Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   38 / 84

111K to 114K   out of 251.8K words

ta yabayae wanda batasan dalilin faduwar gaban ba ,
A hankali ta sauko daga saman gadon cikin sanda, tana mai karba sallaman,
Sam ta manta cewa yar rigace a jikin ta saida taga ya kauda kai yana mai komawa baya,
Tai saurin komawa cikin dakin tadauko hijab din ta tayafa,
Zaune yake a saman kujera yana mai dafe da kan shi da hannu guda alamar gajiya, atare dashi ga kuma su Assalam nata faman mashi surutu,
Sannu da zuwa ta iya furtawa ta wuce wurin da fridge yake dan dauko mai ruwa,
Tai mamaki kwarai dataga cewa ya,shaye duk gora guda na ruwan da ta aje mai don ko cup bai dauka ba,
A kunyace maryam ta gaishe shi,
Inda ya karba mata ba wani sakin fuska kamar kullun,
Ta juya zata wuce don kiran anty a wayan ta, don ta,tafi gurin barka a makwabta,
Kamar daga sama taji yakira sunan ta, a wani murya na kasalance,
A tsorace maryam ta juyo, sai yanzu ta kula da kalar kayan jikin shi,
Wani yadine na maza fari mai taushi kamar lece,
Sai kyalin fari yadin keyi har yana kashe ido,
Saidai duk da tadan ta takure dan zaman motar da yadan yi,
Kanta ta maryam kasa don jin abinda zaice mata, saboda bazata iya jure kallon shi,,,
Muryan shi taji yana cewa ya jikin mama hope taji sauki sosai,
Tana wasa da yatsun hannunta ta hada su wani cikin wani
Tace taji sauki sosai yanzu Alhamdullah, ba,a magane cewa tayi ciwo ai,
Masha Allah yace,
Tana kokarin barin gurin kuma sai taji yana cewa, ga keys pls a shigo ma anty da kaya ciki,
Kayan tsarabane sosai kamar yadda yasaba kawowa yazo da su, Manja, Irish, sai Doya gudan mai yawa,
Almajirai tasa suka kwaso zuwa cikin gidan su inda Anty Dije ta samay su akofa gida tsaye tana sallamar yaran,
Tare suka shigo inda Anty take mai, korafin rashi sanar da ita, zuwan shi,
Kayan da tagani yasa tai tsai da maganar ta, takasa karasawa,
Wai kai Yusuf baka gajiya da dawainiya haka kulun,
Kai ya langabar kamar yaro karami yace ana gajiya da yiwa dan uwa dawainiya ne Anty, ?
Taji dadin maganar shi har cikin ranta sosai, don yadda yake nuna cewa shi nadu kamar yadda minin Anty yai mai nasiha bayan musuluntar shi,
Dacewa yadauke su tankar jini guda don yin haja zai sa yarage wa zuciyar shi radadi,
Sanan kuma mutum bai zama baida yan uwa aduniya
Don haka yazama yana sake jikin shi dasu har zuwa lokacin da yan uwanshi zasu huce dashi,
Abinci suke kokarin gabatar mashi amma sai ya, dakatar da su dace bazai iyaci ba don yana jin ciwon kai a halin yanzu
Daga Anty har maryam a lokaci guda suka waigo shi
Maryam wace sai, yanzu ta lura da cewa tun da yashigo yake dafe gishin shi wanda ita tadauka ba komai bane,
May ke da,muwar ka Yusuf, ?
Lafiya kalau nafito amma sai naji kawai na kusa shigowa Minna kai,na yai,wani sarawa,
Sannu suka dinga mai gaba dayan su har yaran yana amsawa a hankali,
Masaukin shi ya nufa don yaje ya dan watsa ruwa ya huta,.
Amma sai yaji kan nashi kamar yana karuwa ne,
Ibrahim yakira don tare suka zo dashi cikin sauri ya,samay shi,
Saidai yadda ya samay shi din ya bashi tsoro sosai don wani irin yake ji, a kan nashi,
Ga wasu jijiyoyin sun fito mai rada, rada a lokaci guda saman goshin shi,
Ibrahim yakira mahaifin shi, ya sanar dashi abinda ke faruwa,
Ba bata lokaci Abdulsamad ya iso masaukin na Yusuf inda kallo guda yai mai yafahinci ko may ye,
Sosai rashin lafiya Yusuf yake cigaba, a dan kan kanin lokaci,
Asibiti suka tafi cikin daren nan, don yadda yaje ji tankar kan shi zai tsage a lokaci guda,
Bayan yan "yan tambayoyi da likita yai mashi sai kuma su ka bashi magani da,sauran yan shawarwari,
Kamar kar su dawo masaukin shi abin sai kuma yafi da karfi,
Sai wani kugi yakeyi, yana tallabar kan shi ko kuma ha dinga bugawa kamar zai fasa,
Wayar shi ce tai kara don haka Ibrahim ya dauka dan ganin mai kiran don yasan cewa ba zai iya daga wayan ba, shi Yusuf din,
Anty Dije yaga anrubuta,,,
Muryan wani taji yadauka alokacin da take kokarin yi mashi sallama,
Ji tayi yana cew sorry mai yawan baya da lafiya saboda sanin dayayi kowaye anty dije ga Yusuf,
Cikin rudewa take ce wa subbahanallah, tambayar shi ta yi cewa yana ina, yanzu,?
Nan dai Ibrahim ya sheda mata gidan da Yusuf ke sauka a wani Lolo, Ested, dake GRA,
A motar kanin Illiya costume suka zo gaba, dayan su,
Maryam wace ke dauke da Abubakar a kafadar ta ta, da kuma wani basket,
Cikin rudewa anty dije ke fadar umm,uhmm subbahanallah,
Wanan wani irin ciwo ne haka, acikin dan lokaci guda,
Gaskiya wanan ciwon yakamata a san abin yi akai bawai abarshi a haka ba
Don dare ake ma gudu, kada abin yafi nan worse, ko ya kukagani,
Ibrahim yace ai yaga mahaifinshi yace yana zuwa yafita,
Bai fi minti biyu ba da fadar haka sai ga malm, Abdulsamad da mahaifin Jibrin sun shigo,
Tundafa nesa mahaifin Jibrin ke cewa subbahanallah a,a,a
Wani malami suka shigo dashi dan matashi ba wai wani babbba ba,
Tun bai taba Yusuf ba yace akwai matsala fa aciki,
Rukiya yai mashi sai,gashi yai wani irin atishawa mai karfi,
A, hankali yafara mai,da numfashin shi, guda guda daga haka sai barci yadan dauke shi,
Su Anty sunkai wani lokaci a tsatsaye suna kallon ikon Allah,
Saida dare yadan yi malam Abdulsamad yace ai su tafi gida har zuwa safe, su dawo,
Tunda zuwa yanzu yasamu barci insha Allah komai zai zo da sauki ai,
Duk kan su jiki ba wani kuzari suka iso gida zuciyar su fam da tambayoyi,
A lokaci guda yakoma wani dan feyau, dashi duk ya zube yawani je may ,
Kwance yake yawani dunkule guri guda, kamar jariri, aciki,
Mafarki yayi da wasu na binshi da wasu irin makamai masu cutar wa,
Da gudu suka biyu shi sai da zo gaban wani mutum mai wasu kaya shudi,shudi sai tsaya inda ke binshi a baya baya,
Kamar zai fadi sai ce La ilaha illah ant subbaha nika in,ni kun,tu minal zalimin,
Da karfi ya furta a fili yazabura ya mike zaune, wani iri yaji akan shi lokaci guda,
Zaune ya mike tana mai dafe kan shi sai wani zufa yake yi,kamar yana acikin ovon,
Addu,oi sosai suka dinga mai har zuwa rukiyar da karatun alkur,ani mai tsarki,
Barcin da yasamu wanan karon yadan yi nauyi so sai fiye dana farko,

Washegari tunda safe anty ta hada mai abin kari a cikin basket,
Amma sai maryam tace ai masa kunun kamu da kosai, don wata,kila zaifi son su da ruwan tea din,,
Ita kadai anty tabawa abin karin nashi takai don ita, babu motar da,zai zo da ita,yanzu,
Sai da gari yawaye ya haska sosai yasamu farkawa daga barcin,
Inda yai yar madifar rashim tashe shi da ba,ayi ba da guri har gari ya waye haka,
Zaune yake ya takure wuri daya can kuryan daki
Dai,dai kwanar wani dan standing drower dake a cikin dakin,
Falo ta tsaya ta aje kayan sai kuma ta ja tai saye guri guda,
Tana kallon Ibrahim wanda ke kokarin aje kayan saman dan dining table din da,ke dakin,
Ibrahim ne daga inda yake tsaye yake mata magana cewa, ta shiga aiyana nan zaune,
A nutse ta rika takawa har zuwa cikin dakin,inda yake,
Duk da baida lafiya sanyin A, C ne ya gauraye dakin, sai kamshim turaren shi da yake yawan shafawa akai a kai, watau turaren THE,,,
Babu kowa a dakin sai shi kadai,
Jin sallamar Maryam yasa shi dago kai a hankali, ya kalle ta, yana mai ansa mata sallamar ta,,,
Ban garen da yake zaune a takure idon shi a lumshe,
Yabude su a hankali ya sauke su ida tak ke tsaye a bakin kofa
Maryam ta kalla, shi sai, taji wan irin tausayin shi ya kamata lokaci guda,
A marairaice kamar mai shirin kuka maryam tace ina kwana, Uncle
Kamar yadda taji su Assalam naki ranshi da sunar,
Tace mai ina kwana ya jikin,
Kanshi yadago yakalle ta saida taji gaban ta ya fadi don yadda idon shi sukayi wani irin ja,
A hankali kamar mai jin zafin furta magana ya ansa mata da cewa lafiya Maryam,
Ya anty da yaran suke, wani iri taji lokacin dayake maganar don dagani yana jin jikin shi so sai,saidai daurewa da yakeyi irin ta maza,,,,



ZEEEE. ,MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Rubutun novel tankar wani fadakawa ne ga al,uma,
Duk novel dole akwai sakon da yake isar wa zuwaga al,uman,hausawa da musulmai, baki daya,
Don haka mu fahintar da matasan mu alheri a ko yau,she ba mu koya masu yadda rayuwa zata gurbace ba,,
Allah yasa mu dace baki dayan mu Allahuma Ameen πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘



Maryam takai wani lokaci tsaya daga inda take,
A hankali tace mai cikin sanyi murya mara sautin furtawa
Ga abin karyawa nan a falo, nakawo ma,, Anty tace ya jikin naka?
Saida yadan gyara zaman shi yakara dan dunkulewa guri daya, sanan
Ya dago jajayen idon shi da suka rine sukai mai ja jajir kamar garwashi,
Gabantane yakara ba da dam sai ji tayi tankar ba Yusuf wanda ta sani bane take kallo a lokacin,
A hankali Maryam ta isa har kusa dashi, kai kasa cike da jin nauyi Maryam, tace mai kasa hannun ka a goshin ka kadinga karanta,
Falaq da Nas da Iklas,, kowani uku, uku, katofa, a hannu, kashafe kan ka da shi,
Har zuwa jikin ka, sai,ka kara karantawa a cup kasa a ruwa, tare da Ayatul,qursiyyu,
Sai kuma a samu wanda zai karanta ma suratul,Jinn, gaba dayan,ta
Duk gankali shi ya tattara yake sauraron ta, don jin bayanin da take mai,
Tana kai nan tace mai Allah yasa mu dace Allah ya bada sauki,
Ibrahim wanda ke tsaya tun fara,zancen ya ce ma ogan shi ya kawo mai abin karyawa ne, a falon, aka aje,
Da kyat ya iya dan girgiza mai kai, a,alamar a,a,
Marayam tace mai a kwai kunu da kosai a ciki da ta damo mai,
A hankali yace wa Ibrahim yakawo mai kunun kawai bada kosai ba,
Ya,dan yunkura a hankali ya zauna da kyau,
Dan karamin kofi ne amma sai ya kasa shanyewa duk,
Da sauri maryam ta fita zuwa falon sai gata dauke da cup da goran ruwa,
A hankali ta dan durkusa gefen shi ta balle goran ruwan ta tsiya,ya ruwan kusan rabin cup din,
Ta kai cup din daidai bakin ta tafara jero mai addau,oi acikin ruwan,
Tsawon yan mintoci tana tofe ruwan dasu har zuwa inda takai aya takara dan tofawa,
Mika mashi cup din tayi tace ya sha yadan shafa saura,
Ido takafa mai har saida taga ya shanye ruwan saura kadan sai tace wa Ibrahim ya shafa mai aduk jikin shi,
Mikewa tayi a hankali da niyar barin kuryan dakin cikin mutuwar jiki,
Ido ya,bita dashi don bai taba sanin tana dakirki ba haka sai yau dayaga ta tausayawa ciwon shi sosai, har da bashi addu,a,
Muryan ta yaji tana cewa Ibrahim yai mai kamu a goshin shi ,
Daga haka tasa kai, zuwa waje, inda ta ke kokarin barin gidan don komawa,
Babu wani sallama taji kawai tayi karo da mace, tana kokarin shigowa gidan,
Aisha ce cikin wani dogon rigar dinkin material ja mai laushi, dinkin mai dogon hannu ya dane mata cas,
Ganin Maryam yasa Aisha yi mata wani irin mugun kallo naje wace,
Inda ta aje yar pos din ta da ta sa kudin mashin din ta tanufa,
Ke, daga, ina kike haka,?
May ya kawo ki,nan,? Zata kara magana sai ga Ibrahim ya budo labulen kofar yana cewa Maryam wai yace kice ai,mashi tuwon dawa ya ke so,
Wani mugun kallon ke baki isa bada amsa ba Maryam ta watsawa, Aisha wace ke tsaye tana mamakin ina wanan tsaleliyar budurwan mai zubin fulani tafi nan,
Jin muryan Maryam, yakara ruda ta a lokacin da taji Maryam nace wata irin miya za ai mai,
Juyawa Ibrahim yayi zuwa cikin dakin yadan leko yace wa maryam wai ta shigo,
Kusan a tare suka shiga dakin da Aisha wace ke wani irin shu,umin kamshi, duk gidan ya bure da shi,
A kwance tasa mashi kasan dan karami carpet din dake tsakiyar dakin ya kifa kan shi a filo,
Da kyat ya dan iya juyowa inda take yana ce mata,
Ki min irin wanan miyar da kika taba yiwa mama a Bobi,
Aisha wacce a lokacin har ta kara inda yake kwance tana kokarin zama, gefen shi gab da shi,
Maryam ta kara watsa mata harara tasa kai abinta zuwa gida,
Zuciyar ta fam da Allah waddai da irin halin rayuwa irin ta,su Aisha,

Maryam na barin gidan Aisha ta waigo inda Ibrahim ke kokarin kawar da cups din da aka bata,
Sai ce mai Aisha tayi wanan yarinyar yar gidan waye ita,?
Yar gidan Anty ce Ibrahim yabata amsa a,takaice,
Yusuf wanda tunda ta shigo bai,yi magana ba yace mai ya faru da kike tambaya, ?
A hankali tana kokarin kai hannu gare shi don wai ta taba lafiyar jikin ta ji inda sanyi ko zafi,
Cikin wani irin karfi ya hankade hannun nata tun kafin takarasa kaiwa a jikin shi,
Cikin wani irin murya yace mata
May ye haka pls, ?
Murya irin ta mai shagwaba, tace, to ba zan ji inda zafi bane jikin naka,
Tsuki ya ja yana mai juya kwanciyar shi ya kauda kan shi gefe guda,
Idon ta yakai ka inda yar brief case din shi take a yashe can gefen gado a kasa,
A hankali kuma takara daga ido tana mai karewa dakin kallon tsab,
Shigowar yan dattijan biyu ya banna wa Aisha tsari a lokacin,
Sam batai farinciki da shigar su a daidai wanan lokacin ba
Dattijo Abdulsamad na ganin ta ya ran shi ya baci don baya ra,ayin irin yaran nan sam, masu zubar da mutuncin su, haka,
Don yanayin shigar ta kawai ya ishi mutum yagane kowace iri ce ita don ba kunya a tare da ita sai fitsara

Dole tabar dakin cikin fushi don ganin manya suzo,
Gaisawa sukayi da shi cikin cijewa yake magana
Don shi kadai yasan yadda yake ji a jikin shi lokacin,
Sai wani zufa daya tarso mai daga jikin shi duk da sanyi A,C dake dakin,
Sun tambaye yadda yake ji tanzu sai yake sheda masu yadda ya kwana,
Sai kuma zuwan Maryam da taimai addua yashe sai yaji wani irin abu kamar a fisge mai wani abu daga cikin kun,nuwar shi,
Yace saikuma wanda tace Ibrahim ya shafa mai ajikin shi
Shi tun lokacin yake jin wanan zufan na tartso mashi, daga ko ina na jikin shi,
Juna suka kalla suka kada kai, don jin maganar tashi,
Mahaifin Jibrin yakalli kofa inda Aisha tabi yanzu zuwa waje yace,
Ita wanan din dai da naga ta fita yanzu, tai maka addu,an,
Ibrahim' da shi kan shi Yusuf sukace a,a a lokaci guda,
Ibrahim ne ke fada masu cewa Maryam kaunar Anty Dijen shi inda yake zuwa cin abinci idan yazo,
Yusuf din ne ya mike zaune a hankali yana maida numfashi guda guda gami da yin ajiyar zuciya,

A, kamshin gaskiya wanan al,amari akwai jinnu a cikin shi, ko sihiri,
Duk da halin da Yusuf ke ciki na jin jiki bai hana shi yin yar murmushi ba,
Ya dan kalli inda suke yana mai yin murmushin karfin hali ya ce ciwo ne kawai dai zo min a haka, baba,
Su ma dai murmushin sukai mai a lokacin don, sun san bai san komai ba, tukun daga sheri dan adam,
Ibrahim ya kalle cikin yar karamar murya yace mai ya kuna mai hearter yai wanka,
Da tai makon Ibrahim yasa mu ya mike zuwa cikin makewayi don ya dan watso ruwa ko zai ji sanyi a jikin shi,
Ita,ko Aisha ganin cewa wa yan,nan yan dattawan biyu basu da niyar fitowa yasa ta cewa bari taje ta dawo idan sun wuce,
Don ta sa rai acikin yar briefcase din nan nashi da tagani a yashe,
Ibrahim ko yana ganin Yusuf ya shiga wanka shima sai ya hau

38 / 84