewa ga kaya nan tabawa Issilam
Yasa shi tada motar shi yana mai yi muzu horn yai tafiyar shi,
Maryam wace alokacin take cewa A,A, ya daina hadata da kafiri Arne,
Yaga tashin motar shi nan yadan mata dariya cikin barkwanci yake ce mata yau dai na hana shi tsaya wa,
Maryan wace ranta yakai kololowat baci ta wuce zuwa ciki batare da ta,tsaya yi mai saida safe ba,
Shiko A,A da gangan yake mata wanan wasan don yasan cewa tayi hating din Joseph din,
Tun zuwan shi bai hutaba akan ciwon Assalam don duk wani zirga,zirga da sayen magani yakan shi tun zuwan shi
Da har yana cewa zai dauke yaron zuwa Abuja, Turkish hospital,
Saiga shi yaji sauki sosai kamar bashi bane mai ciwo da duk yatayar wa mutane a hankali,
Kuyi hakkuri pls ba yawa yau
ZEEE MAKAW
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣3⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,
Wanan watan Azumin haka su,kayi shi rabi badadi saboda ciwon Assalam,
Don bawanda yasa yaron zai tashi, amna sai gashi yasamu sauki,
Joseph duk hankalin shi ya tashi zaka dauka wani babbane ko dan uwan shi baida lafiya, haka,
Da kan shi yake zuwa yai wa Assalam komai daga wanka har shan magani da cin abinci,
Wanan abin yakara sa shakuwa sosai tsakanin Joseph da mutanen gidan,
Don ba wanda ya isa yasa Assalam yin wani abu in ba Joseph ya,zo ba
Duk yadda kayi yaci abu baya ci inba Joseph ya,zo ba sai,kaga jikin shi har dan rawa yakeyi,
Wanan sabon nasu yana bawa kowa mamaki musan ma idan kaga yadda,sukeyi,
Yau ko da ya shi go sun gama abinci don da, wuri suke fara aikin girke, girken su na azumi don gudun makara,
Shimkafa da miya duk maryam taga har ta,zuba acikin cooler wanda har asuba yana da zafin shi,
Don haka ta saurin zuwa yin sallah la,asar, sai jin muryan Anty tayi tana fadin kawo wa su Joseph abincin su,
Ànty sallah zan yi tukun don nayi alwala
, Kifara kawo masu mana kafin kiyi sallah,
Sai jin maganar maryam tayi wani iri, may anty nata ke nufi da fadar haka,
Amma sai tani tana cewa kin san halin Assalam yana iya cewa bazai ci ba sai wani abin kwadai,
Azuciyar maryam ta ce, watau ita don Dan ta take son yin komai akan wanan Arnen
Muryan Joseph taji yans cewa "No, tabar shi kawai bana jin yunwa, Assalam kuma fruit zan bashi ya sha,.
So, abar ta tayi sallah ta, kawai fitama zamuyi yau, mu dan yawata cikin gari
Ya kare zancen yana mai mikawa Assalam hannu,
Tun bayan fitan su gidan bayan maryam takare sallah sai ta share Anty kawai alamar tayi fushi,,,
Basu dawo ba sai bayan shan ruwa daidai lokacin da har da yaya Illiya most jin Anty Dije yana gida don shima yadawo saboda ciwon Assalam din, tun kwana biyu da suka wuce,
Maryam na,ganin shigowar su takara tamke fuskan ta don gudun, kara wahal da ita kan kafiri,
Juice din subo da kankana da akayi mai sanyi yadan kurba,
Daidai lokacin da yaya Illiya ke cewa Maryam, ke bazaki zo ki yi buda bakin ba
A,a ba yanzu zan ci ba inji maryam take cewa mijin yar nata, da yaji tausayin ta a,
lokacin duk da bawai yafaye damuwa da al,marin ta bane a gidan,
Don tun tana yarinya bai damu da mata wasu abubuwa ba a matsayinta na kaunar matashi wace ke zama da su,
Amma ganin watan Azumi ne ga kuma aiki, yai mata yawa har yadan ji tausayin ta ya,kamashi,,
Maryam ko tana cewa ba yanzu ba ta daga idon ta daniyar wucewa sai ki suka hada ido da Joseph,
Wanda ke kurban juice din dake hannun shi a hankali
Ga sanyi ga kuma kamshin dadi na tashi daga cikin juice din,
Suna hada ido tai wani daure fuska, kamar zata fashe, a lokacin,
A, hankali ya furta cewa may yasa ba,zaki ci abinci
Bayan kin yi azumi kada kijawa kan ki matsalar ulcer fa,
Maryam tadan kauda kai gefe guda ta tsuke fuska tace, tace haka kawai,
Tana duke tana kokarin ajewa mijin yar ta vegetable din data soya mai,
Can yai dan shiru ga mamakin maryam sai kuma ta tsinci muryan shi yana cewa amma da ko tea ne ki dan sha don ki walwale hajin ki, ko, ?
Tace ko banci ba yanzu, ba,abin da zai samay don nasaba da hakan,,
Ànty Dije wace tun farkon zancen tajin abinda kewa kana kuma tasan cewa maryam tun rana fushi takeyi da ita,
Anty tace dama kun bar ta tunda tace ba,za,taci ba ,bataci din, ne kawai,
Yaya illiya yakalli matar shi yace kina nufincewa, idan anyi buda baki batayi a lokacin ko may,
Anty Dije tace, a,a yau dai ne takejin hakan , saboda haka duk zancen da zakuyi mata bazataci ba tunda tace a,a,
Yaya illiya yaidan murmushi yace kin,san dai abin da kikai mata yau din ne,
Tace fushin da ba wani dalili takeyi kawai tunda rana,
Dariya mijin Antyn ta yadinga mata, yana mata ba,a cikin zolaya,
Daga haka sukaci gaba da cin abincin su sai kamshi girki ke tashi duk ya cika gurin,
Daidai zata shiga daki wayar ta yai kara, cikin wani irin zakin murya tace Assalamu, Alaikum,
Daga haka tashige abinta daki batare da kowa yakara jin may tace ba
Sai bayan kamar minti goma sha lokacin har anfara kiraye kirayen sallahn isha,i, wasu gurare,
Sai gata cikin wani katon hijab, tace ma Anty Dije, ciki , ciki,
Anty zandan fita nan bakin kifar gida indawo,, Anty dije tace ana shirin yin sallah zaki fita,
Shi bakon wani iri ne daba zai tsaya har a idar da sallah ba,
Takarashe da cewa kada ki dade fa maryam,
Maryam tafita abinta batare da ta,tsaya koda ansawa ba,
Ankai kamar minti goma sai gata tadawo dauke da leda dakaya ciki ni,ki,niki,
A inda suke ta dangware ledar yaya illiya dake alwala alokacin yace, a,a a gashi ko dan saurayin harda gudun mawar leda buda baki ya kawo muna,
Abin mamaki nan yaya illiya yai alwala yabar Joseph zaune suna hira da Assalam da Issalam,
Maryam wace itama dai sallah take a lokacin tana bin wani massallacin dake kusa dasu,jam,i,
Bayan tahiya ansallamay tadan fakaici idon mutane ta tura sakon ta kamar kullun,
Copy D Wright Things From D Wright Peoples,,,,
Jin sakon yashigo mai cikin mamaki duk daga Anty har Maryam wace a lokacin sun fara Asham, sam baikawo cewa daga gidan bane, don dama bai taba tsan manin haka ba daga gurin su,
Tana sallah amma hankalinta na gurin su don jin subar hira yayi shiru,
Abinda maryam ta kula dashi shi ne undaga wanan lokacin duk jikin shi yai sanyi sosai
Don yar hiran da sukeyi ma da yaran yadaina yanzu, sai yar shirun da yayi,
Suna idar da sallah suka gaisa dashi da Anty, Maryam na,daki ita tafito suka gaisa, da Joseph
Kullun irin ladabin yarinyar nadaure mai kai gata kuma da bahagon hali,
Wanda bakowane zai gane ko may take ciki ba sai wanda yasan ta sosai,
Saboda ganin farkon ka da ita zaka gane cewa miskilace ta karshe,
Bai wani dade ba yacewa Anty Dije zai tafi, don yana son yaga wani,
Maryam da tasan cewa baya cikin hayacin shi sai murmushi tayi, kawai yasamu ya tafi fa kyat don Assalam yace sai sukara fita yawo,,,
Yana fita gidan maryam ta kasa yin hakkuri tadan kalli Antyn ta tace,
Wai Anty shi wanan kato da shi baya jin kunya
Kowa na sallah yana zaune sai wasa da yara baiko jin wani iri, aran shi,
Da mamaki Anty ta kalle ta tace kunyan may zai ji maryam
Runda shi ganima yakeyi ai yafi mu kama hanyar gaskiya,
Ido maryam tadan fitar waje don mamaki tace a hakan sai shirmay kawai, taya ,zaiga yafi kama gaskiya?
Bayan yana sane duk time din sallah sai mun tashi munyi sallah
Sabanin su daga Lahadi sai Lahadi kuma ba wanin abinda za,a taru gabadaya a bautawa Allah dashi kamar yadda musullumai
A kullun sai sun hadu sunyi sallah a guri guda sau biyar a rana,
Haja kuma ranan jumma,a tankar idi ce agurin mumuni, don kowa na donkin samun wanan falalar da ke cikin ta,
Ga Azumi da mukeyi gaba daya babu wargantawa a cikin ta don har da yara da azumin bai wajabta akansu ba, suna kokarin ganin sun samu wanan falalar,
Anty Dije tace, ke kikasan wanan Maryam keda Allah yakebo daga ciki,
Nidai har kullun ina mai mashi addu,an Allah yasa yagane gaskiya, yadawo hanya
Gashi da hali msi kyau tankar wani mumuni, nikai ina kokarin jan shi a jikine,
Ko Allah zai sa yagane gaskiya yadawo hanya, don kinga duk zagin da mutane ke min akan shi wallahi duk ina ji
Nidai nasan cewa kokari nakeyi inga ya kubto daga bata, yadawo daidai,
Allah ne ya hadamu dashi shikuma yasan dalilin kawo munashi anan,
Mutun nawa ke cikin garin nan amma baidamu dasu ba sai mu nan,
Shiyasa nake kokarin ganin ko ke kin daina masa wanan mugun hattaran dakike masa wallahi, hakan baidace ba sam,
Kamata yayi muyi takokarin lurar dashi hanya mafifici cikin hikima,
Chokalin dake hannun ta zata zuba shimkafa tadan aje a plate,
Ta,dan turo bakinta ga ba kamar mai shirin kuka tace,
Wallah Anty haka kawai nidai banson lamarin wanan mutumin, arayuwa na,
Bashi ba suk wani kafiri wallahi haushin sa nake ji ni sam bana son alaka dasu,
Dan bugu Anty takai mata abaya cikin wasa tace aiko wallahi ki bari don haka baida kyau,,,,,
Shiko Joseph tin da Asuba yabar gari, yanufi makardi, don ganin wani abokin kasuwan cin shi,,,
Kwanan shi biyu a can yasamu takardun da yatafi karba anan ne, yadawo Lagos
Ya,nadawowa yasa mu gurin sanar su ana rikici akan farashin mai da suke son su karawa kudi,
Don haka tunda safe ya shiriya tafi depot din nasu ,saidai duk security ne agurin, tako ina suna patrol,
Duk yadda yaso yashiga hakan bai samu ba kuma ga motocin su da yawa aciki harda mutanen shi,
Daga wajen dayake ne ya lura da cewa akwai yan batagari ake son tada fitinar tayi girma agurin
Har yatada mota don yabar gurin sai ganin yayi wasu masu alamar yan Ejebo sun ke,waye wani dan musullumi ba haushe suna kokarin halaka shi,,,,
Cikin wani irin ribas Joseph yai cikin su da karfin Allah ya bude gefen shi yana cewa mutumin yashigo
Shi ma mutu yagane nufin Joseph din yafada motar da karfi ya fisgi motar shi tare da mutumin sukabar gurin,
A jamian tsaro suka isu suka tarwatsa taron mutanen da harbi na gaskiya,
Don gwaunati tabado dokar duk wanda yatada fitina a harbe shi,
Sai da sukai nisa da gurin sosai, san,nan daga shi har mutumin sukayi ajiyar zuciya a lokaci guda,
Gidan shi ya wuce da mutumin cikin tashin hankali, suka isa ganin shi tare da bahaushe yasa kowa nagidan yin mamaki,
Wanan labarin tashin hankali duk ya karade kasa da kewaye cewa ana tashin hankali, a depot din Lagos
Hankali mutane da dama saida ya tashi saboda, jin cewa ana ta kashe,kashen mutane a gurin,
Wanan labarin har su Anty Dije sunji shi sanin cewa Joseph a gurin yake harkokin shi,
Nan da nan anty tasa kudi a layin ta, takira Joseph sai taji ance switch, up,
Hakalin su Anty duk yatashi tana takira bai shiga, duk nobibin shi dake gareta,
A kashe suke ba ita kadai ba har su KB saida sika dinga kiranshi wayar bata shi,
Shiko Joseph yaman ta cewa, ya kashe wayar shi tunda safe da zai shi depot din,
Sai zuwa yamma ya tuna cewa bai, kunna wayar shi ba tun safe ,
A folon gidan nashi suke gaba dayan, su, suna kallo a, TV abinda ke faru a gurin live, ake gani,,,
Duk wanda ya san Joseph hakalin shi a tashe yake, alokacin saboda rashin