Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   70 / 84

207K to 210K   out of 251.8K words

ya kunna ta,
Sakon da yafi daukan mai hankali a,lokacin shine wanda akace idan yabude waya yakirashi pls KB da Jibrin,
Cikin sauri yafara dialing din nomban Jbrin din amma busy yake,
Don haka yakira na KB kb wanda yana gida tare da matar shi ya dauki wayan cikin fada yace, duk da sallaman da Yusuf ke mai cikin taushin harshe,
Kaga daman kun,na wayan, yanzu ko ko angwanci baka fara ba amma ka fara kashe waya,
Murmurs shi yaiwa KB din kawai batare da yasan ko may yake nufi da zancen shi ba,
Yusuf yace kai anfada maka cewa kowa irin kane daga yin aure kakoma baka son zama gurin aiki,
Na bincika ko kana Abuja ance min katafi kwantagora ai,
KB ya din ce au dama sai jiya kaso ka fada min cewa zakai aure ko,?
Aure inji Yusuf din wanda ya tambaya cikin mamaki,
Kai kaidai kila sai na fada wa Jibrin cewa aima rukiya akan wanan auren da sha ma kai, Yusuf din ke fadawa KB din hakana,
Jin called din Jibrin da yayi ya shigo yasa shi katse layin KB din don sam bai fahinci abokin nashi ba yau,
YJibrin yace ango kasha mai,,,,,
Hmmm yace kawai da ya ji abinda jibrin din ya fada,mai,
Zancen ku gudane da KB din yau ashe yanzu ya bugo min waya ba wani abin da yake iya cewa sai zancen aure,
Jibrin yakira Yusuf cikin wani irin soft voice saida Yusuf din yagane cewa something serious zaice mai,
Ya akayi ne man inji Yusuf din ya tambaya cikin taushi,
Kana inane yanzu inji Jibrin yana tambayar Yusuf din?
Ina Lagos yace a,takaice kawai, batare da ya wani zaci komai ba,
Shitt inji jibrin din abin yaba Yusuf mamaki don yasan cewa ba halin jibrin bane hakan,?
Man wai wacece ka aura ne pls,?
Jibrin din ya,sakowa Yusuf tambayan da yaji ta a bazata,
Ban fahince kaba fa inji Yusuf din yacewa Jibrin din,
Jibrin yace to be serious yau andaura ma aure a massalacin Jumma,a ,
What's cikin wani irin murya da har sai da ta razana Jibrin din,
Gaakiya inji Jibrin yace a bisa wakilcin mahaifina da malam Abdulsamad
WARA,FA,A,NAHU, MANKANAN ALLIYAN,, Yusuf yace a lokaci guda,
Yai shiru can yace HASBUNALLAHU WA,NI,IMAL, WA,AKIL
Jibrin yace wai kana nufin baka da labari Yusuf ko may wai ?
A hankali cikin wata irin murya karara yace wlh banda labarin wanan zancen,
Don ban masan anyi ba ni,
Kit, ya kashe wayan ga sanyin AC a falon amma wani irin zufa ne yaji ya karyo mai a goshin shi,
A hankali yadan rike gefen kujerar da yake a zaune inda ya fara hawan steps din da zai sada shi da dakin shi a hankali,
Tafiya yakeyi kamar mai ko yon tatata, don da kyat ya ke iya daga kafan shi zuwa saman,
Saman gadon shi yafada jagwal kamar wanda kwai ya fashewa acikki,
Aure, Aure ? To da wacece haka da har ban sani ba ,
Idon shi ya mayar ya rufe a hankali, Aisha, no no
Sadiya never yace cikin juya kan shi,
Maryam maryam yakar furta wa a fili, sai yace sam ba,zata yarda ai muna aure a haka ba,
Don har yanzu bawai ta yarda da shi bane ai balle a daura masu aure,
Ina ba ita bace saboda sam hakan baima yu,yuwa ai don shi yanzu maryam tafi karfin shi zai barwa aminin shi kuma ogan shi,
Wanda yakewa kwadayin shiga musulunci very soon,
Who the he'll is she. ?,,,

Maryam ta zaune gurin da ta idar da sallah tayi addu,an fatan alheri dakuma neman kariya agurin Allah,
Tana jin muryan Anty Dije da yaran ta afolo suna magana akan wai abinci yayi yaji yau,
Ita dai batace komai ba saboda damuwan dake damun ta a cikin zuciyar ta,
Sallaman matan gidan su suka ji sai kuma abayan su baba matan guda tana dauke da kwandon goro a kan ta,
ร€nty Dije ce eace ke cewa mama kune tafe da ranan nan haka lafiya dai ko ga ku da kwandon goro, mana,
Marya wace take saye da hijabin ta har kasa saidai fuskan ta ya koma wani dan fayau , da shi,
Har kasa takai tagaida su daya bayan daya,,
A hankali ta mike tsaye daniyar barin falon don bata san ko may yakawo su ba,
Muryan baba yaji yana ce mata ta dakata, kada ta tafi tukun,
Komawa tayi gurin da ta tashi takara dan zaunawa a wanan karon,
Saidai atakure take gaban ta nadan faduw kadan kadan,
Ungo nan maryam inji mijin mahaifiyar ta wanda ke gefen baba sam maryam bata san cewa dashi akazo ba sai yanzu,
Da sauri tadago kai don taga ko may ye yake cewa wai ta karba,
Kudine amma acikin envelop suke dan nawan karba tayi kamar yadda ya umurce ta da ta karba wai,,
A hankali takai hannun ta takarbi kudin babane yai gyaran murya yana cewa Alhamdullahi,
Maryam maryam din jin ankira sunan ta tadan dago kanta ta kalle shi a hankali,
Ya ce karbi wanan rike tukun,
Ta mika hannu a hankali ta karbi kudin hannun mahaifin ta,
Yace to madallah ina Dije anty tace na,am baba yace Sadakin maryam ne nan na mika mata,
Daga maryam har Anty dije cikin wani irin tashin hankali hankali suke kallon baba, din,
Ba dai kr azaune ya na gyada kai, yace kwarai kuwa don dazun nan aka daura wa maryam din aure da yaron nan,,,
Dammm gaban maryam din ya harba a lokaci guda dakin taga yana juya mata a lokaci guda kunnuwan ta yai mata wani kara tsuuuuu daga haka bata kara sanin inda take ba,
Da,sauri Anty da kishiryar maman ta sukayo kanta ,
Ruwa masu sanyi a ka watsa mata, ajikin ta har zuwa kan ya hankan yasa ta sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi,
Da sauri ts bude idon ta da suke a rufe tana tambayar baba ni bani maryam ka daurawa aure,
Anty tace mata cikin kulawa, maryam kwantar da hankalin ki don baba ya tafi,
Hannun Anty din maryam takamo tana cewa, Anty mafarki nakeyi ko, ?
Ya baba zai mun haka anty komai nawa daban baba ke mun,
Da sauri anty dije ta kwabe mata baki tana cewa,
Baki da hankali ko kuwa babane kike nufin cewa bai son ki ko kuwa,
Kuka wi, wi, wi maryam tasa a lokacin ta kwanta bisa kafadan anty
Duk da Anty najin kukan har kasan zuciyar ta amma sai ta kyale maryam din a jikin ta koda hakan zai iya sa taji dan relief,

Mahaifin Jibrin dattijon,
yar shi ta,bashi shawaran daya kira don yaji ko may ke gudana,
A hankali Yusuf ya jawo wayan shi don ya kira, dattijon,,
Sai da yatabbatar da cewa yanzu dattijon ya dawo gida da ga massalaci,
Mahaifin jibrin din yana zaune ya jawo tiren abincin shi a gaban shi don yaci,
Hannun shi ya fara wanke yayin da kiran Yusuf ya shigo wayan nashi,
Cikin sauri mahaifin Jibrin din ya dauko waya, ya karba kiran,
Gaisawa suka fara yi a cikin mutunci nan yake tambayar Yusuf ko yana ina me yanzu,
Yusuf din yabashi ansa da cewa yana Lagos ne ai ,
Tau inji mahaifin jibrin din wanda ke kokarin bude kulan abincin dake gaban shi,
Kamshin mashanu ya na tashi wanda yasa dattijo dan lumshe idon shi,.
Yaushe zaka dawo inji mahaifin jibrin din Yusuf ya ba shi ansa da cewa
Sai nan da kwanaki don yazo yin wasu aiyukane idan yagama zai shigo,
A zaton shi dattijon zai mai bayani akancewa ga yadda maganan take ,
Amma sai kawai yaji yana mashi fatan Alheri a rayuwa tare da fatan gamawa lafiya,


ZEEE MAKAWA YALWA
[4/28, 06:55] Anty Lantana: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
FUREN JUJI
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
8โƒฃ4โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

Barka da jumma,a yan uwa Allah ya sada mu da alherin dake cikin wanan ranan,,,,,,,,,,
RAMADAN KAREEM๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘


Kwance yake saman tafkeken gadon shi mai cin kusan mutun biyar,
Barci yake son yi saboda jikin shi akwai a gajiya, amma yakasa saboda tunanen da yasha mai gaba,
Kara juyawa yayi ko zai samu barcin yazo mai amma ina yakasa
Mikewa yayi daga kwanciyar dayake ya sauko da kafafuwan shi kasa a hankali,
Anty Dije ce ta fado mai arai agurin ta zai samu amsar damuwar shi,
Kan shi yadaga a hankali ya kalli agogon dakin goma saura nadare don haka baya son ya takura mata,
Balle ma matar aure ce duk kiran da zai mata da ranane ko kuma idan tana da magana itace kan kirashi da dare,
Gurin window dakin ya nufa inda ya yaye labule ya zuge glass din a hankali,
Wani irin fresh air ne ya shigo dakin a lokacin maidadi ya bude hancin shi ya shaki iskan ya dan lumshe idon shi,
Ya dan kai wani lokaci agurin tsaye yana kallon yan motocin dake wucewa a titin jefi,jefi,
Tsayin mintoci yana tsaye a gurin har na,wani lokaci sai kuma ya maida window yarufe kamar yadda yake da farko,
Bathroom ya shiga inda watsa ruwa da kuma dauro alwala, don yai sallah nafila kafin ya kwanta,
Wanan nafilan da yayi yasa shi samun relief mai sosai
Don yayi barci mai nauyi har da mafarkin wata,zukekiyar yarinya tana shayar dashi wani abu mai dadi a cikin cup din tankagaram mai daukan ido,
A daidai lokacin da yake kokarin dago kan shi ya kallo fuskan yarinyar sai kawai yaji wayar shi tana kuka acikin daren,
Cikin jin haushin wanda duk ya katse mai wanan mafarki mai dadi da shiga rai da yake yi, ya farka,
Hannu ya mika daidai gurin da wayan shi ke caji ya dauko wayar acikin kasala don duk jikin shi a mace yake jin shi,
Samuel ne ke kiran shi da sauri ya duba time karfe biyu da wani abu na dare,
Cikin sauri ya mustsike idon shi, babu abin da ya fado mai a rai kamar Dady shi,
Don har gobe yana mutuwar son mahaifin shi a rayuwar shi,
Fatan shi Allah ya nufi dad din shi da musulunta a rayuwar, shi,
Yana daukar wayan muryan Samuel din ne cikin daga murya yake cewa,
Brother Dad baia lafiya tunda rana yadawo daga filling station,
Yana kiran sunan ka yana cewa ,Na, lie, Joseph no, go, marry, just like that, yana ta shan giya, ko na karbe, sai ya ansa ya sha,,
Yanzu dai gashi har ta kai, jikin shi duk ya sake bai masan inda yake ba ga jikin tsufa,
Yusu ya ji wani irin zafin jin wanan mugun labarin a zuciyar shi,
Don haka ya rintse idon shi saboda takaici sai a yau yakara godewa Allah akan kwato shi da Allah yayi daga cikin kafirci,
Amma a fili cewa Samuel yayi zai turo likita ya duba mahaifin nasu,
Daga haka suka kashe wayen zuciyar bakikirin da jin wanan labarin takaicin da yayi,
Barcin da bai koma ba ke nan saboda wanan mugun labarin mai takaici da Samuel ya sanar dashi,
Yasan cewa ire iren wa yan nan dabi, un kesa wasu mutane suna masu gori masu karancin imani,,,,,,

A hankali ta sako daga kan gadon ta,, ta na kokarin taka, kasa, amma tankar ansa ta takawa dole ne saboda irin yadda take jin tafin kafar ta yai mata nauyi,
Toilet ta fada ta watsa ruwa saboda nauyin da take jin jikin ta yai mata,
Daga haka ta dauro awala tazo zuwa gabatar da sallah,
Bayan idar da sallah takai wani lokaci, a gurin zaune a takure, sai ta baka tausayi,
Wani tunane ya a zuciyar ta, nan da nan gaban ta ya fadi tawani runtse idanun ta,
Yanzu ita ya zata iya rayuwa da Yusuf a. matsayin mijin ta
Wani irin taji a zuciyar ta. Inda ta runtse idon ta cikin jin kunan a zuciyar ta,
Ita da wani ido zata kalle shi wai mijin ta yau, ita ya zata zauna da shi a matsayin zaman rayuwar aure,
Ita ya zatai zama da yan uwan Yusuf kafirai arna a matsayin yan uwan miji dangin miji,
Ya kuma zata kwashe da yan matan shi da tun ba,a kai ko ina ba har sun fara kai mata hari,
Hawayen da ya taru tun farko a idon nata sune suka samu hanyar sulalowa,
Bayan hannun ta tasa ta dan share hawayen a hankali,
Dago kan da zatayi sai sukayi ido biyu da Anty ta wace ke tsaye tana kallon ta, cikin daure fuska,
Inda take zaune tanufa ta samu saman stol din gado dake gefe ta zauna cikin damuwa ,
Maryam ban san may zan fada maki ba wanda zai sa ki yarda ki daina wanan halin,
Maryam tadago indon ta da sukai jajajir tace dagani taci kuka, har ta gaji,
Idan zakiyi hakkuri kiyi maryam kiroki Allah yasa hakan yafi zama maki alheri,
Amma ba ki zauna kina ta rusa kuka har ki jawa kanki matsalar rayuwa,
Still hannun ta ta kara sawa tagoge fuskan ta da yakoma kamar kamfanin fanfo,
Saman jikin anty ta fada tana ta rusan kuka har sai da tasa duk daurewan Anty itama saida tai kukan,
Ya illiya mijin Anty Dije ya katse masu kukan inda ya kira wayan yana tambayar matar yadda abubuwa ke guda na,
Daga karshe yace abashi maryam din yana da magana da ita,
Yace maryam ta ansa da naam cikin muryan kuka wanda yasa har saida yaji wani irin tausayin ta yakama shi,
Maryam bana son wanan kukan da kikeyi pls, ki saurareni da kyau ki kwantar da hankalin ki, kiji abinda zan fada maki,
Don dole badon taso ba tai shiru tana sauraren abinda mijin yar nata ke ce mata,
Sai kai take kadawa alamar to ya cigaba da mata nasiha,,
Nasiha masu ratsa jigi ya ya iliyan yai mata wanda don dole badon taso ba tai shiru, saboda maganganun sun bi jikin ta,
Sosai maganar shi tasa maryam dan sakewa don daren ranan har taci abinci kadan,
Sai dai rashin kuzarin da bata dashi don ta kasa sake jikin ta,
Safiya ce ta fado mata a rai don duk wanan tashin hankalin da take ciki alamu ya nuna safiya din bata da labari akai,
Kira guda gana biyu ta dauki wayan tana cewa yar halas kin ki ambato yanzu umma ke tambayar kwana biyu wai baki shigo ba,
Jin shiru yasa safiya din cewa hello, muryan maryam kawai ya tabbatar mata ba lafiya,
Cikin kuka maryam tace Safiya baba yadaura min aure yau,
What inji Safiya tace wa maryam cikin daga sautin tambayam ta,
Shehekan kukan da taji maryam din nayi ya tabbatar ma da maganar gaskiya maryam din ke yi,
Duk da dare ya soma a lokacin hakan bai hana Safiya neman izini gurin mahaifiyar ta ba,
Kwatsa sai ganin ta sukayi tayi sallama, a gidan
Lokacin maryam wace ta dunkule a cikin bargo saboda sanyin da takeji ga ruwan sama an lema agarin,wuri ya dauki sanyi,
Anty ce take mamakin ganin safiya ciki dare saboda bata saba,zuwa a wanan lokacin ba,
Amma kuma sai ta nasa cewa ai kila safiya din ta samu labarin abinda ya faru da aminiyar ta,
Bayan sun gaisa ne Anty dije din tace wa safiya sai kikaji labari kwatsam ko,
Ki shiga tana ciki ai don haka safiya, ta shige dakin su maryam din cikin damuwa,
Ganin yadda yaga maryam din a kwance yasa ta karasa gurin ta da,sauri tadan dafa goshin kan ta,
Sai a lokacin maryam din ta bude idon ta ganin safiya ce yasa ta,saurin rungumota zuwa jikin ta,
Nan suka dan yi kukan su suka,share hawayen su saboda kukan bashine mafita ba,

Tun da gari yawaye yake ta faman aiwatar da,duk wasu abubuwan da yake da bukatan yi don ya samu ya koma Abuja ,
Abinda yafi bashi mamaki shine rashin kiran shi da,su KB basu yi duk cikin wanan lokacin shima dai share su yayi ya kama abinda ke agaban shi,
Jirgn yamma yabi zuwa Abuja don haka acikin dare ya isa Abuja,
Driver shi yazo yadauke shi zuwa gida duk da agajiye ya ke bai hana shi daga waya ya kira mahaifin shi ba,
Don yaji lafiyan jikjn shi saboda yakira kafin ya taso akace yana barci ai,
Yanzu da yakira bayan shigan shi gida ko daki bai shiga ba yakira don yaji,
Inda yai sa,a ance yana zaune don haka aka bashi waya don su gaisa da mahaifin na shi,
Maganar farko da Mr Emanuel yayi shi ne, Joseph are you married with a hausa girl,?
Daddy just relax iam coming home tomorrow insha Allah,
Jin haka yasa Mr Emanuel's saurin kashe wayan,
Yusuf

70 / 84