Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   43 / 84

126K to 129K   out of 251.8K words

yadan dago kai yana kallon Anty Dije,
Wace ta ke tsaye ta kura mai ido cikin mamaki take kallon shi,
Yaushe ka shigo garin nan Yusuf ?
Tambaya acikin mamaki take mashi ita shiko sai murmushi yakeyi yana kokarin cirewa Assalam bottiry din rigar shi,
Amsa yaba ta a takaice da cewa shigar dare nayi shiyasa, ban fada wakowa cewa zan shigo ba,
Dago kai yayi ya kalli Anty yace mata, Sallah Jumma,a nake son mutafi kada mu makara ,
Daga haka Anty tashiga shiriya Assalam din da,yake jirah,
Da sallamar ta tashigo gidan a gajiye don tafiyad ta kawai ya isa ya sanar da mai kallon ta cewa ta gaji,
Dakin ta, ta,fada tana kokarin cire, rolling din dake a kanta,
A hankali ta sabule abayan da ta aza saman kayan jikin ta, wanda yanzu haka nauyin shi yakai mata ko ina,
Cikin shigar da tayi tunda safe, ta,fito, tana sayen da wani shocking material, mai laushi,
Cikin kayan da yaya iliya yai mazu ne na sallah,yadin grey colour mai dan adon jan flower, cikin sa da kasan shi,
Direct gutin fridge ta nufa don ta dauki ruwan sha, kamshin da taji yasa ta dan dagowa da mamaki
Kamar tai magana ko tai tambaya saidai kuma ta shere kawai,
Sallah maryam ta gabatar tadan kai wani lokaci a zaune ta lazumi sai ta mike, inda suke aje abinci ta nufa,
Abinci ta debo a cikin plate sai kayan garnish din da ta zuba a sama,
Zaman ta yai daidai,da shigowar su gidan daga dawo,wa gurin sallah jumma,a
Gaban tane ya bada wani , sautin kara don dai gaskiya ,
A,lokaci guda suka hada ido inda yai sauri kawar da idon shi,
Amma zuciyar ta sai wani bugawa yake kamar wace taga abin tsoro, a,lokacin,
A hankali ta furta mai kalman sannu da zuwa, ta mai sune kanta kasa,batare da ta kara dagawa ba,
Cikin falo ya,shiga tare da Assalam a hannun shi sai carpet din sallah, da ya rika,
Sai bayan shigar shi ciki sanan tadan samu sukin fara cin abincin ta ,
A hankali take cin abinci amma karan plate din ta yana kaiwa a inda suke,
Anty Dije wace, ta fito tana kokarin hadawa Yusuf abinci, take,ce wa Maryam,
Nasan cewa Baba zai shigo yanzu tunda an sauko daga jumma,a
Maryam tace aikuwa tun fada nashigo nake son fada maki cewa, ashe,
Wai abokin ya din nan na kan wuri wai yasamu zakkah daga wani bawan Allah,
Wanda ba ,a san kowaye ba yai ta bi massalataiya yana bada sadaka saboda Allah da Annabi,
Anty Dije tace da, zun fa Almajirin nan ke min labari wai sun tsaya kallon wani mutum ne da ya bude gidan shi sai yaga kudi a kofa cikin ledar an rubuta Zakkah,
Yusuf wanda tunda suka fara hira yake sauraron su sai murmushi kawai yayi
A lokacin Antyn nashi ta shigo dauke da dan tiren da ta hado mai abinci aciki,
Annan take cewa muna can muna maganar wai wani ya tsunci zakkah a kofar shi ashe ma ba mutun guda bane,
Masha Allah yace alokacin da yake kokarin bude plate don zuba abinci,
Muryan Babane ke gaisawa da Maryam a kofa,
Maryam din ke cewa Baba Oyo,yo, cikin tsigar shagwaba,
Baba yace ja,ira yau ina diyan naki suke suka barki da taro,
But yaran suka fara fitowa da,gudu suna taron Baba wanda ya shigo masu da yar ledar tsaraba,
Suna karban ledar suka fara kokarin budewa maryam ce takarba don ta bude masu,
Tadan zauna saman gefen simintin su, zaman ta yai daidai da fitowar Yusuf,
Har kasa ya tsugun na kamar yadda yaga hausawa na gaida mahaifar su ya gaida Baba,
A,a to Bawan Allah ka shigo garin ne, ?
Sannu ka kaji ya aiki ya jama,a da kuma ko kari yau da kullun,
Allah yai maku albarka kaji, Allah ya taimaka ya rufa Asiri,
Ameen Ameen Yusuf ke ta fada kawai, kanshi a duke
Ita,ko Maryam sai kokatin bude ledar tsarabar baba takeyi wa yaran daje tsa, tsaye a kanta,
Dankali ne soyayye da Awara mai yaji da salad ya sayo masu, kanta aduke tace su dauko plate a sa masu,
Alokacin taji muryan Yusuf yana cewa Baba za,a kaika ka dauki photo
Ina son bana kashiga cikin masu tafiya zuwa Makkah insha Allah,
Da sauri Maryam tadago kai tana kallon shi, sai dai kwarjin shi bai bari ta kai,wani lokaci tana kallon nashi,
Baba daje a zaune bai san lokacin da yakai zaune ba a saman dan simintin da Maryam ke zaune gefe,
Yaro may kace ? inji Baba, ,,
Anty Dije tafito da goro manya farare a cikin leda tana kokarin mikawa baba,
Maryam tace, yau baba bazaici goro ba Anty don kin ga ya kasa magana,
Da kuwa ya sakar mata yana maicewa karbi nan yan nema,
Abinda Yusuf wanda ke kokarin komawa cikin falon ya fada maryam da su Assalam ke fadawa Antyn,
Da sauri ta kalli Yusuf tace O, O ni Hadiza, Yusuf ban san may zan saka maka dashi ba wallahi, aduniyar nan,
Kafin suyi magana sai muryan baba sukaji kawai yasa kuka wi,wi,
Yanata zabga addu,a acikin kukan,
Bai iya kara cewa komai ba ya mike kawai yabar gidan,
YUSUF yabi bayan shi da sauri tare da jarban goro. A hannun Anty yabishi da shi,
Nan yabar su Anty da maryam suna ta famar sadudar maganan,
Bai,wani dadewa ba yadawo tare da Assalam wanda ya,bishi da baya,
Sai a lokacin Yusuf ya dawo yadan tsaya ta waje yace tare nake son su tafi da, Baba Abdullsamad,
Insha Allah, da Ibrahim wanda zai raka su,
Ita dai Anty dije sai mamaki zancen kawai takeyi,
Ta kalli, yusuf din tace mai wallahi ban san may zance ma ba, gaskiya,
Saikuma takama hawaye kawai da dan karfi Yusuf, yace Subbahanallah,
Ganin maryam yayi tana goge fuskan ta wanda hakan yasa hankalin shi ya kada tashi,
Falo ya koma inda Anty take zaune tana faman share kwallan dake ta faman silalowa daga idon ta,
Guri ya samu yana cewa anty haba, haba dai Anty pls ki daina don girman, Allah
Yi,wa irin su Baba irin haka tankar taki ne a rayuwar mutum,saboda neman albarka duniya da lahir,



ZEEE. MAKAWA
[3/17, 07:45] Anty Lantana: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
5โƒฃ3โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Masoya Novel din furen juji tare da sauran yan uwa musulmi na duniya,
Ina maku fatan alheri ga wanan safiyar jumma,an da muke a ciki,
Ya ubangiji Allah ka sada mu da alherin dake cikkn wanan ranan,
Sherin dake cikin ta ya Allah ka kare mu kaimuna tsari daga gare shi,
Allah ya karawa Annabi daraja Allah ka kara daukaka musulunci,,,,,
๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘

Gaba daya jikin Anty Dije har Baba da maryam yai sanyi saboda jin wanan albishir da Yusuf yai masu na bazata,
Anty Dije ta daga kai zuwa kallon inda Yusuf yake zaune tare da Assalam don su ci abinci,
Ta, lankwasar da murya tace Yusuf yau na rasa kalar muryan da zanyi ma godiya da shi,
Saboda ban san may zan iya furta ma akai ba, al,amarin ka na daban ne Yusuf
Shigowar ka cikin mu wani babban alheri ne atare da mu,
Gaba daya shigar ka musulunci ta zama ma duk wanda ke rabe dakai alheri,
Duk da zamanka Furen kan Juji da farko ban hango wani sheri atare da kai ba sam har izuwa yanzu da kazama wani haske a cikin al,umma,
Kafin tai magana sai ya rigata farawa da cewa, batare da ya kalle ta ba,.
Narasa albarkan mahaifina na cikina Anty may zai sa bazan bida ga bayin Alkah da suka nuna min kauna ba,
Abinda duk nakewa iyayyen mu ina masu ne saboda neman albarka acikin rayuwa,
A kullun ina rokon Alkah yasa yan uwana su gane gaskiya su,dawo cikin hanya ma,daidaiciya su ma,
Maganar shi taba kowan su tausay da yake fada inda ya ci gaba da cewa,
Abinda ke sa ako,da yaushe nake yawan zuwa nan gurin badon komai bane don in cika wani gibi dana rasa nadaga yan uwana,
ร€nty Dije baki kyamace ni ba tun ina Joseph dina har zuwa yanzu,
May zai hana in maki duk wani abinda nasan zai iya saki a farin ciki,
A koda yaushe jinku nakeyi tankar yan uwana na ciki daya, saboda irin yadda kike min.
Yar kwalar dake shiri silalowa a idon ta tashare, da gefen hannunta,

Zaune take a bakin gadon ta tana jin lokacin da a,ke ta kiran sallah la,asar daga makwabtar unguwar su,
Amma sai taji yau takasa tashi kamar yadda ta saba yi idan taji kiran sallah,
Sai,da taji fitar su shida Assalam sanan tai yunkurin fita,
A kofa sukaci karo da Anty Dije, wace ke kokarin shiga gurin maryam din,
Suna hada ido da Anty Dije sai ta harare ta ,tace Maryam nikan ban san may Yusuf zai maki wanda har zaki iya mai godiya a duniyar nan ,,,
Nadai ga da mama bata da lafiya irin tai makon da yai muna a gidan รฑan,
Yanzu Maryam agaban ki fa yau yaiwa baba wanan irin alherin da kowani musulmi ke fata,
Ina sauraron inji kin mai godiya amma sai naga cewa har boyewa ma kikayi don kada ku hadu,
Maryam na in,in niya tace wallahi Anty yanzu nake son in zo in mai godiya amma sai naga yafita,
Bata ce mata komai ba banda hararan da ta kara binta dashi , ta juya takoma inda ta fito,
Azaton maryam yafitane sai ta fita waje tsakar gida,
Da Yusuf suka hada ido yana zaune saman dan dakalin simitin da ke gefe yana alwala,
Idan ba idon take mata karya ba wani irin tsadaden murmushi taga ni makale a fuskan shi,
Cikin sauri takawar da kanta gefe guda tana mai jin wani nauyin shi,
Kamar ta juya takoma ciki alokacin sai dai ta daure kawai ta, nufi hanyar kitchen din su tankar bata gan shi ba,
Tunda Yusuf yafita wanan lokacin bai dawo gidan ba sun shiga gari da Assalam da sauran abokai,
A cikin shigar kananin kaya yadawo da dare bayan sallah isha,i, tare da Assalam wanda ke dauke da ledar kayan sweet kala,kala,
Ko da yai sallama ya shigo maryam tana cikin shigar wasu English wear sun mata kyau so sai,
Duk da dare ne mutum zaigane cewa ta gyara fuskan ta tsab da kayan makeup,
Ga kamshi dake tashi kamar wace ke sana,ar kayan kamshi,
Muryan ร€nty Dije ce ke cewa maryam don Allah zo ki tafi hakana kin san halin As,ma,u da saurin rufe gida,
Jin muryan Yusuf yana cewa bissimilahi alokacin da zai zauna,
Maryam dake tsaye tana kokarun sa, takalma tace mai,
"Sannu da dawo wa"
A , kasalance yace "Yauwa"
Assalam ke cewa little mummy ina zaki zani nima,
Kai wani irin son yawo ne haka ?
Kadawo ko zama bakayi ba zakace wai zaka,
Assalam kai baka gajiya da yawo ne wai, kazauna taje tadawo ko ita dare yayi don dai ina son takarbo min kayan yau ne,
Dare ya,yi gaskiya bari mu sauke ta kawai inaga zai fi,
Da mamaki maryam tai saurin dagowa don batai tsan,manin haka ba sam
Idan son samune ita gaskiya sam bata son shiga motar shi
Saboda yana jagula mata hankali duk lokacin da tashiga,
" Wai, har hankalina yakwanta inji Anty Dije ta juya gurin maryam tace kin ga ai kin samu sauki
Ai yanzu zan dawo da sun zauna kawai,
A, lokacin ya mike tsaye yadauki Key's din shi da yazube saman center table,
Gadan gadan yanufi kofar fita wahe batare da yai mata magana ba,
Ai, da sauri maryam tamara mai baya don gudun masifar Anty,
Acikin motar shi yake zaune, tun daga nesa zakaji sautin karatun Al,kur,an mai girma yana tashi suratu Fussilat,
Maryam nakara so,wa ta bude motar daniyar shiga,
Amma sai batafa Assalam aciki ba shi da yaja mata wanan tafiyar,
Da sauri ta kara lekawa cikin motar ko zata ganshi a baya saida baya ciki,
Turus tayi tana zazare ido,
Sai ta dan ja baya tana dan zare ido kamar mai jin tsoro
Ganin har ya kuna motar ya sata saurin shiga jiki ba karfi kamar an zare mata lakka,
Ta zauna a hankali tare da cewa ya akayi Assalam bai zo ba kuma,
A hankali yafara tafiya batare da yabata amsa ba ya hau saman titi a hankali,
Gyaran murya yayi a hankali cikin wani irin soft voice yace aike ce karshen fitowa
May yasa baki fito da shi ba ke, ?
Maryam wace tasan gatse ne yau mata, ta juya abinta cikin natsuwa, tana kallon fitilon dake a gefen hanya,
Sai dai kira,an dake tashi a motar take bi a hankali,
Wayar shi ce tai kara alokacin ya dauka yana yar fara,a
Sadiya sorry nadan fitane zuwa wani guri sai dai kila bazan dade ba,
A hankali ya mika hannun shi yana kokari rage karar sautin dake tashi,
Maryam wace taga ya rage saurin tafiyar da yakeyi batasan lokacin da tai yar tsuki mai sauti ba,
Sai,dai jin karar tayi yafito fili wanda sam bataso hakan ba ita,
Ok to kiti hakkuri tunda ina gari aiko zuwa gobe ne zan shigo,
Eh a hanya nake zan kai maryam unguwa ne amma ba dadewa zamuyi ba ai,,,
Tuni maryam kan ta yadauki caji saboda jin kiran sunan ta da akayi a zancen
Bata karasa jin haushi ba sai,da taji ana cewa maryam ce kuma yau baki sani ba ?
Saida su kayi sallama da juna tukun san,nan yadan ci gaba da tukin motar shi,
Maryam yace cikin wani murya da zakace dole akasa shi yin magana alokacin,
Fuska a daure yace may yasa ki kai muna tsuki, pls,?
Wani kululu taji don ai tambayar raini wayo ne wanan
Amma a fili sai cewa tayi yaushe ?
Murya kasa,kasa irn ta wanda bai son magana da yawa, yace may Sadiya tai maki ki,kai hating din ta dayawa haka, ?
Bakaramin kaduwa magana tasa maryam ba,
Amma sai taga cewa tai shiru kawai shine daidai, yafi tace zata bada amsa,
Maryam pls stop hating me like, dis,
Wani abune ya soke ta akirji da ya furta wanan magana
Murya na rawa tace ni
"Ya Yusuf " ?
Kai ya kada mata alamar eh,
Cikin kwantar da murya tace,
Nashiga uku ta furta a fili,
Azuci kuma tace maganar Anty yau ya tabbata ashe ko shi yasan cewa bana son al,amarin shi,
Kafin wani lokaci hawayen da suka cika mata ido suka zubo,
Are you crying maryam,?
Why ?
Matsowa yayi gab da ita yana mai mika mata hankici don tagoge fuskan ta,
Da sauri maryam tadan ha baya kadan kamar wace taga abin tsoro,
Ki yi hankuri pls ban san cewa maganar zatai maki zafi haka ba ?
Har da zubar da hawayen ki masu mahin manci, da ma,ana,
Cikin hawaye wasu nabin wasu tace may kai min dazan yi hating dinka
Bayan yawaita alherin ka a,garemu ko da yau she,
Murmushi yayi ya ce gaskiya bana jin dadin the way you are treating me,
Haka kawai maryam ta samu kanta da cewa,
Insha Allah bazan sake ba Ya Yusuf,
Fuska daure yace sam bana son ina batawa mutum rai maryam bansan ko may nake maki ba haka, ?
Ki fada min in daina pls,
Wani irin nauyi da kunya ya kamata tace,
Subbahanallah wallahi ni ba abin da kai min,
Ganin sun shigo cikin uguwar da zasune yasa shi cewa ina ne kwanar gidan da zasu tafi ?
To ki share fuskanki pls kada ki shiga tagane cewa kinyi kuka pls, ?
Ba musu maryam ta goge fuska da wanan kyalen da ya bata, ta goge fuskan ta a hankali,
Murya kasa, kasa irin ta mai rada furta, na gode,
Shiru maryam tayi batace komai ba,
Wani dan iska ya furzar daga bakin shi,
Kai maryam ta sadda kasa kawai,
A hankali ta bude motar tafita,
Binta ya,yi da kallo har ta shige gidan,
Sai a lokacin yai yar ajiyar zuciya,
Don yaji yarinyar raba shi mugun tausayi sosai, don bai zaci cewa tana da saukin kai haka ba,
Saboda yazaci cewa zatai mai rashin kunya idan yai mata magana,
Bai wani dadewa ba yaga tafito da wani kumshin kaya, dagani kayan sun mata nauyi tana ja,
Da sauri yafito yakama mata yabude bayan mota yasa mata,
Komawa

43 / 84