Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
Ita dai a rayuwar ta, wanan yariyar da yar ta sun mata wallahi
Babu ruwan su sam su duk yadda mutum yake basu kyamar shi ne ko ? Ba kamar sauran
ba,
Juyawa tayi ita ma tai adduan da maryam ta koya mata na barci,
Kusan satin shi hudu a can sanan yazo garin su inda zai gana da iyayyen Naimat na ainahi ,
Don ya gabatar masu da Ibrahim a matsayin wanda ke son yar so da aure,
Garin can ciki ne irin babakun arnan dajin nan ne wa yanda ko Christianity din basu damu dashi ba sam,
Da farko sunyi murna amma daga baya da suka ji cewa ai Ibrahim musulumi ne sai murnan su ya koma cikki
Nan da nan suka hau ihu cewa su sam basu yarda ba
Don suna da labarin irin irin wa yan nan musulumai din,
Sai da kyat aka samu wani dan tsoho daga cikin su ya sa su amince da zancen,
Don haka dama shi Yusuf yasan halin mutanen su na daji shi yasa ya shigo garin da shirin shi
Kyauntan goro da kudi yai taba manyan su sai addua irin na kafirci ya tashi,
Daga karshe sun yardan mai cewa ba komai kamar yadda ya irike ta agurin shi tun farko,
Ko yanzu yaci gaba da hakan ba matsala yana iya yai mata aure,
Da kwarin gwiwar shi ya dawo inda yazo yaci gaba da karasa abubuwan da,suka rage daga fannin shi,
A kwance take saboda yau kusan kwana biyu ke nan tana fama da zazzabi mai sa zafin jiki,
Duk yadda Anty taso akai ta asibiti sam maryam taki,
Saboda mugun tsoron alluran da take ji, arayuwan ta,
Hakan yasa Anty Dije ta kyale ta a gida sai paracetamol take ta din kira mata,
Koshi kamar zata amaye duk cikin ta idan ta sha shi, sai saa yake tsaya mata, a ciki,
Naimat ce ke ta faman da wainiya da ita inda maryam din sai godiya take zabga mata,
Ruwa masu zafi a ka bata ta watsa wanan ne sanadiyar samun yin barci da tayi,
Barci mai nauyi yai awon gaba da ita a lokacin saboda irin yadda taji jikin ta yai dan mata kwari,
Yau su Assalam suna gida suna wasa koda ya iso da murnan su da ihu a gurguje suka tare shi,
Yana murmushi ya rungumay su a jikin shi, Assalam ne ke cewa uncle ba ka zo mun je shan ice cream ba
Assalam yace har hawa saman lilo
Issalam ce tace ba Uncle din little Mum yakai mu ba ranan da ita, kuma,,,,
Wani iri yaji azuciyar shi amma sai ya dake kawai batare da ya nuna wani kaduwa ba,
Duk kowa da ya kamata ya gani na gidan ya ganshi sai ita kadai ce bai gani ba,
Ya rasa yadda zai tambaya ko ina maryam din take
Naimat ce yau ke zirgazirgan kawo mai abinci sabanin maryam din,
Da yaren su yace wa Naimat yau ina wanan yariyar ne what are they calling her,?
Wani mugun murmushi Naimat ta kumay a cikin cikin ta ,amma a fili sai tace
O, wo, Maryam
Ai tana daki bata da lafiya kwana biyu ke nan,
Da,sauri ya cire cup din ruwan da yakai bakin shi saura kiris ya kware da shi,
Cikin damuwa yace may ke damun tane haka ?
Fever ne nake gani saboda bata je asibiti ba balle a ji ko may ke damun ta,
Lokacin Ànty Dije ta iso gurin da dauke da tiren abinci a hannun ta,
Kara gaisawa sukayi inda take tambayar shi lafiyan Abdull
Kuma tana mai korafin may yasa bai zo da shi ba a gwada mai na hausa a gani, tunda ance convolution ne ke damun shi,
Aikin shi yayi watau murmushi, batare da yace komai ba, akan zancen,
Ashe little mum bata da lafiya, ne ?
Ya tambayi anty a takaice,
Wallahi fa kadai Yusuf kasan halin ciwon ta bata shan magani bata son allura kuma,
Cak ya mike yana mai cewa, yana ina ne ?
Yau ne rana na farko da ya taba shiga wani daki dake a cikin gidan duk shigowan da yakeyi gidan,
Saboda shi mutum ne mai kokarin tsare mutuncin shi baya wuce gona da iri,
Tambaya ya yi da cewa tana cikki ne ansa taba shi rai a bace mata,
Kai tsaye ya nufi hanyar shiga dakin inda Anty Dije ta daga kai tabi bayan shi da kallo,
Tausayi da kuma kaunar irin halaiyar shi na kulawa da na tare da shi ,
A kofar ya tsaya yana sallama a hankali, jin ba a ansa mai ba yasa shi kutsa kai cikin dakin,
Kwance take tana barci a cikin wani blanket brown, mai jikin mussa,
A hankali take mai da numfashin ta guda guda, Naimat ce ta biyo shi dakin,
Motsin da taji daga cikin barcin shi ya sanya ta bude, idon ta a hankali ta sauke su a cikin idon shi cak,
A rau nane ya kira sunan ta a lokacin da take yun kurin tashi zaune,
Sai dai ina nauyin jikin ta bai bari ta iya tashi zaune dan, sam bata jin dadi,jikin ta gaba daya a lokacin,
A hankali ta furta sannu da zuwa ya Yusuf, cikin daure da nuna jin zafin ciwo a fuskan ta,
Duk da a kwance take bai hana shi gane cewa ta ramay ba,sosai tai wani yar fayo da ita,
Gab da bakin gadon ya isa yana kallon ta,
A hankali yace maryam may ke damun ki ne wai haka ?
Kanta takara mayarwa a filo ta re da cewa babu komai,
A rau nane yace ki tashi muje asibiti a diba lafiyan ki pls,
Banza tayi da shi tankar bata ji shi ba, don in akwai abin da tai hating shi zuwa asibiti,
Anty Dije ce tashigo dakin itama a lokacin tun a kofa taji muryan shi yana cewa ta tashi su tafo asibitin
Baki ta tabe tace lalai kina da aiki maryam ace kina ciwo babu zuwa koda dan chemist,
Kina kwance ba wani maganin kwarai da kike sha,.
Kan shi ya dan girgiza yace bari kawai mutafi asibitin ina ga zai fi ai ko yana mai kallon maryam din,
Mikewa yayi yanufi kofar fita ya na cewa Naimat ta shirya ta su samay shi a waje,,
Batare da jiran jin ansar may zatace ba kawai ya fice da ga dakin,
Tsam tayi tai wani narai,nairai da ido kamar wace zatai kuka,
Tunda take ba,a taba yi mata irin wanan shi,shigin ba,irin haka,
A dadafe suka fito da ita, da Naimat, daga cikin gida,
Tsaye yake jingine a jikin motar shi,yana kallon yadda suke tafiya,
Wani tsadaden murmushi, ya sakar masu don ganin yadda suke tafiya tankar bata da jini a jiki,
Kanta ta kawar gefe cike da jin haushinsa, na yadda ya jagulamata tsari sai ta tafi hospital,
Likita ya auna ta yace high fever ne yai mata yawa,
Amma za ai mata,allurai da sauran test test, da ya kamata ayi,
Aiko gurin allura akai ta fama da Maryam, din sai da kyat da boni aka samu akai mata,
Sun sha dariya sosai shi da Naimat don har kuka sai da tayi gurin yin alluran,
A falon suka samu Anty Dije zaune nan suka zube har maryam din wace ke dan dukunkune cikin hijab din ta,
Sannu anty taiwa maryam tana sheda masu cewa ko zata sha tea ne,
Kai kawai Maryam ta girgiza alamar a,a bazata sha ba,
Yusuf yace a hado tea din a kawo mai zai bata da kan shi,
Kujerar da take a zaune ya zauna a mafi kusa dashi,
Cup din tea din yadago daniyar kai mata a bakin ta,
Da sauri ta kauda kaj tace a hankali cikin muryan irin ta mai jin jiki,
Zan sha da kai na pls
Ido ya kafe ta dashi inda babu shiri ta fara kurba a hankali tana dan lumshe idon ta,
Sai da tayi rabin kofin tukun sanan a hankali tace ta koshi,
Wani yaro ne yashi a lokacin yana cewa wai a fadawa maryam A, A yana magana da ita awaje,,
Gaba daya gurin yai tsit inda Naimat ce tace kaje kace bata da lafiya kaji,
Bayan kujerar ta koma ta kwanta kawai ta na mai , maida numfashi guda guda,
Yaron ne yadawo yana cewa wai yace yasani gaishe tane yazo yi, dama,
Amma wai ga wanan akawo mata leda ne shake da kayan fruit,
A gaban Yusuf wanda ko kallon arziki yaron bai ishe ta ba,
Batare da yadaga kai ba yace wa yaron kai zo nan dauki ledan ka kai gidan ku kace arabawa kan,nin ka kaji,
Basu Maryam da Naimat ba har Anty Dije saida hankalin ta ya dan tu humi Yusuf, din
Wanan fruit, din daine bai min ba a zuciya na bari zan samo maku masu kyau,
Wani ajiyan zuciya yayi gami da fesar da wata iska mai sauke relief,
Gyara zaman shi yayi wani irin mugun haushi ne yake ji a zuciyar shi,
Baban su Anty Dije ce yazo gidan don gaida maryan da jiki
Tunda Anty Dije tace mai ai maryam bata da lafiya har sosai,
Baba ya tausayawa maryama yadda yaga ta koma,
Anty ce ke fada ma Baba cewa yanzu Yusuf ya kaita asibiti,
Juyawa baba yayi inda Yusuf yake zaune yana kokarin hada maganin da maryam din zata sha,
Cikin tausar da murya baba yace kai wanan yaron Allah yai maka albarka kaji,
Ban san may zan maka in saka ma da alherin da kake muna ba,
Kai haba dai baba ai duk yiwa kai ne wanan baba idan ban maka ba wazan mawa irin haka
Dakai da iyalen ka kun nuna min kauna da yarda a fili baba bakku taba yi min wani abinda zai nuna min cewa ni badaga cikin zurian ku nake ba,,
Anty Dije ce take ce wa baba kako ji yadda akai mai, a gidan yarinyar da yake bida,
Ta, ce wallahi baba mugun zagi akan wai iyayen Yusuf ba musulmai ba ne,
Nan dai ta kwashe komai ta shedawa baba yadda akayi,
Baba sai faman kada kai yake yi don al,ajabin maganar da yaje ji
Baba yace wai ina ki ke, Dije ?
Ta amsa da cewa naam baba,
In har abin ya zama haka ga kaunar shi nan ai sai su shirya ko ?
,,,,, ,,,,,,,, ,,,,,,,,, ,,,,, ,,,,,,,,
SEENABU ZEEE IDRIS MAKAWA,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣3⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
IYAKA NA ABBUD WA,IYAKKA NA,STA,IN
Gyaran muryan da baba yayi ne yadawo da duk kusan wanda ke acikin falon da tunanen shi,
A hankali maryam wace ga zafin ciwo ga kuma nauyin maganar baba a tare da
Ta dago ganin ta ido taf da hawaye wani na bin wani,
Tace cikin kwantar da murya baba may zai sa ai mun wanan acikin yan uwana ?
Baba ko don ban da uwa a gidan zai ai mun irin wanan acikin mu,
Baba kasan cewa ina da wanda nake so zan aura don may za ai min wanan hadin tankar wace bata da gata,
Murmushi baba yayi kafin ya kauda kai ga kallon mamakin da yake yar tashi da yai bugun gaba da ita,
Sai baba bai taba tsan manin cewa maryam zata iya yi mai haka ba,
Maryam wani irin daci taji a zuciyar ta ya wani tokare mata makoshi
Baba kaji tausayi na kada kasani abin da ba ra,ayina ba,,,,,,,,
Bata kara sa maganar ba Anty Dije ta daka mata wani irin tsawa a lokacin,
Murmushi baba yakara yi yace maryam may yai zafi haka ,
Ki kwantar da hankalinki ki bi zabin da nai maki zaki ga alheri a cikjn sa
Ni mahaifin ki na bazan cutar da ke ba har abada, ke dace zan iya bugun gaba dake a hanlin yanzu ba tare da na samu wani matsala ba,,,,,
Kasa karasa maganar yayi saboda ta makale mashi ,,
Sai kawai yamike batare da cewa kowa kallah lahu ba ya mike yafita
Yusuf wanda ke zaune tun fara zancen kamar ruwa ya cinye shi bai ce kala ba,
Ya mike yabi bayan baba,
Don yaga ya fita lafiya a irin yadda ya bar gidan a cikin bacin rai,
Wajen minti talatin bayan fitan Yusuf da baba,
Ba wanda ya kara, magana kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi,
Jiki babu kwari maryam ta mike tayi cikin dakin su inda tana shiga ta rusa wani irin ihun kuka cikin ban tausayi,
Sai da tayi kukanta ta ci mai isar ta batare da kowa ya shigo gurin ta ba,
Anty Dije ce ta shigo dakin da sallamar ta gami da tura kofan,
Dauke take da kulan abinci da kwayoyin maganin maryam,
A kwance maryam din take a takure, guri guda can gefen gadon ta,
Maryam takira sunan ta, kamar wace zatai kuka itama don ganin irin yana yin da yar uwar ts ke ciki,
Wani irin kuka maryam din takara sawa wanda yasa jikin Anty Dije makyarkyata,
Saboda sam bata taba ganin maryam din ta acikin yanayi irin haka ba,
Hasalima dai sam ita bataso baba ya yanke irin wanan hukuncin akan yar uwar ta ,taba,
Maryam ta kara ambatawa cikin sarkewar murya tana cewa,
Zauna tayi a bakin gadon dab da yar kaunar na ya
Hannu takai saman jikin maryam din wace jikin ta a hanlin yanzu yai wani irin zafi radau,
Ido ta tsura mata sai kuma taji saukan hawaye ita ma a idon nata,
Magana ta fara yi kamar haka,
Kiyi hakkuri maryam da hukuncin da hukuncin da baba ya zartan batare da yin wata shawara akai ba,
A halin yanzu babu abin da zamuyi akai sai dai mu bari har zuwa lokacin da hankalin shi ya kwanta,
A hankali maryam ta taso cikin yanayin jin jikin da takeyi ta kwantar da kanta a saman ciyar yar nata,
Tace Anty da gaske ko dai baba baya so na ne kamar sauran diyan shi?
Da sauri Anty Dije ta toshe mata baki,
Hawaye wasu na bin wasu ta, ta ce maryam kada fa don rayuwan ki ya baci, ki kama sake maganar da bai dace ba akai,
Yanzu karbi magani ki sha maryam insaha Allah zan san yadda na bullowa baba yafita batun wanan zancen,
Anty don Allah kada ki bari a rabani da A,A saboda ina son shi kamar yadda yake so na,
Wani irin kululu cikin ta ya yi tace subbahanallahi maryam ai komai na Allah,
Murya kasa,kasa tace irin ta may jin jiki tace don Allah anty ki taimaka min kada baba yai min haka pls Anty,
Ta kara riko hannun Antyn na ta tarike su gam tana she,shekar kuka,
Da kyat Anty maryam ta samu maryam ta dan sha ruwan kunun da takawo mata tare da bata maganin ta don ta sha,
Da kyat ta hade maganin da take ji tankar tana hadiyan guba ne a lokacin,
Yusuf wanda ke jin kanshi tankar zai tsage mai gida biyu, a lokacin,
Tunda yafita waje ya hango baba har ya sha kwanar xuwa gidan shi, ko,
Don haka sai yaji sam baya da bukatar komawa cikin gidan,
Kawai sai ya sa kai ya shige motar shi kan shi yake ji yana mai wani irin dan ciwo, ciwo kadan kadan
Sannu sannu yana jin muryan maryam yadda take wa mahaifin ta kuka
Abin na,soya mai zuciyar shi ciwon kan shi ya na karuwa a lokacin,
Yana shiga gidan shi yaron gidan shi mai kula da gida yana ganin shi ya taso cikin murna
Amma yau sai ya kula da cewa Yusuf maigidan nadhi bai a cikin hankalin shi,
Don haka bayan sannun da yai mai sai kawai ya fara kwasan kayan maigidan nashi yana shiga da su ciki,
A hankali ya tura kofan falon sanyi da kamshi ne suka daki hancin shi duk da bacin ran da yake ciki bai hana ya jinjina wa yaron mai kula da gidan ba a irin yadda yake kula mai da gida,
Saman kujerar falo mai kama da Royal chair ya fada a saman kujera daya,
Yana dafe da goshin shi da yake ji yana kokarin tsage mai gida biyu,
Hannin shi guda dafe da goshin shi kan shi na dage yana yana kallon sama,
Idon shi a rufe suke ga kuma hannun shi dafe da