Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   29 / 84

84K to 87K   out of 251.8K words

ba saida nasamu kwararar hujjoji daga Alkur,ani maigirma,
Eyy,Eyyyy, he's finish wooo,
Abinda sukace gabadaya kusan lokaci guda ke nan,
Watau, Joseph ysi nisa har da Alkur,ani ya,yarda dashi,,
Yusuf yace saida na hada duk wani hujja wanda zanyi depending a kai sanan nida kaina nakai kaina wurin limamin central mosque na Abuja ya musuluntar da ni,
Saboda haka duk wani wanda ke zargin cewa wani ne yajani zuwa cikin islama ba gaskiya bane,
Ni YUSUF ban musulunta akan abin duniya ba ko mace ko aboki,
Na musuluntane saboda Alkur,ani maigirma,
Sai duk wanda ke cikin fadar musulumi suka dauka gaba daya dafadin Allahu Akbar,
Yace nakai lokacin da zan zabawa kaina abinda nake so daga addini, sana,a da kuma iyali,
Cheer, God wooo,
He, don go far,

A nan maimartaba yai masu warning akan cewa duk wani wanda ke son kawo mai fitina ko tashin hankali acikin kasa ashirye yake da yadauki mataki akan mai shi tunda har wanda suke magana yace ra,ayin shine shiga addinin da yakeso don yakai shekara talatin, yanzu,
Kuka sosai Mr Ema yadinga yi acikin fadar mai martaba yana fadin cewa a taimake shi amayar mai da danshi cikin Christianity,
Amma ba wanda ya bashi goyon baya haka suka tallabe shi zuwa bakin motar dasukazo dashi yana kuka, wi,wi,
Yana kiranan sunan joseph yana zuba gwalancin su,
Shiko yusuf dama yarigasu barin gurin don haka gidan Anty Dije yakoma,
Saboda yadan samu relief of mind, din shi sai,dai kana ganin yadda idon shi ya rine kamar garwashi zaka gane cewa, yana cikin tashin hankali,
Yadan dade yana waya da Alhaji sabo inda yake fada mai abinda yafaru dashi yau da mahaifin shi,
Maryam wace ke cikin bayi a lokacin tana jin abinda yake fadi har zuwa lokacin da yashigo ciki da rinanun idon shi,
Falo yazauna jagab saman kujera two siter dake cikin falo,
Maryam wace kafin yashigo,,tafito ko daga bayin
Tana cikin shigar atamfa, buje da riga masu ruwan multi, colour,
Dinkin yai mugun karban jikin ta kayan da tasane tai adon jin ma,a dasu, da rana,
Taso taje ziyara gidan su safiya amma sai taga yau Anty bata jin dadin jikin ta sai tafasa shine tashiga bayi ta gyara jikinta don tana fashin sallah,
Acan ne taji muryan Yusuf din yana waya dawani yana fada mai irin yadda yaji gamay da mahaifin shi,
Wani irin tausayin sa taji don tasan da zafi ace mahaifinka na kuka akan ka,
Inbadon addinin gaskiyabace kamar yadda Yusuf din yace da sai ya fasa yakoma gurin mahaifin shi
To amma ba,zai iyaba sam ya shiga isalama kenan har mutuwar shi acewar,
Bashiga bafita shiga sojan badakkare,
Tana bude labulen dakun tafitowa suka hada ido, ya sakar mata rinanun idanun shi da suka kada sukai ja ,
Kan ta, takawar gefe cike da jin tausayin shi alokacin,
Direct gurin fridge tanufa tabude tadauko kwalin madarar youghot mai sanyi mai hoton bafillata, na company Mrs Ghali, youghot,
Ta hado da cup din glass bata tsaya ba sai,gurin shi direct,
Ta, dan rage tsawonta ta fara zuba wa acikin cup din a hankali,
Sai a likacin yuduf ya bude idon shi dasuke lumshe yasauke su akanta,
Ta mika masa youghot din a hankali, batare da ce mata kala ba yakarba ,
Yakafa kai a hankali yana lumshe ido don sanyi da gardin youghot din,
Saida ya shanye glass guda a hankali ya cire cup din abakin shi murya kamar mai rada yace nagode Maryam,,,
Maryam ta mike daniyar barin gurin don jin ajiyar zuciyar da yayi,
Yace may ye sunan wanan madarar,
A, hankali tace Mrs Ghali, youghot,
Masha Allah yana da kyau,,,



ZEEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣5⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,


Garin duk yai mai zafi, gabadaya baya jin dadin rayuwar shi sam,
Don haka ya yanke shawarar ya koma gobe ,gobe tun bai dauki wani lokaci ba,a garin saboda bai ita jure ganin mahaifin shi a haka
A ranan bai kwana gidan su ba hotel ya kama,,
Da safe ya shigo gidan cikin shirin shi na tafiya, yaso yatafi batare da yayi sallama da Antysa ba,
Amma sai yaga cewa zai dade bai shigo ba don haka yakamata su,yi sallama, da Assalam din shi,
A bakin kofa sukayi kicibis da maryam wace ke kojaein fita siyo madu breads na break fasta,
Idon shi ya kade yayi ja, kamar mara lafiya,ya wani fada,
Dan Rabawa maryam tayi gefen shi ta wuce inda zata,
Saidai jikin ta ya,ba,ta, cewa yana kallon ta bayan ta wuce,
Maryam tashigo rungumay da breads har guda biyu, a gefen hannun ta,
Anty Dije tace kagani ai nace kabari,ta dawo ba nesa ta, tafi,ba,
Nan Maryam tagane cewa tafiya zai yi, acan cikin ziciyar ta sai taji tausayi shi yai dan mata yawa,
Don ta san cewa hakan nada nasaba ga maganar da taji yanayi jiya awaya
Bayan maryam tashiga a,gagauce ta hada mai ruwan shayi tafito dashi rike a cup, tanufo shi,
Idanu ya zaro don bai tsanmani hakan ba,daga wanan yariyar
May yasa yanzu take sasauta mai fiye da,da,?
Bakin,ta na dan rawa, tace, gashi na hada mai ai Anty,
Sai yau zata ce magana mai kama da ta mutunci tashiga tsakanin su,
Hararan ta ya yi ,yace, wanan ai yai min yawa, ga kuma zafi,
Kanta na kasa duke saboda bazata iya jure irin kallon hararan da yai, mata ba,
Muryan Anty ce ya katse su adaidai lokacin da yake shirin karban cup din tea din
Anty Dije wace je cewa gaskiya, Yusuf wanan tafiyar dai kamar ba shiri zakayi ta,
Nan da nan idon shi suka canza zuwa tsantar bacin rai,
Ba Anty Dije ba har maryam da ta dauko mai wani dan stol a falon su saida, taji wani iri,
Yace cikin dasasar murya, mahaifina ke son kawo min matsala Anty,
Yaki hakkuri da zancen musulunta na sai daga hankalishi yake yi,
Duk da nasan cewa zuga shi akeyi akaina, lokacin yadan fara kokari kurba shayin da maryam takawo mai,
Ammakin shi sai yaji baida mugun zafin da ya,zata zaiyi,
Idon shi yadago ya kalli inda maryam take tana kokarin aje mai wata yar kujera irin ta zaman mata, hannu ta na dauke da ruwan pure water leda,
Itama anty zaune takai saman farin kujerar roban da maryam ta aje mata dan nisa kadan da Yusuf din,
Nan yaci gaba da fadawa Anty Dije yadda duk suka kwashe da maihaifin shi tare da sauran yan kabilar su,
Yadago idon shi rinannu ya sauke su ga, maryam daniyar yace mata ta kwashe kayan tea din ya koshi, saboda bai faye cin abinci da safe ba haka,
Idon ta suna a rintse tana mai jin zafin labarin da yake fadawa Anty ta,
Muryan shi da taji yana cewa nagode zan tafi kada inyi rana ahanya, don gobe akwai inda zantafi indan Allah yakaini,lafiya yau,
Sai ji tayi bakin ta na furta,zancen da takeyi a zuciyar ta,
Kadaure da,duk wani, kalubalen da zaka samu daga gurin su saboda bara,zana ce kawai suke kokarin yima,
Ko zasu iya juya ka idan sunyi hakan don kawai suyi galaba akan ka,
Kawai ka bar su suyi tayi watarana zasu daina gaba daya don zasu saduda,dakan su,
A,cikin mamakin ya ware idon shi yana kallon ta, yau itace ke nuna concern din ta akan shi saboda yazama musullmi dan uwan ta,
Ashe dama saboda akidar addini take gwada mai wanan tsanar, tunda yaga suna dan hurda da Jibrin, sai KB ne ba su shiri har yanzu,
Saida takai aya tai shiru dan kanta daga haka tajuya da nufin tabar gurin,
Anty Dije ce tace mata maryam amma fa kinsan cewa mahaifin shi, ne taya zai yi mashi haka,
A ladabce tace to, anty baki ganin cewa suna iya jan ra,ayin shi yakoma masu,,
Murmushi yayi yana mikewa, tsaye yadan kalli inda take yace, kina ganin kamar zan iya komawa cikin su ko,?
Kanta ta sada kasa saboda kallon ido da idon da suke fuskanta a,tsakanin su,
Yace ai,ni na shiga ke nan insha Allah sai mutuwa kuma,
Ya juya gurin Anty Dije yana mai ce mata idan Assalam ya tashi sai ta, massa sallama,shi yatafi,
Kudi masu yawa yadebo daga cikin aljihun shi ya aje wa anty a gefen , yasa kai yafita,
Bayan fitar shi, wajen minti uku Anty takasa koda motsi balle magana, saboda yawan kudin da ya aje mata,
Maryam ce ta zo da zuciyar ta daya ta dauki kudin tafara kirgawa,
Abin a tagani, yasanyata saurin dago kai ta kalli yar nata, cikin mamaki tace dubu dari Anty,
Da sauri anty ta dago kai ido waje tace dari,fa Maryam,?
Dan tsuke fuska Maryam tayi, tana kokarin mikawa Antyn ta kudin,
Allah yakai idon yar uwar nata a fuskarta, cikin mamaki tace wa Maryam, may kuma akati,
Maryam wace dama ta cika fam, tace to shi ance masa kina kwadayin kudin shi ne kokuwa,
?
Cike da mamaki yar ta ke kallonta don maganar ya daure mata kai,
Ban fhince ki ba inji Anty Dije,
To may da,zai wani baki kudi haka, batare da wani, dalili, ba, ni wallahi ban son abinda mutum zai min gori akansa sam,
To ke Maryam may ye naki aciki da har zaki dinga wanan zance,
Dama tun jiya yake ce min, zai bar kudi wanda zan dinga mashi sadakar kosai da, sugar duk jumma,
Sai a lokacin Maryam ta danji dadi har cikin ranta don azaton ra yagan su mabukata ke nan, shi yasa yabasu kudi,

Kwana biyu bayan tafiyar shi sanan mahaifin shi yasan cewa yabar gari,
Don haka ya kara daukaka fushin shi, don yasan cewa da gaske Joseph keyi yabar Christianity ke nan har abada,
Ya jijiga kan shi shi kadai a zaune saman kujer da ke bakin gidan man shi, yace impossible,
Waya yadauka yakira wani aminin shi dake zaune a Lagos din
Yusuf wanda a lokacin yadawo agajiye daga inda suka tafi can kusan boarder,
Ya zube saman kujerar dake cikin falon nashi, yana mai da numfashi guda guda
Kokari yakeyi yadan sasauta aninin da ya ke saman wuyar rigar shi don yadan ji shahakat,
Ido biyu yayi da wasu murda murdan katai cikin bakaken kaya da wani bakin glass a idonun su,
Addu,an da yagani cikin teach your self islam da yana ce saida ya haddace yai saurin zo mai arai,
A zuciyar shi yace bari ya fara gwada, wanan damar yagani,
Batare da ya nuna razana daganin su ba yace
LA,ILLA HA,ILLAH ,ANTA SUBBAHANAK INNI KUN TUN MINAL ZALLIMIN,,,,,,,
Cikin nuna rashin jin tsoro yace masu cikin natsuwa,
what's, do you want from me,?
Zagayowa sukayi inda yake zaune suma suka dan zauna mutum guda daga cikin su ne ya tsaya saitin kan shi da bindiga a hannun shi yana wasa da ita tankar bawani mugun abu yarika ba,
Mafi tsawo da kauri daga cikin su ne yadan gyara tsayin glass din idon shi yace,
Bama son komai daga gare ka,saidai kai kawai muke bukata, yana mai nuna Yusuf din da yatsar hannun shi,
Daga haka wanda ke tsaye ya sai mai wani kyale ya toshe mai hancin shi dashi,
Sai farkawa yayi yagan shi a cikin wani daki mai kama da dakin gwauraye,
Don yar katifa ce a kasa kawai sai wani dan tarin kaya mai kamada kayan wanki,
A hankali ya bidakin da kallo cikin mamaki, yadda har suka kawo shi nan batare da sanin shi ba,
Kusan minti goma sha da farkawan shi yaji anturo kofar dakin,
Wasu dattijai ne su uku cikin shigar coth da wando bakake
Fuskan su babu walwala acikin ta sam, sun kai wani lokaci suna kallon shi batare da sunyi mai magana ba
Guda daga cikin su ne yadan rage tsawon shi kamar yadda Yusuf din zai iya jin shi daga inda yake a kwance,
Yace mai ,Mr joe Y ,d u chose to live ur parents religion's,
And you even go to the wrong part,
A, hankali ya dago kanshi ya kalle shi tare da yin murmushin karfin hali irin ta, mayaudara yace,
That's where I want my life to be,,,,
Girgiza kai yayi alamar wanan yayi nisa, sosai baijin kira,
Dafa mai kafada mutumin yayi yana mai cewa kada ka yi taurin kai dan samari,
Bazan so ace wani abu makamancin haka yasamu daga cikin ku ba saboda ba,karamin, embraced zaka jawa zuriar ku ba,
Yusuf wanda kan shi yake a duke, yadan dago kan shi cikin wata malaciyar dariya,
Yace may ye na embracing acikin ra,ayin addini kuma ina, kowa abinda yake so zai yiwa kan sa zabi,
Mikewa mutumin yayi ya fara tafiya zuwa hanyar kofa,
Saida yakusa fita dakin yai wa sauran dake kokarin bin bayan shi,
Yace masu No Need of westing our time here,
Wa yan nan kaitan mutanen da suka dauko shi, daga gidan shi sune suka baiyana adakin
Bisa ga umarni wa yan can mutanen da suka fita suka fara dukan shi,
Sai addu,an daya iya abakin shi yake karantowa, Allah yakawo mai dauki,
Ya jibgu so sai a gurin su,suka dan fita, zuwa,, shan taba waje,,
Mutum guda daga cikin sune yadawo, daga baya yakawo mai ruwa a ledan pure water,
A hankali ya dan duka wajen shi cikin kashe murya, yace mai I will, free soon,
Daga haka yamike yai waje da sauri, gurin yan uwan shi,
Can cikin dare rashin sallah da bai samu yi ba duk ya damay shi,
Kamar daga sama yaji karar jiniyar yan sanda ya ji ya tunkaro, uguwar da suke,
Ba,afi yan mintina ba yakama jin karar bindiga, natashi duk unguwar yakaure da karan bindiga, zat tashin hankali,
Shiru yaji har nawani, dan lokaci, sai can yaji motsi alamar ana zuwa daidai kofar dakin da yake aciki,
Gaba daya suka hankado dakin cikin irin hikimar su ta yan kaki,
Kwance yake a daure, a hannu da kafa, shi a takure waje guda,
Kafin yan wasu mintoci har sun sance shi ko,
Da taimakon su, suka dan tallabashi zuwa, bakin motar,
Asibiti suka wuce dashi don diba lafiyar jikin shi Alhamdullah baiji wani mugun ciwo ba sai yan kananan raunuka da yasamu kawai ajikin shi,
Yusuf, yasamu sauki don har an sallamay shi bincike yanuna cewa sanadin musulutar da yayi ne yasa akai mai wanan ta,asar
Saidai wai ba,a san ko suwaye ba shi da kan shi yace a kashe case din don yasan cewa yana iya samun hannun mahaifin shi aciki dumu dumu,
Tun daga hospital yasa a sai, masa,ticket din fita waje,
Saboda yana son yaje yadan huta har komai ya samu natsuwa,
Kafain tafiyar shi yayi ta samun kiran waya daga yan uwa musuluma na kwantagora suna masa jaje dafantan Allah yakara tsarewa
Saura kwana biyu ya wuce mai gadin sho yashigo yana sheda mashi cewa, yana da bako a waje,
Tun daga nesa ya sheda shi ,daya daga cikin wayan nan da suka kawo mai hari ne suka sace shi,
Shine mutumin da yace wa Yusuf zai yi Free din shi a lokacin da yaje a hannun su,
Nan dai mutumin ke fada mai cewa, abokan mahaifinshine wa yan, nan mutane,
Duk abinda yagani da sa hannun mahaifin shi aciki,
Yaji cewa zasu mai dashi dan defar life shi yasa yaje ya report din su gurin yan sanda mafi kusa,
Amma cewa yayi ma police yana tuhumar akwai wanda akasato a gidan nan don yana jin ihun mai shi
Godiya sosai Yusuf yai masa in da yakawo alheri mai tsoka ya ba wa mutumin,
Amma sai yace aa shi abinda kawai yaje bukata yasamu aikin yi,
Don dama rashin abinda zai yi ne gashi da iyali, shiyasa ya shiga wanan harkan,
Kwarai Joseph ya tausayawa mutumin, don yasan talauci ne yasa shi ,shiga harkan da bai dace ba,,,



ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Kiraye, kirayen, sallah asuba ya kaure ko ina da musulmi sukafi yawa acikin duniya baki daya,
Shima Yusuf wanan kiran,sallah na asuba ya tashe shi a lokacin,
Duk da karfe bakwai na safe jirgin su zai tashi suwa, South korea, inda sonny deon yake zaune,
Massalacin da ya saba zuwa, yin sallah jam,i can yanufa ,
Batare da jin wani shakar komai, ba ko tsoro,yafito kai tsaye,zuwa, yin jam,in,
Bayan ya idar da sallah yadade, zaune gurin yana lazimi har zuwa dan waye wan gari kadan,
Yana isa airport batare da bata lokaci ba jirgin su yadaga yabar kasan, don sai sun

29 / 84