Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   34 / 84

99K to 102K   out of 251.8K words

Ya taka har zuwa gaban Daddy din wani kwali dake daure da wani zare ja kamar na gift,
Ya fara aje wa a gaban daddy din ya dago kai a hankali cikin ladabi yace ma mahaifin shi wanan keys din gidan manka ne komai da yadangace shi yana a ciki,
Sai na biyu dake daure da wani blue din zare again, yafitar shima a gaban daddy din ya aje again,
Mr Ema wanda yake tsaye sororo yana ma dan nashi kallon mamaki da tsana,
Yaji muryan Yusuf din yana cewa wana wasu kudine da ya diba daga cikin kudin mai din a na sarrafa su a wani fanin to shi ne yahado kudin gaba daya har takardun business din, suna a ciki,
YUSUF yadan sunkuyar da kan shi yace babu saura komai nashi a hannun shi, yanzu,
Saboda addinin shi ya haram ta mashi cin dukiyar shi,
Aiko Mr Ema ina wuta yasaka Yusuf saboda wanan ce damar da yake hange da zai ja ra,ayin Yusuf din da shi,
Sai,gashi Yusuf din yana sanar dashi cewa wai addinin shi ya haramta mai cin ko kwandala daga dukiyar shi,
Jiki a sanyaye Yusuf ya juya dan barin falon cikin kunar rai yake tafiya saboda irin kalaman da Dad ke fadi,
Sa kai yayi yafita tare da yiwa falin wani kallon mai kama da ta karshe,, sai kuma ya waiga inda su Samuel da Ruth suke tsaye cirko cirko,
Kawai sai ya juya da karfi alamar shi kan ba,zai iya barin addinin shi ba komai zai faru ya faru
Amma yayi sallama da rayuwar kafirci da suke ciki har abada,,
Yusuf na daga labulen falon zai sa kai Ruth da Samuel suka sa wani irin kuka mai ban tausayi suna cewa
"Brother pls don't go,
Brother come back to us pls we don't want to loose u,
Tsawa Mr Ema yadaka masu saboda takaicin, da kukan su ke kara mai saboda yasan cewa yayi rashin dan shi na kwarai, da yake da shi,
Yana magana yana biyu bayan Yusuf din wanda ko waigawa baiyi ba tunda yasa kai,
Sai kuma ya koma ya zube a saman kujerar dake a bakin kofar yasa wani irin kuka mai sauti,
Shima dai Yusuf din yana shiga mota ya sa kyalen dake hannun shi ya goge hawayen da yadan gangaromai a fuska,
Drive yaja mota a hankali yabar harabar gidan,

A cikin dakin hotel din da suka sauka yake tsaye yana kallon titin da motoci ke zirga zirga akai tankar rana ce ba dare,
Muryan Dad ce ke mai yawo a kwakalwa yana cewa,
Saboda kai Joseph nasha kunya nasha takaici kasa banda mutunci acikin church din mu gabadaya,
Wasu ma ko gaisuwar arziki bamayi dasu sabo suna ganin cewa ban fi karfin family di na ba,,
Ka nemi kudin ka ka gina gidan ka barmin nawa,wanan ba naka bane,,,
Murmushi irin ta
takaici yayi yace watau dama Dad ta wanan hanyar yaso ya kamashi ke nan ko,?
Allah yasa ya samu Sheikh ya warware mashi wanan matsalar dake damun shi tun tuni,
Muryan yan kan,nen shi yaji suna kukan kiran shi yadawo kada ya tafi ya bar su pls,
Wa yan nan maganganun da ya ke tunawa sun sa shi ya shiga cikin damuwa da, wani tsananin tashin hankali sosai,
Nan da nan idon shi suka canza kala saboda damuwa,
Guri ya samu yakai zaune yana mai hada hannaye shi biyu guri guda,
Yadan tallabo habar shi da su yana dan bubuga kafar shi a kasa a hankali,
Tunanen da yazo mai gamay da yan uwan shi ya,sa,shi mikewa da sauri,

Sai washegari yasamu shiga cikin gari gaida mutane,
Gidan Abdulsamad yafara zuwa ida suka dan dauki lokaci mai tsawo suna tataunawa, a tsakanin su,
Yana tashi ya wuce sai gidan mahaifan Jibrin inda suka nuna mashi jindadin irin yarda yake girmama su
Yakawo Alheri mai yawa yai masu,
Wasu dattawa ne zaune a kofar gidan su jibrin idan rana yai zafi anan suke taruwa kagin ai sallah azuhur,
Kudi ya debo adadin da bai,san ko nawa bane ya basu don su raba,
Daya daga cikin su daya yake kwance yamike zaune yana tambaya dangidan waye ya basu kudi haka,
Sai cewa guda da ga cikin su yi, ai yaron nan tubabben nan ne,
Au to shine wanda ya tuba din nan, dan gidan katon Arnen nan maigidan mai hanyar Lagos,
Duk wanan maganar a kunnuwar Yusuf akayi su duk da yaji daci a zuciyar amma afili sai ya daure yana murmushi kawai,
A daidai zai shiga mota suka yi kicibis da Sadiya Mohammad joda
Karo na biyu kenan suna haduwa da ita,tun,da ta ganshi sai duk tashiga,,rudu saboda Allah yasa mata masifar son shi,
Itace tafa ra gaishe shi cikin rashi kulawa ya amsa mata,
Ya dan bar uguwar su Jibrin ke nan Kiran Aisha yashigo wayar shi
Sam yarasa may yasa bayason lamarinta yanzu tun bayan muzuluntar shi
Yake kokarin jabaya ga alamarin Aishan saboda sam baya son abinda zai sa sa a sabawa Allah ubangji
Ce mata yayi zai koma ne yau ko gobe kawai amma sai bai son ya fada mata gurin da yake don kada ta cin mashi,,,,,,,


ZEEE MAKAWA,,,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Saye take da wani leshi mai ruwan kwai, (yellow), mai laushi, anyi mai yan ada da wasu duwatsu blue,
Dinkin buje da riga akai wa kayan sun dane jikin ta har surar jikin ta yafito fili,
A cikin sauri take shiri saboda, zata kamfanin Bobi ne yau don diba jikin mahaifiyar ta kamar yadda baba ya umurci Anty ta barta ta tafi,
Saidai ya umurta da kada ta tafi sai yazo tukun,
Ganin baba bai zo ba yasa Maryam din cire hijjab din ta don ta dai taimaka wa yar uwar nata da wasu ai yuka, kafin ta wuce,
Da sallamar shi ya shigo gidan kamar yadda ya saba yi tun bayan musuluntar shi,
Aguje su Assalam da Issalam suka dake wa Abubakar wasa saman kujerar falo
Suka rungu may shi yana murmushi yafara kokarin daga su sama kamar yadda ua saba yi masu,
A kunyace maryam ta gaishe shi saboda kayan da ke saye a jikin ta,
Yasha Voil mai kalar ruwan fari, kal, ajikin shi,wacce ke ta faman kyalli, da daukar ido,,
Kan,ta mayar kasa, cike da kunya don kallon da sukayi na hada ido a lokaci guda, don kada ya zata ko shi take kallo,
Saida ya shiga falo yazauna saman kujerar dake facing din kofar ta yadda duk wand ya gilma zaka iya ganin shi daga ci,
A hankali yakewa yaran yan tambayoyi gamay da school da kuma rashin zuwan su makaranta yau,
A tare suka hada baki suna,cewa ai yau weekend ne har da little mummy ma yau bata zuwa,
Shigowan Baba da yayi ne cikin yin sallama yana mai neman Anty Dije, wace ta dan shiga cikin babban gidan su maigidan ta,
Cikin damuwa Baba ya fara magana yana cewa, Maryama tun dazu ina can gurin bidan dan kudin da zakiyi kudin mota da kuma wanda zaki dan sai masu tsaraba,
Tunda ba,a zuwa gaida mara lafiya hannu sake amma ban samo wani abin kirki ba dan kudin da duk nake bi bashi tun jiya nake bi ko zan dan samu wani abu daga ci,,,,,,
Bai,kai ga karasawa ba Yusuf wanda ke zaune a falon yafito don su gaisa saboda Assalam ya fada mai cewa ga baba tsoho nan, ya shigo
Sai yakasance Baba din nata ma Maryam bayani a lokacin,
Maryam tace Lah baba dama kabar shi ai Anty ta bani kudin mota ko ,
Kai kawai dama nake jira don kace kada in tafi sai ka shigo
A,lokacin Anty Dije tadau dauke da wani bakin leda mai giwa a hannun ta,
Cikin yar fara,ar ta take gaida baba tana cewa yanzu ake ce min ga ka can ka shigo yanzu,
Dama na tafi ne, in dan samo mata abinda zata rika,
Allah yai maku albarka in ji Baba yake sawa yaran nashi,
Wani iri Yusuf yaji don jin yadda Dattijon ke ta sawa yaran shi albarka akan dan abu kadan,
Ina ma ace shine yasamu irin wanan mahaifin mai sawa diyan shi albarka haka,
Muryan Dadtijon ya katse mai yar tunanen shi yana cewa,
A ina , ta, shiga mota ne Dije, ?
Anty Dije tace dama cewa nayi ta tsaya a bakin hanya kamar zai fi,
A,a a,a inji Baba yace tashiga ta cikin gareji kawai yafi sauki don shiga mota bakin hanya ai hatsari ne Dije,
Baba yace idan kin tafi ki gayar muna da mahaifiyar taki Allah y bata lafiya
Duk suka amsa da Ameen,
Harda Yusuf wanda ke zaune a falon yana jin su,suna mai bashi sha,awa
Daga haka Baba ya fita suna, ta ce mai baba sai anjima inji su Assalam,
Maryam ce tafito daki acikin shirin ta tasa dan gyale blue,ta yane fuskanta,sai wasu yan takalma, suma blue daidai adon duwatsun Lecce din jikin ta,
Cikin dan siririn murya,kamar kulun taje sallamar yar nata,
Yusuf dake zaune tare da su Assalam suna hira yana jin su, amma hankalin shi yana gurin su,waje,
Muryan Anty Dije cikin tausayin yar kaunar nata wace take ji a lokacin kamar su tafi tare, saboda basu san halin da mahaifiyar nata ke ciki ba,
Duk da bawai sun saba da mahaifitar nata bane amma sai duk ta damu tun da baba ya fada mata cewa mahaifiyar ta bata da lafiya,
Ànty Dije tace cikin murya mai rauni, maryam tsaya mana ga Yusuf ya kaiki tasha ko,
Maryam wace har takai kusan kwanar fita cikin gida alokacin,
Tace wa yar nata ai da ta barshi kawai sai in hau mashi a sauke ni,
Assalam da Issalam ya umurta da su tashi su raka little mummy,
Yaran na murna suka fito waje cikin dauki kowa na kokarin saka takalman shi a kafa,
Maryam, wacce a lokacin har taku sa isa kofar gida sai ji tayi yace wacce gareji ne za,a kaita wai ?
Anty Dije tace, inda zata samu motar zuwa kamfanin bobi,
Ok garej na hanyar Minna ko,?
Motar ya nufa a,lokacin da ya budewa yaran gidan baya suka shi itako tai kamar bata gan su ba sai kokarin tare mai mashin takeyi,
A gabanta ya tsaida motar ya bude mata gidan gaba gefen mai zaman banza,
Su Assalam dake bayan motar ne suka dan leko suna ce mata little mummy, kishigo, muje
Sai a lojacin tadan daga kai tasaci kallon Yusuf wanda tankar hankalin shi na gurin sai tin A,C din motar,
Ba yadda ta iya dole ta, bude gaban motar tashiga ta na mai wani kauda, kai gefe, guda,
Basu yi wani nisa da uguwar su ba yadauko wayar shi yana tuki da hannu guda guda kuma yana kokarin bidan nobar waya,
A cikin harshen IBO yake magana da mai, shi wanda ya kira da suna, Uchenna,
Abinda zata iya jiya ce rice, akwaiyiro ho ,oil and anything good for makeurimo,hauw,,
Jin yaren da yakeyi ne wani iri kamar ba magana yakeyi ba, yasa ta kara kauda kai tana mai jin lokacin da,Issalam ta kamo mata kai ta bayan sit ta rungumo ta,
Haba Issalam ki daina mana kada ki shake ni pls,
Gidan wani mai na saida petroleum ya dan Parker motar shi kamar mai jiran wani abu,
Ganin da tayi sun dan kai wani lokaci gurin tsaye, yasa ta fara kallon agogon wayan ta,
Lokacin kusan karfe goma na shadaya na safe saura rabi,
Karar, wata mota ce kewa Yusuf, horn ,p, p, p, p,
Waya ya dauko yakara yin yare, su na IBO yana cewa Emba, ok akwarihu, moi,duwobo,
Daga haka taga sun karkata motar su zuwa saman titi sunbar gidan man,
Suko yaran dake baya sai rawan wakar daya sa ke yi na wasu diyan larabawa,
Gani ankusa kaiwa kofar shiga tashar motar da zasu kaita yasa maryam fara gyara rolling din gyalen ta tana kokarin daukar yar jakar ta dake gefe,
Fiwww suka wuce kofar shiga cikin tashan, abinda yabata mamaki har takai ga waigawa ta kalli Yusuf wanda ke dukan sittiyarin motar yana bin kidan da yaran kewa waka, cikkn harshen larabci, cikin nuna rashin damuwa,
Sai kawai batare da ta ankara ba taga sun share kwanar Barack sun doshi babban titin zuwa minna,
Abinda yasata sake wani irin ajiyar zuciya wanda bata san lokacin da yafito fili bba,
Tafiya yai nisa baka jin komai sai sanyin A,C da gauraye motar kowani sako,cikin motar,
Gudu yake shararawa kawai abin shi, duk da sanyi yadan takura mata amma bai sata yin magana ba,
Sai ma dan waigawa da tayi bayan motar danjin yaran dake bayan motar sun yi shiru,
Barci sukeyi gaba dayan su amma a dan takure saboda yawan sanyin motar,
Da an rage madu wanan sanyin kada yasasu mura tace batare da ta kalli gefen shi ba,,
Saida yai kamar baiji taba zuwa can sai taga yana dan rage karfin A,C din a hankali,
Wani abin da maryam ta dan lura dashi shine wasu motoci da guda ke gaban su guda baya,
Amma da yake tasan cewa hanya ce tazuwa har abuja kaduna kano da sauran su sai kawai ta share taci gaba da kallon, dajin da suke ketawa,
Shiko sai gudu yake shararawa abinshi cikin ko in kula,
Cikin yan mintina kadan sai gasu, a cikin garin kamfanin Bobi
A hankali ya fara tafiya ganin cewa sun shigo cikin gari a lokacin,
Dan sassauta murya yayi yadan waigo ta yace ta ina ne gidan yake,
Zaman ta tadan zakuda kadan tashiga yimashi kwatancen gidan ,a hankali sai kawai gasu a kofar gidan,
Kamar ko yaushe mutum ya je zai iske mutane zaune agidin iccen cediyar dake kofan gidan,
Maryam tasha mamakin ganin motocin da suka jero tare ashe wai tafiyar su guda ne,
A gidin wasu itace lim dake gefen wani guri kamar daji suka Parker motocin su,
Sai a lokacin maryam da wani nauyi ya lulubeta dan kunya,
Ta,iya furta nagode a hankali
Bakomai yace lokacin da yake kokarin ganin su Assalam dake bayan mota akwace, suna ta kwasan barcin su hankali kwance,
Kafa guda tafara fitar wa waje inda kafar ta guda ke cikin motar,tana kokarin daukar yar jakar da tasa tufafin ta aciki,
Suko mutanen dake a kofar gidan gidin icce hankalin su naga motocin don suga ko su waye suka shigo ,
Maryam na,dago kai da niyar ta fito sai gani wasu murda, murdan kaita tagi har mutum shidda tsaye a kofar motan
Gaban ta ne yaba da dam, dammm, saboda ganin irin yanayin shigar su,
Kwantar da hankalinta tayi ta fahinci cewa tare da Yusuf suke don ganin yadda suke kokarin rike kofar da ya bude don ya fito,
Kusan a tare suka fito daga motar tana kokarin saba hand bag din ta dake dauke da kayan ta kala biyu kacal,
Sai a lokacin ta fuskance shidaga inda take sukayi ido hudu kafin kiftawa da bissimillah takawar da nata,
Bata san may yasa ba take jin nauyin shi bata jimirin kallon shi,
Nagode takar furtawa cikin kwantar da kai, sai kuma tadan leka mota tana kallon yaran dake barci acikin motar,
Allah tsare hanya takara fadi kamar wace bata son furta hakan a hankali,
Daga haka ta sa kai zuwa cikin gidan kawai batare da ta saya jiran komai ba
Jama,an gidan sunyi mata sannu da zuwa tare da nuna jin dafin su daganin ta,
Dakin mahaifiyar ta tawuce direct don ganin bata waje alokacin,
Can take kwance ta kuryan dakin ta saman wata kodaddiyar tsohuwar katifa duk ta latse,
Ga tarin tsumakara birjit a ko, ina saman katifan, dake akai,
Dan wani tsohon tebur dake dakin dauke da wasu kwanoni irin nada daban daban,
Sai kuma wasu buhu,hunan hatsi dake jingine a gefe an,dan rufe su da wani tsohon tsuman ragar zani,
Kwarai maryam ke tausayawa mahaifiyar nata wace ke kwance ko kai bata iya dagawa sosai,
Wasu mata mutum biyu suna daga kofar dakin suna cewa aiko ke maryam anga sauki yanzu sosai,
Ai kwana biyu da suka wuce baki ko iya tsayawa ashe,?
Muryam mijin mamace kecewa ku kauce ga baki nan shigowa,dan Allah,
Maryam tai kokarin aje jakarta asaman wanan tsohon tebur din, da niyar tadan fita bakin su shigo,
Idon,ta cak ga Yusuf wanda ke rike da hannun su Assalam,
Mamaki nauyi kunya duk suka taru mata a, lokaci guda,
Daga kofan dakin kokari yakwyi ya cire takalmin shi masu tsada dazasu iya kai kimanin kudi dubu hamsi ko faye da hakan,
Wata daga cikin matan taje tadauko mai

34 / 84