Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
mai sai yace na dubu goma, ai sai mai kati yaja yai tsaye,
Don shi a zaton shi, gatse ake mai,
Shiko a lokacin hankalin shi na can yana bidan wani takarda da yake son yaba mai shi,
Yana dago kai yaga ko mai shago ya kawo mai katin sai yagan shi tsaye gaban shi,
Hannu ya mika don yakarba sai mai shagon katin ya ce mai a nadauka bakar magana kai min, sir
Cikin mamaki yake kallon mai katin shiko ya koma da sauri don dauko katin,
Saidai mai shago ya tarar da katin bai kai na dubu goma ba don haka ya tsaya yi mai bayanin baikai ba ,
Hannu ya mika yakarbi wanda yasa mu yana mai mika mai kudin da yakirgo dubu goma,
Cikin mamaki mai shago yace ai na dubu bakwai kawai aka samu maigida
Cikin hausar shi kamar ba haihuwar IBO ba yace, kabar shi kawai daidai lokacin da yata da motar shi yabar gurin,
Mai shagon katin yai tsaye sororo ya bi shi da kallon ikon Allah,,,
It's been a long day without you my friend and,i will tell you all about it when i see you again ,we have come a long way from where we began,oh i will tell all about it when i see you again, (Wiz_Khalifa feat charlie puth)
SEE YOU AGAIN,
Baka jin komai a cikin motar sai wanan wakar ke tashi yana kokarin loading kudin da ya saya awayar shi, yana maming din wakan a hankali,,,
Phase 2 ya karkata motar shi zuwa, hanyar tudun wanda don yai saurin kai shi uguwar, phase 2,, din
Daidai, roundabout din da ya mike zuwa,Kwangwara, da Kan Wuri,
Ta, window motar ya ga ana mai hannu alamar ya tsaya, dan murmushi yayi dan ganin wanda ke kokarin tsaida shi a lokacin,,,,,
Wuri ya samu a gefen hanya, ya parker motar shi daidai lokacin da wanda ya tsaida shi ya iso gurin,,
Hannu suka mikawa junar su alamar gaisuwa a tsakanin su,
Cikin nuna jin dadi daganin junar su yasa suka rike junar su, suna ta dariya,
Kafin minti biyu sai ga gurin da suka tsaya yafara cika,
Duk wanda ya gansu cikin farin ciki yake tsayawa ya basu hannu,
Mutane da ke wuce wa sai kallon su sukeyi cikin mamaki,
Komay ke faruwa haka aka tsaya a gefen hanya,,,,,,
ZEEE MAKAWA,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎
Fatan alheri ga dukkan wayanda suka nuna min kaunar su da kuma kulawa,
Sai misalin karfe shidda da wani abu yadawo gida daidai lokacin da abokan shi ke shirin alwalal sallah magrib ,,
Tun fitar shi yana can phases 2 tare da abokan shi
Friendship din su ya dauko asaline tun a makarantar primary, daga nan kuma suka jona secondary,
Tun a lokaci baida wasu abokai sai yaran hausawa
Duk irin fadar da mahaifin shi da yan uwan shi ke yi mai bai sa ya daina bin diyan hausawa ba,
Kamar yadda akasan diyan IBO da rashin son dan bahaushe shi nashi halin na daban ne,
Don har abincin su yake ci ,idan yaje gidajen su, ziyara lokacin yana karami,
Bayan rasuwar mahaifiyar shi baban shi yaga cewa duk akidar shi kusan na hausawa ne yasa shi dauke shi zuwa kasan su don ya karasa karatun shi a can,
Yana gamawa sai kuma akatura shi, kasar Malaysia yin karatu can,
Acan Allah ya hada shi da dan wani millioner, dan yaren su na IBO
Amma shi bai,damu da karatun da sukaje yi ba,
Sai Allah yasa shi da ya maida hankali yana hadawa har da na Emzon yayi mai su test da sauran aiyuka,
Exam ne kawai, Emzon kezama yayi a haka har Allah ya taimake shi suka kare karatun su,
Bayan dawo wan su karatune Emzon ya jona Joseph, a business din harkan man petrol
Daga haka Allah ya taimake shi ya cigaba tun suna yi da kudin Emzon har suka daina hada kudi a tsakanin su,,
Wasa,wasa Joseph ya fara na shi harkan sai gashi ya canza wa uban shi sana,a daga saida manja, yakoma harkan petroleum, shima,,,,,,
A kofan gidan su ya iske baban shi zaune a saman wani benci, da wasu yan dattijawa kamar shi
Kwalaben giya ne suka tara birjik agaban su, sai shewa suke yi suna ta hayaniyar hiran irin bidirin dazun da akayi,,,
Yadan dade zaune cikin motar shi kafin ya fito ya fitowa sai yai kokarin bin ta kofar baya don ya shige cikin gida,
Muryan Mr Emanuel yaji cikin yar buguwa yana kiran shi yazo su gaisa da abokan shi,,
Bsdon yaso ba ya karaso har inda suke zaune,
Kwalban giya yake kokarin mika ma dan nashi yana wani irin dariya sama sama,
Kai kawai Joseph ya kada mai alamar a,a ya taka tabaya yadan juya zuwa cikin gida,
Yana shiga wanka ya wuce yi direct bayan fitone ya iske wayar shi na ringing,
KB aka rubuta barobaro a cikin harshen hausa yace KB ya,ya dai,?
KB ya ce mai yaga jibrin din da yake bida yadawo gari shiyasa ya kira shi don yafada, mai
Yace ka gane ne KB yanzu kabani a wa biyu pls, zan zo in samay ka muje gidan su,
Eneka sister shi ce tafado Dakin tana cewa brother muna jiran ka a,palour pa,
Saida yadan kara kamar minti goma yafito cikin wasu yan kananin kaya,
Yasamay duk a rusunne pastor yana tsaye sai addu,a yake zabgawa suko suna ta fadin Amen, Amen,
Bin sahun su yayi ya jona su a haka akai ta masu wana addu,an har zuwa wani lokaci,
Baban shi dama a buge yake tatil da giya tun a nan ya tuntsire ya fara nasari,
Joseph ya ciro kudi tare da dafa ma pastor baya har zuwa gurin motar shi, ya mika mai kudin yana nuna godiyan su da wanan ziyarar da pastorn yai masu,,,
Daga nan baikoma ciki ba, ya wuce zuwa inda KB, ke jiran shi su tafi,
Gidan su jibrin Bala suka tafi cikin daren nan,
Jibrin na cikin gida akace wai ana mai sallama,
Bai wani bata lokaci ba yafito , yayi mamaki kwarai ganin Joseph yasa shi yin wani dan ihu, har saida yajawo hakalin mutane,masu wucewa, gare su,
Yayi farin cik kwarai da,ganin Joseph yace Yusuf Joseph ke nan duk sai suka dariya a lokaci guda saboda, tuna wa da wani zamanin da yawuce a baya,
Inda Joseph ke cewa shima sunan shi Yusuf Joseph, ne, kama yadda Kabiru lawal Jibrin Bala,sai Musa Aliyu,
Shima Joseph sai ya cire Joseph Emanuel ,,
Yace ya koma Yusuf Joseph,
Dariya yayi yadankai wa jibrin din dan duka ga kafadar shi cikin dariya,
Suka kara lalewa, da junar su, nan fahira ya barke a tsakanin su na yau she rabo,
Sun dauki wani dan lokaci sanan sukabar uguwar yamman inda gidan su jibrin bala din yake,,
Kafin su rabu Joseph ya debo kudi masu yawa ya mika wa jibrin din yana mai bashi hakkuri,
Kan cewa bai san cewa zai kwana ba don bukin yazo na nada sabbin shugaban nin church din su da akayi, kuma duk ya kashe kudin shi ga jama,a
Tun da ya aje KB a uguwar tukura, yasa kai zuwa gida ziciyar shi fam da tunanen halin yadda ya ga abokan nashi ciki,
Duk da goma na dare ya wuce har da rabi hakan bai hana shi cin ma yan uwan shi zaune suna jiran shi ba,
Ya bude falon kusan lokaci guda bakin su ke cewa brother welcome,
Ya ansa masu da ce how you na dey,?
Saida yadan shiga daga ciki tukun sannan yafito cikin wasu yan kananin kayan barci,
Sai a lokacin ya tuna cewa bai co wani abinci ba don haka inda suke cin abinci ya wuce sakwara da miyar ego yaji egushi da naman shano,
Ya wanke hannuwar shi ya fara ci, sai da ya gama cin abincin sanan ya isa, inda yan uwan shi suke zaune yake tambayar su inda baban su yake,
Da hannu suka nuna mai hanyar kofar dakin shi,
Anan suka fara mai korafi kowa da abinda yake so amai da ga cikin su,,,
Wa yanda zaiba kudi yaba su, wa yanda kuma zai, sayo wa abu yai masu alkawari,
Tunda safe yai asubanci yabar gari yadauki hanyar lagos, saidai zuciyar shi fam yake da tunanen yadda ya yaga abokan shi suka koma cikin dan lokaci guda,,,
Bayan tafiyan Joseph abokan shi suka dinga rumors a gari cewa Joseph yazo wasu su ce yadawo,
Kafin wani lokaci sai maganganu ya karade gari wasu nacewa aiki yasamu mai tsoka,
Wasu nace harkan business din zamani yakeyi watau, dai smuggling, wasu kuma suka ce ai dan shan jini ne,
Inba haka ba ya zaiyi kudi haka cikin dan lokaci guda, kamar yafi su bida,
KB ne a saman babur din shi, yana tafiya zuwa gidan wani dan uwan su don ya kai sako,
Hadewa sukayi da jibrin a daidai junction, anan suka dan tsaya don su gaisa,
A haka suka sako hiran Joseph cikin zancen su, inda suke yaba alherin da yazo yai masu,
KB yace wai ko kasan cewa mutane da daukar wa kan su wahala da nauyi wai har sun fassara dukiyar Joseph da wata, ma,ana,,,
Cikin mamaki jibrin yace kai mutumina bari zancen nan pa,
Yace wallahi man ni ma su jamil suka tare ni hanya suke ce min wai ko da gaske ne zancen da sukaji game da Joseph ance wai yayi fitacen kudi,
Jibrin ya kada kanshi yace kai mutum mutum abin tsoro ne wlh,
Yanzun nan har sun fassara wanan guy din dawatq ma,ana ko,
Allah ya kyauta kawai suka iya cewa suka dan kara taba hira sukabar gurin cikin alkawarin kara haduwa nan gaba,
Daidai wanan lokacin Joseph yana zaune a cikin kayattacen falon shi da garin lagos zaune yake cikin shigar kananin kaya,
Kallo guda zakai mai ko ba,a fada maka ba zakasan cewa kaya ne, masu tsada a jikin shi,
TV yake kallo a zahiri saidai gaskiya ba wai abinda ke faruwa a cikin TV yake kallo ba,
Don dai zuciyar shi na can tana tunanen abokan shi na kurciya da yagani cikin halin taimako,,
A hankali ya furzar da yar iska daga bakin shi yana dan bugun hannun shi a hankali,
Jinkarar bude kofar da akayi a lokacin ya dan waiga don ganin wanda ya shigo cikin falon a lokacin,
Inok ne ya shigo wani abokin shi ne da suke yawan mu,amula indan yana Lagos da shi,
Inok yazo inda yake suka yar lalai hannu cikin nuna kulawa,
Inok yana kaiwa zaune yace wa Joseph kai aboki nai muna sabon kamu fa,
Duk da nasan cewa kaiba dan wanan harkan bane , nasan cewa wanan karon zaka kamu sosai indan har kaga cik din nan,,,
Kwantar da bayan shi yayi a saman kujera yadan waigo inda Inok ke zaune yana murmushi ya ce nagode da gudun mawarka amma kasani cewa ni wanan harkan bata a gabana yanzun haka,
Indadai wani business ne kasamo muna danafi kowa farin ciki da kai yau,
Baki bude Inok ke kallon Joseph yana mamakin irin halinshi na ko in kula ga mata,
Gashi dai yaro matashi mai jini ajika aman ba ruwan shi da harkan mata,,
Sai cewa yayi wai kai joe wani irin guy ne kodai matane baka so sai maza,
Cikin mamaki Joseph ya kalleshi alamar mamaki karara a fuskan shi yace
God forbid bad things,,,,,
Me, Joseph doing such bad habit in my life never,,,,
Daga haka yamike tsaye ya haye sama abinshi ya ma kulle kofar dakin shi yabar Inok zaune a falon
Ido kawai Inok ya bishi dashi har zuwa lokacin da Joseph yabugo kofar dakin da karfi
Inok ya mike tsaye yana mai watsar da hannuwar shi alamar haka take gare shi,
Sai da Joseph ya tabbatar da cewa Inok yabar gidan sannan ya fito ya dauki makullin motar shi yabar gidan cikin kunar rai,
Direct inda suke shan whisky ya nufa can ya zauna yadan sha kadan sanan yabar gurin zuwa gidan wani kawun shi da yake son ziyara da dadewa,
A can gidan yakai dare tare da uncle Sam, inda suka dan taba hira gamay da halin da family su ke ciki,
Kafin atafi saida yaiwa babban dan uncle sam , alkawrin samun aiki,
Sai bayan yadawo kamar da kwana uku ne yakira nobar wayan jibrin da yabashi ranan da suka hadu ,,,
Sun kai wani dan lokaci suna hira cikin mutunci inda suke ta hiran classmates din su,, da kuma irin gidajen da suke zuwa idan antashi makaranta,
Sunyi dariya sosai idan sun tuna da wani abu da sukayi ada suna yara,,,,,,,
A haka sukyi ban kwana da junar su har zuwa wani lokaci,,,,,,,,,
Kwance yake yana barci a saman tangamay may gadon shi,
Karar wayace ta katse mai barcin dayakeyi , a hankali ya diba kowaye yakirashi cikin dare haja,
Monday yagani rubuce, acikin muryan barci ya dauki wayan ya kara a nunen shi yace,
Hello, a bangaren Monday ya ansa da cewa hello sir,
Anan Monday ke sheda mai cewa wai motar man su guda da aki loading zuwa westnorth ta samu matsala a hanya har mai ya tsiyaye,
Awani dan kauye kuma sunyi iya kokarin su su tasarya abin ya gagara shiyasa ya bgo mai wayar,,
Mikewa yayi zaune daga kwanciyar da yayi batare da yaba monday ansa ba ya kashe, wayar,shi,
Wurin window dakin shi yanufa tsaye yake yana kallon hasken fitilun da yadan haska duhun dare, kamar yadda taurari suke haska sama,
A fill ya furta Monday, I will delling with u, soon, gurin fridge ya wuce yadauko ruban ruwan sanyi ya kwakwade shi dukka, lokaci guda ya cillar da robon kasa,,,,
A ranan barci rabi da rabi yayi don zuciyar shi na kuna ga irin rainin hankalin dasu Monday ke yi mashi,
Don kashi na uku kenan suna mai wanan hasarar da kuma wawaso,
Tunda safe ya shirya tafiya zuwa arewa batare da sanin kowa ba,
Sai da yai nisa yai wa KB waya, yana msi tambayar shi idan har bai komai yana son ya raka shi wani uguwa,
A suleja suka hadu, suka kama hanyar zuwa inda minday yace sun samu matsala,
Har zuwa adamawa babu tanker motar dasuka hadu da ita a saman hanya, da zasu dawo kuma suka kara bi ta wani sabon hanya da akai masu kwatance
Still a nan ma basuga komai ba, sai mota guda suka fani kuma ba ta company su bace ,
Kiran monday yayi yace ya fada mai daidai inda motar tasamu matsala gashi a cikin North,
Cikin rudani Monday yace what, You mean you are in North now yace mai of,course,
Jin yadda monday ke in,inniya yasa shi kashe wayar shi,,,,,,,,,
ZEEEEE MAKAWA,,,,,,,,,,,,,,,
[1/22, 2:17 PM] +234 805 298 5148: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJ
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎
Assalamu Alaikum yan uwa dan Allah kuyi hakuri don ina sane da sunan da yakamata in sa wa , wanan novel din sai dai a gaskiya ina ganin kamar akwai wace ta riga tayi novel da wanan sunan, ( FUREN KAN JUJI)
Hakan yasa na can za wa nawa suna namaida shi FUREN JUJI dafatan zakuyi maneji dashi hakana,,, nagode,,,,,,,,
Sai musalin shadayan dare suka isa cikin garin kwantagora,
Gidan su KB ya wuce direct don ya sauke shi, tare da tsarabar da sukayo ma yan gidan su KB din,
Tsarabar doya ce da manja,don saida buth ya cika fam,
Acikin daren ya wuce zuwa gidan su dake can uguwar sabon gari,
Duk da dare yayi amma yasamu yan gidan su sun dawo daga church suna kokarin cin abinci,
Cikin murna da farin ciki suke tariyan shi, shiko ya na dan buga masu kafada ahankali,
Inda mahaifin shi yake zaune saman dogon kujerar dake falon gidan nasu da gashi sai yar singilati da gajeren wando,
Sai abin fitar da ke a hannunshi yanadan fifitawa a hankali,
Daidai satin kafan uban yadan duka inda uban yadan dafa mai kai ya na cewa you are welcome, ba,,,,
Joseph Why d, you like to travel in d