Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
Matan kauyen sai shigowa sukeyi da sunan gaida mama da jiki,
Amma azahiri gulma ke kawo su don wasu basu ko iya boye gulman su sai su dinga latsa katifa ko taba wani abu ace irin na wance na wance ne,,,,,
A, dadafe yafito daga cikin motar shi da taimakon Samuel yasamu yau yafito zuwa shagon,
Inda yakan zauna can nisa kadan saman kujera yadinga kallon masu harkokin su a cikin gari,
Wani dan kabilar su saman wata mashin ta matasa yazo ahan mai,
Ganin Mr Ema a gurin yasa shi zuwa gaida shi har inda yake,
Anan bayan sun gaisai sunyi ya kwana biyu ya jiki mutumin ke tambayar shi cewa a she, Joe yana gari ne, ?
Da mamaki yakara tambaya yana mai kada kai da kafar shi yana rage haushin da maganar ta rasta mai acikin zuciyar shi,
Inda mutumin ke tambayan shi cewa ko suna da mara lafiya ne a asibitin tagwai, ?
Wani sabon mamaki ne ya kara kamashi inda yake cewa, w
Watau Joseph yana nan yana yiwa hausawa da yaran su dawai niya ke nan,
Zaune yake idan kagane shi a lokacin zaka dauka cewa, cikin jin dadi yake
Amma sam cikin tashin hankali yake inda yanzu yasha alwashin cewa, sai ya koyawa Joseph hankali tukun,
Akwai wasu samari yaran hausawa yan wi,wi yan daba su yayi haya,
Inda ya fada masu abin da yake da bukata su yi mashi akan Yusuf,
Shiko Yusuf yana can a unguwar Rimaye ystafi kaiwa wani malami dake unguwar sadaka,
Wanda zai tallafawa almajiran shi da su a gina masu babban daki inda zasu dinga kwana,
Malam Shehu mai almajirai na Rimaye yai mamaki kwarai da wanan alherin da Allah ya basu cikin lokaci guda,
Addau,a na muhinmin yasa ai mashi cikin, dafifin almajirai inda yabisu da sadakan yan hamsin,
Sai wani makarantar matan aure da ke Kan Wuri, bayan sectaria inda yakai masu sadakan abin zama tare da kara masu girman makarantar,
Wanan abin ya jawo magana sosai duk da duk inda yakai alheri sai yace dan Allah kada a fadi a saya shi domin Allah yayi,
Amma ina mutane saboda mamakin irin halaiyar shi sai an fada cewa da ace sauran masu kudin mu zasuyi koyi da shi da sun taimaka wa al,umman musulai, da basu dashi,
Daga hotel din ya ke yana sauri saboda yana son zuwa gurin wani mutum da zasu yi hurdan ,Noma a shekarar bana,
Wasu matasa ne a saman mashin guda uku, suka biyu shi,
Dafari bai kula da cewa shi suke bi ba saidaga baya ya hankalta da su,
Sannu,sannu ya fahinci cewa shi suke bi, a baya a hankali yasa signal, ya tsaya gurin wani katon iccen mangaro,
Security guard din shi ya kunna nan da na signal yakai gurin security din shi da koyaushe a cikin shiri suke suna biye dashi,
Kafin yafito yaji saukar sanda a bayan motar shi duk da hankalin shi ya tashi amma sam bai nuna masu tsoro ba,
Muyan matasan yan daban yayi suna cewa kai karamin dan isaka wa zai yarda da musuluntar ka,
Har yanzu mu kafiri kake a gurin mu. Don bamuga ka iya sallah ba tukun ko sabbi saukan mata baka iya ba,,,,,,
Wasu bakaken motoci ne wulk guda biyu suka gani shake da security cikin bakaken kaya suka tun karo su,
Da gudu suke kokarin haye mashin din dasukayo haya don su gudu,,
Cikin rashin sa,a sai guda yafadi kafin yai wani yunkuri aka cafke shi,
Nan da nan gurin ya cika da jama,a makil, mutane da son ganin gulma,
Shiko dan matashin sai cewa yakeyi
Dan Allah kuyi hakkuri ba nikadai bane turo mu Ema mai manja yayi muyi mashi haka wai yai mashi laifi,
Yusuf najin haka ran shi ya baci sosai bai tsaya ba sai kawai ya shiga motar shi
A fusace ya isa gidan nasu tun daga wahe yake kwaka wa mahaifin shi kira,
Wanda shiko Ema yana can yana fada da samarin nan yace may yasa suka bishi a cikin gari,
Jin yadda Yusuf ke kiranshi yasa shi katse wayar don jin abin da yazo da shi,
Yana zaune falin shi saye da wata yar babban ringar banga ta lace, baka, kanshi saye hular su ta yan kabilar IBO,
Dad if you want to killed me killed me by yourself pls,
Amma kada ka sa kanka cikin harkan yan daba yaran da basu san komai ba sai kudi,
Su jawo maka magana kawai
Idan da suna da wayo da wallahi bazasu karbi aikin ka ba akaina,
Gaskiya baba wanan abin da ka aikata yabani mamaki,
Dad idan kaso pls kayi hakkuri da musulunta na dan ba zan taba komawa cikin kuba don kuma muna maku fatan dawowa hanya mafi alheri,
Daga haka yasa kai yabar gidan cikin bacin rai, da kunar zuciya,
Direct police station, yanufa don yasa a sake yaran don shi sam baiga lai,fin su ba,
Duk yadda police sukaso a dau,kaka karan bai,yardan masu ba saboda yasan cewa mahaifinshi zai wulakanta akanshi,
Duk abinda ake ciki Mr Ema nada labarin komai saboda yan leken asirin da yasa tabaya,
Tun da yabar police station din yaji kawai ya ma rasa inda zai nufa,
Kai tsaye ya kama hanya sai kamfanin Bobi, inda ya shiga garin bayan la,asar lokacin har maryam sun gama girkin abincin dare ko,
Cikin mutunci mutanen suke gaishe shi tare da nuna kulawar su da jin dadin su,
Sai godiya suke mashi akan irin taimakon da yaiwa mama,
Wani dan dadttijo yace yaro mungode kaji, Allah ya hada hankulan da diyagga kaji,
Sam bai fahici manufar su ba saboda hausan shi bai,kai can ba,
Tare da kanin mijin mama suka shigo cikin gidan shi yai mashi iso,
Harzuwa dakin mama Alhamdullahi don yau mama,azaune take saman tabarman roba da maryam ta shimfida, mata, a can gefen dakin ta,
Kai tsaye inda take zaune suka nufa inda Awalu ke mata sheri yana cewa a,a,a yaukan sauki yasamu kece zaune a waje,
Yusuf yana kokarin zama yana gaushe ta yana kuma yi mata ya jiki,
A cikin gwari,gwarin hausar shi yake ma mama ya jikin yakuma take ji yanzu,
Sai a lokacin maryam ta iso gurin shi cikin sakin fuska taje mai sannu da zuwa, dakuma ya hanya,
A hankali bayan ya furta mata cewa lafiya ya jikin mama sai take ce mai ya su Assalam da Issalam,
Saida yai murmushi sanan yake cewa, gaskiya yau bai samu zuwa gidan su ba,
Amma dai sunyi waya da Anty Dije da safe, kafin ya fito,
Yauce rana ta farko da wani magana mai dan tsawo ya taba shiga tsakanin su,
Maryam na kokarin mikewa ne taji muryan mama tana cewa ke yar baba ki ki bashi abinci a daki,
A razane maryam ta dago kanta don tasan cewa, bazai ci ba,
Amma sai taji baice komai komai alamar zaici,
Muryan Awalu ne ke cewa, haba yaushe Alhaji zai iya cin ,abincin mu,
Maryam ta fahinci zai ci don haka bata kara cewa komai ba ta hada mai a saman tire takai mai dakin mama inda ta dan fito,
Sai cike take da jin kunya kalar abincin nasu da zai gani,
Tuwon dawa ne da miyar danyen karkashi sai, naman kassa na rago da aka zuba, aciki, irin local miya akayi shi bawai da stew daban ba,
Ruwa ta debo mai a,randar kasa mai sanyi cikin kwanon sha,
A hankali taji muryan shi kamar mai rada ya na,cewa,, ki dan taimaka min Maryam da ruwan wanke hannu pls,
Ruwan tadebo,ta,mai a,cikin wani silver mai fadi,
Sautin murmushin shi taji yana cewa, Awalu yatafi ni kadai zan zauna a dakin,
Babu shiri maryam ta koma, can gefen katifa, ta zauna tana dan wasa da yatsun hannun ta,
Daga inda take zaune tana ganin yadda yake cin abincin hankali kwance, yana mai lunshe ido,
Shikam ashe akwai wanan irin abincin har yanzu anayi,
Rabon shi da irin wanan tun suna yara da yake bin su KB da jibri gidan kakan nin su, suna ci,
Saidai daga ita har shi ba mai ma wani magana, shidao kokari yakeyi da farko, yaci kada mama suce yana kyamar su, sai kuma koyi da sunnah dayaji ance yana da kyau,
Amma sai gashi ya buge da ci sosai fiye da tsanmanin shi,
Saida ya kusa gamawa yadago kai yakalle ta inda take zaune a takure,yace,
May sunan wanan abincin,?
A hankali tace tuwon dawa miyar karkashi,
Yana mai tsamay hannuwar shi zuwa cikin ruwan wanke hannu yace,
Dazan dinga samun shi akoda yaushe da bazan ci wani abinci ba sai shi,
Kanta ta gyada almar mamaki, jin maganar shi,da yayi ita da take ganin ba zai iya ciba, sai ga shi ya buge ga santi,
Yunkurin mikewa tayi ta kwashe kwanonin agaban shi,
Amma sai taga ya ciro kudi masu yawa ya aza saman ture din yace pls kiba matan gidan nan su raba,
Muryan ta na rawa tace, kai haba abin ya,yi wa gaskiya,
Kamar ba shi take ba don sai ma kokarin goge hannuwanshi da yakeyi,
A, hankali ya fara kokarin mikewa zuwa bakin kofan dazai fita,daga dakin,
Ya juya da kyau ya fuskan ce ta yace aikin Alheri bai yawa ga inda ake bukatar yi,
Ba rokona sukayi ba can,cantar hakan naga yadace nayi,
Idan nabar wanan taki bazan kara zama free man ba sai lokacin dana dawo kuma,
Cikin nuna kariya tace mai Allah ya saka da alheri Allah yasawa saura albarka,
A, a maryam albarkan iyaye nake bukata ba ta kuba yaran zamani,
Kala maryam batace mai ba don kada maganar su yai nisa sosai,
Da sauri ya nufi hanyar fita waje tun kafin ta gama hada kayan abincin,
Kowa agidan sai murnan kudin da ya raba musu su keyi dubu guda guda kamar a mafarki,
Wasu daga cikin sun ne ke cewa maryam gaskiya kin yi dace,
Da mamaki maryam ke tambayar zuciyar ta kamar ya ta dace,
Caraf ta ce masu nifa ba komai a tsakanin mu dashi gaskiya,
Sam basu yarda ba sai zolayar ta sukeyi, suna mata ba,a
Maganganu barkatai suka dinga yi akai kowa na fadar albakar bakin shi,
Sosai lafiya yasamu ga mama wace yanzu take iya yiwa kanta wasu abubuwa,
Mama da maryam ce acikin dakin suna yar hira ta sakanin uwa da , "yar ta,
Yar baba may ke a tsakanin ki da wanan bawan Allah ne wai,?
Cikin wani irin kallon mamaki maryam ke kallon mahaifiyar ta,
Mama tace duk da naga alamar ba wai kina son shi ba ne
Ki daure ki kalli kyawawan dabi,un shi kiyi nazari akai,
Maryam takai wani,,, lokaci tana jimamayn zancen mama azuciyar ta,
Washegari sai gasu shida KB da Jibrin da Assalam
Sai kayan fruit niki,nike da sukazo dashi daga can kwantagora,,
Ranan Dan wake su maryam sukayi da mai da yaji, sai kunun gumba yaji kayan yaji yana ta kamshi,y
Sosai sukaci wananyaci jiyw, danwaken gaba dayan su har shi Assalam din nan yusuf ke masu hiran irin abincin da ya ci jiya da yazo,
ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣6⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,,
Yan uwa har wayau ina mai kara maku tuni akan barnan da wasun mu ke kokarin yadawa acikin al,uma,
Baidace abin da ke boye mu fito fili kara muna yada shi ba fa,
Musa jin tsoron ubangijin mu da mairubutawa da mai karantawa,
Allah yasa mu gane gaskiya,👏👏👏
Zaune yake a office din shi dake a cikin Abuja, inda yanzu yafi bada karfin zaman shi,
Gaban shi tarin takardune yake dubuwa sai gefe guda inda system din shi yake a bude dagani aiki yake acikin sa,
Baka jin komai sai karan na,urorin sanyin da ke office din suna ta aikin su,
Sosai hankalin shi ke ga wasu takardu da yake diba inda yake nazarin su,
Kokari yakeyi ya kara haffako da arzikin masana,artar shi da Sonny yabar mai shikadai yanzu,
Duk da Sonny din ba,wai yabar masa abanza bane, don abi biyu zuwa uku yabar mashi,
Na farko dai, yasan cewa sun samu riba sosai da gurin cikin dan kankanin lokaci,
Sai kuma kokarin da yakeyi na yabar duk wata harkan business din shi a Nigeria, kwatakwata, saboda rayuwan shi a yanzu a can take don iyayyen shi sun mutu,
Nabiyu kuma yanzu Yusuf ya zama musulmi irin wanda ba guda ba jada baya, hurda dashi zai mashi wuya don yana gudun yazo ya jefashi a cikin kamar yadda shi ya shiga,
Na uku yana tausayin abokin shi Joseph acewan shi don yadda yaga yan church suna ta faman bugo mashi waya akan ya cire shi a harkan shi,
Wanan abin yasa yaga cewa Yusuf ya cancanci yabar mai wanan gurin amatsayin tukwicin zaman da sukayi suna business a tare da dadewa,
A hankali ya dan juya da kujerar da yake zaune yana mai nazarin, takardan da ke hannun shi,
A hankali ya cire glass din dake idon shi ya kara kurawa takardun ido, har zuwa dan wani lokaci,
Bakomai bane sai takardan wani business din motoci ne da suka sawa hannu da dadewa kuma gashi har lokacin business din ya yi,
Sai,dai matsala guda gashi basu tare da Sonny yanzu don haka bai san ya abin zaici gaba ba,
Don dai harkan ba karamin alheri zata jawo masu samu so,sai ,
Bai bata lokaci ba gurin kiran Sonny don ya tunar dashi akan zancen business din da zuwa yanzu komai ya kammala ko,
Kira guda ga nabiyu Sonny din yadaga wayar yana mai cewa A,loo,
Nan dai suka gaisai da junar su suna mai, ya kwana biyu ya aiyuka,
A tsanake Yusuf yai,wa Sonny bayanin komai kamar yadda da farko suka tsara,
Kafin Yusuf yacigaba da bayani Sonny ya katse shi yana mai ce mai, to ai yanzu wanan business din yadawo nashi shi kadai
Cikin mamaki Yusuf ke sauraren bayanin Sonny din don hali irin nashi sai antona
Abinda shi Yusuf bai sani ba shi ne, yanzu Sonny yafi karfin wanan karamin business din,
Don ya na harka da masu hada kwaoyoyi mahaukatar kudi nazo mashi ta ko ina har bai san ya zai yi da su ba
Allah ne yafitar da Yusuf daga ciin wanan har kan kafin abin yai kauri,
Har sunan shi ya shiga cikin bata gari ,
A je wayar yayi cike da mamakin halarcin da Sonny yai mai a rauyawa,
Hannu yadaga sama yai,wa Allah godiyar irin wanan baiwa da yai mai a,cikin lokaci guda,
Ga baiwar samun haske na shiga cikin addinin musulunci dayayi,
Ga kuma ta samun cigabar arziki da yayi acikkn lokaci guda ta yadda bai taba zaton arzikin shi zai kai haka ba,
Wanan samun cigaban yasa Yusuf daukar ma,akata da dama daga kasan kwantagora, saboda cigaban su,
Har mai Sudan saida yasa akakira mashi Yusuf yakara yi mai godiyar irin taimakon da bawa kasan shi tare da taimakawa matasa,,,
Maman Choima yanzu sun dawo abuja tare da Ejoma wace idan baka sani ba zakace blood sister din Yusuf ne ita,
Saboda yadda take taimaka ka mai tsakani da Allah ga al,amarorin shi,
Ejoma ta dade a cikin zuciyar ta tana son ta zama musulma kamar yadda tun tana yarinya take da ra,ayin haka,
Saidai batai dace da musulumin kwarai wanda zai tsaya akanta yaga cewa ta musulunta,
Sai ma baya da yajuya mata don kada ya sha wahala, akanta,
Kwance take rub da ciki saman gadon ta,dake dan karan dakin nata na cikin gida Anty ta,
Tana saye da wani dogon riga baki mai yar hannun shimi, har kasa rigar tie ce ta mastse ta ta tsakiya inda tadan cire top din rigar ta aje saman kujerar ta,
Dakin yasha gyara dan har wani kyali ties din kasan dakin keyi gawani kamshi dake ta shi ,
Takardun ta ke nazari tana kuma dan rubuto a gefe guda, daga kwancen,
Wayar ta, touching kiran ardriod tana gefe guda saman gadon sai waka ke tashi,
Wankan Fadar bege, inda yake wakarshi mai take, Sarki Jiran Halittu, mijin juwairah,
Tanayi tana dan maming din wakar daga kwance,
Issalam ce ta shigo dakin da gudun ta tana rataye da jakar makarantar ta a baya,
Sai kokarin cire takalman ta takeyi kuma tana kallon kofar shigowa gida tana dariya,
Maryam sam bata kai hankalin ta ga abinda yarinyar ke yi ba,
Sallama yakara yi cikin kwantar da harshe kamar a mafarki taji muryan, nashi,
Don dai baji Anty ta na zancen zowan shi ba kamar yadda ta saba yi,indan zai zo,
Dammm gaba