Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
raini yana son shiga a tsakanin su don tafara mayar mai da magana mai zafi,
Tsuki yaja yace why tausayi zai ja mai raini a gurin ta,
Zai yi kokari ya killance kan shi daga harkokin ta bazai kara sa mata ido ba,
Tun bayan barin shi gidan bai shigo ba har sai zuwa misalin hudu na yamma,
Lokacin duk sun kare aiyukan da Anty Dije tabar ma,su yi,,,
Saidai fuskan shi kawai zaka kalla kasan bai a cikin good mood yau din, saboda yadda idon shi suka kada sukayi jajir da su,
Kallo guda tai mai tunda ya shigo ta kauda kanta daga ganin shi
A take wani yanayi maikama da zazabi ya sauka mata, sai taji kawai kwanci take so a lokacin,
A kan gado ta zube sannan ta lumshe idanun ta a hankali a sannu take jin yadda zuciyar ta ke bugawa,
Muryam Na,imat ce a kanta tana cewa Maryam lafiya ki ka kwanta by dis hours,
Kwanci bayan dis hours yana kawo wa mutum zazzabi fa,
Ido a lumshe ta ansa mata da fadin lafiya kalau, nadai dan kwanta ne kawai,
Dafata tayi tana cewa to ki tashi wanda kika kwanta don shi shima ya wuce bai tsaya ba tunda yaga jeloup din taliya mukayi,
Cikin wani hanzari tamike zaune dan jin cewa bai ci ba ya wuce,
Tambayar Naimat tayi cikin damu to may zai ci da ya wuce,?
Aida kin tambaya ko da abin da yake so ai mai ko,?
Kin san halin brother baya son dogon magana shi yasa kawai na kyale shi,
KB yana gari don haka yana fita ya juya akalar motar shi zuwa gidan,
Wayar shi ce alamar kira ya,shigo mai a lokacin,
MARYAM BLACK,
Yagani a rubuce kamar yadda yai serving din sunan ta,
Cikin hanzari ya mija hannu yadauki wayan adai,dai lokacin da ya tsaida motar shi,kofar gidan KB,
Da sallama yadauki wayan yana cewa maryam ya dai ?
Kafin ta ce wani abu sai tai dan shiru saboda Naimat da ta tsure ta da ido,
A ladabce tace Ya Yusuf baka ci abinci ba kawuce,
Murmushi yayi dan jin dadin kula shi da tayi, yace No bana cin taliya ne yanzu shi yasa
To amma shine bakai magana ba sai aima wani abin,
No, no no ki barshi kawai zan sha drinks ai,
Wani ajiyan zuciya tayi har sai da yaji ta acikin wayar,
Sallama taimai inda yake ce mata yagode cikin wani murya maikama da na tausayi,
Jingine wayan tayi a saman kirjin ta , tana tunanen irin saukin halin Yusuf din,
Yanzu ya shigo fuska murtuk kamar an aiko mai da sakon mutuwa amma sai gashi taji muryan shi kuma yanzu normal,
A gidan KB Yusuf a waje yake tsayawa saboda baya son irin yanayin matar KB din,
Don ita ko maza sunkai nawane zata iya zama acikin su,
Ko kuma takama gittawa a gaban su cikin shigar matsatun kaya,
Shikuma hakan ke sa yana kare idon shi da daukar dumbin zubi,
Duk yadda KB yaso su shiga Yusuf yaki sai da KB din yace mai ai ba kowa sun tafi gidan su gurin bukin aure,,
Ya,samu akwai abinci da aka zubawa KB din shi ya dan ci amma kadan saboda bai ji test din abincin ba, sosai,
A lokacin da yakora ruwan mai sanyi da KB din ya dauko mai acikin fridge
KB din ne yadan dube shi yace wai ya ake ciki ne akan zancen ku da yariyar nan ne,
Ina sa zuwa yanzu har anyi engagement sai kuma na shiru kawai
Man ya kamata fa ka maida hankali ka aje iyali zuwa yanzu,
A je roban ruwan yayi a saman tebur din gaban shi ya ce,
Ai kasan komai a sannu akeyin shi idan time yayi ba,wani bata lokaci ,sai ayi,
KB yace gaskiya ne ba shakka haka maganar take aure dan lokaci ne,
Washegari duk kan su gidan gyaran jiki sosai akai masu,
Daga adon lalle da kuma dilka, sai kuma kitso da aka yarfa ma su gwanin ban sha,awa,
Gaba dayan su sun fito shar da su, duk wanan shirye, shiryan sunan da za,a yi ne na haihuwar kaunar mijin Anty Dije da tayi,
Ita kanta maryam tasan cewa sun yi kyau duk da ita ba ma,abociya son yin kitso bane,
Allah ya tai make su har aka gama masu Yusuf bai shigo ba saboda yar tafiyan da yayi zuwa kauye,
Da sallama ya shigo gidan inda ya fara cin karo da Na,imat wace a yanzu duk ta juye ta zama bahausa sat,
Saida gaban shi ya fadi irin yadda yaga ta koma alokaci guda kai Musulunci ma Rahamace ya furta a cikin ran shi shi kadai,
Anty Dije ce cikin shigar wasu dinkin Senegal's da mijin ta yasayo mata da sallah bara,
Da fara,ar ta a fuskan ta ta shigo falon gurin Yusuf, din tana tambayar inda ya tafi,jiya,
Maryam najin shi daga dakin su amma sai taki fitowa su gaisa,
Duk hiran da suke yi da Anty Dije sai ya tsunci kan shi da rashin jin dadin ganin maryam din kamar ya tambaya ina ta ke sai dai ya daure,
SAFIYA ce ta shigo gidan da sallamar ta Anty Dije wace ke kokarin aje cup din da tasaha kunu a saman tebur ta dago kai tana amsa da yar fara,ar ta a fuskan ta,
Da murmushi makale a fuskan ita Safiya ta zauna saman daya daga cikin kujerar falon suka gaisa,
Sanan take tambayar maryam din
Anty Dije tace barin kira maki ita tana can dakin kusa da kitchen kwance,
Lokacin da Anty ke shirin mikewa ita a lokacin maryam ta shigo falon da murrmushi makale a fuskan ta,
Wani irin mugun shock yaji da yana cewa Naimat ta canza cikin dan lokaci sai ga kuma maryam kamar wata Amaryan wani gwauna,
Da sauri ya kauda idon shi gare ta da ya daga don amsa mata sallamanta,
Safiya ce ta tare ta da cewa ke wanan irin haduwa fa kamar wata, amarya can,
Hararan ta maryam tayi tace ina kwana Ya Yusuf, kamar bai gurin
Amsawa, yayi batare da daga kai ba
Safiya taci gaba da cewa Anty shiya sa Dan iskan ga ya wani leke mata kamar kaska,
Ni wallahi Anty A A din nan Allah yakawo wanda zai kifar da gwaunatin shi a zuciyar maryam,
Dan takaitaccen murmushi Anty Dije tayi tace,
Wanan ai tai nisa Safiya indan kin ce ba shi ba yanzu zaku bata ne,
Cikin daure fuska maryam tace wa safiya, gaskiya ke sai mun hau sama dake tukun ina ga zamuyi daidai,
Ta juya tai hanyar shiga dakin su tana magana kasa,kasa,
Safiya ta juya tana fuskantar Anty Dije tace wallahi, anty bana son zan cen wanan mutumin sam mugune har na karshe,
Nan dai sukai ta zance a kan A, A din har zuwa dan wani lokaci,
Yusuf wanda kan shi ke a duke yana ta faman dadannar wayar shi bai ce masu uffan ba,
Daga karshe rai a bace Anty Dije ke cewa, ai duk abin da zai mata Allah bai bashi ikon cutar da ita,
Maryam tafito cikin shigar wasu kaya kamar les a jikin ta sai dai ba masu nauyi bane su tai wani irin bala,in kyau,
Naimat ce a bayan ta ita cikin shigar wasu kaya da Yusuf ya dinko mata,
A tare zasu tafi gidan kaunar mijin anty dije inda ake suna,
Ga kayan ci da na sha nan kala kala da suka dafa da,soyawa wanda za,a tafi mata dasu,
Ganin yau gidan da taron mata yasa Yusuf mikewa yana ma Anty sallama,
Yusuf don Allah ko yan matan nan ka fara sauke min su a gidan bukin pls,
Daga kai yayi ya dan kalli gefen da suke idon shi caraf a cikin na Maryam,
Da sauri maryam din takawar da kanta gefe guda cikjn sauri,
Amsawa Anty Dije yayi da to badon yaso ba, a haka aka dinga loda kayan da zasu tafi dashi a cikin motar shi,
A hankali suke tafe inda yau kidan turanci ne ke tashi a cikin motar shi, ga sanyi AC da ke ratsa masu jiki a hankali maryam ke bin wakar da ke tashi a cikin motar,, le me love you, ,don't give up , i won't, give up, now, know, know,
Kusan duk wakan suke bi, a motar inda Naimat ta kawar da dan shirun da ya biyo baya,
Tambayar shi tayi ya zancen shi da Sadiya ne wai an gyara kuwa?
Bai bata ansa ba sai ma jefo mata tambayar da yayi cewa tana bukatar tace, tazama cikin su,
Kafin Naimat tai magana. Safiya ce tace mai wai, haryanzu zancen yana nan ashe ?
Naimat tace nafison brother ya samu mata wace zata iya kula da mu yan uwan shi a duk irin halin, yadda muke,
Kin san fa mu a yaren mu mace ce ke kara karfafa zumunci ba namiji ba,,,
Idan munzo gidan shi ba,a tare mu da fuska mai kyau ba ya zamuyi
Kinga ke nan zumunci ya baci saboda ita mace ita ce mai zama gida,
Tunda Naimat tafars magana ba wanda yace mata komai har ta kai aya,
Bayan ya sauke har zai wuce sai Naimat tace dan Allah brother ba dadewa zamuyi ba ,
A,lokacin har su maryam sun fara tafiya, zuwa cikin gidan bukin ,
Safiyane amma kasan cewar haihuwan fari ne gida tab yake da jama,a daga fanin mijin ta har na,ta da abokan arzikin, ta,
Bayan sun gama shigar da kayan da,suka fara zuwa dasune a ciki,
Sai suka samu gefe guda saman fararen roba dake karkashin wani runfa suka zauna,
A daidao inda suke zaune akwai mata gun,gun a zazaune saman fararen kujerun roba,
Wa su, kujeru da wasu matasan mata suke zaune akai su uku sai kallon inda su maryam suke suna kus,kus,
Sai leken su maryam akeyi, tun farko maryam ta halkanta da su amma sai ta shere su don gudun zargi,
Amma kawai sai daya daga cikin matan ta tasao har inda suke, zaunr tace, wai kamar Ejoma wanan ko ?
Safiya ce tai carf tace Naimat dai ko, ?
Matar tana murmushi tace gaskiya kamar su yai yawa sosai ,
Naimat tace nice da sauri ta waiga gurin da yan uwan ta suke zaune tace,
Itace bana fada maku ita bace, ashe kin musulunta ne,
Safiya tace haba tunda har kin ga zahiri may ye na tambaya pls,
Ke ko yar uwa don ance mata tubabba shine wani abu,
Haba amma hakan ya zama tozarci ko tunda har mutun ya riga ya zama musulumi,
Sai gudan tace to am a ai don an tuba ba a taba cewa batai zama kafira ba ada,
Innalillahi, maryam tace cikkn nuna bacin rai ga matan,
Haba dai Anty Rukkaiya ai wanan bai dace ba ga addini ko ?
Safiya tace ga wanda yasan addini ke nan maryam
Wai mutane sai su manta da cewa da wanda yai shekara dubu da wanda ya shigo yau fuk guda suke ga Allah,
Har ma wanda ya shigo yau idan ya rike addini saima ya fika don shi baida zubi tukun yana tare da gafaran ubangijin shi,
Haka abin yaso yazama kamar fada a,tsakanin su don Safiya ta dauki zancen da zafi,
Su basu ko farga cewa Naimat ma bata gurin ba tunda taga irin yadda abin ya zama tozarci ta sulale ta fita kofar gida,
Sai da wasu manyan su suke tambaya wai akan wace,ce ake zancen
Safiya taje ta nuna Naimat taga babu kowa aguri ,
Da mamaki take kallo. Maryam tana tamba yar ta cewa ina Naimat din take,
Mikewa su kayi a,lokacin da ake cewa matan basu da gaskiya
Su daina yiwa mutun tozarci irin haka saboda hakan yazama cin fuska,,
Naimat wace ta koma can kofar shigowa gidan tai zaune cikin bacin rai,
Shigowar Anty Dije ce yasa tadan yi kamar ta sake, fuska,
Tambayar ta Anty ke yi ko may yasa ta fito waje, ina kuma su Maryam da Safiya,
A wanan lokacin suma suka i,so gurin suna neman ta ta,
Ko ba,a fada ma mutum ba yasan cewa a cikin bacin rai take kawai,
Safiya ce tai kokarin yiwa Anty bayani kamar yadda akayi da matan
Cikin bacin rai anty ke cewa su tsaya ta samu wanda zai maida su gida,
Sai yanzu take, da ta sani tabar su agida kamar yadda su ka bukata tun farko,
Cewa su bazasu zo ba za su zauna gida kawai har ta dawo ita da yara amma sai tace tun da buki yaune kawai su tafi tare kawai, yafi, shine har maryam ta gai,yato safiya don su tafi tare,
Zaune yake jikin shi duk kamar ba nashi ba Naimat tana ta labarta mai abinda ya faru,
Sai hawaye take ta zubar wa tana ta kokarin share hawayen da ya zubo mata a fuska da gyalen da ta yafa ajikin ta,
Maryam tana tsaye gefe guda tabi lafiyan bango tana sauraren yadda yake bata hakkuri,
Wani irin tausayin su take jin ya kama ta a lokaci
Batasan cewa hawaye na biyo mata fuska ba har sai da taji mutum tsaye gab da ita
Ta yadda bazata iya ko da motsawa ba handky ya mika ma ta batare dayi mata magana ba,
Girgiza kai tayi alamar aa ya barshi kawai yana kallo tasa habar hannun ta ta goge hawayen
Ko karin wucewa take yi zuwa ciki a lokacin batare da tace mai uffan ba,
Sai dai babu hanyar da zata bi ta wuce ko ka dan ga kamshin shi da ya cika mata hanci kamar kamfanin turaren,
May ki,ke,wa kuka maryam kifada min dan Allah
ZEEE SEENABU MAKAWA
[3/25, 21:09] Anty Lantana: πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
FUREN JUJI
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
6β£1β£
ZAINAB IDRIS MAKAWA
IYAKA, NA,ABBUD WA,IYAKA NASTA,IN,,ππππππππ
Tsaye yake a tsakiyan falon gidan shi daga shi sai singlet da wandon shi dogo dake jikin tun da rana,
Safa da marwa yake yi a,cikin falon, a inda ya goya hannayen shi a bayan shi,
Komawa yayi yadan jingina bayan shi da bango kadan,
Yadan daga kafar shi guda ya dage a bayan bangon,
Da sauri ansar da tunanen shi ya bashi akai yai sauri girgiza kai tankar da wani yake magana alokacin,
Ina sam ba gaskiya bane sam sam yariyar da bata ko kai Ruth shekaru ba,
Ina sam wanan zancen banza ne may zan so gurun maryam,
Ko shi saurayin nata ai kawai rigimar tane ya kai ta amma ai da,sauran ta, kawai dai don tayi saurin fara karatu ne kamar yadda yaran hausawa ke saurin shiga makaranta,
Tsuki mai tsawo yaja batare da ci gaba da tunanen ba ya juya zuwa bedroom din shi,
Hakan ya fada saman gadon shi batare da tsayawa sauya kaya jikin shi ba
Sai cikin dare daidai lokacin da ya,saba tashi don yin kiyamallaini ya mike zuwa bathroom,
A gurin da yai sallah asuba yana lazumi nan barci ya kara daukan shi mai tsawo,
Wani mafarki ne yadan dauke shi zuwa duniyar mafarkai,
Tafe yake yana rike da hannun wata, mace wace, ke dauke da tsohon ciki a jikin ta
Tafiya matar keyi da kyat tana faman ciji baki don wahala,
Iya tausayi matar ta bashi hakan ne yasa shi zuwa ya dan taimaka mata,,
Dukawa tayi don wani irin azaban zafi da ya ziyarce ta, da sauri ta fisge hannun ta gare shi,
Ta dan kai wani lokaci agurin duke tana fama da murdan ciki,
Sannan matar ta dago fuskan ta da yaga ni shi yasa shi ja da baya cikin wani irin mamaki
Sai kokarin nunata da yatsa yake saboda bai san cewa itaba ce ke wanan wahalar,
Juyawa yayi daga inda yake a kwance,, daga haka sai yabar wancan mafarkin na farko,
Wani mafarkin kuma shiga yi inda yake tsaye yana tura wata yar matashiyar budurwa a saman wani lilo
A,hankali yake tura ta inda kanta yake duke, sannu a hankali ta dago kai zuwa saman kirkin shi ta kwantar da kai
Sun dauki tsowon lokaci a haka da ita sai dai sam baya iya ganin fuskan ta,
Ya kai wani lokaci agurin yana kwance a kasa saman carpet yana barci,
Zuwa yanzu tun bayan musuluntar shi yasaba da irin wanan kwanciyar a saman abin sallah shi idan ka gan shi ya dunkule guri guda zaka,zaci cewa ba shi bane,
Γ yadda zaka ganshi matashi dan kwalisa mai i,limin zamani kuma ga naira ta zauna zaka zaci cewa ba zaiyi jimirin jurewa yin ibada ba
Badon komai ba kuma sai,don za,a iya cewa haye yayiwa addinin a sama ,