Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   61 / 84

180K to 183K   out of 251.8K words

Mr Ema sai yaga Yusuf yadauko cup ya dan tsiyaya ruwan litop din yana kurba a hankali suna hiran business,
Inda mahaifin nashi ke fada mai cwa yanzu business din shi bai gane komai akai, saboda yaran dake gurin macutane,
Yusuf baiji dadin jin hakaba don haka yai alkawarin zai diba al,amarin company yai gyara akai,
Sai zuwa wani lokaci yai masu sallama ya nufi gidan uwar dakin shi, Anty Dije,
Bai wani dade ba a gidan don rashin ganin kowa yara,suna makaranta, maryam kuma bata gidan,
Don haka sai yaji gidan yai mai girma kamar bakowa a cikin shi,
Abubakar dan Anty Dije ya lake mai ya shuri yaron suka fita, tare,
Gidan man mahaifinshi yanufa inda yaje ya dan fara bincike akai,,,

Maryam wace yuwa yatayar badon taso tashin ba ta mike ba shiri a lokacin kusan karfe biyu saura,
Alwala ne taje ta dauro tazo tayi sallah,sai a lokacin aka shigo mata da wani kula green da plate guda biyu,
Danwake da mai da yaji ne da yankakken salad yasha kayan hadi,
Safita takaraso dakin bayan kaunar ta da tashigo da jug da cups a hannun ta,
Sosai tasamu taci dan waken ba kadan ba saboda tana,son shi dama,
Sai bayan sallah la,asar ta shirya tafiya zuwa gida
Zuwa dan a lokacin ta dan sake jikin ta, ba kamar yadda tazo ba,
Tafe suke da mai mashin din, da ya dauko ta daga, Usubu, uguwar su Safiya,
Suna tafe mai mashi na ta zuba mata surutu maryam wace sai addua, takeyi a bayan mashin Allah ya kai su lafiya don surutun yai yawa,
Yusuf wanda yake tafe daga gidan man mahaifin shi da ya ziyarta,
Kamar a mafarki yaga maryam a saman mashin,
Wani irin mugun mamaki ne yakama Yusuf din
Maryam akan mashin duk da ya ce mata baya so,
Sosai ya take motar ya cin masu, tana saye da wandon Jen's da wata yar riga karama pink sai katon hijabin da tasa, a sama, wanda baka gane irin kayan da ke a jikin ta,
Saboda mashin din da ta hau sai wandon Jen's din yafito don ta tattara hijab din kafatan saye da wasu plat shoes mai belts,
Horn yai masu amma sai mai mashin din yai zaton cewa ana masu ne don su kauce, a hanya,
Karo nabiyu da ya kara yi da karfi yasa su wai gawa har maryam din,
Fuskan shi daure tamau a cikin glass din motar da yake a ciki yana ja,
Kallon da tai mai kawai yasa ta fahinci mai yake nufi,
Cewa mai mashin din tayi ya sauketa inda a hankali Yusuf yazo gab da ida take ya Parker motar shi,
Shiko mai mashin sai kallon ikon Allah yakw yi kawai wanan irin tsaleliyar motar ga kuma mai tukin tankar bature,
Kudi tabude yar pos din ta daniyar ta bawa mai mashin din ,
Amma sai Yusuf yabashi dubu daya nan mutumin yai ta zabga godiya, har zuwa lokacin da ya bude gaban motar tashiga,
Sai a lokacin ta,ga Abubakar wanda ke barci a seat din baya,
A hankali yafara tafiya duk da gaban ta yana mugun faduwa bata yarda yagane hakan ba don ta wani dake afili,
Maryam yace acikin wani irin murya da ba,a,ta iya fassara shi ba,
May yasa bakya ji ne wai for Allah sake may kike ji ga hawa mashin kina hada jiki da mazan wasu,
Innalillahi ta iya furtawa don jin abinda yace
Wani iska ya fesar daga bakin shi saboda haushin da yake ji ko zai samu relief,
Yadan waigo inda take zaune a takure saboda sanyin A, C da ya fara ratsata,
Yakara cewa I hate dis wallahi mace a saman mashin macen kuma wai,,,,,,
Sai kuma yai shiru ya mai da hankalin shi ga titi,
Maryam wace tun tana jin haushi da takaici zuwa yanzu abin mamaki ya koma bata, kawai,
Sai ido ta samai yana ta masifa kamar wani mijin ta can
A,A wanda yake tsaye bakin titi wajen wasu kanikawa ya hango su tafe a haka,
Nan da nan wani irin gululun bakin ciki ya soke shi a zuciya,
May guy din ga dan IBO ke nufi da shi ne wai, akan maryam,
Don, dai ,something is fishing
Jibrin ne yashigo garin yakira noban Yusuf yaji ko yana inane a lokacin,
YUSUF ke cewa a cikin bacin rai gani zan shiga gidan sister, yanzu ok mu hadu a can Jibrin din yabashi ansa,
Yana kashe waya yadan juyo inda maryam take zaune ciki dakewar fuska ya ce cikin sasauta murya,
Maryam ke fa kikai min alkawarin bazaki kara hawa irin wanan mashin din ba, tsakani da Allah,
Maryam saboda rudewa da yanayin da yai magana
Tace Ya Yusuf dama kake son in fita da kafa tun daga gidan mu har Usubu gidan su Safiya,?
Shiru yayi dan a lokacin baida ansar bata da zai mai sanyi a rai don haka kawai sai ya share da ita,
A kofan gidan Anty suka samu su Jibrin din suna jiran shi,
Hannu ta mika da niyar dauko yaron inda akayi dai,dai da shima yamika nashi don daukan, yaron,
Kansu sne ya buge a lokaci guda ga kuma numfashin juna dasuke jin saukar shi tankar a hade suke sauke shi,
Maryam ce tai saurin jaye jikin ta tabar mai yaron don ya hi,
Yaron dake ta sharan barcin shi hankali akwance,
Ta dan tka kadan Yusuf din Yace dakata ki shiga dashi pls,
Cak tatsaya har zuwa lokacin da yakaraso zuwa inda take,
Mikamata yaron ya yi inda suka kara hada numfashinsu fiye da wanda sukayi adazu cikin mota,
Wani irin yarrrr taji wanda tunda take bata ta jin irin wanan yanayin ba,
Ga kamshi mouth fresh din shi tana ji kamar a hancin ta,
Sai kamshin turaen shi na THE da kaure ko ina ta juya agurin kamar yanzu ake fesa wa,
A hankali ya sauke mata yaron a hannunta da ya hade da nashi kamar bai sani ba,
Tajuya a hankali zuwa cikin gida da yaron rungumay a hannun ta kamar wace bata da lakka ajikin ta
Saida yaga shigewan su sanan ya juyo inda Jibrin da sama ila suke a tsaye bakin motar su suna kallo drama n secret lover's,
Gira Jibrin yadan daga mai cikin tsigar shakiyan ci
Daure fuska Yusuf din yayi tankar bai fahinci may suke nufi ba,




ZEEE. MAKAWA YELWA SEENABU
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
7⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

A hankali maryam ta mika hannu don daukan Abubakar wanda ke barci a bayan mota,
Shima Yusuf a lokacin yakai hannun shi da niyar dauko yaron wanda ke ta barcin shi hankali kwance,
Hakan yakawo masu sanadin musayan numfashin su a lokaci guda,
Cikin sauri maryam tai yunkurin jayewa sai dai kuma ba bu filin da zata iya hakan,
Shi Yusuf din ne bayan ya lumshi idin shi cikin jin wani irin yanayi na daban,
Ya dauko yaron yafito dashi daga cikin motar mika mata yaron yai kokarin yi sai kuma hannun shi yadan kara,shigewa a na ta,
Yarrr, taji tai saurin kokarin saita numfashin ta dake barazanan tsayawa, don shock,
Nan ta dan wuce su jibrin dake kokarin fitowa daga cikin nasu motar shi da samaila,
Anty Dije wace ke kitchen a lokacin taji motsin shigowar maryam gidan a lokacin kuma ga Abubakar a hannun ta,
A nutse ta shimfide yaron wanda ke ta faman barcin shi hankali kwance kamar ko wani yaro,
Da mamaki Anty ke kallon ta na ina suka hadu da ita .
Ansa ta ba ta da cewa, a,saman hanya ina saman mashin muka hadu, dasu,
Daga haka ta juya zuwa ciki inda ta kwabe hijabin jikin ta saman kujeran dake kusa da inda take tsaye ta aje shi,
Wandon Jens din dake a jikin ta sai yar karamar rigar da tasa akai dai,dai iya kugun ta, ya tsaya mata ,
Shiyaba wandon ma,anan fito mata da surar jikin ta tsab waje,
Mazaunan ta da suka dan baje a baya suka sa Sharp din fitowa fili da kyau, sai kuma kirjin ta da,surar su ya baiyyana tsab waje,
Sam maryam ta shafa da cewa Yusuf yana a waje saboda hankalin ta na gurin da Anty ke girki,
Dai tsakiyar gidan ta dan bar kofan shiga ciki ita kuma bata karasa kitchen ba Yusuf da Jibrin sukai sallama a cikin gidan,
Sau guda yadan daga kan shi ya kallin wanan hallitan na maryam yai sauri kawar da kan shi yana mai cewa Barakallah masha Allah,
Ta wutsiyar idon shi yadan saci kallan jibrin ko ya ga irin abinda yagani,
Amma sai yaga shi jibrin hankalin shi na gurin Anty Dije wace suke ba,a da ita,
Mamakin wanan irin girma da kyau da maryam tayi a lokaci guda yakeyi,
Duk da ta ramay tadan yi wani faiyau da ita saboda yan maganganun dake ta tashi a kwanakin nan,
Gaskiya wanda duk yakawo sa hijab Allah ya saka mai da,alheri saboda ba karamin abu ya boye wa mata ba,
A hankali ya zauna yana mai lumshe idon shi tankar mai jin kasala,
Duk hiran da Anty da Jibrin keyi yana jinsu idon shi a lumshe suke,
Ya dan kai bayan shi a makarin kujerar da yake zaune akai,
Hannun shi yasa yadan shafo fuskan shi da su round ya furzar da,iskan da ya kumshe a bakin a fili,
Ismail ne ya kira jibrin din yana mai ce mai yazo mana su karasa gida ya shige ya manta da shi a waje kawai,
Jibrin ya ce mai idan ka gajine kawuce mana kawai kada ka takuramin fa,
Kasan ina tare da ogana ne,
Sai a lokacin Yusuf yadan bude idon shi da suke a rufe tankar mai barci a lokacin,
Yace kaje ka samay shi mana kada ya gaji da jiran ka, a waje,
Jibrin ya ce kai ina bai isa ya hanani abinda nake son yi ba, pa,
Katashi mu tafi 212 MOTOR, S ina son ina son in duba mota acan,
Da mamaki Jibrin ya ke kallon shi yace Man duk motocin sa ka bari a Abuja sai a kwantagora zaka sai mota,
Ansa Yusuf ya bashi a takaice da cewa basu da motocin kwaraine a gurin,
Jibrin yace su na dasu mana lates one masu kyau kuwa,
Sai bai kara cewa komai ba yai shiru kamar bashi yai magana yanzun ba,
Ànty Dije ce tace kai amma ai maganar Jibrin gaskiya ne ko Yusuf kamar Abuja zai fi motoci manya ai,
Hannun shi ya dake a saman goshin shi yacire a hankali,
Saiga rinanun idanun shi sun fito waje jajir da su kamar mai ciwon kai,
Yace cikin wani murya mai rauni Anty ki duba fa ki gani for Allah sake ai maryam ce nagani asaman mashi, again,
Jibrin wanda ke kallon shi a cikin mamakin may zai sa ya nuna concern din shi haka akan wanan yarinyar karama,
Anty ce ta tare shi da fadin ai indon hawan mashin ne duk shi muke hawa Yusuf,
Shima baban Assalam naji yana cewa idan ya samu kudi zai yi kokari ya siyo mota ya ahe muna,
Anty barin duba idan nasamu maikyau sai a saya ko anan din ne zai fi idan ma har zan aje maku driver ne kafin ku iya yadinga kai ku duk inda kuke so zaifi,
Yusuf inji anty dije tace kayi hakkuri har zuwa gaba pls don mutane zasui ma zancen mumunar fassara akai,
Kaga zasu ce ai don abin hannunka ne baba yake son baka mar,,,,,,,,,
Sai tai shiru don tunawa da tayi cewa Jibrin yana gurin kuma shine wanda ya hada connection tsakin Yusuf da Sadiya,
Tsab yamike tsaye yana cewa nifa anty ba ruwana da zancen mutane don ban zuwa gidan kowa tun farko sai nan,
Fita yayi daga cikin falin batare da yai masu sallama ba ko yace wa jibrin su tafi,
Anty taga kai takalli fafadan bayan shi har zuwa ficewar shi,
Jibrin ya tambaye ta da hannu cikin alamar may ke faruwa,
Ansa ta bahi da kafada ita ma batasani ba, gaskiya,
Tun wanan lokacin Yusuf ya canza gaba daya bai daina zuwa ba amma baya wani walwala a gidan kamar farko,
Don shi a ganin shi Anty bata sin abin hannun shi ne shi yasa ta doje wa zancen motan da koyaushe yake mata magana,

Maryam yau da wuri ta gama duk wani aiki da zatayi don tana son yin kallon wani series film a wani tasha,
Yaro ne mai zakin murya ya shigo gidan da sallama yana cewa wai ana sallama da maryam inji wani,
Maryam wace ke zaune a kasan falon su saman wani dan filo, taji gaban ta ya fadi dam,
Din tasancewa ba kowa bane A,A ne don shine mai wanan dabiar, kamar tace wa yaron bata nan sai dai ta daure ta ce kace tana tafe,
Maryam tafito cikin shigar wani bakin dogon riga har kasa yana da kwaliya na wani pink colour, sai gyale kayan da ta dan yane fuskan ta dshi,
Yana zaune cikin motarshi kafar shin guda ya daga waje,
Fitowar maryam tun daga nesa yake sakar mata, murmushi,
A zaton shi tunda har tafito wanan dan IBO barazanane kawai yai mashi,
Ya masan cewa koda da gaskiya ne maryam bazatai wani wuyan shawo kai ba zata huce tayi hakkuri,
Tun daga nesa yake kara kare mata kallon cikin so da kauna
Yarinyar na burge shi tana bashi sha,awa uwa uba ga hakkuri,
Irinta ce ya dace ya aje agida matsayin uwar ya, yan shi,
Don zatayi hakkuri da duk wani kwaran nashi, a rayuwa,
Barka da fitowa yace mata kalman da ya fara taron ta da,shi ke nan,
Sai dai yau ansar da yasamu sabanin na kulllum ne, yaji,
Lafiya dai ko malam tace mai cikin daure fuskan ta tankar bata san shi ba,
Cike da mamaki yake kallon ta don jin tambayan da tai mai,
Amma da yake dan duniya ne sai yai murmushi yace cikin kwarewa da zolaya,
Haba sahibata fune duk akan tafiya ba sallama, ko may ye haka nan, ?
Dan dakatawa yayi ya kalleta yayin da take a tsaye hannun a harde da juna saman kirjin ta,
Maryam don Allah dai ki fahince ni sai kuma yadan dakata ,
Can ya dan kalle ta yace wallahia office din mu ne aka turani wani course na sati, a Lagos,
Kuma zan makara idan nace sai nazo nan na fada maki ,
Zai ci gaba da tsarata maryam ta dakatar da shi da hannu cikin wani murya tace mai enough,
Malam is over now bawai wani ya fada min ba ni da kaina na ganka
Shima cikin murya makama da ta fada yace kina nfin karya zan maki ne ko may,
Maryam tace mai cikin dakiya kamayi ai bawai wani ne yafada min ba,
Kabani kunya wallahi duk yardan danayi dakai malam nake jin ka araina fiye da,duk wani da na miji,
Bata karasa taji yace o wo, ke nan wanan dan iskan iyamurin ya hure maki kune,ko,
Kin arda dashe sherin da ya kulla min ke nan akan ki,
Dariya tayi tare da yar shewar bakin ciki tace dakata kaji
Daga yau karka kara zuwa gurina kuma kayanka da ka kawo min ka aiko a karbar ma abinka,
Indai nice mai yin aure to na fasa kaje gaba kasamu daidai da irin ka acan,
Har zata tafi , sai kuma ta juyo tadan tako har inda yake, tace mai, kadaina, daukar alhakin kowa wallahi nida kaina ba na gan ka a gurin ba wani yafada min ba na ganka a kwanar kwangwara face to face da yariya a rungumay,
Ido yafitar yafara borin kunya maryam juyawa tayi abin ta batare da ta tsaya jin abinda yake cewa ba, tashige gida abin ta zuciyar ta na mata kuna da wanan baki rana da ta gani,
Kiris ya rage ta fashe a lokacin son irin yadda take ji a bin a ranta ,
Yakai wani wani lokaci gurin kamar wanda bai da kuzari bayan shegewar ta,
A hankali ta iya furta Innalillahi wa inna ilaihin raji,un ,
Sai ta rintse idon ta gam tana mai jin radadin da take ji yana ragewa a hankali,
Tagumi maryam tayi daga inda take zaune ta rasa, abinda yake mata dadi,
Don dai iyakar cuta A,A ya cuce ta sai dai kawai Allah ya isan mata,
Kai Allah ma ya isan mata din tunda bai kai ga nufin shi ba a gare ta,
Muryam anty dije taji a bayan ta tana cewa tashi ki shiga ki kwanta, dare ya soma,
Jiki a mace ta mike a hankali ta na dan dingisawa don kafarta yai mata nauyi ,
Saman katifa ta

61 / 84