Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
ba zata ce wani abu ba sai wasa da wayan hannun ta da takeyi,
Maryam yakara kiran sunan ta cikin wani yanayi da yasa ta rikicewa amma sai tadaure tana mai dago kai ta dan dube shi ,
Yanayin da tagani ga fuskanshi ba wasa aciki a lokacin don haka tai saurin dukar da kanta kasa tana sauraron shi,
Ki daure ki fada min ra,ayinki a ganay dani amna dan girman Allah ina rokon ki da ki fada min gaskiyar abin dake zuciyar ki,
Kada ki duba abinda ke tsakanin mu da baba ko Anty Dije,
Saboda nayi alkawari bazan taba auren macen da bata so na ko wace bana ra,ayina ba,
Ni mutum ne da bani da ra,ayin yin aure ,aure a rayuwa na,
Don haka sai wace nasan cewa tana sona ina son ta zan aura bawai don ra,ayin wani ba can daban,
Pls kada kuma kiji kunyar gaya min gaskiya don nasan ba dadi ka kalli mutun face to face kace mai baka ra,ayin shi,
Amma ni agare ni gara hakan da ka yaudari mutun kafada mai karyan don kawai yaji dadi,
Don haka maryam ina sauraren ki ki fada min ra,ayinki agamay dani pls ?
Maryam wace kanta ke aduke lokacin a cikin zuciyar ta hakika maganganun uncle gaskiyane,
Amma kuma taya zata fada mashi cewa yanzu ta amince dashi kai tsaye ya yarda da ita,
Bayan yana sane da irin yadda akai ta kwasa da ita akan shi,
Dakuma irin yadda son A,A ya ke azuciyar ta har bata iya boye,
Tambayar ta ya karayi sai taga ai kawai tafada maigaskiya zai fi,
Abin mamaki kuma sai taji bakinta yai nauyi ta furta mai ko wani irin kalma,
Saidai kuma i zuwa yanzu karyane tace bataji wani abu akan Yusuf din ba ,
Saidai tana kokarin karyata haka din da takeji a kan shi tun bayan dogon sharhin da safiya ta zaunar da ita tai mata,
Gashi kuma ya tsure ta da idon ta rasa yadda zatai magana har ta fada mai gaskiya,,
Ganin baida niyar kauda idon shi gare ta dole ta daure ta ce ma wani abu saboda tasan yin shirun nata baida mafita,
Kasa,kasa yaji muryan ta tana cewa kasan ai aure nufin Allah ne idan har Allah yakardara ni matar kace kamar yadda mahaifina ke bukata to,,,, sai kuma tai shiru batare da kara cewa komai ba,
Murmushi Yusuf din yayi yadan gyara zaman shi yace Uhum maryam kifitar da duk wani kunya da shakku kiya magana don har yanzu banji kinyi maganar da nake son ji ba
Tabbas maryam nasan aure nufin Allah ne, amma ni abin da nake son in ji shine Yusuf ina sonka ko kuma a, a yusuf bana sonka,
Da sauri tadago kanta dake duke takalle shi shima din ita yake kallo sai yadan daga mata gira yace yes,haka din ne mana gaskiya,
Hmmm kawai tace saine kuma tace, amma dai ai nayi maka bayani ko ?
Tuna dai abin da kikace a baya kawai kince Aure nufin Allah kuma mahaifinki ke bukantan kiyi,
Don haka kenan bake ke bukatan aurena ba har yanzu maganar mahaifinki ne kawai kike bi,
Cikin sauri tadago kanta don jin abindayace tare da saurin cewa Injiwa ?
Amsan da taba shiya dan sa shi dariya dan haka sai ya mike tsaye daga inda yake zaune,
Gurin da take nufa kamar daga sama taji hannunshi acikin nata saikuma taga yakai tsugune agaban ta yace,
Will you marry me ?
ZEE MAKAWA YELWA,,
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
7β£5β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI
Barka da jumma,a yan uwa musulmai masoya novel din furen juji,
Allah ubangiji ya karawa Annabi Mohammad, S,A,W daraja,πππ
Jin hannun shi cikin nata, ya runtse, cikin nashi abinda bai taba faruwa da ita ba, ke nan,
Aiko nan take jikin ta yafara rawa, don wani irin mugun tsoro ne ya shige ta alokacin,
Shiko Yusuf yana ganin haka ya fahinci halin da take ciki hakan ya sanya shi kara rike hannun nata sosai,
A hankali tadago idon ta da suka sauya zuwa na mai kuka, ta na mai wani irin kuka,
Shima kallon nata yakeyi cikin cikin wani irin yanayi,
Ido cikin ido kowa ke kallon dan uwa, wani irin kallo da kowa da abinda zuciyar shi ke fadi,
Kallonta yake yi ita ma dai kallin nashi take tin cikin tuhuma da kaguwa ya sake ta, ba tare da sun daina ba,
A hankali ya dago hannun zuwa bakin shi ya dan subban ta,
Cikin wani irin sauri maryam tai kokarin jaye hannnun nata da yasha riko,
Sai kallon kofa takeyi da alamar kada wani yazo ya riske su a hakan, ta ke wa gudu,
Safiya ce tai murya tankar mai waya tana cewa hello,
Ai ko nan take wani irin kunya ya lulube maryam irin kunyar da bata taba jin shi ba don gani take safiya ta ga halin da suke ciki,
Cikin sauri da wani karfi ta fisge hannun ta yi masa wani irin kallo na don may, tai wani kasa da kan ta alokaci guda
Ko shi Yusuf din sakin hannun ta yayi batare da bata lokaci ba don a zaton shi fitowa safiya zatayi a lokacin,
Ya koma a kujerar da ya taso da farko ya dan kai bayan shi a kai ya kwanta,
Ya na mai da numfashi da sauri da sauri kamar wanda yai wasan tsere,
Jikin shi yaji yai mai wani irin sanyi gaba daya, don irin yanayin da ya riski kan shi alokacin da ya rikewa maryam hannu,
A lokacin safiya ta kara so falon tawa maryam din wani irin kallo cikin wasa tace lalai ma maryam,
May uncle ke fada maki haka da har kika mantacewa ina cikin daki tun dazu,
Gashi har nagaji da jira ki na kai ga fitowa don ba gadin daki nazo maki ba,
Kallon Yusuf din tayi wanda idon shi suke a lumshe tankar ba shi ba ne wanda ya dagulawa kawar ta lissafi har take ba tun kuka,
Kallon shi tayi kamar ta yi mai magana sai kuma ta fasa kusa da maryam ta dan zauna,,
Don ta kawar da shirun da sukayi a falon kowa da abinda zuciyar shi ke sakawa,
Safiya, ce ke kokarin jan maryam da dan fira dan ta sake jiki,
Maryam ta kasa cewa safiya din uffan sai da kai kawai take iya ansa mata,
Γnty ce ta shigo dauke da wani ruba tab da wake mai ruwan milk a ciki,
Maryam wace sai yanzu tai magana tun bayan halin da ta shiga, don haka har sadiya tagaji da fira da ita,
Yusuf wanda ke zaune a gefe batare da yace wa kowan su komai ba ,
Sai tunanen zuci kawai yake yi, a cikin ranshi duk ya dabur ce,
Tsam yamike yana mai yiwa Anty sai anjima jiki ba kwari,
A lokacin da ya isa gidan shi zama yayi saman wani kujera, sai tunane kawai yake,
Zuciyar shi tace mai Addu,a ce kawai ta kamance ka salim,
Ka roki Allah shine kawai zai kawo ma ka mafita ,
Abinda zuciyar shi ta dinga raya mashi ke nan a lokacin,
A take kuma ya amince da hakan, don haka da sauri ya mike zuwa bathroom din shi inda ya dauro alwala,
Itako maryam bayan fitan shi suka hada ido da safiya sai kawai safiyan ta kwashe da dariya
Wani dan filon kushin dake a gefen maryam ta dauka ta jefawa safiya din inda ta cabe shi a hannun ta,
Tana ci gaba da yi,wa maryam, din dariya har da kyalkyatawa,
Anty dije tagane may suke nufi amma sai kawai tashare su tankar ba ta fahince su ba,
Don ta kauda zancen sai cewa tayi dan wake take son yi da wanan waken da aka bata gashi kuma milk colour ne zaifi kyau ga dahuwa,
Sai a lokacin safiya tadan rage sautin dariyar ta tace wa anty aiko zai yi kyau so sai da dan wake ,
Har zuwa yamma Safiya na gidan sai a lokacin Jibrin yazo ya dauke ta ya mai da ita gidan su,
A gogon dake false n gidan ya nuna goma saura na dare yanzu,
Hakan ya ba wa Anty dije tabbacin cewa Yusuf ba zai shigo cin abincin dare ba ke nan yau,
Don haka ta umurci maryam da cewa ta rufe masu gida don dare ya yi ko,
Wanka tayi ta shirya cikin kayan barcin ta wando da riga masu ruwan light green,
Ta daure kanta da ribon kamar kullun takawo gyale dan karami ta daure kan nata dashi,
Zaune take bakin gadon su tana adduan shiga barci kamar yadda ta saba,
Wayan tane yai kara a lokacin alamar kira ya shigo mata,
Ta dan jima tana kallon wayan tana tunanen may zaice mata kuma yanzu,
Har wayan na batun katsewa takai hannun ta tadauka tare da yin sallama cikin wata murya,
Muryan wace ta sa Yusuf, kara rikicewa da jinta har ya rasa irin ansar sallamar da zai mata,
Tunane ya farayi bayan ya karba wayan yana mai cewa,
Shin wai dama haka wanan yarinyar take tun farko ko dai yanzu ne ta koma haka,
Jin muryan ta tana gaishe shi yasa shi saurin tuna cewa a saman layi yake fa,
Ansa gaisuwar na ta ya yi cikin wani muryan da zaka zaci ba ta shi bace,
Shiru, ne yabiyo bayan gaisuwar amna sai Yusuf din yai kokarin kauda shirun nashi,
Maryam ina abinci na ya tambaye ta cikin wani murya tankar ba tashi bace,
Uncle abincin ka yana kitchen mana ko kazo ne mu bude gida,
Sai da yai murmushin jin yadda ta rude a lokaci guda,
Ya ce No na hutar da ke ni ina gidana ai, yau bana jin cin abinci sam,
Kawai sai maryam ta tsinci kanta da tambayar shi ko saboda may ?
Ya ce saboda ke maryam
Yau kin sani a cikin wani yanayi kin ruda min zuciya ta kwata, kwata bani da sukuni yau,
Maryam yadda tayi tankar Yusuf yana ganin ta a fili don nuna kan ta tayi tana tambayar ita,?
Sai da yadan lumshe ido shi tankar maryam tana ganin shi, a fili itama,
Yace Yes of course ke, maryam don kin sa duk na wani susuce akan ki,
Idon ta tadan runtse saboda bakon ya,na yin da take ji a yau,
Uncle din ya koma mata tankar wani bako wanda bata taba gani ba arayuwan ta,
Daga haka yaci gaba da dan mata kalamai masu dadi a hiran nasu,
Maryam wace sam ta kasa sakin jiki da shi sai ansawa da Eh
Ko Um,umm takeyi sune kawai ansar nata da take iya bayar ba,
Harzuwa dan wani lokaci sannan yai mata sallama,
Sannu sannu ya dinga dan jan ta da hira tana dan sake jik wani lokaci tana hira dashi sama sama a kunyace,
Wanan dan kwanakin da sukayi dan sabo maryam ta kara haddace ko waye Yusuf din,
Tsab ta karanta halayan shi saboda shi mutum ne wanda keda wata irin baudadiyar ra,ayi,
Idan har ba sanin halinshi kayi ba da wuya ka iya fahintar shi,
Gashi miskili irin na karshe din nan gashi da saurin fushi,
Abu dan kan kani zai bata mai rai amma kuma sai dai yana da saurin saukowa daga fushin
Ga yin alheri a gurin shi tankar zuban habo daga hanci,
Alherin shi irin ta bajintace, sai gurin da mabukaci na gaskiya yake yake yin ta,
Abubuwa da dama maryam ta fahinta daga gare shi alokaci guda,
Ko dan da farko bata damu da yanayin shi bane saboda kyamar da ta dora mai na gaira ba dalili,
Tafiyan shi yazo kusa don haka ji yake yi tankar kada ya koma a wanan lokacin,
Amma kuma yazama mashi dole yakoma din saboda harkokin shi da ke cen,
Dama abinda ya kara tsayar da shi akan binciken da yakeyi a shagon mahaifin shi ne,
Badon rai yaso ba yai sallama da su ya koma Abuja cikin jin wani iri,
Sai bayan tafiyan shi ne Sadiya tasamu labarin cewa ai ya koma,
Duk tasan cewa wanan zuwan da yayi kawai dai hakkuri tai ta yi don ba wani kulawa da ta samu daga gurin Yusuf din sosai,
Jin shi shiru da tayine ya sa tabugowa wa Jibrin tana tambayar shi ko Yusuf din yana garin KG har yanzu,
Amma sai kawai taji cewa wai ai Yusuf din ya koma, ko
Sadiya wace wayar ya kusa sullubewa daga hannun ta saboda kaduwa,
Hankalinta yai mumunar tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye,
Jibrin takara kira tana tambar shi ko may ya fahinta akan ta gurin Yusuf
Bai boye mata komai ba ya fayyace mata a kan zancen,
Wani irin mumunar faduwan gaba taji bayan taji cewa wai yasamu wata
Sai yanzu tagane takuma fahici ko may yasa Yusuf duk zancen shi akan anty je ne,
Idan ita kuma anty dijen ashe makircin da take kullawa ke nan,
Don su mallakeshi su hada,shi da maryam din yarinya karama da ita,
Gumi taji yana fito mata don jin wani irin zafin dake fitowa daga cikin ta,
Ji takwyi tankar an watsa mata ruwane a lokacin
Dije kinyi kuskure a rayuwar ki in har kina tunanen zaki iya rabani da Yusuf a lokaci guda,
Dije sai na raba ku da yusuf sai na dasa tsana da gaba a tsakanin ku,
Takai,wa hannunta guda naushi tana cewa daga yau zan fara yaki da duk wani wanda keda hannu acikin wanan maganar,
ZEEE. MAKAWA YELWA
[4/15, 22:27] Anty Lantana: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
7β£6β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
YAURI
*_Masoyan Yusuf da Maryam ku kwantar da hankalinku kar hawan ruwanku yatashi, abunda nikeso ku gane shine sadiyafa real lover ce_*π
*_Koda yake naga ya'n yusmar team sun fi yawa amma kusani sadyus fa suma sun yunkuro sunce sune masoyan Yusuf na asali domin kuwa su ba hadin iyaye bane_*π
~*SADYUS team#*~
&
~*YUSMAR team#*~
π€
_Alherin Allah ya kasance atare da duk wani masoyin Annabin rahama_ πππ
πall
Sannu a hankali yake saukowa a matakalan jirgi, Saye yake cikin shiga irin ta,su ta mutanen kasar waje,
Sai yar far glass da ya zauna mai a ido dagwas, kamar an auna shi,
Daga inda ya ke ya hango shi yana saukowa a hankali,
Murmushi yayi don ganin abokin nashi wanda yai mai tafiyan bazatan ,
Duk da sun dade basu ga junan su ba kowan su yaga dan uwa ya canza a lokaci guda,
Hugging din juna su kayi,cikin farinciki da jin dadin ganin junan su,
Surprise Sonny ya cewa Yusuf bayan yadan bubuga ma Yusuf din baya,
Hannu rike da juna suka wuce gurin da ake ajiye motoci,
Direct gidan Yusuf suka wuce inda suka samu taro daga kakan Yusuf din wace ke ta farin ciki da gani Sonny din,
Sosai soni ya sake jiki ya kwashi girkin gargajiyan da aikai masu tsab ya zauna ya baje ya kwashi abin shi,
Shima Yusuf yaji dadin wanan irin sake jikin da Sonny din ya yi,
Wani tsadaden hotel aka kama ma Sonny din tare da yan rakiyan shi su uku,
Sai bayan ya hutane ne Yusuf ya samay shi cikin shirin shi,
Yana saye cikin jallabiya fara kal sai wata yar farar hulla da ya aa a kan shi ,
Hannu shi yana rike da wani dan farin tasbaha mai kyau yana ja a hankali,
Sonny wanda a lokacin yana zaune yana game tare da wata yar zukakkan budurwa wace da gani yar kabila ce,
Tun shigowar Yusuf din Sonny ya kalle shi saida yaji gaban shi ya fadi saboda irin yadda yaga Yusuf din ya mai wani irin kwarjini a ido,
Zaka ce wani babban malami ne idan ka gan shi,
Gurin zama Sonny din ya nuna ma Yusuf don ya zauna,
Batare da ya kara ko da second a gurin ba ya juya zuwa wani dan karamin korido dake ta wajen dakin ya tsaya,
Sonny wanda yagane komay Yusuf din ke nufi dole ya sallami yarinyar da suke zaune tare saboda yagane cewa saboda ita ne Yusuf bai karaso gurin ba,
Sun kai wani lokaci, tare suna tataunawa akan har kan business din su,
A nan Sonny yagane cewa Yusuf na, son karin taimako a harkokin shi don bunkasa har kokin shi,
Bai wani ce ma Yusuf din komai ba a lokacin saboda shi kadai ya san may ya nufa a zuciyar