Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
gyaran dakin
Inda ya kwashe sauran kaya yasa acikin wardrobe din bangon dake dakin,
Ya kule ya tura keys din a cikin aljihun shi ya koma falo don ya karya,
Sai a lokacin ya lura da cewa Aisha ta ta,fi kila don bai ganta ba,
Har waje ya leka yagani ko zai ganta sai dai babu ita babu alamar ta ya ja yar guntuwar tsuki yakoma cikin don shi sam batai mai ba,
Yusuf yafito yasamu babu kowa a dakin dan haka sai yadan zauna a bakin gado,
Cikin shigar jallabiya yadan samu yafito falon shi yazauna,
Remote din TV ya dauko ya kuna TV, inda ya kamo NTA kwantagora,
Ya soma kallo,
A inda yake a hankali ya soma jin kan shi na wani juyawa kamar za,a kife shi a gurin,
Addu,an da ta koya mai ne yazo mai arai don haka yadan lumshe idon shi yana mai rike kan shi da hannu guda,
Sannu a hankali yake yi yana tofawa a hannun shi ya shafawa asaman kan shi har bayan shi,
Kamar an wallawale shi yaji saidai kuma yaji baya kaunar kallon TV don haka yabar shi a kunne ya koma ciki,
Sallama take ta kwadawa babu kowa a falon hannu ta dauke da basket, din abinci,
Sai TV da ke ta aiki shi kadai, a lokacin, babu kowa agurin
Tai mamaki kwarai na rashin ganin wani a gurin a lokacin,
Don haka sai tai shawaran ta diba dakin ko suna ciki,
Babu kowa a dakin sai shi kadai, ke kwance saman gado,
Idon shi a rufe tayi sallama ta shiga a tuna,nen ta ko barci yakeyi a lokacin,
Don haka sai ta juya a hankali don ta koma falo ta aje basket din,
Da wata dishashiyar murya yakira, sunan ta a hankali,
Batare da ya bude idon shi ba dake a rufe,
A, take jikin ta yai wani sanyi,
Cikin dakiyar murya tace ai ina ce ko barci kakeyi, ta samu kanta da fadar haka,
Shiru na dan wani lokaci bai sauke hannun shi da ya dafe goshin shi ba,
Don haka sai tai niyar juyawa still don ta aje abincin dake a hannunta,
Da sauri ya sauke hannu yakalle ta da rinanun idanun shi da sukayi jawur, sai kace wanda yai kuka,
Da sauri maryam tace subbahanallah,
Wanda fadar hakan yai daidai da shigowar Ibrahim wanda yaje dayan dakin yai wanka,
Ibrahim yace mata cikin muryan damuwa,har kin dawo ko ?
Ta amsa mashi da eh a takaice,,
Muryan Yusuf sukaji yana cewa cikin lumshe ido dan Allah ki kara yi min addu,an dazu don naji dadin shi sosai wallahi,
Basket din ta aje ta koma falo kamar dazu da dawo dauke da ruwa da cup,
Wanan karon a bakin gadon da yake zaune ta zauna da kanta,
Baiyi aune ba sai jin hannun ta yayi a saman goshin shin
Sannu a hankali tafara rairo mashi addu,oi tare da wasu ayoyi masu koran shedan,
A hankali ta zare hannu ta daga goshin na shi da ta rike,
Wani irin, lunshe ido yayi lokacin da yaji ta zare hannun ta daga goshin shi,
A cikin cup din take addau,a akaro na biyu indon ta a lumshi take rairo karatu,
Daga shi har Ibrahim kallon ta sukeyi cikin mamakin jin yadda take rairo karatu, cikin murya mai dadi,
Bayan tagama ta tofa sai ta mika mashi, tabash da kan ta ya karba yashan ye,
Sai yadan rage saura kamar yadda tace dazun, ayi, ibrahim ne ya matso da sauri, yakarba ya sha,shafa mai ko ina,
Har inda take taji yadda yake ajiyar zuciya, da karfi,
Tsam ta mike tsaye daga zaune zuciyar ta duk a chakushe, ,
Saboda dagani ko ba,a fada ma ba kasan yana jin abu, so sai,
Karan kara sauke ajiyar zuciya yayi tare da yin wani irn, atishawa, mai karfi,
Shiru yabiyo dakin duk kan su uku ba mai cewa komai har zuwa wani dan lokaci,
Kowa da abin da zuciyar shi ke sakawa, alokacin,,
Sautin muryan shi taji yana cewa ta taimaka ta zuba mai abin ci
Ba musu ta nufi gurin basket din nan,ta zuba mai leda guda na tuwon ta bude bai cikin place plate,
Amma sai yace ta rage ahankali takai duban ta ga abinci wanda ko rabin plate bai yi ba,
Dankadan ta zuba mai ya mike zaune da kyat, yana cije labe,
Takwao ruwa tazoba mai sai ta aje mai wani plate don wake hannu,
Kadan yaci yature plate din yace ya ko shi,
Su hudu suka shigo wanan karon on tare da wani tsoho mai farin gemu taf ga fuska,
Wanda sun shigo ba,a dade ba su KB da Jibrin suka shigo su ma wanda isowar su ke nan garin,
Ibrahim yakara basu labarin duk abin da ya faru bayan fitar su
Tsohon nan mai farin gashi yai yar murmushi irin ta manyan masana,
Kallo guda tsihon yai mashi ya matsa kusa da Yusuf din ya kamo mai hannun shi ya rike acikin nashi ya mai furta wasu addu,oi,
Sai ya sake hannuwar na Yusuf yakalli inda malm Abdulsamad yake yace,
Yace wallahi sihirine mai karfi akan shi, irin wanda, duk wanda akai mawa shi sai Allah,kawai,
Yace wasu kafiran aljannu aka hada shi dasu, don yaji cewa kasar kwantagora tafita a rayuwar shi kwata kwata,
Abdullsamad yaka da kan shi yace nasan za,ai haka gaskiya shi yasa naki bari mukaishi asibiti kamar yadda aka bukata, akai shi din,
Yace nasan halin mutanen mu basu barwa Allah abu sai in sun ga cewa abin yafi karfin su,
Yace wallahi akwai wace aka haukata, mace, saboda kawai ta musulunta, yace mai makon yan uwa musulmai su dauketa ai mata magani ko Allah zai kawo mata sauki sai akabarta har ta mutu hakanan,
Sai daga baya labari yazo min nan cewa ga irin abinda ya samay ta ai,
Amma a,lokacin ni banda karfin da zan taimaka mata, har manya nadinga bi ina fada masu amma ba wanda ya kula, mun,
Yace haka wata kuma itama mace ce wani abu suka turo mata agaba takoma wata iri duk inda taje sai kokarin tabudewa mutane suka gani taje yi, har ta kare a hakan,
Balle irin kabilar mahaifin shi Yusuf din ko a cikin IBO tsiron su ake ji don mugun tsafin su,
Shima ai an mashi mai kyau ke nan, tun da basu haukatashi ba,
Mahaifin Jibrin yace ina fa mai kyau malam Abdulsamada a haka,?
Allah dai ya haushe shi kan su kawai, zamu ce, yanzu kan dole ne mu tashi tsaye sosai gurin ganin mun yakince su,
Dakuma badhi tsari madu karfi ajiki da addu,oi masu kariya daga sammu,
Jakar da ya shigo da ita ya bude ya ciro wani shake ya mikawa, mahaifin jibirin din yace su shaka mai a fara gani,
Sai,kuma yafida wani kulli acikin wani tsunma, ya,mika masu, yace a samo garwashi mai wuta, amai hayaki da shi, yau zuwa gobe gaba daya kafin ya dawo,,,,,
ZEEE MAKAWA
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
4β£8β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Har kulun kira ga marubuta yan uwa na musada alheri ga al,uma yafi sada shedanci ga al,uma,
Bin ra,ayin wasu don farauta masu zuciya bashi zai taya ka zaman kabari, ba,
Duk sakon da muka rubuta gobe sai an tambaye mu akan shi,
Mutuwa ba fashi haka Hisabi ba fashin yin shin gobe kiyama,
Tun a makwancin ka zaka gane makomar ka,
Allah kaba ikon rubuta alheri a sakon nan mu,
πππππππ
Tun da ya shaka shake yake wani irin atishawa mai karfi, babu kakautawa,
Sai ya baka tausayi idon shi sun rine sunyi ja jajari kamar garwa shin wuta,
Sai hayakin da tsohon ya bayar yace ai, mai shi gaba daya a ranan,
Daga gidan Anty Dije akazo da gawayi wuta saboda basu san mutane su san cewa, Yusuf baida lafiya haka, har labari yakai wa mahaifin shi,
Wanan malam tsoho din shi da kanshi yazo tare da wasu yaran shi,
Duk wanda ke cikin dakin akace yafito waje ya samu guri kada ya tsaya kuma tsaye,
Idan ma son samu ne dan Allah duk su watse subar malm Abdulsamad da , mahaifin Jibrin,
Haka akayi kuwa don su KB da su jibrin da Ibrahim duk barin uguwar su kayi, gaba dayan su,,
Fara karaun su malam bada wani nisa ba sai murya sukaji da yare ana magana,
Malam tsoho yadaga kai ya kalli Abdulsamad don ya yi magana,
A cikin harshen IBO suke ta gwalancin su da malam Abdulsamad din,
Abinda suke cewa shi idan ba yabar kasar kwantagora ba bazasu bashi peace of mind ba zasu jagula mai lissafi,
Yai ma malam tsoho bayanin abinda suka ce, sai kuma cewa da sukayi saida a ka yanka masu katuwar bajimin shanu suka sha jinin shi sunyi ma wanda yasa alkawarin cewa za su yi mai aikin shi kamar yadda ya kamata,
Malam yaba yaran shi umurni suci gaba da karatun alkur,ani kawai, babu tsayawa,
Wani irin ihu suka tsala saida wasu suka firigita murya sak na irin IBO din nan tipical one wa yanda basu da imani sam,
Sai suraitai sukeyi da yaren su na IBO suna ta zun duma asharrr,
Duk wanda ke tare da Yusuf hankalin shi ya tashi a lokacin don ganin irin yadda yadinga yi,
Sun jima akan shi sosai sai daga bisani suka ji muryan su suna cewa sun bar shi har abada
Duk da haka ba,a daina karatun ba saida sukaga cewa ya daina komai da yake dazun sanan su ka dakata,
Kwana biyu suna sintiri akan shi tare da bashi addu,oin da zasu taimaka mashi,
Sai yau da yaciki kwana biyu da samun sauki, Jibrin ya kwaso su Anty tare da Safiyar shi da maryam sukazo gaida Yusuf a gidan shi dake Abu,lolo,Eastern,
Maryam da Anty da yaran su , suna bayan mota zaune inda Safiya ke zaune gaban mota tare da Jibrin,
Iyakar burgewa sun burge Maryam sosai tun lokacin da Anty tace wa Safiya ta zaune gaba tare da Jibrin din,
Saida suka tsaya wani shago sukayi mai tsaraban kayan fruits kala,kala shake a leda duk da Jibrin yace kada su saye, akwai shi cike a gidan,
Amma sai Anty Dije ta, ce su dai saye tunda ba,a zuwa gaida mutum hannu saje,
Zaune yake saman sallaya a folon shi ya kunna tashar madina yana sauraron kira,a,
Yana saye cikin wata yar farar jallabiya mai guntun hannu,
Da sallama suka shiga inda Ibrahim yatare su cikin mutumci,
Γnty Dije tace a,a lalai Yusuf jiki yai kyau, tunda yau gaka zaune,
Yana kokarin tashi zaune don tariyae su hannun shi yana dauke da casbaha, yana ja,
Da murmushin maganar da anty tayi yakai zaune da kyau saidai bayan shi na jingine a kujeraa,
Kafin ya kai karshen murmushi sai Anty Dije takara cewa gaskiya dai ya kamata yanzu ace Yusuf ka aje mata kodon taimaka maka da wani abu,
Yar dariya mai sauti yakarati daidai lokacin da ya zauna da kyau Assalam yana kusa dashi zaune,
Jibrin wanda ke shigowa adaidai lokacin yaji maganar da Anty taiwa Yusuf sai ya cabe zancen da cewa ai barshi kawai anty,
Dama akwai wata Cousin sister dina da ta sani gaba da zancen Yusuf tunda dadewa,
Ibrahim dake ta gurin fridge yana aje ledojin da suka shigo da su yace,
Aiko zakayi fada da Aisha idan taji ka da wanan zancen,
Kai Aishan may can inji Jibrin wanda ke kokarin zama saman kujerar da Yusuf ya jingina akai,
Daidai lokacin yadago kai inda Safiya da Maryam suke zaune guda saman kujera guda tana zaune a hannun kujerar,
Murmushi yai masu yana mai ansa gaisuwar da safiya tai mai,
Itama maryam gaishe shi tayi a hankali tare da tambayar shi karfin jikin shi,
Duk hiran da akeyi daga Maryam har safiya babu mai cewa komai daga cikin su,
Sannan ita Maryam bata jinko mai gamay da Yusuf har kasan zuciyar ta,
Kamar yadda shima Yusuf din bai, jin komai gamay da maryam azuciyar shi sam,.
Dan daukar ta yajeyi a matsayin yan uwa kawai daga ita har Anty Dije,
Daga kofar shigowa gidan suke jin murya ana sallama,
Ibrahim ne ya leka dan ganin mai yin sallaman alokacin
Baban su maryam ne da Anty wai yatafi gida ake cemai sun zo nan mai,gidan bai jin dadi shi ne,
Duk sunyi mamakin ganin baba amma sai suka ga cewa kanin ya illiya ne ashe yakawo shi,
Baba yai mai fatan alheri tare da fatan samun sauki,
Anty Dije ce take cewa baba yau ba,a fita kasuwa ba ke nan ko ?
Kaiyya Dije ai kasuwan sai a hankali yanzu, mutum ya fita tun safe karshe baifi yasamu abin sayen abincin rana ba kawai,
Yanzu kinga aiduk dan jarin ya karae sai maneji nakeyi, kawai,
Allah ma ya taimakeni nasamu makwaci mai albarka shike taimaka min watarana,
Baba bai dade ba ya mike yana cewa to shi zai koma, inda su Assalam ke cewa baba tsoho ka sayo muna mangwaro a kasuwa,
Maryam tace akin a saya maku nawa kuka bashi jari,
Baba yace a,a yar Baba kyale su ai zan sayo masu ko kadan ne,
Saidai ba kamar da ba leda ce ya miko wa Yusuf yace abin gyaran baki nagani a hanya nasiyo ma,
Jibrin ne yamike yabi bayan baba da yara suka bishi har kofa suna cewa ya sayo masu abu kaza da kaza,
Sai ga baba yadawo cikin mamaki da kudi rike a hqnnun shi yana gwadawa Anty dije kudin zaikai dubu biyar,
Yadinga sa masu albarja dafatan alheri a rayuwan su,
Sai da baba ya wuce Anty dije tacewa maryam ta dauko wa Yusuf fruit ya sha,
Yadan daga kai yakalli anty yace da na anbarshi ai, don ban dafe da sha ba,
Maryam wace a lokacin har ta dauko wani plate ko daga ciin basket din abincin da suka shigo da shi,
A gaban shi ta aje fruit din har zata juya sai Anty tace mata,
Bude ledar da baba yakawo mugani, ko may ye acikin shi haka, ?
Zogala, ne mai yawa hade da kayan gyaran shi
Wani plate ta,dauko ta juye aciki inda Anty, ta bukaci a zuba mata,
Tayi hakane don Yusuf ya sake jiki yaci zogalar don zai gyara mai bakun shi,
Har safiya saida suka vi zogalan amma banda maryam wace ke zaune ta kura ma tv ido tana kallon yadda ake rubuta haruffa kira,ar da akeyi,
Ke baza kici ba ne, yatan baye ta a hankali saida safiya tadan tabo ta sannan tagane da ita yake yi,
Kan ta dake kasa ta girgiza tana wasa da wani dan stone da ke makale a gefen kujera,
Idon ta kem akan shi sai yanzu ta ga irin raman da yayi cikin kwana biyun nan,
Harda wani dan kwarmi kwarmin gurin idanun shi yayi,
A hankali yake cin zogalar shi hankali kwance ba abin da ya damay shi,
Kallon shi sosai taba da himmar yi, hakan yai daidai da dago idon shi daya don yace ta miko mashi ruwa,
Kanta ta mayar kasa da sauri, cike da jin kunyar shi na kama ta da yayi tana mai kallon kurulla,
Maryam help me with water pls,
Yace alokacin da ya kura mata ido,
A kunyace ta ansa mashi da to,
Tamike a hankali har zata fara tafiya sai kuma ta tsaya tadan kalli inda yake tace mai sanyi ko kuwa,
Kai ya girgiza mata alamar a,a mara sanyi yake so,
Goran ruwan majidadi water ta aje mai a gaban shi, ruwa mai kyau da tsabtar sha,
Sai cup da ta hado mai dashi nan yaron anty Abubakar yaga ruwa sai yaron ya hau tsalen cewa abashi ruwan yasha shi ma,
Yaron na,ta kokarin zillowa daga jikin uwar shi,
Abubakar sadiq ko ruwan kake son shane inji Yusuf wanda hankalin shi ya kai ga yaron,
Kyale shi kawai, a,a haba anty ruwa fa yake so, ko banza aikin san mai sunan ba abin wasa bane fa,
Sunan amin ma,aikin manzon Allah ne, shiyasa nake girma ma duk mai wanan sunan,
Ruwan ya tsiyaya a cup ya cewa Maryam miki min shi yasha,
Yaron ke faman kwankwadar ruwan amma ita maryam duk wani irin shock ke jan ta,
Saboda dan hucin numfashin Yusuf dake bugo ta,
Shima bangaren Yusuf din hakane yake ji kamshin turaren Bushrah da black oud din data shafa duk ya wanu susuta shi,
Zogalar da yadaina ci ke nan saboda wani irn mugun kasalar da ya sauka i a lokaci guda,
Assalam ne ya cinye duk sauran zogalar
Idon shi yana a lumshe bayan shi da wuyar shi suna jingine