Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
bayan ta yana cewa kedawa ke fada haka maryam ?
Da sauri ta juya bayanta cikin dan tsorata don sam batasan ya shigo gidan ba a lokacin,
Bayan ta ta juya sai ta gan shi tsaye cikin wasu kaya masu shigen na indiyan musulmai,
Maganar su Anty Dije ne yafado mata arai cikin dan kankanin lokaci
Sai cewa tayi cikin dan wani murya kamar mai shagwaba,
Wallahi yaya safiya ce muguwa Anty ta aiketa sayen drink shine nace mata, tasayo min irin wanda nake so
Amma wai sai ce min tayi wai ita ai ta riga tabar shagon sayarwa ko kuma bazata koma ba,
A hankalo ya isa gurin dayan kujerar dake facin din wanda take zaune akai,
Cikin mamakin yadda yau ta sake jiki tana mai magana cikin mutunci da nuna kulawa,
A dan matse fuska yace ina Assalam da Issi suzo mutafi in kai ku ku sayo,
Wani iri maryam taji a cikin ranta na yadda zasu fita a tare gudun kada wani ya gan su ya zaci wani abu,
Amma sai gargadin Anty Dije da Safiya ya fado mata a rai,
Murmushi tayi a fili tace uncle kada na wahal da kai da abarshi kawai zai fi,
Kallo mai kamar harara yai mata yace ku sa may ni a mota pls
Kanta kawai ta gyada alamar to,
English wear ke ta cikin jikin ta don haka sai ta dauko wani katon hijab din ta , ta feshe shi tsab da kamshi ta zumbuda saman kayan nata,
Da ita da yaran suka fita bayan ta shedawa anty inda zasu da uncle din,
A can dan nisa kadan da kofar gidan ya parker motar shi,
Wata bakar Jeep ce mai kama da wani siffan abin ruwa,
Da karasowan su ya bude motar ta yadda zasu shiga ciki dukkan su,
Assalam wanda yasaba idan zasu fita ya shige gaba tare da shi
Yanzun ma kokarin shiga gaban motar yaron kayi
Amma sai Yusuf din yake ce mai, ya koma baya tare da Issi su zauna yabarwa little Mum gaba,
Suna barin gurin anty dije wace ke tsaye bayan labule tana leken su tai wani yar ajiyar zuciya,
Kira,an shek Ahmad suleman kano ke tashi a cikjn motar a cikin surar Al,imran ,
Maryam din wace itama bin karatun takeyi a hankali,
Inda Yusuf din ke ta sharara gudu a saman titin,
Cikin yan mintina kadan sai gasu a bakin wani store wanda akai wa rubutu da manyan haruffa 212 plaza,
Shagon yakai shago a wurin girma don haka suna tsayawa a wanan store din,
Maryam ta daga kai tun shigowar su motar,ta kalle shi,
Yagane may take nufi don haka yadan juya inda su Assalam suke ya ce,
Mufita mu zagaya kowa ya dauki abinda yake so kunji,
Cikkn zumudi suka firfito zuwa cikkn shagon inda yake rike da hannayen yaran,
Itama maryam din dole tabi bayan su badon ranta yaso ba,
Sosai suke ta sayayyan su shi da yaran inda yake biye wa duk wani shirmay nasu yana taya su jidan kayan da suke so, agurin,
A, baya baya maryam ke bin su wace har zuwa yanzu ko tsinke bata dauka ba,
Ganim bata da niyar zuwa yin abinda ya kawo su yasa shi ce mata,
Kinfasa sayen drinks din ne ko ?
Kai ta gyada mai alamar ,a,a don haka atare gaba dayan su suka tafi gurin,fani abin shaye shaye da yan tonde, tonde,
Sai kuma ya wuce zuwa gurin su man gyaran gashi da kayan kamshi dana wanka,
Juyowa yayi inda take yace sun ishe, ki ko a kara wasu,
Da sauri maryam ta kada kai alamar sun isheta,
Gurin biyan kudaden kayan da suka lodo ya nufa inda yabiya su makudan kudi a ka kai masu har cikin motar su,
Wanan karon a hankali yake tafiya ba kamar lokacin da zasu zo ba,
Sai can daga bisani ya dan karkato kanshi inda take yace,
Maryam ina saurayin ki naga tun da nazo ban gan shi yazo ba,
Kamar maganar bai soke ta ba tace, kai yaya Yusuf, har da yar kaunar taka kakesawa ido,
Surukin kane fa , yaya yusuf takare zancen a cikin zolaya,
Tsaki ya ja yana mai yar hararan ta yace, Allah dai ya kiyaye ni surikina mai mutunci ne,
Duk da ansar ya bata mata rai amma sai ta cije tace mai cikin dan sasauta murya,
Kai ya Yusuf duk wanan biyayya da girmamawan da yake maka, zakace mai hakan ?
Tsuki yaja cikin dan sasauta murya, yace, to be Frank maryam wanan guy din wallahi bai dace dake ba sam,
Gaban tane ya fafi dammm saboda jin abin da yace,
Muryan yaran dake bayane suna kokarin bude wani kwalin biscuit sai fada ga kaure a tsakanin su,
Sosai yanzu ya lula a saman titin cikin yan mintina ya iso kofar gidan nasu
Tun daga nesa kafin su karasa kofan gidan maryam ta hango motar A,A a tsaye amma yana acikk zaune,
Gab da motar shi uncle ya tsaya da tashi motar a gefe guda,
Cikin kidimaywa da nuna tsoro maryam ta bakina rawa take cewa malam tun yaushe kazo, shine baka kirani ba,
Hararanta yayi cikin daure fuska yace daga motar wa kike maryam,
A lokacin Yusuf dake kokarin kwasan kayan da suka,sayo yana jin su,
Dukar da kan ta tayi kasa tai shiru, sai daya kara dan dago fuskan shi acikin bacin rai yace,
Maryam ban fa fahince ki ba tambayar ki nakeyi fa,
Cikin gagawa yake azaman bude kofar motar shi,
Ya nunata da yatsan shi yace kada ki raina min wayo ki mai da i ban san abinda nakeyi ba fa pls
Nan da nan idon shi ya canza yai wani jajajir tsatsan bacin rai duk ya baiyana a fuskan shi,
Sosai rayuwan ta yai mata daci akan irin yadda yake mata agaban mutane,
Idanu a runtse tana jin wani irin zafi da bacin rai tace,
Dakata malam kadaina fada min irin wanan kalaman,kamar wata yar cikin ka,,,
Cike da mamaki A,A ya ware ido yake kallon ta don ta bashi mamaki irin yadda tarufe ido tana bashi ansa,
Juyawa tayi kawai zuwa cikin gida batare da takara koda second a gurin ba,,,,,
SEENABU MAKAWA,,
HπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
6β£5β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
IYAKA, NA,ABBUDU WA,IYAKKA NAS,TA INN,,,
Har kulun addu,a na,gare ku da fatan alheri ga duk masoya novel din furen juji, Allah yasa a gama da duniya lafiya Allah,sa mu, dace da rahaman Ubangijin mu,,,,
ππππππππ
Shigowar Maryam ya yi dai dai da fitan Yusuf da ga cikin gidan,
Dan gefe ta samu ta dan bashi hanya, tankar baisan cewa da ita a gurin ba ya sa kai zuwa waje abinshi batare da ya ko kalle ta ba,
Duk da rayuwan Maryam bai mata dadi ba soboda irn yadda ya nuna mata,
A kofar, gida Yusuf ya hango motar Yusuf din yana kokarin barin unguwar,
Sau,guda yadan kalli gefen da ya hango motar A ,A din yai wani saurin kauda kan shi, batare tankar A,A yasan da shi a gurin,
Sai bayan yaga shigewar shi daga kwanar
Yai wani irin dogon tsuki kamar wanda ya ga wani abin ki, ko tsana,
A hankali Maryam, takarasa shiga cikin gidan nasu inda ta,samu Anty Dije wace, ke zaune da yaranta duk sun zagaye ta,suna son a bude ledar da sweet din su ke a ciki don su sha,
Jiki kamar mai jin kasala ta zube a saman wani kujera da gefen wanda yar ta ke zaune a kai
Anty Dije ta dogo kai a hankali ta kalle ta nan take ta fahinci kaunar nata na a cikin yanayi,
Gaban ta ya ba da sautin faduwar gaba tana tunanen indai ba wani abin bane ya hada maryam din da Yusuf din ta,
Amma to ai shi Yusuf lafiya ya bar su yan inda ma yake sheda masu tana waje tukun,
Sai kawai tai saurin kawar da wanan zarkin da zuciyar ta ke kokarin fada mata,
Ledojin da yaran ke ta kokarin son ta bude tace wa Assalam ya kwasa ya kai wa maryam,
Muryan Sadiya,ce ta suka ji a bayan su tana cewa
"Eh" an dawo bari muga abinda aka siyo ma, manyan mata,
Sai a lokacin maryam ta maka mata wata hararn "mind you, a cikin wasa,
Sadiya din ce takaraso gurin itace ta karbi ledan tafara budewa,
Kayan da ta gani fam a ciki da kuma Price's din su ya sa tai saurin dago kai ta kalli inda maryam take zaune,
Maryam wacce hankalin ta,bai gurin a lokacin tana kokarin diban wayar da taji sako ya shigo,
Muryan sadiya ce, dake kokarin cewa maryam ki ce barna kikayo wa Bros yau,
Sai a lokacin idon maryam ya kai a kayan da Sadiya ta zazzage a saman ties kasa,
Ba karamin kaduwa tayi ba don ganin irin yawan kayan da Sadiya ta ware cewa, duk nata ne,
Baki ta bude da niyar za tai magana sai kuma maganar ta makale mata yakasa fitowa,
Guda guda ta dinga bin kayan da kallon har idon ta ya sauka asaman wani dan kit, mai adon ruwan silver,
Rashin sani ko may ye a cikin wanan kwalin yasa ta tambaya Sadiya da cewa may ye a cikin kwalin,
A hankali sadiya ta bude kwalin wasu set din turare ne kusan kala hudu a ciki, amma duk na desame product,
Sai su man shafi masu kyauda da,tsada, kafin su karasa kallo yara suka dinga shigowa da caton din drinks din da ya sayo masu, a can,a
Ba Maryam ba har anty da safiya sai da sukai mamaki irin yawan drinks din da a ka shigo da shi,
Maryam mamakin ta shine cewa yaushe a har ya sai masu shi bata sani ba,
Dai lakacin da suka shiga shagon ya umurci wani da ya loda mashi su a mota, kafin su fito,
Safiya ce ta dan juya gefen da maryam take tana cewa, o ya sai ki zo ki ta sha tunda don ki a ka siyo ,
Batare da maryam tai magana ba tamike kawai niyar wuce wa dakin
Muryan Anty Dije ce ke cewa maryam din wa zaki bar wa wanan kayan a,nan,
Cak ta tsaya guri guda don jin maganar da yar na ta , ta yi,
Idon ta, takai kasa gurin da kayan suke zube, Safiya ce tagani tana ko,karin maida kayan a cikin ledan su,
Dukawa tayi ta dauki leda, daya daga cikin ledojin tai gaba kawai a,binta, ta bar sauran inda suke,
Bayan ta anty dije tabi da kallo tana mai tausayawa rayuwan yar kaunar nata,
Saman kujeran su ta zobe kayan gefen Naimat kadan,
Safiya ta biyo bayan ta dauke da sauran kayan a hannun ta,
Dai dai, gefen maryam ta zauna inda ta dauki hannun ta ta dora a saman ciyan maryam wace, ke kokarin cire, dan kunnen ta,
Sunan maryam din takira a hankali, tare da kara dafa ta don su fuskan ci junar su,
Maryam ina son ki bani aron hankalin ki nan ,a cikin murya mai nu fushi maryam din tace ina jinki ai,
Murmushi safiya din ta dan yi wanda bai kai ciki ba mai alamar yake,
Maryam may ke tsakanin ki da uncle Yusuf, ne ?
Batare da ta kalli inda safiya take zaune ba,tace a takaice, may ki ka gani halan, ?
Hmmm kawai safiya ta ce ma maryam din don jin ansan da ta bata, a takaice din,
Maryam look duk da nasan cewa ,ba wai zaki fada, min ai,nihin gaskiyar zancen gaskiya ba,
Akan abin da ke a tsakanin ki da uncle din ba amma aini kuma bawai yarinya ba ce da ba zan iya gane ko may kuke a ciki ba,
Kin dai sani, ?
Ta karashe zance tana mai yiwa maryam din wani irin mugun kallo ,
Barin fada maki gaskiya idan zakiyiwa kan ki fada wallah maryam kiwa kan ki don naga wankin hula na shirin kai ki dare,
Safiya may kike shirin fada min ne wai akan uncle ne ?
May ke a tsakanin na dashi ban da mutuci kawai,
Amma zaki zo ki wani dinga min tambaya kamar wani ya aiko ki yi min shi,
Sanin halin maryam da safiya tayi kawai sai tai dariya maimakon ta mai da zance wasa,
Ba kamar yadda ita,maryam din ta dauki maganar tankar da zafi ba,
Hakan da maryam din tayi bai hana Safiya ci gaba da mata zancen Yusuf din ba,
Maryam kiwa kanki fada wallahi don dai uncle zai so ki ya kuma rike amana, ba kamar yadda A, A da ki,kewa rawan kafa yake gwadamaki ba,,
A hasale maryam ta juyo tace kamar may ki ke nufi A,A yake gwada min safiya,?
Maryam inji safiya wace ta kira maryam din cikin nuna kulawa,
Ki yarda da zance na pls akan cewa da nai maki cewa akwai wani abu a tsakanin ki da uncle yusuf wallahi,
Wani irin mugun takaicin safiya ne ya rufewa maryam din ido wanda har yakai ta iya wa safiya din maganar komai a lokacin,
A hasale ta juyo da karfi tace Safiya tun,da har kin matsa da,cewa akwai,
To kwai din samay don naga cewa magana kawai ki ke son yi,
Maimakon safiya din ta biye mata sai ta mike cikin wasa take wa maryam din idan yai tsami ai maji,
Don Ruwa Baya Tsami banza inji, Maman Farida,,,,,
Sosai suke ta harkokin shirin bukin auren Naimat wanda yanzu saura yan kwanaki kadan ayi shi,
Γnty Dije wace tai matukar kokarin wajen ganin cewa taiwa amarya duk wani abin da ya dace ai mata, alokacin aure,
Kaya masu kyau nagani na fada yaiwa Naimat din na daki,
Sai a,wanan lokacin ne su Anty suka san cewa akwai yan tsirarrun Christiatorchi da dama agari wa yanda suka musulunta,
Kamar hadin baki sunyo gaiyyan junar su zuwa gurin karar wanan bukin
Maryam wace ke ta kokarin kawo masu ruwan sha tare da abin sha a lokacin tana jin irin yadda suke tawa Naimat murna da arzikin shigowa, cikkn muzulunci,
Anan take jin wata far addatijowa tana Naimat magana a cikin gwari gwarin hausan su,
Cewa kada kiyar da ki irin musuluntar Nao,mi, wace kusan sau uku tana musulunta tana kuma komawa Christian,
Saboda kawai wai ta kashe auren da tayi da musulmi,
Wanan maganar da maryam taji a lokacin yai matukar bata mamaki
Bata san lokacin da tasa bakin ta azancen ba tana mai tambayar su ko lafiya, ta dinga wanan irin Riddah hakan ?
Daya daga cikin matan wata mai hausan da ba daidai ba ta juya gurin da maryam take rike da kwalin drinks a hannun ta tace, acikin magana a hankali da kuma bacin rai da kaico a fuskan ta,
Kin san wasu basu da karfin imani a tare da,su, don haka auren da taiwa musulmi da zaran ya mutu sai ta koma matsayin ta na Christian,
Idan kuma wani musulmin yazo again ya aure ta sai ta kara canzawa zuwa cikin islama,
A haka har tai wanan kusan kashi uku yanzu haka tana a cikin Christian ne,
Maryam kara tambayar matar tayi da cewa kuma an kasa samu musulumi wanda zai rike ta,
A matsayin amna tun da tana da ra,ayin yin addinin muduluncin,
Sai matar tai wani irin daga hannun ta zuwa harba ta rike a cikin nuna wa?
Tace wasu maryam wacce tsayuwar ta da zancen da sukeyi ya jawo ra,ayin mutane da dama gurin su,
Matar tace ai kin san halin mutanen musulmai yanzu ba wai taimako da sukewa irin wanda ya musulunta haka,
San,nan kuma ita wanan matar, kishiyoyin ne ke hana ta zama a gidan mijin,
Bawai itace bata son zaman auren ba, saidai kuma mai maimakon idan tafito tasamu gidan wasu musulmai ta zauma a a sai dai kawai ta koma gidan su ta zauna
A haka yau da gobe sai kawai muji cewa ai ta koma Christian again,
Sai da maryam tai wani irin ajiyar zuciya mai nauyi sai ta ce Allah ya kyauta,
Duk gurin suka amsa da fadar Ameen Ameen, gaba daya a lokaci guda,
Daga haka maryam ta wuce zuwa gurin da suke aiki sai dai zuciyar ta cushe da bakin cikin halin da wanan matar take ciki,
Tun zuwa lokacin da takoma haka kawai sai ta tsinci kanta a cikin damuwa da maganar,
To sai dai kuma ta ina zata fara wa zance daga karshe ma zuciyar ta ya bata shawara akan
Ita wace,ce da may ma zata iya tallafa mata tai tsuki tana mai cewa ina ma a ce musulman mu masu zuciya ne kamar yan mabiya