Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
dadin wanan baccin da ya samu yayi ,, don yaji saukin
Don da bai yi barcin nan na a haka zai wuni cikin bakin ciki da kunci,,
Wanka ya fada yana fitowa ya wuce massallaci,
Bayan yadawo ne yaji shi wani wasai da shi duk wani bakin ciki da kuncin da yake, ji ya daina jin su,gaba daya,
Dining table ya nufa inda yasamu hamza ya hada mai abincin shi, haka ya dinga cusawa a cikin shi, har sai da yaji yayi dam,
Komawa yayi saman two sitter yadan kwanta kamar mai yin barcci, hannun shi rike da goshin shi,
Tunane yake yi don sai yanzu yasan ko may ye so,
Tabbas bai taba sanin cewa ana son mutum irin yadda yake jin Maryam a,rayuwar shi a halin yanzu,
Kusan kwana biyu yana cikin wanan damuwar idan kaga walwalar Yusuf sai idan yana tare da,Sonny ko Jibrin
Lokacin da Sonny ya gama abinda yakeyi a garin su,
Don haka sai suka fara shirin tafiya kwantagora ganin kayan al,adu kamar yadda,Sonny din yaji labarin su daga bakin Jibrin abokin hiran shi da yawo,
Shiri na sosai sukayi saboda irin shigar da zasuyi yana bukatan kudade, da sauran abubuwa,
Ba su wani dade a hanya ba ko da suka taso,
Saboda irin gudun da sukeyi ga kuma motocin su lafiyyayu ne so sai,
Sun iso lafiya garin sai dai wanan karon bai wuce direct gida Anty nashi ba,
Sosai tun a hanya Yusuf ke kallon tsarin kasan hausaw yana mai yabawa da irin abin da yake gani,
Shigowan su garin yakara sa Sonny rudewa sosai don gani yadda garin ya tsaru tsab,
Yusuf ne ya dan sulale zuwa gidan Anty nashi don ya sanar masu da zuwan Sonny,
Ya iso kofan gidan su Anty Dije din inda yaga samarin dake fira kamar kullun
Sun mike sukayo kan shi cikin murna danuna jin dafin zuwan shi,,
Wanda hakan ba karamin dadi yaiwa Yusuf din ba, a cikin ran shi,
Don ko ba komai sun nana mai kulawan su gare shi,
Nan suka,shiga jiddan kayan tsaraba zuwa cikk cikin jin dadi,
Anty Dije ce ya riske a kofan kitchen tana kokarin dauko plate a mazaunin shi,
Tana ganin Yusuf da jin sallamar shi ta mike da fara,an ta tana mai sannu da zuwa da bakin da babu sanarwa,
Ya yai dariya duk da yau kawai sai ya tsinci kan shi da jin kunya da nauyin anty din,
Yakaraso gaban ta yadan rusunna, yace Anty barka da gida,
Cikin dan hararan wasa tace gaskiya Yusuf kana son muyi fada yanzu,
Dariya yakara yace tuba nake Anty na tafiyan bazata yazo min,
Shiru Anty tayi cike da mamaki, jin abinda yace batare da taga wani alamar waaa a fuskan shi ba,
Sai kuma batayi magana ba tace to sannun ku da zuwa,
Ya amsa da cewa yauwa Anty mun samay ku lafiya,
Sai dan satan kallon ko ina yakeyi ko zai hango maryam da idon shi,
Ya dan fuskan ci anty din yace wanan karon fa sa bako nazo anty,
Gaba daya hankalinta ta mayar gareshi don jin abinda yace,
Falin suka shiga a lokacin,sanan yakara cewa wa qn a bokin nawa dake South Korea shine mukazo dashi don yaga gari,
Zama yayi yana mata bayanin makasudin zuwan Sonny kwantagora,
Maryam wace kamshin Yusuf kawai ya isar mata isowar shi gidan daga gurin da ta idar da,sallah ta kwanta,
Zubur tamike daga saman abin sallah da take kwance tafito daga dan wajen window inda zata ita hango Yusuf din,
Daga inda take tadan daga labule tana hangen shi,
Yana saye cikin wasu kanan kaya da suka kara mai kyau suka fitar mai da kurciyar shi da,wayewar shi fili,
Hannayen shi suna zube a cikin aljihun wandon, shi,
Wani irin lumshe idon ta tayi lokacin da hancin ta ya shakan mata kamshin shi,
Jikin shi ne yabashi cewa ana kallon shi don haka yadaga ifon shi, zuwa kallon gurin da take,
Daidai lokacin da ta bude lumsasun idanun ta suka hada ido da Yusuf din,
Cikin sauri maryam din ta sake labulen tayo baya tana mai dafe kirjin ta tankar wace taji tsoro ko taga abin tsoro,
Wani irin lalausar Murmushi ya sake a lokaci guda,
Son Maryam din ne yaji yakara shigan shi a lokaci guda,, bai taba jin yana son mace haka ba sai wanan karon,
Muryan Γnty ce ya katse show din itace ke kiran maryam din,
Sai da ta sa wani dan karamin hijabin ta baki a saman kayan dake a jikin ta sannan tafito cikin tako guda guda,
Kanta a kasa ta karaso gaban su saboda kunya, duk ya rufe ta,
A hankali tace mai sannu da zuwa uncle ya hanya,?
Tafadi a hankali kamar wace bakin ta ke ciwon magana cikin wani irin taushin murya,
Daga Yusuf har anty yanayin maryam ya basu tausayi , sai dai duk suka share,
Ta juya zata wuce ne anty tace cikin murya maikama da rauni,
Tsaya mana maryan ku gasi zan dan shiga gidan lami in samo kankara ne,
Bayan wucewan anty ne makwabta Yusuf wanda ke zaune dan nesa kadan daga gurin da take tsaye kamar kwance saman bayan kujera,
Kanshi yadago yadan kalle ta cikin wani irin yanayi mai rikitar wa,
Da sauri maryam takara dukar da kanta kasa tana wasa da yan yatsun ta,
Batayi aune ba sai ganin mutum tayi a gaban ta tsaye yana mata wani shu,umin murmushi,
Murya kasa kasa yace baki yi murna da gani na ba ke nan ko ?
Jin hakan yadan sata saurin dago kai suka kara yin ido biyu karo na biyu da shigowan shi,
Ido ya kashe mata wanda hakan yasa maryam din duk ta wani rude a lokaci guda, ta dago idon ta cikin rudewa da razanar
Nan da nan gangan jikinta yadauki rawa don jin numfashin Yusuf din gab da ita,
Ganin irin yadda maryam din ta rude a lokaci guda yasa shi tsayawa yana mata wani irin kallo cikj. So da kauna,
Ji yake a lokacin tamkar ya rungumay maryam din da gagawa,
Amma yin hakan haramun hakan bazai yiyu a garesu ba,
Dole ya tillasta kan shi da dan ja da baya daga kusan tan junan da sukayi suna fuskan tar junan su,
Maryam yakira sunan ta cikin wani kasalalen murya tankar wanda ya tashi daga barci,
Yace may yasa kika ki bugo min waya tun daga wancan ranan da kika kirani,?
Idan kuma nakira baki picking, Why maryam,? why ?,
Yafada tankar wanda zaiyi kuka alokacin don wani irin abu da yaji yana fusgan shi,
Tabbas komai yana iya faruwa a irin yadda yake ji akan ta
Da gagawa ya juya zuwa gurin da yatashi da farko ya zauna,
Lemon da Anty Dije ta aje mai saman table ya tsiya a cup,
Sai lokacin maryam tadan saita kanta daga ruduwar da Yusuf yasakata a ciki cikin yan dakikoki,
Muryan shi taji yana cew ina da bako maryam,
Ina son ki shirya muje ki gaida shi,
Da sauri tadago kan ta takaima gurin da yake kallo,
Kai ya gyda mata yace yes zuwa gobe zan zo in dauke ku keda,su Assalam mutafi,
Sai alokacin maryam tai wani irin ajiyar zuciya har Yusuf din yaji ta daga inda yake,
Kallon ta yakara yi kawai cikin wani shu,umin murmushi sai kuma ya mike tsaye batare da yakara kallon ta ba saboda ba zai iya jurewa ba a irin yadda yake ji,
Don maryam din yaga takara mai wani kyau da girma ga kuma haske da tadan kara, akan bakin tada ke shining,
Daidai zaifitane yace sai ki shirya zuwa gobe din zan kiraki in fada maki time,,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YALWA
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
7β£9β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Anty Saffena, Anty Nafessa harzami, Anty Hafsat Yusuf, Maman Farida, Anty Bintu katsina, Maman Walid, lovely Daughter na Jamila Safiyanu,
Tare da duk wacce ban samu ambatar sunan ta ba aciki da fatan zaku yafe min rashin sa sunan ku a jerin sunayen da nazano,,
Allah ubangiji yakara dauka da bude da rahamansa agare mu baki daya, nagode kwarai yan uwa da irin kulawar da kuke bani a kullun tare da fatan zaku dinga hakkuri dani a koda yaushe,
πππππππ
Saye take cikin,wani dogon riga, mai ruwan Jan colour,,, duwatsun jikin rigar ,farare, ne,
Dinkin dogon hannu ke a jikin rigar ,
Sai gyalen rigar tadan yi roling din kanta dashi,
Sai yar karaman, jaka fara da ta rika a hannun ta, shima yana da wasu stones farare,
Assalam da Issalam suna sanye cikin shigar English wear, masu kyau da daukan ido,
Safiya ma tana saye cikin wani dogon riga light, green, mai kyau dinki shi kamar ta banga, rigar ya karbe ta,
Wanan karon Jibrin ne ya zo da su, daga gidan Anty Dije zuwa gidan Yusuf inda su kaiwa Sonny masauki,
Abincin lunching ne suka dauko daga gurin big Anty din nasu,
Waje suke zazaune saman fararen kujeran roba, suna shan iska, shi da Sonny,
Motar da ta stsaya daga dan nesa dasu kadan hankalin su ya kai garesu,
A hankali suka sako kafan su daga wajen motar, kafan maryam dake saye cikin wasu fararen takalma masu wasu belts a bayan su,
Sonny wanda hankalin shi na gurin motan don ganin cewa a kwai mata a cikin motar shiko dama mayen matane,,
Maryam wace kafar ta kawai ke a waje, ita bata fito ba tukun,
Yaran ne suka fito da murnan su don hango uncle da sukayi zaune daga nesa saboda basu san cewa yazo garin ba,
Sai safiya ce tafito a gaban motar tare da Jibrin din,
Yusuf wanda ke rugumay da yaran ajikin shi yana masu magana hankalin shi ya koma gurin da ya hango ta fitowa daga cikin motar,,
A hankali tafito daga cikin motar yayin da take dan gyara rigan ta a hankali,
Daidai lokacin Safiya ta zagayo ta iso gurin da maryam din take tsaye,
Sonny dake masu kallon kurulla kamar yana son ya, ga,no munin mutum daya daga cikin su,.
Tafiya sukeyi jikin su na wani rausayawa kamar kifi,,
Sonnu wanda numfashin shi yai kamar zai dauke saboda ganin wa yan, nan zukakkan yan matan dake tafe in suke,
Kuma wai duk a cikin wanan garin da yake ma daukan kauye a idon shi,
Wani irin kyaune ga wanan yariyar dake baya saye da Jan riga haka,?
A cikin wanan takon nasu na natsuwa har suka karaso inda su ke zaune,
Idon Sonny din har zuwa lokacin da suka karaso gurin nasu kyam a kan su,
Maryam wace wanan kallon da yake masu duk ya takura ta ji take kamar ta shake shi,
Kujeru suka basu suka nuna masu gurin zama inda Yusuf din yai masu nuni da su zauna,
Ko zaman a cikin natsuwa sukayi shi tare da nuna kamilanci a tare da su,
Sai a lokacin da, Yusuf yaga sun zauna ya dan waigo da hankalishi gaba daya gurin su,
Yana masu sannu da zuwa a cikin harshe hausa,
Sai a lokacin ya waigo gefen gurin da Sonny din yake zaune tankar ruwa yaci shi,
Muryan Yusuf ne yaji yana cewa Mr Sonny meet , Maryam and Safiya our fiance,
Firgigit ya farko daga tunanen da yafara yi naganin yana holewa da wa yan nan kyawawan yan matan ,
Hannu ya mika wa maryam da niyar wai su gaisa,
Kai maryam ta gyada mai, alamar a,a cikin wani shu,umin murmushi amma acikin rata sai kiran Wa,iyazu billah, takeyi,
Subbahanallah lokacin da sautin muryan ta cikin wani irin murya ke cewa is forbidden in our religion,
Amma sai ta daga mai hannayen ta biyu ta hade su guri guda alamar gaisuwan musulmai,
Ba Sonny din ba har, Yusuf da Jibrin ma sun mato a sauraron shi,
Wow, yace I like your style girls,
Ai fa tuni maryam ta tafi da imanin Yusuf din wanda yake jin tankar a yau yafara ganin maryam din tashi,
Ga kuma wani abin bajinta da tayi a gaban shi yanzu wanda yakara sa shi jin ta a ran shi,
Duk yadda ta ga,suna girmama Sonny da mutunta shi bai sa tayi gigin bashi hannu ba,
Kamar irin yadda wasu wayayyu keyi wai saboda waye wa ko boko,
A gaskiya duk yadda zai yi insha Allah dole sai ya mallaki wanan yarinyar a rayunwar shi,
Nan ya shiga gabatar mashi da su da yaran da kuma bashi dan labari akan yaron shi a bokin shi Assalam,
Maryam ce tadan diba agogon wayan ta sai tadago kai ta dan kalli gurin da Yusuf yake zaune rungumay da Assalam
Alamar zasu tafi taimai da kai inda take nuna mai time cikin hikima,
Wani lalausar murmushi ya sakar mata saboda tun dazu yagane cewa a takure take zaune saboda ,
Irin mugun kallon da Sonny ke mata, daga inda yake zaune,,
Yusuf din ne ya mike tsaye daga inda yake yana cewa Jibrin ka mai da su gida saboda time din sallah ya kusa,
Ganin Yusuf din ya mike suma suka mike tare a lokaci guda suna mai yiwa Sonny din sallama,
Dakatar da su yayi ya shiga daga cikin gidan dan jim kadan yafito hannun shi dauke da wasu ledoji masu a lamar,tambarin shago a hannun shi,
Ledan dake dauke da tambarin, kamar na yan kwallo,
Ya,mikawa, maryam, sai kuma Safiya, da ya mikawa gudan,
Thanks, suka ce mai a lokaci guda yayin da kowace tadaga ledan suna mai gwadawa Yusuf din da Jibrin,
Yar dariyan yake yi maikama da yake, a fuskan shi,
Amma shi yusuf a ran shi jiyakeyi tankar ya shake Sonny din saboda irin manyatacen kallon da yaga yanawa maryam din,
Shiko Sonny wanda ya kashe su da ido sai mamakin wanan sarauniyar kyau da yagani a gaban shi,
Kamar yadda Jibrin yazo da su da farko hakama wanan karon shi da kan shi ya mayar da,su gida,
Shigar su gida yai daidai da shigowan kira a wayan ta,
Ko bata diba ba tasan cewa Yusuf ne,
Maryam, tayi yar murmushi, tadiba tana mai lumshe ido,
Don haka batare da ta tsaya gurin Anty Dije kamar yadda tai niyya ba,
Ledan tsaraban kawai ta aje mata a gaban ta, ta shige dakin su,
Itako safiya dama tana kofar gida bata karkare shigowa ba sun dan tsaya da Jibrin din ta a waje,
Maryam tana shiga daki tai receiving din kiran tana mai kara wayan a kunnen ta
Tana mai cewa Assalamu Alaikum, wani iri yaji a kunen shi yarrr a lokacin da sallamar ta yadaki kunnen shi din
Murmushi yayi yana tambayar ta da cewa sun isa gida lafiya ko,
Ta ansa mai da cewa lafiya kalau har ta shigo ciki ai,
Dariya yayi yana cewa
ai yasan ko minti nawa ne zai kai,su gidan dama,
Sai kuma taji a lokaci guda yai tsuki, ya wani ja wani, irin numfashi,
Cikin sanyi jiki murya maryam ke tambayan shi ?
My ya samay ka uncle, kuma,?
Ya saki wani ajiyan zuciya yace,
Kyale ni kawai maryam nayi da na sanin zuwan ku gaida wanan dan iskan wallahi,
Mutum kamar maye kadinga kallin matan mutane haka,agaban ma,ajen su ,,
Baki ji yadda kirjina yake min zafi ba wallahi inda badon bako na bane da ba,abin da zai hana in dake shi yau,
Sakin ajiya zuciya maryam din tayi ta lumshe idon ta,
Tace kasan wanda baida tauhidi bai dauki irin wanan abin a matsayin sabon Allah ba,
Tace amma sai naga kamar mun fi shi laifi ai muda muka tafi hakana gurin shi batare da mun sa zumbudeden hijabi ba
Yusuf daga inda yake ya lumshe idon shi saboda jin abinda maryam din tace don tabbas gaskiyar maganar ke nan,
Wani irin kishin abinda Sonny din yayi dazu ya baibaye mai zuciyar shi,
Sai da kyat yai kokarin kwantar da zuciyar shi, saboda kasancewa Sonny bakon shi, ne,
A haka sukayi sallama da maryam din yana mata godiya akan irin yadda suka yi da bakon nashi,,,
Bayan sallamar su yai zaune yana mai kallon wayan nashi tankar maryam din ce a gaban shi a lokacin
Sai kuma ya juya tunanen irin hali rayuwa na maryam,
Abinda yafi burgeshi da ita shine, hakkuri, ladabi girmamawa uwa,uba addini, gashi ba ruwan ta da duniya,
Don dai ya fahinci cewa Maryam irin matan nan ne dake kona mutum farat daya,
Don duk abinda zakai masu da wahala su tanka ma akai,
Maryam ce zaune tare da Safiya agaban anty dije wace mamaki ya cika,ta,
Ledan safiya ce akafara zazagewa inda sukaga wani dogon riga da turare guda biyu, sai kudi zube sabbi kar dasu, zasu kai kimani dubu dari koda hayi akai,
Sai kuma aka jawo ledan Maryam, wanda ke