Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
maryam ga key a,dauko wa an nan kayan dake cikin motar,
Wani irin haushin taji don tasan zai bata mata lokaci ke nan,
Da sauri ta kalle shi tace saidai kila ba yara a wajen ko, ?
Daga shi har anty ido suka zuba mata dn jin maganar ta ,
Wanda ya nuna tana uzuri ne hakan yasa tace masu ba yara,
Anty Dije tace maryam sai kace ba wace iyakarta cikin kwantagora ba,
Wallahi Anty bana son in makara ne saboda sun riga sun sa cewa bazan zo ba ma sam,
Nikuma ina son basu mamakine su ga na riga kowa isa gurin,
Takara sa fada cikin shagwaba kamar yar karmar yariya mai shirin yin kuka,
Da ga ida yaje zaune ido kawai ya zuba mata alokacin ,
Don yadda take maganar kamar wata yar goye,
Anty ce tace inbanda abinki maryam tun da ga sauki Allah yakawo maki kawai da kin kwaso sai kibi Yusuf ya sauke ki tun da hanyar su zaki bi,
Kai kasa cike da jin nauyi likamata bin shi da antu tayi tace,
Ai basai na bishi tun da bai tashi ba kawai zanbi motar kasuwa,
Muje in sauke ki idan nadawo zan samu yara su sauke kayan,
Wani irin nauyi maryam taji a lokacin sosai, don jin ansar shi,
Ba musu dole ta jawo gyalen ta ta yafa tare da murza mai turare tako ina
Tsaye yake a bakin motar shi yana waya fuskan shi na kallon ta cikin gidan nasu,
A nutse ta ke takowa zuwa ida motar shi take, waya yaje yi amma kallon tsab yake kara mata ,
Tsayawa tayi daga dan nesa dashi kadan ta yadda bazata ji may yaje cewa ba,
Yagane nufinta don haka ya tsaida wayar yana ce mata bissimillah mana mutafi ko,
Mamakin irin saurin kwashe dabi,un shi na hausawa,musulumai da yayi da sauri takeyi,
Bayan motar ta tukara inda yace mata haba dai ai bayan ba guri duk kayane a ciki,
Dawo gaba kawai ki shiga ina ga zai fi,
A hankali ta saje hannun ta nufi dayan bangaren ta bude,
Kamar kullun sanyi da kamshi dai yana nan a motar nashi,
Ya na kokarin tada motar ne yake ce mata ina,ne gurin da zaki din,?
Tace mai MARAFA parks,
A takai ce tai maganar don haka bai kara tambayar ta ba,
A marairaice kamar mai shirin kuka tace, don Allah ina son zan dan tsaya Blue, sea, super market,
Batare da ya kalli inda take ba yace mata ok kawai, .,,,,,,,,,, ,
ZEEE MAKAWA,,,,,,
.πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
5β£0β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
UBANGIJI ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA BAKI DAYAN MU YAN UWA MUSULMAI,,,,
πππππππ
Dan zagayawa take yi, cikin super market din, tana dan dibawa ko zata samu, abinda zata saye a matsayin gift , duk da bawai wasu kudine masu yawa acikin jakar na taba,
Layin sai,da kayan kamshi take dan zagayawa don dibawa,
Duke take tana kokarin ciro wasu set na shafa, irin ta mata, acikin wata, yar kit,
"Yan mata ya kike kwana biyu, ?
Muryan take tunane a ina tasan shi ne wai, don ko bata waiga ba tabbas tasan wanan muryan,
Bashir Alhasan ne tsaye da wasu kayan da mafi yawan matasan maza hausawa ke sawa a yanzu,
Tunane takeyi a ina tasan wanan fuskan ne wai, kafin second ta tuno, dashi.
Bata san lokacin da ta sake wani dan munrmushin da iyakar shi fuska,
Ina yuni tace cikin yanayin muryan nan nata,,
Yar kwaikwayon ta yayi hakan yakara sata sake wani lalausar murmushi again,
Tsayuwar shi yagyara yace ai nasan dama kida baki fada min inda kike ba wata rana zamu kara haduwa ne,
Yakara zancen, yana mai dan rausayar da kai, kamar wani kara min yaro,
So ya kwana biyu ya karatu Maryam Abdullahi ko,
Yana mai mata wani kallo irin na wayyaun maza,
Kafin ta bashi amsa yakara jefo mata wani tambaya,
May a kazo saye ne haka, ?
Bata bashi ansar ko guda ba sai dai yar murmushin da takeyi a kasa kasa,
Set din kayan, da ta dauka ya mika hannu ya karba yana dan karanta sunan shi,
Yace da alama dai gimbiyar gift take dibawa ko,
Hannu taga ya mika can ciki ya dauko wani babban set mai kaya kala kala cikin kit din,
Yace ina ganin ai wanan zai yi ko,
Maryam wace sai binshi da ido take don kara tan,tance halin shi,
Sai ya dan daga kai saman yana karanta wasu set haka, dake gurin,
Yadawo da kanshi yana mai kallon ta fuska a sake yace bazamu layin Sweet bane ko?
Kai ta girgiza mai alamar a ,a bazata ba, don haka yadan daga kafadar shi alamar ba ruwan shi,
Zan wuce ta furta, a hankali, kamar mai maganar rada,
Ok muje ko yace mata tana kokarin ce mashi ai ya barshi,
Sai ganin Yusuf tayi tsaye da alamar tun tsayin su gurin yake kallon su,
Tsaye yake a bakin wani da kantar kaya yajin gina da wani bango dake gurin kafar shi a harde, acikin wani,
Biye Bashir yake da ita, duk tawani kunya da ganin su da yayi, atare,
Suna tafe sai yaba kyawon kwaliyar ta yake yi yana kokarin cusa ta gwaunatin gare ta,
Sun kusa kaiwa inda Yusuf yake tsaye cikin dakewa sai wayar shi yaje latsa,
Maryam ta dan kalli Bashir,ta juya inda Yusuf yake tsaye tace,
Ga yayana ku gaisa dashi,
Wani kallo yai wa Yusuf na second, inda yagane cewa ba karamin mutun bane, don komai na jikin Yusuf zaikai kusan million, guda,
Yana yar dariya yace au kice min bake kadai bace dama,
Hannu ya mikawa Yusuf suka gaisa, sai dai Yusuf din,ya, na yin hausa sai Bashir din ya dan waigo maryam,
Tagane may yake nufi a cikin style ta kada mai kai alamar eh,
Amma tunda nayi ni,yar biyan kudin, wa yan nan kayan ina fatan cewa yayan mu zai bari in biya ?
Fuska aba walwala, Yusuf yace wa maryam indan kun gama sai ki samay ni a mota, ina jiran ki,
Daga haka ya juya zuwa waje inda suka aje motar su,
A tare suka fito dafa cikin plaza din da bashir wanda motar shi take aje a gefe guda,
Gurin motar Yusuf Maryam ta nufa ganin haka Bashir yadan fidda idon shi yana mamaki hafin maryam da wanan guy din,
Yusuf na kallon su daga cikin motar shi dake makale da tin tak glass,
Sun kysa kaiwa gurin motar maryam taja tai tsaye tace mashi, to na gode kwarai Allah saka da alheri,
Yadan sa key holder din shi ya sosa kan shi,
Sai kuma mukara haduwa ko maryam makarasa zancen mu ko ?
Da,sauri maryam ta dan kaleshi, tace yaushe kuma zamu kara haduwa ai ko yau sa,a ce,
Sai,da yai yar dariyar maganar ta, san,nan yace, aini dama ko yaushe a cikin sa,a nake,
Kai kasa cike da jin nauyi maryam tace to shi ke nan nagode badamuwa ki, sallamar min da yayan mu,
A nutse kamar kulun ta isa gurin motar inda tadan kwan kwasa mai glass, ,
Tana shiga motar yataya suka harba saman titin, sai dai a hankali yake tukin shi
Duk da kasan cewar motar babbace amma hakan bai,sa,shi yin gudu ba,
Sun dayi tafiya kadan, batare da, yawaigo inda take ba yace,
Wani, kuma sabon mayaudarine kika,samu, haka ?
A cikin mamaki take kallon shi ido a zazzare
Kallo, mai kama da harara ta yayi yace, gaskiya maryam ko wanan bai dace da ke ba, sam wallahi,
Kanta aduke tai shiru saboda wani irin bakin ciki da ya tokare mata mokoshi,
Ya dago ya kalle ta idon shi ya canza zuwa bacin rai,
Haka itama maryam domin maganganun sun daga mata hankali,
Idanu a runtse tana jin wani irin bacin rai, da kunar zuciya,
Haba ya Yusuf, ai wanan maganar bai,dace ka fada min ba,
Cike da mamaki, ya ware ido yana kallin ta don sam bai dauka maganar zai sa bacin rai haka ba,
What maryam bakya son a fada maki gaskiya ne, ?
, a,fusace kamar wace zatai shirin kuka, tace mai, haba dai daga ganin mutum kawai zaka yanke man hukunci akan shi,
Yakamata ace katambayeni bayani akan shi bawai kawai a yanke mun hukunci ba
Ya Yusuf ya,kamata ace kana cikin wa yan da zasu shedeni,
Kamar yadda kake tuhumar ina hurda da yan duniyar samari,
Ma,ana nima din yar duniyar ce ke nan ko,?
Murmushi ya yi kawai har zuwa lokacin da ta kare fadar maganar ta,,
Hakalin shi ya mayar a,titi, sanan yace,
Don nasan cewa,ke yarinyace karama , duk sun fiki wayo da sanin duniya,
Sam baki dace dasu ba gaba dayan su ,bai,kamata ace kina tsayawa dairin su ba,,
Daga haka ya mai da kan shi a kan titi sosai, bai kara,bita kanta ba,.
Saida suka kawo unguwar ya tambayi maryam tai mai kwatance a takaice ,
Kofa ta bude tana kun,ku ni, tana cewa wanda ke tare da irin su Aisha da sadiya ba ace mai ya bari ba sai wace ba ruwan ta za,a sawa ido,
Lock din motar ya dan na tayi tayi ta bude ta kasa sai a lokacin ta waigo in,da shi,ke zaune,
Kamar ba shi take jira ya bude mata kofa ba, sai kawai,ya kama lalabar wayar shi,
Cikin murya mai nuna karaya zuciya da kuma kuka, tace mai,
Ina son zan fita ne
Bai juyo ya kalle ta ba, tankar da dutse take,
Sai da yagama taba wayar shi san nan ya dan,na unlock, motar ta bude,
Ran ta a bace ta sa kai kawai tafita batare da ce mai komai baya,
Bayan ta ya bida kallo a hankali, sai kuma yai saurin kau da kan shi yana mai cewa Astangafurllah,
Ganin irin tai makon da yai mata bai kamata don ya fada mata gaskiya ba haka tai fushi tafita ko godiya babu,
Ta dan waigo kamar mai rada tace mai nagode
Kai kawai ya kada mata batare da cewa komai ba ya ja motar shi yabar gurin,
Duk da taron bukin yai kyau ya kawatar, ga kuma abokan su na tun makarantar secondary sun hadu,
Rayuwar maryam a bace yake saboda duk kusan ba yan yan mintina sai ta tuna da zancen Yusuf,
Har yanzu kanta ya daure ta rasa gane may maganar shi take nufi ne haka,
Da zaice mata wai ta kara samun wani mayaudari,
Yana nufin cewa A,A din ta mayaudari ne ko may ya ke nufi da hakan,
A haka tai tawa yan uwa yake don kada su gane halin da take ciki,
Zaune su ke su uku afolon gidan Yusuf din suna shawaran abin yi,
Su ke ta shawaran su shi iyakar shi sauraran su yake yi,
Shi iyakar shi, yace masu ummh ko eh ok haka yayi,
Saida,duk suka gama tsarawa san Jibrin ya dauki wayar shi ya kira Sadiya yana sheda mata zancen zuwan su gidan su yau,
Yusuf wanda ke duke Sai a lokaci yai magana ya ce,
Jibrin baka ganin cewa ya dace mu tun tubi iyayen ta tukun muji ra,ayin su kamar yadda shari,a ta tanadar
Amma sai Jibrin yace mai wanan ba matsala bace don yasan cewa za, yarda in da ta fanin shi ne,
Yau itace ranan farko da Yusuf fara,zuwa gurin sa,adiya hira,
A hankali yake nazarin yarinyar sai,dai gaskiya ya du, ba ba wani makusa ga yarinyar,
Kamar yadda ya za ta zai samu matsaloli a gurin ta, gaskiya a yadda yake gani ta,
Da safe yazo gidan Anty don ya karya duk yai rana yau da zuwa,
Anty Dije tafito cikin shirin ta kasancewar wanan karon ya Illiya yana gari, shima
Nan suke hira da Anty Dije zancen yana bata labarin zuwan shi a daren jiya,
Dariya sosai anty dije ke kwasa don yadda irin yadda ya yai ta mausu sheri ma,
Wayar anty ce yai kara a lokacin shine ya katse masu hiran da suke yi,
Hiran da maryam ke sauraro da ga in,da take kwance saman salaya ta,
Innalillah taji anty na na tawa a lokaci guda, da sauri maryam tafito waje da sauri,
Tana jin anty tana cewa injin baiji ciwo ba, dai ko, dausauki sosai, ??
Maryam wace tafito sanye da wani dogon rigaba English , taitsaye tqna mai son jin ko may yafaru
Sai alokacin Yusuf ya,ganta don lokacin da sukayi wanan maganar bai kara sata a ido ba,
Shima Yusuf ido yakurawa Anty don jin ko may ye matsalar,
Inda yake anty ta kalla tare da kara kallon Maryam,
Sanan tace wai baba ne sukayi accident da mashin a hanyar shi tazuwa kasuwa,
Maryam tace subbahanallah injin da sauki dai Anty?
Tace wai suna asibiti za,a diba su, kusan tare suke tambayar ko wani asibiti ne,
Bai kara wani lokaci ba sai mikewar da yayi yana cewa bari je in gani zai fi.
Yasamu jikin da sauki ssai da gurjewa yayi a hannuwa da kafa, , aka dan mai treatment aka sallamo shi,
A, gidan baba duk hakalin su yadaga sosai sabo suna gudun kariya,
Da taimakon su Yusuf ya shigo cikin gida ya na dan dan gyasawa, a hankali,
Anan suka samu su Anty da maryam gidan sai faman sannu akewa dan tsohon,
A hankali yake zayyana masu irin yadda al,amarin yafaru
Kowa na ta mai fatan alheri da Allah ya tsare gaba,
Daya daga cikin yaran nashi wata maison kama da Anty Dije tace
Baba nidai daka hakkura da zancen zuwa kasuwan nan wallahi,
Ba yadago kai a hasale yace idan nabar zuwa uwar wa zamu ci agidan,
Sim sim ta noke don gudun kar baba ya aza mata fada
Rana har bayan azahar suna gidan mahaifin su basu dawo ba,
Kasuwa ya shiga inda yasiyo wa baba kayan kara jini,
Alaiho, da Anta mai yawa sai kwai, tare da fruit da madara,
Zaune baba yake ya na sallamay sallah da yasamu yayi,
Idon shi yakai ga kayan da yara ke shigowa dashi a cikin leda,
Idon shi kem a,kai don ganin irin kudin da aka narkar
Mai sakon ne ke fadawa baba cewa daga gurin Yusuf ne sakon yafito,
Duk wanda ke gurin sai da yai dariyar wanan dan tsohon, da abinda yace,
Wanan duk wa zaici sune shin waya yar shi Da bata karkare kai su maryam shekaru ba tace baba ai muda kaine,
Da,kuwa yai mata yace mata karbi naki yar nema kawai
Inda anty take zaune tana bawa danta nono baba ya waiga yace wanan barnan dukiyace duk azube alokaci guda acin ye, ?
Dariya duk wanda ke cikin gidan yasa don jin magannar da yayi,
Tunda safe sai yan zu ya shigo gidan inda ya samu maryam tana girki a hakali
Yai mamaki kwarai da yadda ta gaishe shi, saboda tun, wanan lokacin da yai warning dinta, akan samarinta,
Maryam tace ma Yusuf sannu da kokarin Allah saka da alheri,
Albarkan iyaye nake nema don yafi min amfani,
Don haka sai ki daina min godiya addu,a kawai zaki min nima mahaifina yazama tankar na kowa, anan gaba,
Wani irn mugun tausayin shi maryam taji alokacin, kamar tayi kwalla,
ZEEE MAKAWA
.πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
5β£1β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Ubangiji Allah ya taimaki musulmi duk inda yake, Allah ya karawa Annabi daraja,πππππ
Zaune yake a falon gidan shi yana kokarin balle bottom din rigar ta wuya,
A hankali yadauki kafar shi guda zuwa sama wani dan stol, din katako dake falon,
Bayan shi yamar a makatin kujerar a hankali yana mai sauke numfashi kamar wanda yagaji
Idon shi yadan lumshe a hankali, yana mai tunanen inda yafito,
Shidai yasan cewa yanzu musulmi yake mai sallah farilla biyar a kowace rana
Amma kuma ga yadda yaga al,adar bahaushe ko musulmi zai ce bai mai ba,
Saboda wanda bai tuba ba kafiri arne zasu ce mai suna mai nuna kyamar shi
Sai kuma gashi wani bakon al,amari da yake fuskan ta yanzu nuni da cewa, da ake mai wai tubabbe,
Murmushin bakin ciki yayi ido arufe wani irin mugun bacin rai yaji,
May ya rasa ? may ye bai yi daga fannin addini ?
May za,a iya gwada mashi a yanzu ?
Amma sai ga shi a cikn taro ba ko boyo ko kawaici, ake cewa ashe shine tubabben nan,
May kuma illar wanda ya tuba kawai, ya shiga cikin ku,
Shin may amfanin nunawa mutane hanyar tuba, da ake yi,
Sai kayi kuma