Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   48 / 84

141K to 144K   out of 251.8K words

yace tab ai mukn yau sadiya ta cika muna ciki fam da kayan zaki,
Da gagawa Maryam ta mayar da duban ta ga Yusuf,
Wani sanyi maryam taji gwiwar ta yayi da kyat ta dan mike gami da kakaro wani murmushi tace ,
Au ashe ma kun ci abinci Anty ko tana can duk ta damu,
A sake yace mun ci ko sunci ki zuba min pls don ni yanzu nake da niyar zuwa inci a can,
Kamar da gayya Maryam ta cika mai plate dam da abinci da yaji naman rago,
Sai da yadan daga kanshi ya kalle ta ya kalli abincin sai kuma ya mika hannun shi yakarba,
Gurin karba yai kamar hankalin shi na gurin Assalam sai ya hada da hannun ta ya rike,
Cikin sauri maryam taja baya da abincin ya bare mai a jikin shi,
Batai wani dadewa ba tacewa Assalam su tafi amma sai Yusuf ya ce mata
Su jira shi har ya kare cin abinci sai ya sauke su gida da kan shi,
Zamu iya zuwa ai mai mashin na waje yana jiran mu tace mai,
Abincin dake a gaban shi ya ture gefe ya ce mutafi na sauke ku kawai,
Wani kallo maryam tai mai ta tsura mai idanu sai kuma ta mike ta fadin Assalam mutafi,
Tariga kowa fita don shi ya tsaya daukar key sai muryan Jibrin yaji yana cewa
Something is fishing somewhere,,
Kamar ya tsaya yai mai magana cewa bai son haka kada yarinyar ta raina shi,
Sai kuma dai ya sa kai kawai ya wuce don idan ya tsaya zasu iya hawan mashi,
Shi ko sam baya son haka, don bai so ace gurin zuwa gidan shi wani abu ya samu yar mutane,
Duk da yasan cewa biyayya ne kawai ke sa tana daurewa tana mai abu saboda Antyn ta,
A kofar gidan ya samay su tsaye suna jiran shi sai dai fuskanta a cikin damuwa yake,
Gaba take zaune a tare da shi Assalam yana baya zaune yana ta wasan shi,
Murya kasa,kasa yace, may yasa baki fadawa Anty zancen da kikaji muna yi da Jibrin, ba ranan, ?
Saida tadan juyo ta dube shi sai kuma ta juya gurin window motar ta mai da hankalin ta ,
Kamar bazata bashi amsa ba sai can tace, saboda maganar bai shafe ni ba,
Kuma ban san ko may ke faruwa ba sai kawai in sa kaina aciki,
Wani irin hucin iska mai zafi ya furzar da ga bakin shi,
Yadan daki sitiyarin mota da hannun shi sai kuma ya numfasa,
Daga haka bai kara cewa komai ba har zuwa lokacin da suka tsaida motar su kofar gidan,,,,,





ZEEE MAKAWA
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
5โƒฃ8โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Allah ya karawa Annabi daraja,
Ya Allah ka daukaka musulunci
Ya Allah ka sa mudace da Rahaman ka,
๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘


Duk yadda mutum ke tsan mani hankalin yan church ys tashi sosai,
Hakan yasa suka mai da hankali sosai wurin jawu hankalin mutanen su da cusa masu ra,ayi
Daga can gurin shugaban nin su sai suke ganin cewa ai wani sakacine da dama mutanen suka bayar,
Shugaban Catholic churches gaba daya na kasa ne da kan shi ya sauka garin na kwantagora,
Sai da ya je gurin maimartaba ya kai gaisuwa
Inda ka basu dokoki kamar yadda ake wa kowani irin shigaba na addini don gudun tayar da tanzo ma ko wani tashin hankali,
Bayan sun koma church ne suka zaune yin mintun din su na shuga ban nin su,
Idan zakaji irin kudin da suka ajewa jama,an kasar ta kwantagora da kewayen ta sai mutun yai mamaki sosai,
Badon komai ba sai don kawai su ja ra,ayin masu raunin ima zuwa gare su,
Da kuma wa yan da ake ganin cewa sun karkata ne kila don talauci, zuwa cikin musulunci,
Sunyi rabon mashi,mashin da ke kuna hawa da na dinki ga mutanen kawai
Inda hankalin mutane sosai ya irin wa yanda basu da addini suka dinga shiga kungiyar su,
Father da kan shi ya shirya yadda za,a tunkari Yusuf, da Abdulsamad,
Yana zaune a cikin office din shi yana breakfast,
Cup ne mai dauke da ruwan shayi masu zafi yake korawa a hankali,
Don shi al,adar shi ce,shan tea mai zafi har ya dan kona baki,
Amma shi agare shi saboda sabo da zama kasar America yasa bai jin zafin
Dan tiririn ruwan na tashi saman cup din yana yi sama,
Yayin da sanyin AC ya gauraye office din duk safiya ce yanzu rana bawai wani yi,
Sakatariyar office din shi ce ta shigo da sallamar ta ,
Kallon ta yayi da cup din tea din shi a hannu ya ce, yadai Helen,?
Cikin dan rusun nawa tace boss kayi baki fa ,
Haka kawai yaji gaban shi ya ba da damm, to wasu baki yanzu zasu zo mai a wanan lokacin kuma baida appointment da su,
Sai kuma zuciyar shi ta nasa mai cewa kila wasu masu bukatar wani abune,
Yace wa Helena tace su shigo,
Helen tace da har na ce su koma kawai tunda basu da appointment da kai,
Don na lura ba harkan business bane ya kawo su don sun min kama da masu preaching,
Wani tsawa yadaka mata ya katse mata dogon zancen da take ja dashi,
Ya ce ki ce su shigo nace maki
Umurni na baki ba wai uzuri ba pls, ki kawo min ba , bayan kin fada masu cewa ina ciki ko,
Don su ga na yi masu wulakanci na hana su gane ni ko,?
A yadda Yusuf yai maganar cikkn tsaw yasa Helena, jin tsoro, da sauri ta fita zuwa yiwa bakin iso,
Ba ai wani bata lokaci ba sai gata da bakin sun shigo a tare tana masu iso,
Yana kokari a je cup din tea din shi a lokacin suka hada ido da Peter wani class mate din shi tun primary a kwantagora,
Yanzu Peter yana aikin banki ne a Enugu, amma dai iyayen shi suna zaune still a nan northern Nigeria,
Sai kuma wasu mutun biyu da yake ganin kamar ya san su a da can,
Yai masu sannu da zuwa duk da bai san abin da ya kawo su gurin shi ba,
Yace wa Helena ta kawo masu abin sha, inda ya nuna masu gurin zama,
Bayan sun zauna sai gaisawa ya biyo baya inda suke ta yiwa juna ya bayan rabo,
Ganin yadda Yusuf ya koma kawai yasa suka ga yai masu wani irin kwarjini a fuska,
Saidai ya lura da cewa daga cikin su ba wanda ya sha drinks din da aka aje masu a gaban su,
Sai da suka natsu Yusuf ya juyo yana fuskantar in a serious face ya ce lafiya dai, ko nagan haka,?
kafin su yi magana sai wani daga cikin su ya fara jero addu,oi kamar yadda sukeyi a koda yaushe,
Ameen din da suke fada shima shi yake fada tunda duk addua ce ai,
Ganin yana karba masu yasa suka dan samu karfin gwiwa, kokarin fuskantar shi,
Saida suka gama wanda yafi shekaru a cikin su ne yafara magana da cewa,
YUSUF munzo ne don mu fuskanci juna da kai akan juyawa Jesus crisis baya dakayi,
Munzo ne on behalf of our members,na Catholic churches, don mu baka hakkuri akan duk wani abin da mukai maka har ka canza, religion din ka,
Yusuf ya girgiza kan shi yana cewa ni ba kumin komai ba kawai don na gano cewa Islam itace hanya madaidaiciya,
Kunga yanzu dai nakai munzalin da idan ina ra,ayin abu zanyi don kai na kawai,
Ido suka tsura mashi gaba dayan su suna sauraren shi,
Yaci gaba da cewa ban shiga cikin Islam ba sai da na tabbatar da na samu kwakawaran hujan da zan kafa wanda har yajani zuwa, cikin ta
Ni ban shiga don wani ko wata ko kuma don kwadan wani abu ba, kawai don ra,ayin kaina nashiga,
Mikewa wanda Yusuf yakira da Peter, yayi har zuwa gaban Yusuf din yadan dafa tebur din suna fuskantar juna, inda yace mai
Look Joe, daga million daya har zuwa goma zamu iya baka don kawai kadawo ma addinkn ka daka bari,,
Cikin wani murya mai kama da tsawa Yusuf yace mai ,
Na fada ma cewa badon wani abu nashiga wanan addinin nawa ba kawai sai don irin hujjojin da nake dasu akai,
Mikewa yayi zuwa wajen wani serve dake a cikin office din inda yasa wasu nombobi gurin ya bude,
Kudi ne sabbi kar ya kwaso yakawo masu gaban su wanda kallon su kawai zai sa mutun yasan cewa sunkai miliyoyi,
Yace bani bukatar kudin ko kowani abu kawai don tsira da rayuwata nashiga wanan addinin
Yakare zancen yana mai tura masu kudin a gaban su lokaci guda,
Wanan ya kalli wanan wancan ya kalli wancan,
Jiki ba kwari suka mike tsaye saboda sun san cewa sam ba riba akai,
Har sunkai kusan kofa Yusuf yakira sunan Peter yana mai ce mai i,hope for daga haka kun rabu dani kenan pls,
Ya hada hannayen shi guri daya alamar yana rokon su da sufita harkan shi pls,
Ba wanda ya kara ko juyowa suka sa kai zuwa hanyar fita,
Zuka tan su cushe da bakin ciki saboda sun san cewa sun rasa Joe din ke nan har abada daga cikin su,
Gashi kuma yayi nisa ta yadda basu iya jan ra,ayin shi ba sam,
Wani irin tsaki ya ja yace batatu kawai,
Sai bayan fitar su ne yadaga hannu yanawa Allah godiya da irin baiwar da yai mai ga ta addini ga kuma dukiya,
Sonny ne yafado mai arai inda yaiwa Sonny din adduan shima Allah ya sa ya gane gaskiya,
Ashe har da Abdulsamad sun ziyarta inda yai masu kaca kaca da cewa kada su kara tuna shi daga cikin su,
Sai dai Ejoma ce basu san inda take ba har yanzu tukun,,,

Tun bayan tafiyar Yusuf maganar ta tsayawa maryam arai so sai,
Sai dai kuma ta rasa hanyar da zata fadawa antyn ta cewa ga halin da ake ciki a zancen,
Da bara ce ta fado mata na ta ba wa Anty shawaran zuwa dubo Sadiya din,
Suna zaune a tsakar gida tana,wasa da Abubakar din Anty,
Sai ga kiran yusuf ya ahigo a wayar Anty Dije sun kai wani lokaci dashi su na dan hira,
Inda yake sheda mata cewa ya je gurin ya Iliya mijin Anty yace zai shigo kafin Azumi,
Tai mamakin jin cewa ya tafi gurin shi nan yake sheda mata cewa akwai wasu kayan su da za,a shigo da su sune yaje yin clearing,
Nan yake tambayar lafiyan su Assalam da sauran su amma dai bai tambayi maryam ba,
Itama dai anty sam bata dauki wanan a bakin komai ba ,
Sai zuwa dan lokaci da kare wayan na su ne maryam take cewa Antyn ta
Gaskiya Anty yakamata mu tafi gidan Sadiya mu diba ta kada tace ba ki taba zuwa,
Haka dai tai ta cusawa Anty Dije ra,ayi har dai daga karshe ta amince da cewa zasu, tafi su uku da yara,
Bayan kwana biyu da zancen shiri sosai sukayi i dan ka gansu zaka zata wani guri can zasu,
Ashe wai duk shirin zuwa duban budurwan Yusuf ce,
Kai su akayi a,cikin wata motar da maigidan Anty ya saya ya barta a gida,
Sadiya tana zaune tare da wasu kan,nenta suka kallon tv a dakin mahaifiyar, su,
Suka ji sallaman mutane, kallon su suke yi a cikin rashin sani,
Sadiya din ce tagane su ta ganin Assalam a cikin su,
Nan aka shiga gaisawa a tsakani inda Sadiya din ke nuna yar jin kunya, a tsakani,
Mahaifiyar ta tasa aka kawo masu kunun zaki mai sanyi yaji kayan kamshi sai tashi yakeyi a ciki,
Maryam sai kallon gidan takeyi irin kallon kwam din nan,
Bayan fitar mahaifiyar sadiya da kannen ta ne, suka dan kara gaisawa da Anty
Inda Anty kewa Sadiya kewar Yusuf, din ?
Jin maganar Sadiya tayi kamar don zolaya suka zo mata,
Amma kuma, sai ta tuna da yadda Yusuf ke fada mata halaiyar Anty dakuma irin yadda take son alakar su,
Dago kai tayi tanawa Abubakar dake hannunta wasa,
Sai kuma ta sauke kan ta cikin kwantar da murya tace
Anty Yusuf bai fada maki yana fushi dani bane aiko da ya wuce bamuyi sallama da shi ba,
Kuma nai ta kiran wayan shi bai daga wa,
Nan da nan an nurin fuskan Anty Dije ya sauya lokaci guda,
Cikin damuwa anty ke tambayar sadiya abin da ke faruwa,
Bata boye mata komai ba na yadda kanin mahaifin ta yaiwa Yusuf din daren da yazo zance gurin ta,
Na,imat ba tasan lokacin da tasa kuka ba alokacin,
Tana cewa abin da mutanen su ke yawan fadi ke nan cewa koda Christian ya musulunta gori da hattara da musulumai zasu dinga mai har sai yafi na lokacin da bai shiga cikkn su ba, zร fi da ciwo,
Nan kuma hankalin su yakara tashi ganin yadda Na,imat ke fidda hawaye,
Abu ya taru lokaci guda yai wa Anty Dije yawa, tarasa da,wani zataji,
Sai,da suka samu Naimat (Ejoma) tai shiru san nan suka fara magana,
Maryam na zaune a gefe tai shiru tun da akafara zancen ta na mai jin zafin irin kalamin da aka ta jefawa Yusuf din,
Sadiya ki yi hakkuri zan kirashi in ji may ke faruwa ne ai bai kamata yai saurin fushi ba haka,
Mahaifiyar ta wace itace yar uwan Jibrin din tashigo dakin
Inda take kara fada masu halin kanin mahaifin nasu dan cin mutunci,
Tun a hanya Anty Dije ke ta zabga wa maryam godiya don badon ita da takawo shawaran zuwa diban Sadiyar ba da ba zasu san abin da ke nan ba,,
Cikin ikon Allah ranan Yusuf bai kira anty ba sam tankar yasan da zancen,
Ita ko Na,imat duk hankalin ta ya tashi saboda ji takeyi kawai ta zauna a cikkn yan uwan ta zaifi mata
Kada sai sunyi aure da Ibrahim irin wanan gorin ya biyo baya,
Ji tayi an dafa mata kafada
A hankali ta juya don ganin kowaye maryam ce ke mata murmushi,
A hankali maryam ta zagayo in da Na,imat din take zaune,
Saman hannun kushin din ta zauna a hankali maryam tace
Na imat kada ki sa komai a rayuwan ki pls saboda dama kin san sai an samu irin wanan challenges din,
Saboda wasu basu da tauhidi atare da su just dai suna ansa sunan su musulmai ne kawai,
Ki sani cewa Ibrahim dai kabilar ku guda dashi kin ga ke nan wanan irin challenges din zai zo maki da sauki,
Unlike na ya Yusuf wanda in dai ba haushe mutun ne koda ace shi ya Yusuf din a cikjn musulunci aka haife shi,
Zaman shi na dan kabilar ibo ko bayerabe sai sunyi suka akai,
Kai koma da ace yaren da ke anan cikin arewa ne tare da mu,
Kawai ke dai imani azuciya take ba,a baki ba,
Don haka duk wani tunane ki daina kawai ki sa Allah a gaba kin ji sister,
Kai Naimat ta daga alamar gamsuwa da zancen maryam din duk da tagirmay ma maryam din sosai amma dai yarinyar na bala,in bata shawa saboda irin halaiyar ta,
Ga kuma irin yadda ita da yar ta suke kokarin koya mata addini akoda yaushe acikin sauki,
Sai washe gari ya kira Anty Dije tun daga maganar ta yagane cew akwai matsala don ba haka take mai ba idan suna waya,
Antyna lafiya kuke kuwa naji muryan ki wani iri kamar ba dadi yau azuciyar ki
Anty Dije ce ta katse shi da cewa Yusuf may ke faruwa a tsakanin ka da Sadiya ne ?
Shiru yayi na dan wani lokaci sai kuma can yace tazo gurin ki ne,
Anty Dije bata boye mai komai ba tafada mai yadda maryam taga cewa ya kamata suje su kai mata ziyara,
Nandai ta bashi duk wani bayanin da yadace tai mai alokacin,
Tsawon wani dan lokaci bai yi magana ba sai zuwa can yace,
ร€nty Dije gaskiya bazan boye maki ba bazan iya auren Sadiya ba kuma yanzu,
Saboda ko munyi aure za,a samu matsala sosai, daga yan uwan ta,
Katse shi tayi da cewa kai Yusuf yan uwanta zaka aura kodai ita,
? ,
Murmushi yayi kawai yace bazaki gane bane anty kawai abar wanan zancen zai fi,
Yusuf ko da sunyi challenge din ka ne ai ba yarinyar bace tayi ko ?
Zan dai kira ki anty yanzu zan

48 / 84