Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   56 / 84

165K to 168K   out of 251.8K words

tagani a rubuce saman screen din wayar nata,
Sunan ta kara nanatawa a fili don mamakin da ya mamaye zuciyar ta
Da sauri ta dauka don bata san ko may ya sa ya,kirata ba, a daidai wanan lokacin
Assalamu Alaikum tace a lokacin da ta dauki wayar,
Shima a nashi bangaren wani iri yaji a kunnen shi a lokacin da tai wanan salaman,
Shirun da maryam taji yayi ne a lokacin yadan kara sa ta cewa 'Hello"
Ajiyan zuciya taji yayi a lokacin inda ta ji shi yana cewa hello,
Uncle naga kiran kane shine na dauka, murmushi taji yayi yana mai cewa sorry bake ce ,naje kira ba,
Cikin yar muryan nan nata mai kama da sarewa tace ok,
Wallahi har gaba na yafadi ina ce ko nai wani laifin ne akakirani ai min fada,
Fuskan shi kum she da murmushi ya ce, au ke kuma ba kyason kiyi laifi ko,
Tana yar dariya tace to ai kaine uncle ba wai sai mutum yai ma wani lafi ba zaka haushi da fada,
Murmushi mai yar sauti ya sake yace ke maryam bana son sheri yaushe nake maki fada ni,
A hankali tace ai kai baka sani uncle sai dai kabar mutun yana ji a zuciyar shi,
Muryan shi cike da amon dariya yace nagode da wanan kazafin maryam,
Lah tace wallahi ba kazafi bane nai ma sai gaskiya kawai,
Ni ba ruwana ban ce nai ma kazafi ba ai
A hankali yace gaskiya kin min don dai ni na san cewa fada na dake shine a kan hawa mashin ne kawai,
Sai kuma taji ya kwantar da muryan shi a hankali yana magana yana cewa,
Maganar gaskiya maryam bana son in ga mace wace na sani a kan mashi, wallahi duk nakan ji rai,na ya baci so sai,
Balle ke da kike ta daban a guri na maryam don may bazan maki fadar hawan mashin ba,
Inda za,a yarda min in saya maki mota batare da an tunhumi komai ba da wallahi na dade da saya maki,
Wani irin nauyi da kunya ne ya kamata tankar yana kusa da ita alokacin,
Kanta na kasa tana mai kurawa ties din dakin su ido tace ,
Haba dai uncle kamar wata mai wani matsayi a gurin ka ni a su wa da har za,a sai min mota,
Bai yi magana ba amma murmushi yaiwa zancen nata kawai,
Ok wait and see yace, mata a hankali,
Dariya ta yi mai sauti ta cikin ciki ,kaman ya na mai, ganin, ta,inda take kokari ta shigar da maganar, da cewa ai sai dai Anty Sadiyar ka ko Anty Aisha ko,
Sune manyan mata da suka dace da shiga mota a garin nan don a,san suna tare da kai,
Duk da ya fahinci irin maganar da tai mai amma sai ya dake da cewa,
To sai gashi kuma wace bata kai su ba tana kokarin ta riga su shiga ba,
Murya cike da maganar serious yace mata maryam,
A gaskiya bana son kina hawan mashin din nan pls,
Ya na,nata tambayar shi don jin shirun da yayi ta na bangaren,
Yace mata acikin murya mai taushi da Kin ji ?
A hankali ta ansa mai da cewa ,"To" uncle,
Cikin wata murya yace, mata kin yarda bazaki kara hawa bake nan kin amince, ko ?
A hankali takara ansa mai da cewa Eh uncle,
Nagode nagode nagode maryam insha Allah zan yi kokarin ganin kin daina kwata,kwata,
Kamin wanin su ya kara wani magana, maryam ce tai saurin cewa uncle nagode sai anjima kada na damay ka,
Sai ji tayi yace ai idan kece bazan ji damuwa ba maryam
Saboda may uncle maryam ta tambaya a kage,
Saboda kawai kina kaunata, kina sani natsuwa aduk lokacin da nake waya dake,
Baki ta dan tabe, alamar kaji dashi tace ashe kuwa A,A nada gaskiya ako yaushe yake a cikin fushi yace idan ba ya kirani ba baya kan samu relief,
A she ko zai daina jin relief idan yai wasa don dai kwanan nan zanwa kaunata aure
Don shi naga bada gaskiya yakeyi ba ,
Dariya maryam tayi wanda bai masan cewa ta iya irin wanan dariyar ba,
Tace uncle har ka sani babban dariya ka ma dai yi min miji ke nan ko ?
Kanshi ya hirgiza tankar tana ganin shi a gurin yace No but zan dai yi maki soon,
Duk a cikin gwarigwarin hausar shi da yar muryan shi mai daukan hankalin mai sauraro suke zan cen,
Da haka yana jan ta da hira har dare yadan yi basu ankara ba,
Inda duk kan su suka sake suna ta surutu da junar su,
Daga karshe maryam ce tace mai ya kwanta hakanan don yasan gobe yana da baki yan daurin aure,
Bai musa mata ba sukaui sallama da junar su kowa yana mai farin ciki na rashin sanin dalilin haka,
A haka maryam ta kwata da, yar murmushi makale a fuskan ta,,,

Washe gari aka daura auren Naimat da Ibrahim akan kudin sadaki naira dubu hamsin
Jama,a sun karba gaiyyatar da Yusuf tare da Abdullsamad suka kai masu inda suka sheda wanan daurin auren da akayi,
A kofar gidan su Jibbrin wanda mahaifin jibrin din ya zama waliyin amarya Naimat,
Bai wani bidia,a ba sai walimar da maza sukayi a kofar garkan gidan Abdulsamad, din,
Don haka duk yinin ranan Yusuf bai samu shigowa gidan anty dije ba.
Saboda sanin da yayi cewa akwai mata da yawa yan zuwa yinin buki shiko a rayuwar shi baya son yana shiga gurin da taron mata yake,,,,


SEENABU ZEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣7⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAR YAURI,

Alhamdullahi Rabbil,Alamin


Ànty Dije tare da wasu daga cikin yan uwan su ne suka tafi kai amarya gidan ta dake a unguwar GRA,
Motoci kusan biyar ne suka zo don daukar a maryan sanin cewa ba wai tana da wasu mutane da yawa bane a garin,
So sai ko jama,a suka dan taru don zuwa rakiyar amarya gidan ta, da misalin karfe biyar na marancen, jumma,a,
A bin gwanin ban sha,awa saboda irin yadda, mutane sukayi don Anty Dije, kusan duk wace take hurda da ita tazo mata wanan karar na buki,
Amarya Naimat tasha ado a cikkn wasu lace farare kal dinkin buba, sai farin mayafi da kuma wani farin sarka mai daukan ido,sai wasu, fararen takalma a kafarta
Idon ta alamar taci kuka saboda irin yadda sukayi mata wani irin lub, lub da su,
Maryam ce kawai aka bari don tsaron gida tare da kau da sauran kayyayakin amfani da suka bari a waje,
Sam bata san shigowar Yusuf din gidan ba saidai muryan shi da ta ji gab da bayan ta,
Inda ta juya a yar razane cikin dan rudewa saboda rashin sanin mutum na kusa da ita,
Fararen shadda ne a jikin shi dinkin tazar ce har kasa,
Hannayen shi a harde saman kafadar shi inda ya kura mata ido kawai a cikin rashin sakin fuska kamar yadda yake a kullun,
Sai da tayi kokarin saita kan ta,tukun, na san nan ta samu bakin yi, mai gaisuwa,
Ya ansa mata kamar kullun a takaice sai dai na yau yana da dan banbanci da saura,
Gurin fridge ya wuce direct inda ya bude ya,dauko goran ruwan Inuwa water,
Kafa kai yayi batare da ya jira kofi ba, ya kama kwankwada, inda duk ya kwankwade ruwan tas,
Yau she su Anty za su dawo ne maryam wace ke kokarin shiga store din su, dan aje kaya ta ansa mai da cewa,
Anjima kadan shiru yayi ba tare da yakara magana ba ,
Gurin kujera two site ya nufa nan yazube sama yana mai cewa Ya Allah,
Akawo ma abinci ne ta tambaye a cikin dan dari, dari,
No thanks kawai yace mata inda ya maida idon shi ya kara lumshewa,,
Aikin ta taci gaba da yi abin ta batare da takara bi ta kan shi ba,
Yusuf wanda ke kwance tankar mai barci sai dai a zahiri idon shi biyu yana tunanen duniya,
Wayar shi ce tai kara gurin da, yake aje a gefen shi,
A hakali ya mika hannu shi ya dauki wayar sunan Jibrin ya gani,
Dan gyara kwanciyar shi,yayi ya na mai kokarin daukar ,
Tambayar shi Jibrin yake, yi ko yana ina ne haka
Sai da ya ja dan guntun tsuki kafni ya ansa mai wayar shi, tu kun,
A takaice ya bashi ansa da cewa gidan Anty mana ,
Jibrin yai yar dariya kafin yai mai magana, tukun
Da iskanci ai ba na fadama cewa zan dan gudo in huta ba kafin su dawo,
Ansa yabashi da cewa an fa kawo kayan da ya ce akawo mai ga mutumin yana neman shi,
Sai da yadan lumshe idon shi, sannan ya dan sukunyar da kan shi yana mai kallon ties din falon yace,
Ya ce gaskiya Jibrin bazan iya zuwa in duba ba saboda ina hutawa yanzu,
Amma zai iya kuzo nan ai maryam tana gidan sai ta tayaka dubawa, ko,
Jibrin din ya ansa mai da cewa gashi nan zuwa tare da mutumin,
Yusuf din ya ansa mai da cewa ya yi kyau sai kun ka raso ina ciki idan kunzo,
A lokacin ne kuma su Assalam suka shigo gidan daga can cikin gida gurin kakan,nin su,
Ganin yana bukatar hutu yasa maryam kiran yaran zuwa gurin datake,
Aiko can gurin ta suka dan bata lokaci sai dai jefi,jefi tana kallon shi idon shi a lumshe suke,
Ba ai wani dadewa ba Jibrin yai sallama tare da mai kayan,
A kofar falo suka yi sallama maryam wace ke zaune da yaran suna kallon a wayar ta takarba masu sallaman su,
Dukkan su a falo suka zube sai kayan da mutumin ke kokarin budewa daga cikin wani buhu,
Zannuwa masu yawa tagani suna fitar wa daga cikin buhun,
Jibrin din ne yasawa maryam wace ke ta waje kira,
Sai da ta dan ja aji irin na mata tukun sannan ta mike zuwa ida suke,
Tun daga nesa ya tsai da hankalinshi gurin ta irin yadda take tafiya,
Tabbas maryam ta, tara abubuwa da dama da sai yanzu yake gani su daga gare ta,
Idan ma don kyau ne ta na dashi uwa uba kuma hali duk yarinyar tana da,su,
Cikin yaga da nuna isa ta yan matan taka ta iso gare tana mai cewa gata,
Tankar ba shine yakare mata wanan kallon ba haka yanzu,
Wayar shi kawai yake, ta famar tabawa ya Allah chatin yake yi ko kuma game,
Jibrin ne yadan kalle ta yace ki taya mu zaben zani mai kyau daga cikin wa yan nan pls,
Kurawa zannuwan ido tayi zuwa dan wani lokaci
Sai ta jawo wani mai ruwan zuma, daga ciki yana da wani ado kamar gidan sugar
Shi ta mika masu tana mai cewa wanan kamar yafi dama saboda baida ado da yawa so sai,
Kai ya daga ya kalle ta da mamaki don jin cewa ra,ayin su yazo daya, da ita,
Saboda tun da aka zube zanuwan idon shi yake akan wanda ta zaban
Har zata juya don barin gurin saboda rashin sanin ko may za su yi da zannuwa haka,
Muryan mutumin taji yana cewa zan,nuwan ai kudin su kaza ne,
Dan juyowatayi tace wa mutumin kai malam fadi gaskiya yaushe kudin su ya kai haka,
Jibrin yace wa maryam ta fada masu kudin kayan a takaice maryam tafada masu
Amma kuma sai tace sai dai in har zasu bashi yadda yace ne saboda tai mako,
Dariya duk suka agurin ban da Yusuf wanda dan murmusawa yayi inda ya bukaci mutumin da ya bashi turmi talatin,
Yace idan basu isa ba zai kirashi ya karo mai,adadin yadda ake so,
Daga haka mutumin ya kwashe kayan shi ya tafi yana mai zabga masu godiya,
Inda maryam take ya dan kalla yana mai cewa ki kwashe su ki adanawa anty kafin ta dawo,
Mamaki takeyi zuciyar ta,ace kaya masu yawa haka kuma kala guda,duk, za,a saye, koma na may ye oho,
Sai kawai ta tsinci muryan Yusuf yana cewa duk wace tazo muna wanan farin cikin za a bawa
Cikin mamaki tadan kalke shi kamar zatayi masu magana sai kuma ta bi umurnin shi tafara kwashe kayan zuwa saman wani kujera,
Hira yaci gaba dayi shida Jibrin inda maryam takoma daki ita da yara har zuwa dawo wan su Anty dije,
Bayanin da Yusuf kewa Anty Dije inda take sauraren shi a cikin mamaki,
Turmin zani atamfa da kudi dubu biyar yabawa ko wace mace da tazo sha,anin bukin,
Bakaramin mamaki Anty tayi jin wanan irin kyautar da yai wa mutanen ta,
Don haka daya bayan daya ta dinga aika masu da alherin su gid kuma tana,sheda masu wanda ya basu,
Ta aikawa iyayen mijin ta dashi da kuma, nata,uwayen
Hakan ne yabawa baba daman kara tunawa da zancen shi na son ya hada zuri,a da wanan yaron,
Saidai yasan cewa mutane zasu zarge shi da cew saboda abin hannun shi Yusuf din ne yake son yin hakan, ,
Amma dai shi in son samu ne yana mai son wanan abin ya tabbata,

Bayan buki da kwana biyu Yusuf ya shigo gidan Anty inda ya samay su gaba daya zaune a falo,
Ya saye cikin wata wagambari,mai ruwan sky colour, sai agogon da ya,daura, a hannun shi,
Hular kan shi baka ce sai takalman kafar shi bakake, sai kamshin da ke tashi,
Ganin su gaba daya afalon har mijin Anty wanda ya,shigo garin bayan kwana daya,wuce,
Wani irin nauyin su Yusuf din yaji ,,inda yai, kamar ya koma baya,
Amma sai mijin Ànty din yace mai haba dai kai,ko shigo mana,
Yace haba dai Yusuf kamar wani bako can idan baka sake jikin ka ba har yanzu da Anty naka sai zuwa yaushe ?

Maryam dauko mai cup mu karya tare, inji mijin Anty Dije yace wa maryam din
Yusuf wanda kan shi na kasa bai daga ba yace wa mijin anty ai baya son tea so,sai yafi da, son ya sha kunu, shi,
Da mamaki yake kallon Yusuf din inda yace kai kan iyalinka sun huta, gaskiya da wahala,
Sai kuma yai saurin kai kallon shi ga Yusuf wanda ke shirin zama a lokacin yace
Ya maganar zancen da Dije tace baba yai maku ne kai da maryam, naji shiru mana,
Maryam wace a lokacin tana kokarin zuba mai kunun shi na gyada dake a cikin jug a cup
Wani irin kallin mamaki ta aikawa Anty nata dashi wace itama dai mijin ta take kallo,,
A hankali takai kallon ta ga Yusuf wanda shima kokarin sauke kai kasa yake yi,
Jin gurin yai tsit ne yasa Illiya dagowa yai wa kowa kallon mamaki kai tsaye ya fara magana,
Mijin Anty Dije ya kai kallon shi ga Yusuf din wanda kan shi ke a duke yace,
Yusuf mu ba,zamu so, ace baku shirya dajuna ba kai da maryam ,
Sabo irin yadda muke tare da kai a matsayin dan uwa daga cikin mu,
Don dai ita maryam nasan cewa bazata kyatare zancen mahaifin ta ba,
Da sauri ta kara kallon mijin yar ta don jin abinda yace a kan ta,
Don Allah ya Illiya ka taimaki rayuwata kasa baba ya janye wanan zancen,
Wanda yake kokarin kwace min daga farin ciki na wanda nake kauna
Wanan furuncin nata na karshe yasa,duk kan su kura mata ido,
Yusuf wanda ke dan motsa kunu a cup ya ansa da cewa tabbas maganar maryam gaskiyane,
Tunda tana tare da wanda take son tun da dadewa
Kaga bai dace ace an rabata da wani ba dan wani,
Wanan maganar da Yusuf yayi ta karshe shi ya,bawa mijin anty tausayi so sai
May maryam ke nufi da cewa a bawa baba hakkuri sam bai taba zaton haka daga gare ta ba sam,
Don haka cikin tsawa yadaka mata cewa baki da hankali a she maryam ina maki daukar mai hankali, ?
To ki san da sanin cewa indai babane iyakar maganar shi ce ya fada ba wai zabi yabaki ba,
Don ma dai kawai Yusuf din ya kasan ce shi bako ne daga cikin mu dakin ga aiki da cikawa,
Hawaye ne ya fara silalo mata daga fuskan ta tana sharewa a hankali,
Mijin Anty Dije yace ina ma wanda kikewa ikirarin cew kina dashi din yake, ?
Maryam wacce saboda haushin irin yadda mijin yar ta yai mata a gaban Yusuf kamar wace ba tada gata,
Yasa ko kallon shi ba tayi

56 / 84