Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   59 / 84

174K to 177K   out of 251.8K words

su amma kuma sai anty ke ce mata maryam wainar zamuyi ko an fasa ke nan,
Yusuf wanda ke zuba kunu a ciku. Cup yana jin an anbai waina sai cewa yayi masha Allah har na manta raboda masa,
Yar harara maryam ta watsa mai ta wutsiyar ido tace,
Cikin wata irin narkarkiyar murya Anty da dai mun barshi kawai ayi wani abin,
Daga Anty har Yusuf dariya sukayi saboda sun gane nufin ta,
Anty Dije tace maryam ke muguwa ce ko don kin ji kanina yace yana son ci zaki mai kurulla akai,
Sai kuma jikin maryam din yai sanyi don an gane nufinta,
Sai cewa tayi nifa Anty ba don shi nace haka ba gani nayi dai kamar baza aci bane kawai,
Waye ba zaici ba maryam abin da muka kwana da niyar yin shi sai dai in kece kika fasa ci din,
Maryam ta juya jiki ba kwari ta fada kitchen girkin miya tafara dorawa tukun,
Miyan kaji ne yaji agushi, sosai a cikin shi sai kuma ta dora farfesun kayan cikin rago a dayan murhun, tafara yin hadin masa,,
Sosai masan yai kyau don tunda dare ta jika danyen shinkafa a ruwa bayan ta gama hada miya, sai ta je ta tsamay shinkafan a ruwa tasamu wani roba mai marfi ta sa aciki,
Ta dauko flower da yis da baking powder ta zuba ta dan sa ata rudu danye kadan sai kuma yan gurorin shinkafa kadan,
Almajirin su da ke masu wanke, wanke da yan sauran aiyuka tabawa yakai mata nika,
Kafin ya dawo ta dauko man suya da duk wanin abin da zata bukata na masa a kusa da ita,
Ba,a wani dade ba yaron yadawo daga gurin nika nan maryam ta zauna tafara suyan masan
Yayi fari yai kyau ba tsami ko kadan kuma yafita za kyau,
Sai da tagama soya masan sanan ta koma takan farfesun da take yi na kassan rago,
Kusan lokaci guda ta kammala komai ta ajiye, a cikin kula,
Daki su ta fada tai wanka takara fitowa wata fes da ita, kamar ba itace tai wanan aikin ba
Azaton Yusuf maryam ba zata yi masan ba ne don baiga tana da niyar yi ba don haka ya mike yana cewa Antyn shi,
Shi zai tafi idan ta gama masa zai dawo anjima yaci,
Anty ce take ce mai ai har angama ko tun,dazun ko,
Maryam anty takira don ta zubawa Yusuf masan, kafin ya wuce,
Duk a zaton shi ko wasa sukeyi mai sai kawai yaga shigowan maryam dauke da kulolin abinci,
Mamaki ne yakama shi don ganin har maryam ta canza shigar ta, ashe daga dogon riga ta koma zani da riga yar atamfa, Ghana, din dan dagwas a jikin ta,
Ta durkusa gaban shi tana kokarin aje kulolim abincin, da ta shigo da su,
Idon shi fes a fuskan ta don har ya manta da cewa anty na gurin,
Anty dije tamike tana cewa maryam dan Allah zuba mai ibda leka nan gidan hafsat yanzu zan dawo ,
Yadda anty tabarta a durkushe tana kojarin aje kulun hakan ne ya bashi daman karewa maryam din kallo,
Lumshe idon shi yayu ya koma saman bayan kujeran yadan kara bayan shi,akai,
Kamshi turaren da tasane ya shiga hancin shi sosai ya shake shi ya koma bude idon shi da sauri,
Cikin wani irin murya maryam taji maganar shi a kunnen ta yana cewa acikin lumshe ido kamar na mai jin barci kin yi kyau maryam ,
Kamar a mafarki taji wanan maganar don bata taba zaton jin haka gare shi ba,
Sai kuma ya daure fuska tankar bashine yai wanan maganar ba,
Daga kai tayi cikin jin nau,yin shi sai sukayi ido biyu da junan su,
A sanyaye maryam tace mai tana mai bude kulalan waina taje tanbayar shi guda nawa zan sa ma a plate,
Baki ji may nace bane maryam yakara tambayar ta ido a cikin ido,
Hawaye ne ya gan garo daga cikin idon ta zuwa fuskan ta,a hankali,
Saida ya dan lumshe idon shi yadan hade wasu miyau da suka tsaya mai a wuya,
Sanan Yace, haba maryam bana son ganin kin bata wanan kwaliyar da hawayen ki
Fitan hawaye daga idon ki tankar rage wani sanadari ne daga cikin jikin ki,
A sanyaye cikin murya kuka tace uncle kayi hakkuri kai wa baba magana a kai na pls,
Ido ya kura mata a lokacin da take wanan maganar,
Ji yayi tankar ya rungumota ba don komai ba sai wani irin mugun tausayin ta da yake ji a lokacin,
Sai dai a gaskiya bazai iya yiwa mahaifinta musu ba kamar yadda yaga tanayi,
Ita kanta yasan dalilin yin hakan nata bai wuce irin halin da surutun mutane zai jefa ta a ciki bane na yadda da auren shi da zatayi,
Don har yanzu al,umma suna mai daukar bai musulunta ba don basu daina nuna mai kyamar kabilanci ba,
Amma sai kawai ya nuna mata cewa shi din na mijine kuma babbane don hakane ya yi kokarin tursasa wa zuciyar shi son ta har kuma zuwa yanzu din yaji cewa ya kama da son ta din,
Don haka ayanzuma yarinyar tausayi taba shi ta re da jin wani irin mugun sha,awan ta da son ta kamar ranshi zai fita,
Haka kawai wanan ganin da yai mata yadinga jin wanan bakon yanayin a gamay da ita,
Ya dan rintse idon shi na dan wani lokaci sai kuma ya bude su still maryam tana durkushe a idan take ,
Ya mika hannun shi a hankali yadafa hannunta dake a saman kulan dake gaban ta,
Jin hannun shi a saman nata yasa tadan cira kai takai mai kallon ya hakane ?
Ya kalle ta a san yaye don shi da kyat yake bude su, yace
Maryam tun ranan da baba yai muna wanan zancen baikara ce min komai ba a kai,
Amma ke har yanzu kinki bari zukantan mu su zauna lafiya akan zancen
Maryam ta kara runtse idon ta lokacin da taji yace mata hakan ga,din,
Kenan ma ahida ba mahaifin shi ba yai biyayya akan zancen sai itace mace kuma diyar ahaifinta wanda shi yakewa ikirarin yaiwa biyayyan akan maganar shi,baba din,
Zuciyar ta takama mata sake,sake a lokaci guda ta rintse idon ta akaro na barkatai dan tsugunin ta a,gurin,
Wani irin damuwane yashige ta alokaci guda har ta dan dinga jin zazzabi na satan ta,
Kallon ta yayi cikin tausaya mata yace ki tashi maryam kada kafan ki yai ciwo,
A hankali cikin raunan,nan murya tace barin sakama masa a plate tukun,
Ya ce to nagode maryam da kulawar ki insha Allah biyayyan ki bazai zama na banza ba,
Taci gaba da zuba mai miya asaman masan da tasa mai kwara uku,
Ta mika mai tare da jawo cup din ruwa agaban shi tana kuma bude mai kulan ferfesun kassan ragon da tayi,
Hannun shi ne ya dan kara taba nata ida daidai lokacin da take kokarin tashi a gurin, shi kuma zai dauko spoon,
Tsikan jikin ta ne ya tashi yarrra ta zamay a hannkali gami da mikewa don barin gurin,
Kallo Yusuf ya bita dashi har zuwa kofan fita falon da ta nufa,
Kitchen takoma ta gyara sauran kayan da ta watsar gurin hada mai abincin,
Falon ta leka ko yagama sai dai ta sha mamakin ganin ko kwaya biyu bai iya cinyewa ba yana ci a hankali,
Tambayar shi tayi da cewa ko masan bai mai dadi bane a baki ,
Bai amsa mata tambayar taba sai dai bude mata kulan dake agaban shi ya yi sai taga ya cinye fiye da rabin masan,
Mamaki maryam tayi don sam bata san zai iya cin masan ba,, sai gashi yabuge ga cin yawa,
Har zuwa lokacin da ya gama cin abincin anty bata dawo ba,
Dama ya riga yagane plan ne yasa ta fita tabar su,
Tambayar ta ya yi da cewa ke bazaki ci abincin bane, ?
Duk da wani irin mugun nauyin shi da kunya da takeyi,
Kai kawai ta iya dan girgiza mai ba tare da tai magana ba,
Mikewa yayi ba tare da yai mata wani magana ba yanufi kofan fita daga falon,
Saida yakai kofan fita batare da ya juyo ba yace mata na gode sai an jima ko?
Inda ya fita yabar ta rakube anan gurin antyn ta tasamay ta tazubar da hawaye,
Kallon ta tayi cikin tausayawa yar uwan nata, tambayar ta takeyi ko may ya faru,
Tana share hawaye take girgiza kai gami da furtawa a hankali da cewa ba komai,

Yasha kwana round about da zai kai shi unguwar sabon gari ,
Sai ji yayi ana kokarin tsaida shi kamar kada ya tsaya saboda a saman hanyane gashi naida security , atare da shi duk da yasan cewa, ba,abinda zai faru da shi acikin garin kwantagora yanzu din,
Guri ya samu yai parking din motar shi a hankali ya sauka saman titin,
Fuskan da yagani sai yake tunanen ko a ina ya san shi,
Gaisuwa sukayi acikin mutunci inda yake tamayan Yusuf din da cewa yazo lafiya?
Lokacin da ya,ke ko karin tambayan shi kowaye shi,
Sai yaji mutumin na fadin kamar baka gane niba,ko ?
Ga kwanaki nai ma waya akan zancen Cikin da Ejoma tayi,
Wani irin kallon mamaki Yusuf ke binshi dashi sai cigaba da fadi mutumin ya yi ,
Ina da tun farko ka fada mincewa duk wanda ya aure ta zaka kashe mai wanan dukiyar aida an aure dani,
YUSUF ke mamaki a zuciyar shi irin yadda wanan mutumin ke maganar shi wani kamar mara hankali,
Yanzu so nake idan da akwai abin da ta haifa har zan karba,
Sai kai min wani dan ihi sani kaga sa in toshe bakin duk wani wanda zai kawo min cikasa ga ala,amari,,,
Zaici gaba Yusuf yadaga mai hannu yanna na cewa ka kai ni koto ina ga zaifi ,
Ya juya kawai abinshi batare da ya ji mai zai ce mai ba ya shige motar shi ya bar gurin,


ZEEE MAKAWA YALWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

AL,HAMDDULLILAHI RABBIL AL,LAMIN


ADDU,AN KU AGARENI NAGODE SO,SAI YAN UWA MUSULMI IRIN YADDA NAI TA GANIN SAKON TAYANI FATAN ALHERI, NAGODE MAKU KWARAI DA GASKE, ALLAH UBANGIJI YA BIYA DA ALHERIN SA👏



Tukin mota yake amma zuciyar shi ta na gurin tunanen halin rayuwa irin na Aminu masuga,
Duk da yadda yake daukar kan shi bakon shiga cikin addini
Kamar yadda mutane da dama ke mai wanan fahinta, cewa bai san komai ba akan addini tukun,
Hakan ba zai sa shi yin wani abinda zai kas,kantar da kanshi gamay da addinin shi ba irin haka,
Mutum yasan cewa ya aikata zina amma saboda rashin sanin kaidar sharia har yana ikirarin cewa idan za, a bashi wani dukiya mai tsoka zai iya fitowa fili yai ikirarin cewa shike dan da yai rejecting da farko, saboda kwadayin duniya kawai,
Kan shi ya girgiza don takaici da abin da wanan guy din yai mai yau,
Allah ya kyauta ya furta a fili ya na mai ajiyar zuciya shi kadai a mota,
Saboda sanyin da jikin shi ya yi bai iya zuwa gidan su Jibrin da yai niyar zuwa ba a lokacin,
Don haka juyawa yayi zuwa gidan shi don ya dan samu natsuwa,

Maryam wace ke zaune ta zubawa plate din da ta zuba ferfesu a gaban ta ta kasa koda kai cibi biyu a bakin ta
Tun cibin farko da takai tasamu ta hadiye shi da kyat saboda sam bakin ta batajin dadin shi ko kadan, alokacin,
Sai dan daukan spoon din tayi tana dan juya,shi a ha kali, amma ta kasa kaiwa a bakin ta,
Wayan ta ne yai kara inda taga A,A ne ke kiran ta alokacin,
Sai da ta juya inda anty dije take zaune taga cewa hankalin ta baya gurin ta,
Sai ta mike a hankali zuwa dakin ta inda zata fi jin dadin sake jiki tai waya,
Bayan ta anty dije tabi da kallo mai kama da harara, ta sake dan guntun tsaki tace a fili mara hankalin yarinya kawai,
Zama tayi saman gadon ta a hakali tana mai ansa mai sallama,
Muryan shi taji yana cew may yasa may ki maryam naji muryan ki wani iri daban,
Ba komai ta furta ahankalin sai ta baka tausayi idan kaganta a lokacin,
Don har idon ta yakawo hawaye ko tankar zasu zubo mata,
A zuciyar ta tausayin kasu takeyi don ta san cewa raba su za,a yi, bada dadewa ba,
A,A ya sheda mata cewa zaiyi tafiya sai bayan kwana uku zai dawo, har ma ya fara hanya ko,
Duk da rayuwan maryam din ya baci don rashin sheda mata cewa zai yi tafiyan da bai yi ba da wuri sai bayan ya fara hanyar tafiyan shine zai kirata ya sheda mata,
Fatan adawo lafiya tai mai inda take ce mai Allah ya bada sa,an tafiya ya karba cikkn dadi rai da cewa Ameen nagode tawa,
Bayan sunyi sallama ta kashe wayan takai wani lokaci zaune inda take tana tunanen irin rayuwan A,A narashin sani darajan abokin zama,
Ku san ko yaushe haka yake mata wanan halin wani lokaci ma sai ya kai inda zai tafine zai kirarata ya sheda mata,
Safiya ta nuna mata rashin faidar irin wanan halin amma so ya hana taga lain malam din nata,
Kiran sallah dataji anayi na la,asar yasa ta aje wayan tamike don zuwa dauro alwala,
Anty dije ce a waje take ce mata, zancen zuwa dibo Naimat da sukayi ta shirya anjima idan Yusuf ya shigo sai ya kai su saboda safe yara zasu school,
Bata rai tayi don sam batajin dadin irin haka da anty ke mata tana wani cucusa ta ga Yusuf,
Gidan Naimat ne za,ace sai ya kaisu ita da yara, saunawa tana zuwa ita da su a saman mashin,
Matsala guda dai yanzu shine dan fitinar hawa mashin yana gari, zai sa mata ido,
Rai a bace ta ansa ma yar ta da cewa aida abari kawai weekend sai mutafi mu yini mata ko ?
Maryam kece fa kikace kun yi da ita jiya zaku zo ayau din ko?
Bata kara cewa komai ba don tasan ceqa ba yarda Anty zatayi da wani excuse din da za ta bayar ba,
Tuwon semo da miyar yauki sukayi don Yusuf dake agari kawai in badon yana gari ba suna da sauran abinci da zai kai su har dare,
Sai kuma gashi yau din Yusuf din baiwani yawan shigowa kamar yadda yake yi ba idan har yana gari,

Jibrin ne yakira shi a waya yana mai complain akan KB wanda yanzu sam ya canza sosai,
Har zuwa lokacin da Jibrin din yakai karshen maganar shi Yusuf bai ce mai ufan ba,
Sai ma murmushin da yai mai alokacin da yaji cewa ya kai karshen korafin,
Yace Jibrin kafi kowa sanin halina a halin yanzu ,
Nai maku hanyar wanan business din ne don ku samu madogara har ku taimaka ma wasu daga cikin mutanen ku,
Tun a wanan lokacin ni ban kara damuwa ko wani irin hali kuke ciki ba ,
Idan har nace zan dinga bin didigin may kuke ciki da aiyukan ku ke nan badon Allah natai maka maku ba.
So kamai don Allah kafita batun shi kasa mai ido kawai , nadade da sanin irin halin da yake acikin tun lokacin da yai aure,
Addua kawai nake mai akan Allah ya sa ya gane gaskiya batare da yafada acikin halakaba
Kaiwai mu bishi da addua kaji pls ka dai na yiwa dan uwanka mugun fata,
Tsigar da yake magana ne yasa Jibrin jin wani irin nauyi don shi ya,kamata ace yai wanan maganar amatsayin shi na dan uwa kb da sukafito cikin kabila daya,
Nan yake shedawa Jibrin cewa ai yana kwantagora saboda yana son yai spending din sometimes with his Dad,
Wanka ya fada don ya dan ji dadin jikin shi ko zai rage jin kasalan da yada may shi, tun dazun,
Wasu kananan kaya yasa wando da riga duk bakake sai kwalar rigar ce kawai ke da ja,
Kamshi turaren shi na THE da JOJOBA yana nan kamar kulun,
Saida yafitane yasamu yadan ba masu gadin shi wmai dan ihi sani kamar yadda ya saba yi masu idan yazo,
Su ko sai addu,a suke zabga mai tankar yau yafara masu irin haka,
Indai har yana gari to sun yake talauci ke nan su sai dai kuma in bayan ya wuce,
Maryam wace a lokacin tana daki zaune tafito daga wanka tana saka riga don shiryawa saboda tasan cewa yau fita dole akan ta,,,,
Muryan shi taji yana sallama tuni zuciyar ta ya tsinke, saboda addu,an ta na fatan kada ya shigo bai ciba,
Muryan yaran

59 / 84