Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
da kujera,
Kamshin yakara dukan hancin shi abinda ya sanar mai da cewa maryam takara zuwa kusa dashi ke nan,
Muryan tace tana ce mai ga ruwa ya wanke hannuwar shi,
Thanks a lot ya furta a yar siririyar murya ta yadda ba kowa ne zai iya jin shi ba,
Bayan ta yabi da kan lo nadan second sai yai sauri ya kauda kan shi dan guda shiga hakkin ido,
Ita ko maryam tana shigowa falon daga gurin da taje zubar da ruwan
Sai ce masu tayi tana mai kokarin daukar gyakenta anty mutafi ko,?
Jibrin muke jira yadawo dafa sayen magani ai, ko,
Dole ta koma ta zauna saman hannun kushin din again zaman da yai daidai da kiran wayar ta,
Kamar kada ta dauka saidai ta daure ta ciro dan ganin kallon da Safiya tai mata,
A,A ne kiran ta saidai kuma ta tsinci kanta da jin nauyin ansa kiran nashi,
Har kiran ya katse bata dauka ba, tana kokarin mayarwa a jakanta ne wani sabon kiran yakara shigowa,
Dole badon taso ba tadauka tana mai cewa Assalamu Alaikum,
A hankali take ansa mai maganar sai kuma tamike tsam daidai lokacin da take cewa mun fitane zuwa unguwa, duk kan mu
Idon kusan duk suka bita da, bishi a lokacin kowa da abinda yake sakawa a ranshi,
Shiru yadan biyu baya a falon sai Yusuf ne ke, cewa Assalam gobe tare zamu tafi massalaci ko,
Sai a lokacin Anty Dije wace ke wani tunane can ta dan nisa tana mai cewa,
Har ka ji saukin fitane Yusuf aidade ka bari har ka, kara, ji sauki, ko,?
A haba no,no,no Anty ai zan iya zuwa insha Allah I am ok now,
Kaiwa a shirya min shi, mutafi,
Zaune yake a gaban dan dan matashin dattijon yana taunan goro yace wallahi Ema ina fada maka cewa shi nagani a massalaci dazu,
Mr Ema ya dan ce no,no,no nafadama bashi ba bashi ba,
Joseph ba zai zo wanan gariba again
Saboda idan yabar zuwa wanan garin, zai dai na sa addin ku a zushiyan shi,
Amma waik,a she min kagani Joseph namu a mosque naku karya ne
Isowar Edowed shi ya tsayar da zancen su da yare suke gaisawa bayan sun gama gaisawa ne Edowed ke ce mai ashe Joseph yazo ne,
What, yafada da karfi har yana dan yi kamar zai mike tsaye sai kuma yakoma ya zauna saboda wani irin duhu da yake gani,
Dauda wanzan nata cewa to Ema nikan zan shige ke nan sai wani lokaci ko?
Kai douda idan zaka tofi ka wushe abunka mana may,nene ne kana damay ni haka,?
Rana ko yar biyar bai samu ba gurin uhan gidan nashi da ko yaushe yakewa fadanci,
Tsaye yake a gaban wani standing table dake dauke da kwalaben giya kala,kala,
Magana yake makama da fada ko kuma rada,,kamar wanda bai,son aji may yake cewa
Samuel wanda yai niyar fita cikin shirin shi nazuwa evening service, jin abinda mahaifin shi ke cewa yasa shi komawa baya yasha jinin jikin shi don sauraron uban,
A hankali ya,koma baya, don gudun kada uban ya gan shi,
Maganar uban ke mai yawo a kunnuwar shi, don may mahaifin su zai ma dan uwan shi haka,
Bayan irin girmama shin da dan uwar nashi ke yi amma ce duk,mahaifin su bai gani ba,
Saboda kawai ya canza addinin da yake bukata, don ra,ayin shi,,,,,
Gaskiya bazai iya kyale wanan zancen ba zai fadawa brother din shi don yasan abin yi tun wuri,
Yadauki wani ikacin don ya gwadawa uban cewa baiji komai ba,
Da harara Mr Ema ya bishi don yau duk haushin kowa yake ji,
Har yadan gwauta shi sai ya sa mashi kira yadawo baya,
Kallo guda yai mai sai yaji duk mahaifin nasu yafita mai a rai,
Tambayar shi yayi ina zai tafi sai yake cewa uban na shi zai tafi, service ne,
Fuska murtuk yakada mai kai alamar yatafi,
Saida Samuel yagama fada ma Yusuf duk abinda yaji uban na fadi ga waya,
Yusuf ne cikin murmushi, yake kwantar wa da kanin shi Samuel hankali da cewa ba abinda zai samay shi insha Allah,
Amma sai Samuel din cikin rudewa yake cewa no, brother you know how uncle Jackson is,
That man can kill person
"I swear,
Samuel just cool down your mind, Dad will not do anything, successful to me,
Da haka yai,ta kwantar wa Samuel da hankalin shi shi har ya yarda
ZEEE. MAKAWA,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Sosai maryam ta maida hankalin ta ga karatun dake a gaban ta,
Na ci gaban zango da,zasu shi badadewa ba saboda sani cewa FCE ba wasa ga al,amarin karatu a gare su,
Cikin sauri sauri take tafiya,saboda kada, ta makara,
Tsaye take a bakin titi tana jiran taxi yazo, sai motoci ke gittaiya a gaban ta,
Wata civic ce da ta,wuce tayo ribas baya ,baya,zuwa inda take, kokarin tsaya wa motar take yi,
Ganin haka yasa Maryam kau,da kan ta gefe, guda, kamar bata gan shi ba,
A hankali ya sauke glass din motar shi yana mai mata wani kallo cikin natsuwa,
Ina zaki haka ne, don na wuce dazun nan kadan naganki tsaye a nan,
Sau guda ta kalle shi ta kau,da kai, saboda kwarjinin da yai mata a fuska,
Murmushi yayi yace, well,
Kiyi hakkuri in sauke ki pls kada ki makara, don ko baki fada ba nasan cewa, F C E zaki dan ganin yanayin shigar ki kawai ya nuna min haka ya karasa zancen shi yana mai daure fuska,
Kai ta,daga ta dan kallan titi ko zata samu motar da zata shiga,
Titin, kamar an, share ba taxi tafe a lokacin, don haka ta daure duk da zuciyar ta bai kwanta daganin mutumin ba,
A hankali ta zagaya zuwa dayan gefen, na mai zaman banza, ta bude a hankali, ta zauna,.
Nagode tace batare da ta kalli gefen shi ba, wakan dan kwairo ya na Sarkin Das Billiyaminu,
Kidan, wakar na tashi kamar speaker din zai ruguje, abayan motar
Sai sanyi A, C da yacika motar da kamshi air freshener da ya gauraye motar,
Tsam Maryam take a cikin motar zaune kawai take amma kamar, jira takeyi, a ce mata ke ta sheka,
Shi bai mata magana ba ita ma din dai batai mashi magana ba,.
Daidai get din farko yadan waigo inda take, a karo, na biyu yai mata magana,
Tun bayan shigar ta motar, tambayar ta, yake yi,
Wani guri zai sauke ta a cikin compound din makarantar,
Da musali har suka kai inda zata sauka motar ,sai a wanan lokacin maryam wace hankalin ta ya kwan,ta ganin cewa, sun shigo cikin mutane,
Tace na gode Allah saka da alherin sa,
Dai,dai yana ribas da motar, shi, ya dan waigo inda take yana cewa kai ba komai ai
Iam Alhasan Bashir, daga zaria GTBank, manager,
Saida maryam ta waiga saboda jin abinda yace, ina fatan hajiyar zata fada min, sunan ta,
Maryam Abdullahi Bobi,
Ta fadi a takaice batare da ta kalle shi ba "nice name yace, kawai
A,lokacin da ya balle mata marfin motar ta fita, batare da kara kallin shi ba,
Har yai nisa da motar ya yadan lumshe idon shi badon komai ba sai don shakar kamshi turen ta da yayi, a karo na biyu,
Yana son mace mai yawan amfani da kamshi,
Yanason mace kamila mai aji,
Yana son mace wace bata canza halittan jikin ta,
Dan ganin Maryam da yayi yau sai yaga cewa duk ta, tara, wa yan nan abu,buwan da yake bukata,
Maryam Abdullahi bobi ya kara nanata sunan a hankali,
Tsaye yake a bakin motar shi, hannun shi a cikin Aljihun wandon shi,
Sam bata ganshi ba sai kokarin gyara saba jakar ta takeyi
Jikin tane yabata cewa ana kallon ta sai kawai ta daga kan ta sama, gurin da tasan ana anje motoci,
Ido biyu, sukayi da A,A dinta yana tsaye hannun shi guda, a cikin aljihun shi,
Sai guda da ya rike kofar motarshi kafar shi na ta ciki kadan,
Damm gaban Maryam ya ba da, amma sai ta dake kawai,
A, tsanake take tafiyan ta batare da ta nuna mai wani darrr dan ganin shi ba kamar yadda takeyi da,
Mamakin yakara kama shi kwarai don bai yi zaton haka ba daga gare ta,
Tafiya yakeyi, amma hankalin shi na ga wanan guy din da yaga ya aje Maryam,
Wayan ke ta kara batare da an dauka ba, har wayan ta katse,
Wani sabon kira takara yi a karo na biyu, sai,dai ko rabi ba,ayi ba a ka daga wayar,
Ke yar kauye ya kike inji Jibrin yaje cewa Sadiya Mohammed joda,
Bayan sun zauna tare da yi wa juna barkwanci a tsakanin su,
Sai Sadiya tai shiru
Jibrin yace ke wai lafiya kika kirani da wanan ranan haka,
Hmmm ai kaima kasani don Alkah dai mubar wasa muyi maganar gaskiya yau,
Jibrin ina mutumin ka ne wai tafada tana yar dariya kasa,kasa,
Duk da ya gane watake nufi amma sai ya dake yana ce mata,
Wai wa kije nufi ne sadiya, haba Jibrin don kaga ina mutuwar son abokin ka shine kake min haka,
Wai har yanzu ki na ga son shi ne,, Sadiya ?
Murmushi tayi, tace ai kaima ka sani Jibri, ka dai ki hada mu da shine kawai,
Tausada taba jibrin don ya dade da,sanin cewa sadiya tana son Yusuf da da dewa,
Amma yau sai ta ba shi tausayi saboda irin yadda yaga,tana mutuwar son Yusuf, arayuwar ta,
Kin gane ne sadiya ki bari zan mashi magana insha Allah zaki kiji ko mai, a guri na,
Sadiya ba tasan lokacin da ta fara zabgawa Jibrin godiya ba,
Murmushi yai mata kawai, yana mai jin tausayin ta,
Don da da farko haushi take ba shi akan zancen amma yanzu yaga da gaske takeyi son Yusuf takeyi,
Jibrin bai ja wani dogon lokaci ba gurin tuntubar Yusuf da zance inda yakara mai bayani akan Sadiya, din,
Yusuf bai wani bashi amsa ba cikakke sai dai yar murmushin dayayi wanda murmushhi wani part ne na rayuwar shi
Don haka sai Jibrin yafara tuntubar Ànty Dije don yasan cewa ita abokiyar shawar Yusuf ne kuma,
Kwarai Anty tai murna da wanan labarin don har ta kasa boye farin cikin ta,
Rana ake kodawa saboda giragizai da suke yawo a sararin samaniya,
Garin sai yadauki zafi gashi NEPA sun dauke wuta,
A gajiye maryam ta dawo, saboda zafin ranan da akeyi duk ya kode ta,
Ànty Dije wace ke ta farin ciki da labarin da Jibrin yaba ta tana zaune da Abubakar sai waka take mai,
Hakan yasa maryam gane cewa, Anty ta cikin farin ciki yau,
Takalmin da tasa na Tommy, shi take ko,karin cirewa,
Ta wallwale daurin dake a kan ta da tayi na rolling, ta wurga a saman kushin,
Fridge ta nufa ta dauko, ruwa a cikin leda sanan tadawo inda anty take zaune ta zauna tana zukan ruwan a hankali,
Sannan tai yar ajiyar zuciya saboda sanyi da taji yadan ratsa ta alikacin,
Anty naga kina wani farin ciki ne yau tunda na shigo, ?
Marya na kokarin, mikewa tsaye, take tambayar yar nata, .
Kedai maryam kani na ya kusa zama ango shima,
Wake nan Anty ?
Maryam ta tanbaya a lokacin kai tsaye,
Yusuf mana,
Taba ansa a takaice, Maryam wace a lokacin ta kusa kai wa tsakiyan falon sai ta juyo tana yiwa Anty nata kallon mamaki kawai,
Yusuf fa Anty ?
Shifa inji anty sai kokarin yiwa Abubakar wasa takeyi,
Cak Maryam ta tsaya don karasa sauraron zancen da anty ke fada mata,
Wallahi ke dai maryam ina wanan cousin sister din ta Jibrin da muka gani a gidan atika,
Dammm Maryam taji gabanta ya bada sai dai bata san ko na maye ba dai,
Sai kuma ta yake baki tana cewa Allah yasa dauka,sirious, dai,
Daga haka tasa kai ta wuce zuwa cikin dakin ta kawai,
Tana shiga daki ta fada saman gado ta rub da ciki ,
A,cikin kasala ta dan jawo filo zuwa kan ta, sai da ta kwanta da kyau kanta na sama yana kallon silin sanan .
Maganar Anty yafado mata arai,
Azuciyar ta tace kai badon aure hafin Allah bane da sai tace, gaskiya basu dace ba sam,
Ita wanan Sadiyar da bata da marmari sam duk yadda kake bata iya gaishe ka ko kuma ta nuna ma sakin fuska,
Ire iren tunanen da taitayi ke nan har zuwa wani lokaci,
Don kan ta tamike zuwa watsa ma jikin ta ruwa don ta dan ji sanyi,
Abinci da take dauki ta dawo ta ci sai gashi har da tuni anty tai mata ,
Duk yinin yau a kasalance maryam ta , wuni
Amma bata san ko may ke damun ta ba, kawai dai sai taji batajin wani kuzari,
Don haka, tun shiganta daki, bata kara fitowa ba har dare.,
Anty Dije ce taga cewa maryam bata fito ba don haka ta, tashi ta aza masu girkin, dare,.
Anty Dije ce,ta matsawa maryam ,da cewa tafito su ci abinci,
Dole badon taso ba tafito ,
Abinci kadan tazuba a plate, amma duk da zaman shi kadan ta kasa cin shi, sai tsakura takeyi tana cusawa,,
Ido Anty ta zuba mata har na wani dan lokaci ,can ta nisa tace, maryam may ke damun ki, ne wai,
Cikin jin wani irin nauyi maryam tace, ranan da na kwaso ne, yasakar min ciwon kai,
Wayar Anty ce tai kara alamar kira ,
Maryam wace, ke kusa da,waya itace ta mikawa Anty wayar,
Da dariya Anty ta karba sallama tana cewa mun kusa shan buki ashe Yusuf,?
Magana sosai sukeyi da Anty ida maryam ke jin yadda Anty Dije take lalashin shi, akan ya daure ya yi wanan abin da jibrin ke kokari ganin ya hada,
Maryam dake zaune a kasa, saman ties, sai ta dan kai kwance, a bayan kushin,
Ta sa kan ta, saman kujerar da take zaune a kusa da shi ,
Murmushi, tayi tana wasa da Abubakar wanda ke ta washe baki, a gaban ta,
So,sai suka dauki lokaci tana kwantar wa Yusuf da hankali akan kudirin su,
Acewar Antyn wai yin auren zai rage mai damuwar shi sosai,
Su,kayi sallama Anty Dije ta dan kalli inda maryam take tana wasa da dan yaron,
Tajima kafin tayi barci a ranan, bayan tabar falon tayiwa, anty ban kwana,
Alwala ta daro ta dinga jero nafilfilu masu ma,ana,
Sai ji tayi zuciyae ta yai wasai, kamar ba ita bace ranta yake a jagule,
Sai a lokacin ta, maryam ke ji a ranta bata jin komai gamay da zancen da akafada mata, ,
Yusuf ya iso kofar gidan Anty Dije, bayan sati biyu, da misalin karfe biyar na yamma,
Da sallama ya shigo cikin gidan alokacin maryam tana zaune cikin shigar shadda kamfala,
Shiri takeyi zata gurin bukin wata abokiyar ta na tun secondary school,
Zaune ta a saman kujera yar tsuguno tana ta faman gyaran fuska,
Dawani guntun broking mirrow, sallamar shi ce tasa ta tsaya wa daga fente fenten fuskan da takeyi,
Da yar fara,ar ta, a fuskan ta ,tare shi
Sannu da zuwa ta iya furtawa a hankali amma tana mai dukar da kai,,
Kallo guda yai mata yaga yadda ta koma kamar wata, classic baby,
Yaji wani yarrr amma sai bai ba da wanan abin yaji wani ma,ana ba,
Kafin ya karba mata anty dije ce tafito, a lokacin,
Ànty Dije ce ta fito daga ciki tana dariya da murnan ganin Yusuf a wanan lokacin,
Oyo, yo da mutane Lagos ne ko Abuja, sai da yai yar dariya na nuna farin ciki, yace ai nafi zama a Abuja yanzu,
Maryam ce ta tashi daga inda take ta dauko yar jakar kayan make,up din ta,
Tagaban Yusuf tayi bi inda kamshin nan nata kamar kulun yadaki hancin shi,
Ga dikin purple shadda kamfalan da tasa ya karbi jikin ta, tsab,
Daidai da zaman shi a lokacin ta dauko mai ruwa a cikin gora, hade da cup
A gaban shi ta dire kayan karo nabiyu kenan da wanan kamshin da ta budawa jikin ta yasa shi lunshe idon shi,
Thanks ya,furta a hakali kamar yadda ako yaushe maganar shi mai rowa ce,
Idon shi a lumshe kamar mai barci taji muryan shi yana cewa,