Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
ma sai taji kawai ya kashe wayan ma gaba daya,
Tsuki tayi ta wurgata da wayan ta kwanta taci gaba da zubar da hawayen bacin rai,
Tana mai Allah waddai da irin halin baba Ado wanda bai san darajan addini ba sai kuri da shi,
Ko a wani nafsi akace mai an kya maci auren wanda ya tuba
Ita dai a sanin ta baba Ado ya hada da al,adace kawai in bashi ba don mai zai kira Yusuf din da wai furen kan juji,,
Sai zuwa dare tayi taji kira ya shigo mata a waya lokacin har ta yi shirin barci, duk da tasan cewa yau ba zancen barci gare ta,
Jibrin tagani barobaro a wayanta, saida tai tsuki tadauka da fadin cewa kaga damar daukar wayan
Don kaga ina kiran ka shine harda kashe min layi ko,
Dariya yayi mata ya ce haka kawai zan yarda ki damay ni ga banza
Kuka ta farayi tana aheda mai abinda Baba Ado yaiwa Yusuf yau da yazo gurin ta,
Innalillahi kawai Jibrin ke ta nanatawa alokacin saboda maganar tazo mashi a ba,zata,
Yace wai ko dai da gaske Baba Ado bai da hankali kamar yadda mutane kece mai mahaukaci
Ra,ra,shin ta ya yi yace ta bari yaje gurin yusuf din yagani ko ya akayi,
Yusuf wanda alokacin yana can cikin bargo yana jin wani irin amai da zafi na damun shi,
Kuma duk yabi layin wayan shi ya kashe gabaya ba mai kiran shi ya samay shi a lokacin,
Jibrin gidan Yusuf din yazo direct don yadiba shi am.a sai yaga duk ko ina a kulle yake,
Dole yakoma badon yaso ba don yana gudun ya ta dashi daga barci,
ZEEE. MAKAWA
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN, JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
5β£7β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
Ya Allah mun gode ma dakayi acikin Al,uman Annabi Mohammad S,A,W,
Allah kaba ikon koyi da Sunnan a tafarki mai umfani,
Ya Allah katai make muslimi kasar Syria da ma na duniya baki daya,
Ameen Ya Allahπππππππππ
Har muslim sha dayan rana ba labarin Yusuf anty dije sai fada takeyi cewa ya na biwa ta mutane yaki zuwa ya yi breakfast,
Ganin sha biyun rana yana batun yi yasa takara, kiran nobar wayar shi ko zai shiga,
Cikin sa,a tasamu kira guda ya shiga, sai dai wayar tana ta ruri har ta kusa katse wa ya samu da kyat yadan daga wayan,
Yanayin muryan shi kawai ya wadatar da mutun yasan cewa yana acikin wani yanayi
Gaban Anty Dije ya fadi Dammm,
Jin muryan kanin nata a cikin wani bakon yanayi da bata sani ba,
Cikin rawar murya tace Yusuf baka da lafiya ne ko may ke faruwa haka, ?
Dan ajiyar zuciya ya sauke mai dan karfi a lokaci guda,
Hankalin Anty duk yatashi ga network kuma ba kyau bata jin shi sosai abinda yake cewa,
Cikin daga murya take kwalawa maryam da ke kitchen kira,
Da sauri maryam ta iso falon don dajin kiran tasan cewa kiran na sauri ne,
Hannunta take kokari gogewa a lokacin saboda ruwan dake a hannun nata,,
Anty ce ke kokarin mikewa tsaye tana sabe da Abubakar dake shan nono,
Maryam don Allah shirya ki je gidan Yusuf ki dibo min ko lafiya,
Don kin ga ba dama in aiki wanan Yarinyar don kada yan uwan ta su ganta a agari,
Wani irin abu maryam taji amma ba tada yadda zatayi don ba zata iya yiwa antyn ta musu ba,
Jiki ba karfi ta shiga dakin ta tafara shiri, wasu, dongon rigar material ta sa inda tasa wandon lages ta ciki,
Sai kamshin da ta feshe jikin ta dashi tsab kamar ba a kitchen ta fito ba duk da dama tayi wankan safe ko,
Ita aganin ta ba kwalliya tayi ba amma duk wanda ya gan ta zai zata gurin wani buki zata alokacin,
Kudin mashin anty ta mika mata, har zata fita takara kiran ta tace da ta tafi mai da kayan breakfast din shi can,
Dole haka maryam ta dauki kayan niki, niki zuwa inda zata tari mai mashin,
Kofar gidan kamar a rufe take amma dai don ta tabbatar sai ta dan tura a hankali,
Mama ki tayi lokacin da taje a bude yake, A,she tun da yatafi, massalaci sallah a,suba da yadawo bai kara rufewa ba,
A,hankali take tafiya, ta ratsa wani dan dogon corridor sanu a hankali ta isa kofar shiga folon ciki,
A kwance ta hango a falon cikin gidan a kasa, bisa carpet,
Yana sanye da da wata yar far singlet da wando short, nica,
Kamar ta koma amma kuma yadda taga yanayin kwanciyar shi, yasa ta kasa wuce wa,
Hannun shi guda yana dafe da goshin shi,
A hankali ta isa gurin shi, ta durkusa daidai tsawon shin,
Gaban tane ya fadi ras don ganin yadda ya koma cikin kwana guda,
Ta kasa wani magana a lokacin sai kallon shi takeyi kamar taga wani abu,
Kamshin maryam din yaji a lokacin hakan yasa shi saurin bude idon shi,
Tabbas maryam din ce a gaban shi ba wai shake bane,
Cikin wata irin murya yai magana tankar ba shi ba,
Yace Maryam,
Kece a tafe yanzu ?
A sanyaye tace mai eh nice
Anty ce tace inzo in diba ka ko lafiya ? tun, jiya baka zo cin abincin ka ba,
A cikin zuciyar shi yace Allah sarki Anty na,
Sai,da ya lumshe idon shi sanan ya ce mata, wallahi maryam,
Bana jin dadin jikina ne tun jiyan kirji na kamar zai fashe ,
Wani irin tausayin shi maryam din taji, don yadda taga ya dafe kirjin da zai dan tashi zaune,
Ya,dan daga kan shi ya kalle ta, yace na so inyi karfin halin zuwa gidan amma ba,zan iya ba gaskiya,
Wani iri taji a ranta sai ta dan lumshe idon ta a lokacin taji hannun shi cikin nata,
Wani irin zafi taji radau alamar yana cikin zazabi mai karfi a tare dashi,
Zuwa kirjin shi yakai hannun nata yana cewa maryam kirji zai fashe saboda yadda nake jin shi,
A hankali maryam din ta saurin cire hannun ta a cikin nashi,
Shikuma ya maida kan shi saman carpet din ya kara kwantawa,
Murywn ta yaji tana cewa tun yaushe ne baka da lafiya ya Yusuf ?
Yadan kalle ta a sanyaye idon shi sunyi wani lusu,lusu da kyat yake iya budewa,
Tun jiya nai bayan nadawo gida, nafara jin haka,
Tace to ka kasha magani ne, ?
Kai ya girgiza mata tankar yaro karami,
Mikewa tayi tsaye daga inda take a tsugune tace barun hada ma ruwan wanka tukun, sai kaji dadin yin break din,
Tamike a hankali ta nufi cikin kuryan dakin ta hada mai ruwan wanka,
Har da maclen sai da maryam ta matsa mai a brush tare da aje mai tawul a gefe,
Sanan tafi tace mai bissimila
Da kyat taga ya mike tare da taimakon dafa kujera da bango,
Maryam na ganin ya shige ciki tai sauri cire hijab din ta,
Ta fara gyara mashi falon duk da tsab yake baida wani datti so sai,
Saidai kuryan dakin ne keda dan gyara shima kafin yan mintina yakoma tsab,
Ta kwashe kayan wankin da taga a wa,wa tse takai, bakin kofar bathroom din ta aje,
Yan,kudaden da tagani ta mayar a karkashin filo ta aje,
Traveling baga din shi ta bude tafitar mak da wasu simple kaya marasa nauyi, ta aje agefen gado,
Ta koma falo ta aje mai kayan break din ta yadda zai iya jin saukin ci,
A kofar dakin ta tsaya tana mai ce mai Ya Yusuf ga abin karin nan fa kada yai sanyi,
Yana zaune a bakin gado lokacin daure da wani farin towel iya gwiwar shi,
Ta juya zuwa falon batare da tashiga cikin dakin ba ko daga labulen kofan,
Tun a cikkn dakin Yusuf yaga canji don yaga ko ina fes tankar ba wanda ya,ba ri da kazanta ba kafin ya shiga wanka,
Haka ma falon yake tass kamar bashi ba sai kamshi ke tashi hade dana cooler
Gefe tadan koma nisa dashi kadan tana kallon yadda yazauna ya harde kafa guri guda
Amma yana cusa abinci da kyat kamar mai cin magani,
Kiran wayar Anty ce ta shigo a wayar maryam din
Cikkin daga murya Anty ke cewa maryam ya akayi gaki shiru baki dawo ba balle muji ko lafiya,
Ganin zuwa kawai tace wa Anty n nasu batarr da tai mata wani bayani ba akai,
Ganin maryam na kokarin hada kayan da yaci abinci yasa shi sauke nunfashi har sai da ta juyo,
A hankali ya furta mata nagode kwarai maryam, ina gaid Anty,
Jibrin ne yashigo falon da sallamar shi yana cewa
Man don Allah dai kayi hakkuri wallahi naso zuwa tunda safe
Sai kawai muka tafi unguwa ni da baba diban wani dan uwar shi da bsi da lafiya,
Ashe haka kukayi da wanan mahaukacin Ado wanda bai san Allah, ba,
Shi har ya,na da ikon da zai gayama wanan magana haka,
Ai gara kai sau miliyon a,kanshi, wanda ko addini bai sani da har zai kiraka da wai tubabbe dan furen juji,
Kai kawai Yusuf yakada yana murmushin karfin hali,
Sai kuma ya tuna da maryam wace a lokacin har ta gama sa kayan acikin basket ta mike tsaye ko,
Ganin Yusuf ya kalli maryam yasa jibrin shima saurin kallon inda maryam din take,
Sai alokacin ya tuna cewa tana gurin ai, bi kamata yaita sake layi ba haka,
Koma maye ai ta gama ji ko a lokacin don haka tai masu sai anjima ta wuce zuwa ciki abinta
Zuciyar ta fam da magana takama hanya, sai muryan Jibrin taji a bayan ta yana cewa tazo ya sauke gida,
Kai ta girgiza acikin murmushin karfin hali tana cewa a,a ka koma gurin ya Yusuf don kada a barshi shi kadai,
Ba musu jibrin ya koma amma Yusuf din yanuna mai cewadan Allah yaje ya kaita kawai ai yaji sauki, ko,
Jibrin yana fitowa ya hango har maryam ta hau mashin sunyi nisa da tafiya ko,
Tsab maryam ta labartawa Anty abin da ya samu Yusuf,
Sai,dai ta boye wa antyn zancen da taji shi da jibrin su na yi,
Saboda ganin Ejoma a guri duk da dai dama bawai fada zatayi ba,
Da su Anty zasu koma sam Maryam taki yarda ta kara bin su,
Don haka ita kadai ce a ka bari a gida lokacin don duk yaran su bi su,
Wanka tayi tai sallah la,asar tare da fara gyara masu gida,
Don daga Anty har maryam basu kaunar ka,zanta sam a rayuwar su,
Shiyasa koda yaushe zaka samu gidan tsab a cikin gyara ga kamshin turaren wuta yana tashi,
Abinci tai masu lafiyayye tuwon farar shinkafa da miyar taushe, yaji busashen kifi,
Har tagama ta sawa kowa a cooler su Anty basu dawo ba sai zuwa yamma suka shigo agajiye,
Take cewa maryam ai Jibrin ne yawuce abinshi bai dawo daukar su ba,,
Taji dadin girki da tasmu maryam ta idar don hakane duk inda zata in har maryam na gida bata shakar komai a fanin girki da sauran harkan kula da gida,
Sai zuwa dare Yusuf yasamu yadan lalaba yashigo garin don ya mike kafar shi,,
Direct gidan Anty dije ya fara zuwa duk da yaso yatafi gidan Abdulsamad akan zancen musuluntar da Ejoma,
Wasu yadine farare masu laushi a jikin don har zaka iya gani yar far singlet din da yasa ta ciki,
Duk da yaramay sai dai har yanzu hasken shi yana nan bai dushe ba,
Yanayin shi kawai zaka kalla kasan cewa bai jin kwarin jikin shi still,
Maryam ce aka umurta da tayi serven din shi a lokacin,
Duk da a rayuwan ta bataso ba don har tana shirin kwanciya a lokacin,
A sanyaye take yin komai yana zaune tare da Assalam suna hira,
Cikin murya irin ta, marasa lafiya yace maryam,
Juyawa tayi a hankali tana kallon su, sai yanzu taga irin yadda ya kara zabgewa da kyau,
Yace may yasa dazun nace kada ki hau mashin kika hau,
Maryam i hate inga mace a saman mashin wallahi,
Baki taturo gaba irin nuna ina ruwan ka to da ni da har zaka samin ido,
Batare da ta kalle shi ba ta ce mota gareni da zan daina hawan mashin,
Ai nima nasan mutunci na kuma har kullun ina kokarin kare kai na,
Cikin sake wani malakacin murmushi yace,
Mota kike so maryam ?
Sai da takalle shi da kyau tace,
Ai don ina yar talakwa ba zan debe rai ga rabo ba ko
Waya san gobe banda Allah,
Kan shi yadafe kamar wanda ya ji ciwo yace,
Ho, ho ho ho maryam wa ya fada maki nufina ke nan,
Da talalka da mai arziki ba duk Allah ne yayi su ba ?
Allah yana ba wa wanda yaso ba don wani dalili ba ,
Yana kuma hanawa wanda yaso ba don wani ya kishi ba,
Sai da ta kau da kai gefe tace,
A wurin wasu ke nan, da sauri ya ce subbahanallah,
Ido ya zuba mata yana mai langabar da kan shi kamar maraya,
Ya ce nidai don Allah alfarma nake nema a gurin ki sam bana son,,,,,,,,
Karasowan Anty Dije ya hana shi karasa zancen nashi,
Zama tayi a can saman dayan kujerar lokacin da maryam ke kokarin tarfa mai man shanu a cikin miyan da ta zuba mai,
Wayar shi tai kara maryam tai sauri daga kai ta dube shi, daga inda take,
Cikin harshen IBO yake magana Abdulsamad ne ke tambayar ko zai samu shigowa
Yadan bashi ansa a ta kaice kawai,
Sai kuma yai shiru yana sauraren shi sai daga bisani ya amsa da to cikin hausa,
Kashe wayan yayi a lokacin maryam na kokarin, barin gurin yace mata atashi lafiya,
Maryam na shiga daki ta samu Ejoma tana kokarin gyara masu gurin kwanciya,
Ce mata tayi ta kwanta kawai ita zata hau kushin kamar jiya,
Kwana biyu tsakani ranan jumma,a aka musuluntar da Ejoma,a cikin massalacin jumma, ta garin kwantagora,
Sosai Anty tai ta aikawa mutane da abin sadakar da sukayi don musuluntar nata,
Kafin marance yayi saiga kungiyar Iyamurai sunyo tsinke zuwa gidan Abdulsamad wai zasu kona,
Su kuma matasan gari sukace wallahi suna sa ma gidan wuta sai sun kashe ko wani IBO dake a garin kuma su kona su,
Saida aka kai su gidan masu gari suka ja masu kunne so sai,
Duk basuga laifin Yusuf ba saboda shi yana da kudi, kuma mahaifin shi nada su,
Abdulsamad bawan Allah suka lekewa kawai, kamar zasu cinye shi danye
Amma shi ko a jikin shi don kawai Allah ya tsawa ba wai wani ba,
Maryam ce ta shirya Ejoma wace yanzu ta koma Na,imat,
Dinkin riga da zani da hijab tasa tare da yin kitso irin na hannin na hausawa, musulmai,
Sosai suka koya mata yadda zatai wanka da sauran abubuwa,
Sai faman washe baki take yi tankar wace akaiwa bushara,
Itama maryam din a cikin wasu koren atamfa super wax take, an masu dinki na half gown, da wani shara sharan gyale da bai hana ganin dinkin nata a fili,
Sai set din wasu dan kunnen na fashion masu kyau da daukan ido,
Ganin bazasu samu shigowa yau ba saboda zirga,zirgan da sukeyi yasa anty cewa takai masu abincin su,
Idan akwai abin da maryam tai hating to wanan aiken don ita aganin ta ai su yakamata suzo su dauka tunda suna da abin hawa, ai
Amma ta ya za,a dinga turata kai ma kato wanda baida mata abinci haka,
Kamar tasan tunanen da maryam keyi sai kawai taji tace mata kutafi da Assalam ko,
Tun daga wajen gidan zaka gane cewa bashi kadai bane a gidan,
Saboda abin hawan dake wajen gidan fiye da guda,
Da sallamar ta tashigo gidan dauke da kulolin abinci masu girma,
Idon su kyam a kan ta har sai da ta dan ji kunyan kallon da suke mata,
Kan ta duke a kunyace ganin yadda suke kallon ta, ta wayance
Yusuf ne yace ke ce tafe da ranan nan maryam karaso mana,
Direct gurin da dining table din tanufa don ta aje kulolin,
Ko may kuma ta tuna sai taja burki ta tsaya wanda hakan yasa shi yin ajiyar zuciya,
Daidai gurin gefen kujerun ta aje kulolin kawai sai ta mike,
Maida kallon ta tayi a kan su tace cikin taushin iji Anty wai akawo maku anan,
KB ne