Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   32 / 84

93K to 96K   out of 251.8K words

Wani, ? Allah ya kyauta min, shi bai mun magana aure, ba nice zan masa,
Kawai dai fita batun shi, zanyi, yafi mun,
A,a maryam sam gaskiya, bai kamata muyiwa A,A haka ba kada mu kasa mashi uzuri pls,
Muzo mu kamashi da laifin daba tashiba shi baima san yayi ba,
Yanzu dai musan yadda zamuyi kafin lokacin don musan mafita
Amma dai kin san bazan iya tun,karanshi da wanan zancen ba,
Kadafa ki manta har yaya illiya yakirashi kan zancen amma sai ya doje kawai,
Shine yanzu kike ganin nizan iya tunkaran shi da wani zance can,
Kenan ma nice mai son ya aureni bashi ba,,
Kai gaskiya duk zancen ya,daure min kai wallahi,
Amma ki barni dashi kawai zan san yadda mukayi dashi,
Sam bazan nuna mashi cewa ma kin san da wanan zancen ba,
Maryam takara goge hawayen da ya kara makale mata tace nagode kwarai safiya da wanan shawarar taki,
Haba maryam kifi karfin haka fa agare ni mayye na wani godiya bayan duk yiwa kaine hakan,
Safiya tace daga gobe zan insha Allah zan tunkare shi,
Shi ko A,A yadauka duk gajiyace tasa maryam rashin shigowa school yau,
Saida wani ke ce mai ai yaganta ta shiga napep zuwa gida yadauka malam din bai shigo bane,
A,A yai mamakin ji cewa Maryam tashigo school ya batare da tai mai waya ko ta iso inda yake ba,
Don haka ba bata lokaci yadauki waya ya kira ta,yanamai tambayar ta ko da gaskakene yau tashigo school din,?
A dakile taba shi amsa da cewa eh, kawai ta kashe wayan ta zuviyar ta na mata kuna, sosai,
Mamaki fam a zuciyar shi don tunda yake da maryam yauce rana ta farko da ta taba mai irin haka,
Wanan abin yai matukar bashi mamaki da daure mai kai alokaci guda don sam bai kawo komai ba sai tunane, may ke faruwa,?
Dadare yazo gidan su amma sai tace ace mai bata nan kawai haka yasa yakara rudewa,

Washegari Safiya ta samay shi a office din shi yana zaune yana aiki acikin computer tar shi yana saye da riga shirt mai dogon hannu fara,bakin wandon Jean's a jikin shi, sai yar farar glass da ya manna wa idon shi,
Da sallamar ta tashiga office din nashi yana ganin ta yadan yi murmushi yana mata iso data shigo,
Bayan sun gaisa ne safiya ta fara shedawa A,A yadda mahaifin Maryam, yasa ta aga ita da yar ta duk dadewanan nan
Shiru yayi har zuwa lokacin da takare zancen ta da cewa mahaifin maryam ya dibar mata wa,adi,
Hankalin shi a tashe yake batare da yaiwa Safiya magana ba
Itama dai din kallonshi takeyi, don ganin irin reaction din da ya shiga lokaci guda,
Saida yaji ta tana huce da iskan bakinta yadan gyara zaman shi yana cewa,
Safiya, wallahi duk na ma rasa may zan ce dake,
Sai kuma yasoma share zufa duk da sanyin A,C dake office din nashi
Aiko magana zakayi don musan mafita, daga cikin
Yadan ce cikin marairaice murya, wallahi safiya akwai abin da nake planing akaine, shiyasa,
Bawai sharewa nayi ba yadda kuke nufi, ba
Safiya tace malam ba fa wai aure akace kuyi yanzu ba fa
Kawai da ka gabatar da magabatanka suga iyayenta don manya su shiga shiga cikin zancen,
Saida ya kara share, fuskan shi karo na barkatai,
Safiya tace kaga aure sai lokacin da katashi ke nan,
Yace nasan da haka safiya amma abin dibawa anan shine kokari nakeyi ingama abubuwan dake gabana tukun
Su kwantar da hakalin su bawai zan yaudareta bane,o something like dat,
Kawai dai zan samu, illiya idan yazo muyi magana akai,
Safiya tace malam idan har bada magana mai karfi zaka je ba kada katafi pls,
To safiya idan sun min haka basuyi min adalci ba gaskiya
Kallon shi safiya tayi da mamamki,
Tace malam waiko kasan duk maganar da kayi da mahaifiyar ka ranan da kukaje da maryam gaida ita duk a kunen maryam ne
Ido waje yake kallon safiya da mamaki da kaduwar jin zancenta,
Nan dai takwashe komai tafada mai wani rin nauyi da kunyane suka lulube shi lokaci guda,
Safiya takare zancen ta da cewa malam don Allah kada k bawa maryam, baya ka guje ma,ta
Sai kuma sai zuciyar ta yai sanyi tana batun sa kuka,
Tamike tabar office din batare da ta saurare shi ba,,


ZEEE. MAKAWA
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
3โƒฃ9โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

Alhamdullah Yusuf ya kammala wani course da yadan kara tsayar da shi kasar Korea,
A harkan business ne dama ya tsaya don kara ita fasaha akan, kasuwanci
Don haka yanzu kimanin watan shi takwas ke nan rabon shi da kasar shi,
Duk abinda yakeyi yanzu hankalinshi yakoma gida Nigeria musan,man kakar shi wace yabar ta kwantagora, tare da Dad din shi,
Saboda yasan cewa babu shiri atsakanin su saboda banbancin churches din su, da suke bi,
Yasan cewa yan church din su Dad basu kaunar mabiya Olumbo,
Sonny ya na hankalce da Yusuf din duk kwanakin nan baya son walwala sosai,
Lafiyayyen abinci tare da abin sha daga yayan icce,aka hada masu a matsayin dinner yau,
Sai da Yusuf ya idar da sallah shi na isha,i tare da,shafa,i da wuturi,
Sanan ya koma yai wanka yafito cikin shirin shi,
Yayi mamaki Kwarai da ya samu Sonny a zaune yana jiran shi,,
Yusuf yadan bashi hakkuri tseda shi da yayi har zuwa wani lokaci,
Cikin daga hannu Sonny wanda,yake saye da wata far coth da wandon shi fari, sai bakar shirt da yasa daga ciki,
Yadan, dago wa Yusuf, hannu alamar ya share ba matsala, kawai,
Nan suka zauna suka fara cin abincin su hankali a kwance,
Saida suka dan dauki lokaci batare dayin wani magana ba sai karar cibin da suke cin abinci kawai kake ji yake tashi,agurin,
Sonny ne yadan dago kai yakalli Yusuf wanda dabi,un cin abincin shi yanzu duk ya canza,ba kamar da ba can, baya,
Murmushi mai sauti Sonny yayi wa Yusuf wanda hakan yasa shu dago kan shi yana mai kallon shi,,
Sai kuma ya daure fuska acikin yar damuwa yace,
Man this your religion is good, and have a nice characters,
Unlike Christianity,
Da sauri Yusuf yadago kai ya kalle shi,
Yace ma Yusuf man see how yo pray everyday,
Bayan yawan sallah da kuke yi a kullun, batare da damuwa da ko kowa ba, alokacin yinta,
Amma su Christian saudaya kawai suke zuwa church a cikin sati, inda wasu ma bawai dole su tafi ba,,
Littafinku mai tsarki muslumai dayawa sun haddace shi a kan su ,
Littafin ku mai tsarki Alkur,an, yana nuna abu guda ne ga kowani irin yare za,a fasssara shi,
Zaku iya shiga kiwani irin massalaci kuyi salkah aduk lokacin da ta riske ku
Ba kamar Christian ba suda da angan ka sai an tambaye ka wani church, kake zuwa a cikin sati,
Idan kafadi wanda ba nasuba, zasu iya bata rai, dakai afili,
Dazaran ance kai musulumi to daidai kake dakowa daga cikin musulmi, kuma a nuna ma so da kauna alokaci guda,
Sai kuma duk abinda ka iyayi dazaran kace Allah shikenan an yarda da zancen ka,kowace iri ce,
Amma su Christian dazaran kace God zaka zama abin zargi ke nan in ma bakai hankali ba sai antara ma taron,mutane,
A bincike ka, wani irin God, kake zance shi god din yan Catholic ne ko god din Anglicans, kona na living faith, kok, shin na deeper, life,
Duk da su ma musulmai suna da wayan nan akidodin a tare da su amma sai kayi nisa sosai a cikin su zaka iya ganewa,
Amma su kan Christian a filli suke nuna nasu,
Zaka iya jin ance maka ai jabun pastor ne wani
Banda musulumai da ko yaya imanin ka yake zasu iya binka sallah, a jam i
Gashi su musulmai aduk lokacin da suke azumin su na watan ramadam mai tsarki, duk duniya zasu sani sanan sauyi zaizo wa kowa daga musulmai har Christian alokacin wanan azumin
Amna baka taba jin wani abu maka mancin haka acikin bautar Christian,
Idan wani abin al,ajabi yafaru musulmai zasu yarda da cewa daga Allah, ne amma su Christian sai su ce wai in Jesus, name, wasu kuma suce karfin shedan ne,
Zaka ga idan mai wa,azin musulumai yana waazi, musulumi koda karamin yaro ne ya kewaye shi yana saurare har zuwa lokacin da za,a tashi koda kuwa mutum nada abin yi alokacin ba zai tafi ko ina ba, ko fitsari azasu yarda su tagiyi ba don kada afadi wani abinda basu ji ba,,
Idan ka lura da musulmi yana girmama pastor afili, badon komai ba sai don sanin cewa shugabane na addini,
Amma,su Christian suna jin haushin limamen musulumai sosai,
Yadda zaka ga musulmai suna girmama shugaban nin su sai kaga su Christian suna kokarin gardama da pastor cin su,
Kai abubuwa da dama nayi searching din su naga akwai bambanci halaiya so sai a tsakani,

Tunda ya fara dogon sharhin shi Yusuf yadakatar da cin abincin da yakeyi yana mai tsura mashi ido,
Acikin zancen Sonny din Yusuf yagano cewa akwai wani magana mai muhin,manci, da Sonny din ke son yi dashi,
Hakan yasa ya tatara hankalin shi gabadaya yana mai sauraren shi,
Yyana kaiwa karshe sai ya kalli Yusuf da kyau ya aje cokalin da ke hannun shi a cikin plate din da yake cin abinci,
Yakara duban Yusuf din sosai, yace a yar fahintar da nayi yanzu Joe nagane cewa muna da banbancin addini sosai ni da kai,
Kaga zancen mu hada harkokin mu kamar yadda muka saba ada bai taso ba ,
Kagane ko?
Yusuf yace,,
Fadi maganar ka kawai ina sauraren ka ai,,
Sonny yadan girgiza kai yana mai cewa don haka na yanke shawara nakuma rubuta komai a rubuce har an sa min hannu, cewa
Nabar maka duk wasu kaddarori da suke a hannun ka saboda nasan cewa kana bukatar taimako yanzu a rayuwar ka so sai,
Nayi hakane don in kareka daga duk wani barazanar da za,a yi kawo maka na cewa zasu iya gurgunta ka daga cikin har kokin ka,
Wata irin karfafan ajiyar zuciya Yusuf ya sake da yaji wanan zancen na Sonny,
Fuskan shi dauke da alamar damuwa mai fayyace mamaki aciki,
Magana Yusuf din ya fara cikin wata irin murya mai ban tausayi don duk mamakin wanan hukuncin na Sonny ya ruda shi,,
Kawai sai yaji Sonny din ya kaure da wani mahaukacin dariya alokaci guda,,
Sai kuma ya koma ya tsuke fuskan shi ya fuskanci Yusuf din karo na biyu yana mai kura mai ido cikin ido,
Yace may zakace min Joe, koka manta cewa da taimakon ka muka kai wanan matsayin da muke aciki ni da abokina
Inda Allah bai hada mu da kai ba ka dage har saida kaga mun gama karatun mu aida ba mu kai haka ba, ko ?
Mikewa yayi ya zagayo har zuwa kujerar da Yusuf yake zaune yadan duko yarankwafo zuwa gare shi yana mai magana kamar cikin rada,
Yace , don't say thanks pls,?
U deserved it
Yusuf wanda kanshi ke a duke don jin zancen yake tankar a mafarki,
Ya dan dago kai ya kalli Sonny din kara na biyu cikin mamaki,
Murmushi na gamsar wa Sonny din yai mai alamar eh,
Haka suka tashi gurin inda Yusuf kewa Sonny adduan fatan shiryuwa hanya madaidaiciya ,
Batare da sanin Sonny ba Yusuf ya gai,yato su jibrin tare da KB inda sukazo mai tare da,Abdulsamad,
Saboda yanzu suyake ji tankar yan uwan shi na jini,
Sunyi mamaki sosai irn dinbin dukiyar da Sonny ya tara a kasar mutane haka bayan ga kasar shi can na haihuwa suna bukatar shi,
Sun yi wa Sonny godiya sosai dafatan kara samun daukaka a dukiyar shi,
Shiko sai mamakin irin yadda suka dauki joe tankar dan uwar haihuwar bawai kawai saboda addini suke nuna mai haka ba,
Sosai Sonny yaji dadin zuwan su inda ya mai dasu kamar wasu manyan guest din shi,
Satin su guda sukadawo gida cike da farinci, dakuma alheri mai yawa,
Saida Yusuf ya tabbatar da cewa komai da ya turo su Jibrin da shi da KB sun kammalla mai
Sannan ya fara shirin komawa gida Nigeria, tare da karfin gwiwa atatare da shi,

ร€nty Dije ce zaune a saman tabarman robar da ta shimfida a,waje saboda zafin da akeyi a garin tankar rana zai dafa mutum,
Gefen ta Abubakar ne a kwance cikin net na yara yana barcin shi hankali kwance,
Maryam ce ta fado gida a daidai wanan lokacin, cikin gajiya tashi gida da sallamar ta a bakin ta,
Anty Dije tadan daga kai, takalle ta gami da ajiyar zuciya,
Tacd don Allah maryam, huta kidan taimaka min muyi aikin nan,
Maryam wace tanawo wani farin kujerar roba dake aje a gefe guda, ta zauna,
Tace wai Allah ana dai zafi gaskiya, sosai shi yasa yau ma banko tsaya jiran safiya ba na sa kai kawai na wuto,
Kallon ta Anty Dije tayi cikin yar tuhuma kamar zata daure sai kuma ta kasa
Tace shi A,A din ya daina dauko ku ne yanzu,?
Maryam wace tambayar yazo mata a bazata,
Shiru tayi saboda ta rasa ansar da zata ba Anty Dije a lokacin,
Kara maimaita tambayar tayi wa yar kaunar nata,
Wacce dama duk kwanakin nan tana lura da bata acikin walwala tun lokavin da baba yazo da zancen ta,
Dan hawayen da take kokarin makalewa, ne yadan digo daga idon ta,
Ki tashi ki dauki abinci kici inji Anty saboda ta fahinci, cewa kuka kaunar nata take shirin yi,
Tausayin irin hanlin da yar uwan nata take ciki takeyi
Saboda ta san cewa tana cikin wani hali saboda so,
Maryam ta share hawaye ta da bayan hannunta ta mike zuwa cikin da kunar su,
Kallo anty Dije tabi bayanta dashi tana mai mata fatan alheri a rayuwa,
Fatan dai Allah yai wa Maryam din zabi na alheri, a rayuwa,
Tunda maryam tashiga ciki tana zaune, a bakin gadon ta ko, takalma bata cire ba akafar ta,
Wayar ta dake a cikin jakar ta ce tai kara alamar kira,
Kamar ta share kamar kullun saida tace bari yau ta dauka taimai kashedi ya daina kiran ta kwatakwata,
Cikin wani irin murya mai birkita maryam a duk lokacin da taji shi,
Wanda yasa gaba daya duk maryam din ta rikice, alokaci guda ta rasa duniyar da take,
Wani irin taji aranta na yadda sam bazata iya fada mai maganganun da ta shirya fadamai ba,
Maryam ta saki wani irin ajiyar wanda shima A,A din yaji kamar yazo inda maryam din take alokacin yabata hakkuri duk da irin kunyarta da yake ji,
Shima A,A din anashi bangaren ajiyar zuciyar don jin cewa maryam din tadan sauko daga fushin da ta dauki lokaci mai tsawo tana yi dashi,
Yakara cewa cikin wata irin murya ransarauniya maryam yadade ga A, A gaban ki tuba yake yi,
Murmushi ne ya subuce mata tai shi a hankali, duk yadda taso tai magana alokacin ta kasa,
Yace Maryam ina fatan zaki bani dama in zo in maki bayanin irin abin da ake ciki,
Shiru tayi saboda sam bata san may zai ce mata ba idan har yazo din,
Tasan dai bai wuce yace mata kawai tayi hakkuri ya aure su su biyu kamar yadda safiya tace yace,,
Wani irin ajiyar zuciya tasake tace, idan zuwar naka bazai zai haifa min alheri ba kawai kabarshi
Yar dariya tayi irin ta mazan da suka san kan su,
Ya Allah dai ya kai mu anjima ki dubi hanyata nagode,
Idan ta ta lumshe tanamai jin wani iri atare da ita
Ajiyar zuciya tayi mai fitar da sauti tana mai bude idon ta, da suka sauka a saman na Anty Dije,,,,,,

ZEEE. MAKAWA
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
4โƒฃ0โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,,

Yan uwa musulmi barka mu da jumma,a , Ubangiji Allah yasada mu da Rahama da Albarkan da ke cikin wanan ranan,
Allah ka yafe muna kurakuraren mu Allahuma Ameen,๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘

Sanye yake cikin wasu, fararen coth, da wani, farare, takalma rufaffu, kayan sun karbi,
jikin shi, sosai, sai idon shi dake saye da dan farin glass karami,
A hankali yake ta,kowa daga matakalar jirgin, guda ,guda, hannun shi,guda yana cikin aljihun wandon shi,
Jirgin su a airport din Lagos ya sauka, inda masu taron shi suka zo,,
Gurin screening yanufa batare da wani bata lokaci ba akai mashi, duk wani screening yadda yakamata,

32 / 84