Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
su keyi wa yayyen su,
Dan tsayawa yayi, cak, Agogon shi yadiba ya dan ya mutsa fuskan shi kadan yace mata,
Cikin dan sakin fuska sorry sister, i don't have time for dat pls,,
Kai Ejoma ta kara dan langabewa tadauki cup tea ta,nufi inda yake tsaye har a lokacin yana kokarin gyara nicktie, din shi,
Cup din tea din dake hannun ta tamika, mai tana cewa brother i beg drink dis ,even small now,
O my god, Ejoma iam telling ,u now, dat iam, late,
Ba yadda ya ita dole ya karba ya dan kurba tsa,tsaye, kadan kadan,
Yamika mata cup din cikin sauri yabar falon don gudun kada Ejoma ta jawo mai wata matsalar kuma
Yana fita Ejoma dake tsaye tadan bi bayan shi da kallo tana dan girgiza kanta,, Busy man ta furta,
Ba laifi don yasa bakin nasu basu karaso ba, gurin da za ai taron,
Wasu yan kasan Cameron da Guinea ne zasuyi wani dan meetings da su ta yadda zasu dinga tura masu mai acikin farashi mai sauki,
Sai kuma kada watau ( Cotton) zasu yi harkan business din shi dasu,
Sosai Joseph din ke jin dadin meeting din tare da bakin nasu saboda akwai abubuwan da ya fahinta so sai a fan,nin kasashen biyu,,,
Tsawon wani lokaci suna wanan, taron har zuwa daidai da lokacin sallah a zuhur,
Kawai sai mutum guda daga cikin su baki,ne so sai wulk da shi,wanda ke cikin shigar bakaken coth
Tare da wani daya wanda shiko wasu kanan kaya yasa sun bala,in yi mashi kyau sosai,
Mutumin farkon ne yafara daga hannun shi yadan kalli agogon hannu, wanda ke nuna karfe, daya da wani abu na rana,
Mikewa yayi zubur yana mai ce ma sauran abokan meeting din I want to pray,
Joseph da a,lokacin yake kokarin diba wasu takardun dake a gaban shi yai sauri daga kai ya kalli mutumin
Wanda shi azaton shi tun farkon shigowar su yadauka dan bishon ne,
Wai a,she muslumi ne, diban shi yakara konawa ga gudan da ke kojarin sance agogon hannun shi
Kamar yadda yaga su KB na yawan yi idan zasu yi, alwala,
Duk a cikin mamaki yadinga kallon su a zuciyar shi kuma cewa yayi,
Ashe shi musulumi bawai dole ta kam ki wani hali zaka iya sheda shi ba ke nan kamar yadda yaga sauran, musullumai suna rike tasbaha ko kuma rawani ko sa tufafi mai nuna sheda,
Kafin ya farga yana a cikin tunanen sai gani wa yan nan biyu dake gefen shi sun mike suma zuwa yin sallah,
Ya kai wani lokaci yana ta al,ajabin wanan abin da yagani a tare da wa yan nan baki nasu, sosai,
Wayar shi tai kara don haka yafita tadan waje kadan daga dakin taron,don,yar karba call din,
Abakin wani daki dake gefen inda,suke taron yaga takalma mutane agurin,
Sautin ladani sallah yaji har inda yake yana fadar Allahu,Akbar, Sami,al,llahu limal,hamd
Kamar ance ya waiga hango su yayi still suna cikin shigar tufafin da Joseph ke tunanen zasu hanasu yin sallah,
Can karshe yanufa ya ci gaba da maganar da yake yi,
Har zuwa dawowar shi sun rarage sallah sun idar suna zaune suna lazimi,
Ya zauna bada wani jimawa ba saiga su Aoudullah sun shigo duk kan su fuskan su cikin fara,a,
Nan suka fara mikawa mutane hannu suna musabi,a da duk wanda ke gurin,
Sau guda yadan daga kai ya kalle su yai saurin kawar da kan shi,
Sai dai haka kawai ya kalli yan uwan shi Christian dake ta harkokin su cikin rashin damuwa,,,,,,
A gajiye tafito daga dakin daukar lectures din din su yar jakar ta na sabale a kafadar ta,
Tasan cewa A,A yana aji a lokacin don haka bata wahal da rayuwar ta zuwa office din shi,
Saboda yanzu ma duk ta rage yawan zuwa gurin shi don guje wa shedan,
A,kwai wani dan korido wanda zai sadaka da wata department namasu yin computer science,
Iccen da ke gurin andan kawata shi da wasu kuherun kasa da akayi wa farin penti,
Can ta nufa da niyar zuwa ta zauna, kafin lokacin shigar ta lecture yayi,
Wata matashiryar buduwar ce zata dan girmay ma maryam kadan,
Zaune take ta hada kai da gwiwa alamar a cikin tashin hankali ,take,don tayi zaune tayi tagumi,
Gefen ta maryam ta zauna tare da fadin Bissimillahi,
Hannu tasa acikin yar jakar ta tadauko wani dan bunch din digestive, biscuit, da wani dan lemon kwali,
Gefen da yariyar data tarar a zaune tadan kalla karo na farko tunzuwan ta tazauna gurin,
Mikawa yarinyar ledar biscuit din tayi tana mai mata Bissimillah,
A hankali yariyar tadaga kai da idon ta da sukayi jawur, a lokacin, ta,dan girgiza wa Maryam kai alamar a,a, tafurta nagode,
Sau guda maryam ta dan tauna biscuit din sai taji kawai bataji dadin yadda ta lura da cewa yarinyar na kokarin share hawayen ta da gefen gyalenta,
Lafiya dai ko Maryam tai katsalandar din tambayar yarinyar,
Wani kuka tasake lokaci guda tace wallahi yar uwa matsalar malam nan ne ke damuna ace mutane yan uwanka musullumai su dinga maka sheri,
A hankali Maryam ta aje kwalin lemon da tafara dan zuka a lokacin ta mai da hanjalinta gun yarinyar,
Yarinyar tace ni sabuwar zuwa ce a wanan school din, gashi na kusa kamalla duk wani abin da yakamata inyi amma gashi HOD din mu yaki samun hannu a takarda na wai bai yarda da results dina ba,
Wani irin mugun tausayi yarinyar taba Maryam jin bakinta kawai tayi yana tambayar yarinyar wani department ne,
Tace computer science, zubur Maryam ta mike ta kokarin gyara gyalen da tai rolling din kanta dashi,
Shigar shi office ke nan yana kokarin dauko ruwa acikin dan karamin Fridge din dake office din,
Da sallamar ta shigo office din sam bai zaci zuwanta yanzu ba don yasan cewa sai ta gama abin da takeyi takan zo su wuce gida, watarana ma sam baya ganin ta saidai suyi tayin waya,
Ganin ta yanzu yasa yasan da matsala fuskanta ya dan kalla yaga damuwa fal acikinta,
Daidai lokacin da yake zama yake cewa lafiya kuwa Maryam,
Ido tadan tsura mai yau babu ko kiftawa, yai mamakin hakan sosai a, ranshi don yasan cewa ba halinta bane hakan,
Zai yi magana sai yaji muryan tana cikin rauni tana magana,a hankali,
Malam banaso sam, sunan ka, ya dinga fitowa daga cikin azzaluman malam makarantar nan,
Masu kokarin kayarda ditan mutane, daga cigaban su,
Kafin taci gaba yadaga mata hannu alamar ta tsayar da zancen ta hakana,
Cikin mamaki yake tambayar ta komay ke faruwa da har tazo mai a haka,?
Nan ta kwashe yarda sukayi da wanan yariyar ta fada mai,
A, cikin mamaki yake tambayar cewa yaushe akai haka da shi,sam bai ma san zancen ba
Can yace ina ita yarinya tana daga waje inji Maryam,
Da sallama maryam suka dawo tare da wanan yarinya,,,
Cikin ladabi tagaida malam din wanda ke dan rubutu a wani dan pepper,,
Yadago kai yakali inda suke yana mai mika mata hannu alamar takawo takardun ta, dake hannun ta,
Ba,bata lokaci taciro su daga cikin handabag din ta, ta mika mashi su, jiki na rawa, kamar zata fadi don tsoro,
Tai mamaki kwarai da taga yasa mata hannu batare da bata lokacin komai ba cikin yan mintuna
Ita ko yanzu kusan wata daya da rabi ke nan tana ta faman bin, ai, mata wanan aikin abu ya faskara,
Sai gashi yau Allah yakawo mata shi a cikin sauki ta samu an mata,
Yana gamawa yadago ido ya kalli yariyar yace mata kin taba gani na akan wanan takardan,
Tace duk lokacin da nazo sai messenger ya ce min baka nan komaya yace ance bazan samu ba karshe ma sai ce min yayi ance takarduna basa yi wai,,,,,,
Bayan fitowar su ne wanan yariyar ta rungumay Maryam tsam a jikin ta tana ta zuba godiya anan take sheda mata cewa sunan ta Safiya,
Tundaga wanan ranan suka kulla friendship mai àkarfi a tsakanin su har takai in har guda baiga guda ba, bai jin dadi,
Yau tsawon kwana biyu kenan Safiya bata shigo makaranta ba,
Don haka Maryam tashiga cikin damuwa sosai,
Nobar wayan ta takira wanda kwana biyu kenan nobar bata shiga koda takira sai ace is switch off,
Yau kira guda Allah yasa nobar yashiga, batare da wani bata lokaci ba aka dauka a dayan bangaren,
Nan take jin cewa ai safiya mahaifiyar tace bata da lafiya suna asibiti da ita,
Maryam taima safiya alkawarin zuwa dubata, insha Allah,
Sukayi sallama tare da aje wayan cikin nuna tausayi,
Maryam ta fadawa Anty abinda yasamu mahaifiyar safiya,da ke asibiti kwance,
Itama dai anty ta tausayawa safiya da mahaifiyar ta,
Cikin wata raunaniyar murya tace wa anty idan tasamu time weekend zata tafi ta dibo maralafiyan,
Anty Dije tace Allah yasa don dai ke ce da kanki kikayi wanan alkawarin don nasan cewa bazaki tafi ba,
Cikin dan marairaice murya, Maryam tace, insha,Allah zan kokarta in tafi, ai saboda safiya nada kokari wlh,,
Da dare suna zaune a harabar tsakar gidan su suna shan iska
Saboda dauke wutan neper da akayi yau garin yai zafi,
Sallama suka akofar shigowa gida, Maryam wace ke kwance saman wata tabar roba da suka baza tana karatu don tana da test a cikin satin nan,,,,
Cikin mamaki gaba dayan su suke cewa muryan baba ne fa,
Cikin farin cike duk suka mike suna tariyan shi,
Wani tabarma aka dauko wa baba yazauna tare da jawo Isslam da Assalam zuwa jikin shi,,,
Sun gaisa sosai da baba sai shiru yadan biyo baya,
Baba yace wa Anty Dije yazo ne yadibi lafiyan su, da kuma zancen maryam,
Maryam wace ke zaune gefe guda gaban ta yaba da damm,
Nan baba yake tambayar Anty may ake ciki ne da zancen
Anty Dije wace ke dan gefe tsugunne tadan kara gyara zaman ta tace wa baba,
Baba maryam fa karatu takeyi yanzu dan Allah ba ba kayi hakkuri har tadan karasa sai ai zancen auren ta,
Baba ya ce, a,a Dije banaki tanaki bane saidai kin san cewa yanzu mutane ba sui ma baya,
Kin,ga gara tun inada rai muyi mata aure kada in mutu in barki da nauyi ke kadai,
Maganar taso taba anty Dije dariya sai dai ta yar murmusa kawai tace
Insha Allah baba kana da rai maryam zatayi aure kuma kaida kanka zaka aurar da abinka,
Amma zancen cewa zaka tallafa min sa abinda zan aurar da ita don Allah baba ka daina wanan zance,,
Allah zai hore min duk wani abu da za,ai mata, baba ya ce haba Dije ayi haka,?
Da ki bari in saida yar shanun da nake kiwo sai in baki ki kara don kinga mahaifiyar ta nasan ba komai za,a samu a gurin ta ba tun da a kauye suke,
Daga Anty har maryam saida tausayin dan tsohon ya kama su,
Anty Dije tace cikun wasa baba kaje ka saida shanun ka kuci abinci da iyalin ka,
Allah na nan zai rufa asiri insha Allah,
Mudai fatan shine kai mata addua Allah yabata miji na gari,
Ameen Ameen baba yafara fadi yana mai jerowa yqr diyar tashi dayake kauna aboye kuma take bashi tausayi kasan cewar ta ita kadai a gidan,
Bayan tafiyan baba nan su ka zauna suna tausayin mahafin nasu mutun wanda baison hayaniya kuma bai shiga harkan kowa,
Auren KB yataso sosai da ma so yake ya karasa ginar shi sai ata da zancen,
Don haka yanzu da ya karasa ginan ya ta da zancen,
Saboda yana bukatar yai azumin bana da matar sa,
Saidai gidan matar sun dan kawo mashi tasa matsalar cewa basu shirya ba,
Nan KB din yabude masu wuta babu sassautawa, cewa shi fa yana bukatar matar kafin watan ramadan,
Maryam dake kitchen tanawa anty aikin abinci tanajin yadda KB ke fadawa wani wanda bata fahinci kowaye ba acikin waya,
Saidai daga karshen zance taji KB din nacewa nifa gaskiya na kashe kudi masu yawa a wanan harkan,
Sannu sanu taji yana rage tsauriñ masifar da yaketa zubawa a waya, da alamar wanda suke wayar ya dan lalashe shi ne,
Cike da takaici maryam ke aikin ta tana sauraren kb wanda ke zaune a falo shida mijin anty dije, da ita anty dijen,
Jin ya ambaci sunan Joseph yasa ta tuna dashi saboda da,dewan da yayi bai shi garin ba,
Zancen tsohon nan yafado mata arai ganin cewa ga mijin antyn ta agari gashi bai zo ba akan zancen,
A cikin hikima da dabara ta tunawa anty da zancen nan anty ta kwashe komai ta fadawa maigidan ta,
Shiru yadan yi yana tunanen zance,
Can yace wa matar shi kin san wanan wani babban al,amari ne,
Don dai da wuya Joseph ya can za zuwa wani addini tunda har kikaga yakai war haka bai nuna wani alama ba,
Don haka kawai kubar wanan zancen kada ku dauko min magana at last,
Maryam dake sauraren bayan nin mijin yar nata sai taji wani haushin shi yakama ta,
Bata san irin halin mijin yar uwar nata ba da rashin son tallafawa addini,
Wanan ai taimako ne amna sai gashi yana kakaucewa,
Batare da wani kwakwaran magana ba mijin yar nata yabar gari,wanda hakan yakona wa Maryam rai,
Dadare bayan tagama komai ta sa wanan sim din nata na boye ta dauko tasa,a wayar ta,
Tai rubutu kamar haka
A TRUE BELIEVERS, BELIEVE IN ISLAM,,,,,
ZEEEE MAKAWA,,,,,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
2⃣1⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Tun Mr Ema yana fushi da dan shi kan laifin da yayi sai gashi yanzu shi da kan shi ke bukatan dan yazo gari,
Saboda irin dadewawar da yayi bai shigo garin ba,
A, gaskiya kuma baida time yanzu kamar da, da bai wani aiki mai yau, don yanzu ko kasar bai faye zama ba,
Duk wanda yadade baiga Joseph ba idan ya gan shi yanzu yasan cewa akwai canji so sai,
Yanzu ya zama mai dole ya shigo badon komai ba saidon kare mutuncin church din su,
Church din su da ke fuskantar barazana daga sauran churches din dakw garin,
Taro ne zasu yi nakasa mai girma wanda saboda hadin kai irin nasu duk inda mabiyi wanan church din yake dole ne yazo da jamar, sa, saboda da ci gaba,
Yan churching su Joseph sun gano cewa ana so a zarta su daga wata kungiyar kirtawa,
Don hakane suka hada wanan taron na ci gaban su,
Shiri so sai Joseph yaiwa wanan tafiyar saboda irin dadewar da yayi bai shigo garin ba,
Maman Choima da Ejoma da danta, sai shi Joseph din dake jan su da kan shi tun daga Lagos,
Tanks god ya furta a hankali kamar yadda yasaba maganar shi cikin natsuwa,,,
A,lokacin da yahango irin aikin da yaita turowa ana gyara masu gidan su,
Ginan yayi mai sosai don tun daga nesa yahango ginan ya fada da anguwa sosai,,
Baka jin komai a motar sai muryan wata mawakin IBO mai waken churches, Rabeca Gebrin,
Joseph nason wakokin wanan mawakiyar mai zakin murya saboda iya fitar da baitoci da takeyi ga Jesus,
A hankali shima yake marming din wakar inda kusan daidai da mawakiyar bakin su ke tafiya,
"Keddo, "Edema yye Jesu, Na,belewawooo,,,,
Shima bin wakae yakeyi yana dan dukar sitiyarin motar,tashi,,
Kyawon motar kesa mutane na waiga wa don bakuwar motace da nobar Lagos,
Mr Ema yai murna kwarai daga ganin dan nashi wanda sun kusa shekara guda bai,zo ba, gashi yai, wani irin fresh,
Yazama full getle man, ya aje wani irin saje da yadan kewaye mai fuska gwanin sha,a wa,
Duk Wanda ke gidan yau murna sukeyi da zuwan Joseph tare da su Granny, da Ejoma,
Kamshi kakeji duk inda kabi kala,kala, a cikin gidan jen yan mabiya churching Catholic,,
Shi kan shi Joseph yaji dadin yadda ya, samu mahaifin shi a cikin koshin lafiya,,,
Inda mahaifin yake ya iso ya dafa kasa da hannu guda yana mai daga kafa guda ta baya,daidai saitin kafar mr Emanuel,
Kan yaron nashi yadafa yana mai yi mai addu,a,acikin ki,rari,,,,
Dan murmushi yayi yana mai mikewa cikin jindadi, samun blessing din ya yi daga mahaifin shi,
Daga Maman Choima da Ejoma duk sun zo inda yake sun gaishe shi,
Ya amsa ba yabo babu fallasa,tunda baida yadda,zai