Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
mika mai hannu, don su gaisai,
Bayan sun gaisa ne yake tambayar mutumin ya maganar take ne,
Da kamar bazai bashi ansa ba saidai yadda yaga Joseph din is serious sai ke ce mai
Yar rainin wayo ce sun saida filin su dadewa shine yanzu tazo wai ita zata gyara wa yan marayun ta,
Wazata nuna wa marayu nida tunda nataso banda kowa balle,
Wani irin kallo Joseph yai wa mutumin don jin maganar rashin imanin da yayi,
Hannun shi nazube cikin aljihun,farar wandon shi dayasa ya juya dakyau yana facing din mutumin,
Ya yanzu may kake so kai tunda kaji mutane sun sheda cewa filinta ne ita da yaranta,
Mutumi yace kadaina cewa filin ta fa malam kace filina,
Daidai loacin matar cikin kunar rai tace karya kakeyi muna fukin Allah,
Joseph ya waiga gurinta cikin hausar shi ya ce kai haba kibi a hankali mana mama,
Ya juyo gurin mutmin yace to nawa ne kai ka sayi filin malam,?
Mutumin yadan yi dumm can kuma sai yace wai dubu ashirin da biyar,
Wani mutum dake gefe yace kai malam Bawa, dubu goma sha biyar fa aka sayar ma,
Joseph yadaga masu hannu yace Ok yanzu fadi muji nawa zaka sayar mata ita da yaran ta,
Nan da nan gurin yai tsit ana sauraren su,
Malam Bawa yadan yi tunane can yace in an saye hamsin na sayar in ba asaya ba shikenan ni inada abin yi,
Matar takara sa kururuwa tana cewa Allah ya isar mata ita da yaranta akan mutumin da kuma kanin mijinta,
Nan da nan gurin ya shiga hayaniya kowa na fadin albarkacin bakin shi,
Joseph yakalli mutumin yace mai in bazaka damu ba zan baka dubu talatin yanzu gobe ka turo in karasa maka sauran don ban fito da kudi ba,
Ai ba laifi inji malam Bawa nan da nan mutane suka kama cewa wai kada akara mai ko kwabo abarshi hakana macuci, kawai,
Gurin matar Joseph ya karasa yace mata mama nawa kudin hanyan ku tace mai dubu daya da dari biyar ne wata uku,
Dubu biyar yabata yace taje tabiya haya saura,tasayi abinci suci
Zuwa gobe zai nemay ta, zai san yadda za,ayi,
Yazo zai wuce yaji wani mutun yanawa wasu mutane bayanin cewa Saida Dan kahirin can ya taimaka mata yaba malam bawa kudin shi,
Duk da rashi ya baci murmushi kawai yayi ya tqre mai achaba da hannu ya hau yana cewa kaini Green Land,,,
Ya samu majalissar su KB ta cika anata hira saman wani tabar ma wasu kuma zaune a saman wani benci,
Gefe guda ya samu a saman tabar man yadan kwanta rigingine fuskan shi na kallin titi yana kallon masu wucewa,
In akwai abinda maryam taki jini a rayuwar ta shine idan zasu wuce ta iske wanan majalissar ta cika,
Duk da bata kallon gefen su amma tana tsarguwa don ji takeyi kamar duk ita suke kallo,
Tunda ta tun karo gurin taga sun cika duk sai taji ba dadi aranta don haka sai ta dan kara sauri tana rike da hannun Issalam,
Shiko Assalam na bayan su yana shuka tsiya wai bazai tafi ba don haka suka dan yi gaba suka bat shi,
Saida yakawo dai tsakiyar inda majalissar matasan yake ya yanke jiki yafadi wurin kalle kallen shi,
Aiko ya yanka wani irin ihu kamar wanda aka zare wa rai,
Duk wanda ke gurin saida ya waigo inda yake kwance cikin kasa yana faman kurma ihu,
Wasu daga cikin yan majalisar suna ce mai tashi ma na wani kuma na ce mai dan nema wurin shegen kallo har ka fadi,
Dole Maryam tadawo baya ranta duk a bace,
Joseph dake kwance yana kallon tun gilmawan su maryam har zuwa faduwan yaron wanda yai tuntube ya fafi kasa,
Yataso daga inda yake kwance,yazo inda yaron yake yanata tsala ihu,
Daidai lokacin Maryam ta iso gurin,
Tadaga hannu zata kai wa Assalam duka a baya hakan yai daidai da tarewan da ,Joseph yayi sai ta samu hannun shi,
Wani irin kamshin turaren,THE ne ya daki hancin ta ba shiri ta mike tsaye daga tsugun nin da tayi,
Shikuma Joseph ya dago da yaron daga inda yake kwance cikin kasa, yana dan kakabe mai rigar shi da ta baci da kasa,
Maryam dake tsaye tana ce mai bazakazo muje ba ko sai mun makara,
Joseph yadago faren idon shi yadan kalleta ya ce ki tafi zan kawo shi,
Shiru tayi tana nazarin mutumin kafin tayi kwafa ta wuce tana mai jan hannu Assalam tana gunaguni,
Hannun yaron ya rike suka shiga cikin green land super market, tare can ya fito da yaron dauke da yar leda shake da kayan kwalama,
Inda ya rike mai hannu zuwa inda yqga yara madu irin uniform din su na shiga,
Har bakin get din islamiyar ya aje yaron inda yadan rage tsawo daidai ta yaron yana ce mai to abikina shiga kayi karatu abinka kada kaba kowa chuculate din da da biscuit, kaji,
Yaron yadan kara goge busashen hawayen dake makale a idon shi da bayan hannun shi yace har da anty ko da,Issalam?
kada mai kai Joseph ya yi waban karon alamar ya gaji da rigimar yaron,
Yace mai duk kan su karka ba kowa, daga haka yada ya wuce shiko Assalam nata dago mai hannu,
Yana komawa gurin yaji Inus nacewa wai ina Joe ya tafine, ko dai har yanzu yana gurin rigimamayn yaron nan ne,?
Ganin da sukayi mai dawo wa yasa sukayi shiru,
Isowar shi yayi daidai da zuwan wasu mutane su uku a saman mashi,
Yan tsofine mutun biyu sai wani matashi da yajawo su,
Kowa dake gurin saida yai mamakin mai yakawo tsofin gurin su,
Mai mashin din ne yai ma yan dattawan nuni da Joseph yana cewa gashi nan ai,
Daidai lokacin da mutanen sukayi wa wa yanda suka tarar sallama, cikin daga hannu,
Sai dan shiru ya biyo bayan hakan na wani lokaci,
Shima Joseph mamakin nuna shin da akayi yake yi a lokacin,
Cikin mutanen mutum gufa ya fara bayani kamar haka,
Malam yat uwqr muce tasa may mu da kuka dazun take sheda muna abinda yafaru,
Ai duk wanda ke gurin saida gaban shi ya fadi da jin maganar mutumin
Don su azaton su wani abu ne yafaru, da wata da Joseph din,
Mutumin ya cigaba da cewa shi ne muke tambayar kokai waye sai wanan saurayin yace muna shi yakawo ka nan,
Mu zo ne muyi maka godiya a bissa arin taimakon da kawai hajjo,
Mungode kwarai Joseph yace kai haba baba aida baku taso ba wallahi da kubari kawai ba komai,
Ai taimako yi wa kai ne, ba wani abu ba,
Koda yake zuwan naku nan yai mun da dadi sosai
Ammmm KB zo don Allah KB dake zaune a kusa da inda ya tashi ya zo kusa da yan dattawan,
Joseph yace don Alkah zaka samo masu gina sai a nuna maka filin aja ma matan da yaranta daki hudu da katanga,
Ai sai yan dattawan na kokarin hada baki gurin cewa Allahu Kbar,
Yaro halan kai dan gidan waye agarin nan don ban mu san ka ba
Wani habibu ne yai saurin cewa dan gidan Ema mai manjane tsohuear kasuwa,
Da mamaki suke kallon shi gudan mutumin yace ikon Allah,
Dan gidan Ema kuma tau Allah ya kyauta ,,
Mungode kaji Allah ya haskkaka zuciya, dukbda bai gane nufin su ba yadai ce Ameen,,,
Mutanen da zasu wuce ya basu dubu biyu yace su biya mai achaba,
Sai bayan sun wuce ne yadan yi ma abokan nashi dan bayani breifly,
Daga haka bai kara cewa komai ba,duk maganar da kowa keyi yana ji amma bai tanka ba,
Shi baima so kowa yaji wanan zancen daya yafaru ba in badon
Wa yan nan dattawan da suka zo wai yi mai godiya ba,
Tun shigowar su gida, yafara kiran mummy zo kiga kayan da aka sayo min ance inci ni kadai bada kowa ba,
Maryam da ta shigo rike da hannun Issalam ta wani zunburo baki gaba tana cewa wallahi anty in har Assalam na muna haka ni bazan kara zuwa dashi makaranta ba,
Dariya maganar maryam yaba a yayan nata, tace idan baki je dashi ba, ai sai ya zauna dama kece mai daurewa karya ai,
Nan Maryam taba yar ta labarin abin da Assalam yai masu hannu takuma mika mata ledar kayan kwalamar da aka sai mai,
Uwar ta karbe ledan tana cewa aiko bazai sha ko kwara guda daga ciki ba, tunda abin da yayi ke nan,
Anty Dije takarbe ledan ta shiga dashi dakin ta,
Wani sabon kuka yasa yana kokarin turje turje a kasa,
Maryam ce tabi bayan anty da sauri tana fadin dan Allah kiyi hakkuri yaya,
Abashi gobe ba zai kara ba, ai,
Da mamaki anty dije ke kallon Maryam ce ta langabe kai kamar zatai kuka don ankarbe ma Assalam kayan shi,
Sai kace ba ita bace ta kawo karan shi yanzu har tana ikirarin bazata kara fita dashi ba,
Murmushi tayi tana cewa kai Maryam abarki kawai daidai lokacin da maryam din ta karbi ledan a hannu anty,
Ido anty Dije ta bita dashi tana murmushi acikin zuciyar ta tana yaba irin son da yar kaunar nata takeyi wa yaranta,,,,,,,,,,
Afuwan ba yawa pls,,,,,,,
ZEEEE MAKAW
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣
BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🐎HUGUMA GROUP🐎
Maryam Abdullahi bobi, diyace ga malam Abdullahi bobi,
Asalin , Mahaifin su daga wani kauyen kwantagora suke wanda ake cewa kamfanin bobi,
Su malam Abdullahi yan asalin can ne saida zama yakawo kakanin su a cikin garin kwantagora da a cikin jahar Niger State of Nigeria,
Sana,ar maihafin su shi ne saida kayan masarufi a cikin kasuwa,
Yana da mata biyu inna hussai da maman, tunga,
Saidai da dadewa can ya, auri wata yar uwar shi daga bobi, saidai gaskiya babu so a tsakanin su ,
Don tana da wanda take so a can bobi, don haka ta tada hankalinta bata zauna,, auren bai dauki wani lokaci ba ya mutu,
Ashe akwai rabo a tsakani don haka aka samu cikin maryam,
Bayan haihuwar maryam ne tai wani aure anan cikin kauyen Kampanin Bobi,
Tunda aka haifi maryam sau guda aka taba zuwa da ita gidan mahaifinta,
Duk yarinyar na ran malam Abdullahi amma yasan cewa kawo ta cikin iyalin shi wani sabon fitina ne,
Saboda sun riga sun tsani uwar Maryam har abin ya shafi yarinyar don zuwan da akayi da ita ko kallonta ba wanda yayi,
Sai Dije ce kawai taita nan, nan da maryam din tana nuna kulawar ta akai,
Amma a lokacin Dije tana secondary bata kare karatu ba balle tayi aure,
Bayan kare karatun tane ta hadu da wani dan makwabcin su Iliyasu ma,aikacin aikin custom ne,
Sukayi aure tun lokacin da dije ta tsaida miji tasha alwashin cewa za ta dauko maryam su tafi tare,
Amma sai uwar ta Inna, hussai tace mata sam bata yarda diyar ta ta dauko mata, wata wahala ba can daga kauye,,
Don haka Dije tabar wanan zance kamar ta fita batun sai bayan auren su da ILiyasu ne
Baba yaje dakan shi bobi ya dauko maryam da yan kayan ta yazo ya danka wa Dije ita amana,
Tun wanan lokacin Anty Dije ke kula da yar kaunar ta , ta cikin amana,
Har zuwa lokacin da Allah yabata nata haihuwa,
Assalam.shine nafarko sai Issalam, wace yanzu daga gareta ba,a kara samun wani ba, tukun har yanzu,
Mijin Anty yana zaune a can jibiya ne bakin border don da lagos yake har ya taba zuwa da su sai da anty ta kusa haihuwan Assalam suka dawo,
Inda mahaifiyar shi tace bata yarda ya koma da ita ba , don in yatafi da iyalinshi wai yana dadewa baizo gida ko kuma aike,
Tun wanan lokacin anty ta zauna kwantagora bata kara bin mijin ta abisa umurnin uwar mijin ta,
Saidai har yanzu abin bai canza ba don gwamma da da yanzu don yanzu baifi ya zo sau uku ba a cikin shekara,
Saidai yakan aiko masu da sako akai akai,
Maryan yanzu tana karatu ne a Girls day secondary school kwantagora,
Tana Ss² yanzu su kuma yaran antyn ta sun fara nursery a wani preravent school,,
Maryam ita ba fara bace kuma ba baka ba yar doguwa da ita bata da jiki tana da hanci madaidaici da ido masu dan girma,,,,,
Yau kusan satin shi biyar da barin gari yana can suna ta harkan man fetur,,
Saidai a kai akai suna yawan waya da abokan shi,
Musan man KB da jibrin wanda dama sun fi shakuwa da su tun suna yara,
Don duk irin wulakancin da ake mai lokacin suna yara na kasan cewar shi dan kirstan acikin su
KB da jibri a gaskiya ba suyi mai sukan ja shi zuwa gidan su ,
Idan kuma mahaifin shi yasani a lokacin yai mai dan karen duka,
Har akwai wani lokaci da ana bukin babban sallah yabar gidan su tun da safe zuwa gidan su KB , da kayan shi dunkule a leda a cewar shi zai bi su gurin yawon sallah ne,
A gidan su anyi bidan shi har angaji kasan cewa idan musulimi suna irin wanan buki su kiristan sukan killance diyan su a gida basu bari su fita ko ina,
Hakan yasa shi yin asubancin barin gida zuwa gidan su KB din,
Dashi akayi ai,kin komai na naman inda aka diban mashi zuwa gida dabara yayi da zai tafi yaba KB saura yace ya boye mai
Baban su KB shi yaraka shi da yaga yana labe ,labe
Suna zuwa tun daga nesa uban shi yafara yi mai sababi saida mahaifin KB ya bashi hakkuri,
Wucewan mahaifin su KB kadan akasamay shi akai ta bugu kusan duk wanda ya girmay shi a gidan ranan sai da ya doke shi,
Yana kallo naman da yaje kwadai yai wahalar aiki aka zuba a cikin ruwan kwata aka murje,
Duk da haka washe gari saida ya koma, wurin KB da zai tafi kasuwa yadan dade gidan sanan ya wuce, kasuwa,,
Iya gaskiya shi Joseph yana jin dadin zaman da su keyi da su KB da sauran friends,
Idan yana cikin su ana hira yakan ji kamar an yaye mai wani nauyi duk da ba magana yake yawan yi ba acikin su,
Yadda suke hira ana challenges din juna ko kuma kuma yayi ta kallon yadda mutane ke ta faman zirga zirga,
Abin yana burge shi so sai don idan a cikin yan uwan shi IBO yake sam babu wanan irin dabi,ar sai dai kawai kulun a na gurin bidan kudi,,,,
Shidai dabiar hausawa tana mai a rayuwan shi don in ba haka ba da irin dukan da yasha yana da ya daina kula su,,,,
Don haka tun dawo war shi, kasar su yake tunane da nazarin irin sana,ar da ya kamata ya jona su KB aikai wanda zai jawo masi cigaban rayuwar su
Batare da,sun dogara da wani ba ko kuma da aiki gwaunati, kamar yadda akasarin hausawa ke yi yanzu,
Yau da ruwa aka tashi a garin na lagos don haka duk wanda yakai wani lokaci a waje go slow ta rutsa da shi,
Joseph wanda shigowar shi ke nan garin a lokacin, da ake tsula ruwan,
Tafe yake a hankali a cikin motar shi yana tafiya kamar wanda bai son yin,,,,
Idon shine yakai ga wani motar daukar kaya watau tirela,
Wace tayo dakon buhu,hunan shikafar yar gwaunati sai,dai,duk ruwan sama yasa duk ta fara jikewa ga masu motar nata wahala, da shi
Wani irin tunane yadar su cikin zuciyar shi wanda tasa shi dan yin murmushi a lokacin,
Gidan shi dake cikin, Apapa ya wuce direct inda yasamu maigadin gidan yabude mai get ya shige ,
Mai aiki naganin shi yatashi da murnan shi yafara kokarin hada mai dan abinda zai ci, tunda yasan cewa ogan nashi baya cin abincin waje,,
Yana ganin oga yasan cewa yau boza tazo don yasan cewa duk sanda ogan na shi ke gari duk kan su dake a karka shin sun yake wahalar kudi,
Wanka Joseph kafin ya fito har an hada mai girki mai lafiya,
Bayan ya gama ne yasamu daya daga cikin kujerun falon ya haye,,,
Don har zuwa wanan lokacin ruwa ake tsulawa, agarin
Don haka yana kwantawa sai shawar da zu dayayi tafado mai a rai, daga karshe ya jawo wayan shi yadan dinga dan,na wa yana