Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
Harara ta sakar ma sa ta gefen ido tace,
Ko a kwai wanda zan wa aiki ne idan nadawo da guri,
Maryam ta shige dakin ta tana kokarin cire hijab din ta, amma ta tuna nen ina Anty taje cikin daren nan,
Don bata ji motsin ta a gidan ba,
Falon tadawo don ta diba dakin Anty tagani ko lafiya,
A hankali ya tako, har zuwa inda take tsaye kofar anty
Yana saye da kananan kaya sun karbe shi sun mashi mugun kyau,
Duk da a cikin dare ne kyalin agogon hannun shi ya wadatar da maigani yasan cewa gold ne,
Ganin shi yanufo inda take yasa ta saurin dan ja da baya kadan,
Gurin fridge yanufa yadauko ruwa a gora tare da hadawa cup din dake saman fridge din,
Baki da gaskiya ne kila ko yace a hankali, sai dai fuskan shi daure tamau,
Batare da tai magana ba ta kara danna mai harara, tace,
I don't want to talks more with you,
B/couse of your wickedness,
So please excuse me ta fada cikin murguda baki, ganin yayo kanta gadan gadan yasa ta saurin shigewa ciki da sauri,
Muryan Anty Dije ne ke cewa wai har yanzu maryam bata dawo ba ne ?
Kai ma da kan ka kake service din kan ka yau, maryam tana ina,
Kamar ba shi ba yace ina ga kamar sallah takeyi,,
Maryan dakejin ya kare ta tai mamaki sosai a,cikin zuciyar ta,
Kamar ba shi bane Yusuf Joseph wanda ta sani a da,
Mai daurewa bai magana bai dariya bai shi ga harkan kowa,
Kodai shigar shi musulunci ce ta sauya mai rayuwan shi
Muryan Anty ce ke kiran maryam din ciki daga murya,
Take gabanta ya fadi don tana gudun tai mata fada gaban Yusuf,
Sannu Anty da dawo tace adan daburce kamar mara gaskiya,
Haba maryam ga Yusuf zaune kin ki fitowa kiyi serving din shi sai da ya tashi da kan shi,
Cikin kwantar da murya tace, Na zata ba yanzu zai ci ba ai shiya sa ban fito ba na tsaya yin sallah,
Ke dai kan halin ki sai ke maryam haba yaushe zakibar bawan Allah azaune yana jiran abinci,
Daga haka batakara cewa komai ba itama maryam din ciki ta koma abinta,
Sai da ya gama takira maryam tace tazo ta kwashe kayan,
Murya kasa kasa ta yadda ba kowane zai ji abin da yace ba
Next time zaki yi bayani ai ,
ZEEE. MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
5⃣6⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Ya Allah ka kara muna imani da tsoron ka azukatan mu
Ya Allah kabu ikon bauta, maka bauta mai tsariki a cikin aiyu kan mu,
Allah ka karawa Annabi dara da daukaka,
Allah kataimaki musuluni karufa mai asiri duk inda musulmi yake a duniya👏👏👏
Ejoma da Ibrahim sun iso kamar yadda Abdulsamad ya buka ta dacewa su zo,
A gidan Ànty Dije aka sauke ta saboda babu halin zaman ta agidan su Ibrahim ko gidan Yusuf ,
Kasan cewar gidan Yusuf babu mace acikin shi
Can kuma gidan su Ibrahim din yazama kamar gidan sarakkan ta ne, yan zu,,
Maryam ta school ko da Ejoma ta,iso don haka dakin Maryam Anty ta kai Ejoma din,
So,sai taji dadin yadda Anty Dije ta tare tankar ta taba sanin, ta ada, can,,
Saboda haka bata samu wani matsala ba da take tunanen cewa za,a gwada mata kyama da farko,
Da yar sallamar ta tadawo gidan cikin gajiya kamar yadda ta saba shigowa gidan,,
A, zaune Ejoma take cikin shigar wata yar bakar buje daidai gwiwar kafar ta,
Sai wani riga mai dan gun,tun hannu, kanta yaci kitson attachment, mai ruwa biyu,
Kumbar hannun ta duk an fente shi da jakumba ja,
Wani irin kallon mamaki maryam ke mata tana wani dan ja gefe guda,
Kamar wace taga wani abin gudu ko kyama amms tans iya kokarin taboye,
Ejoma ce ke mata sannu da dawo wa saboda ta gane maryam ranan da suka je gai,she da Yusuf da yai accident,
Ejoma ta kara da cewa ya hanya, ya gajiya, sister, ?
A, daddare tace, ma Ejoma yauwa, sannu ko,
Dakin ta ta shiga bata zauna falon ba yadda ta saba yi idan tadawo,,
Turus tayi a,dakin don ganin kayan bakuwar mai dan gun,tun buje a dakin ta,
Wani wari hannci ya bugo mata dashi na man bleaching,
Hancin ta ta dafe da sauri ta nufi inda taje aje room fresh din ta, ta fesa ko ina,
Muryam Yusuf ne taji a falon yana magana da Ejoma cikin yare,
Wani irin bakin ciki ne ya ziyarya ci zuciyar ta a lokaci guda,
Anty ce ta shigo dakin don shakar kamshin room fresh din da maryam ta fesa tajiyo shi daga falo
Tasan halin maryam tana iya shuka masu tsiya yanzu,
Sunan maryam din takira wace ke tsaye tana mai da kwankon turen kamshin,
Maryam ta amsa da na,am anty ?
Anty Dije tace cikin tausa muryan ta,
Don Allah maryam kada ki nuna wa wanan bakuwar wani abin kyama ,
Kaunar Yusuf ne anzo da itane zata musulun ta zuwa jumma, ita ma,
Maryam zatai magana anty ce ta tare ta da cewa
Kin san dai Yusuf ya can,canci komai a gurin mu,
Saboda irin yadda yai wa iyayen mu mu,ma kin ga ko dole mu karbi nashi uzurin koba gaskiya ba,
Kai maryam ta daga a hankali alamar gaskiya ne maganar anty,
Sai a lokacin maryam ta tuna da irin halarcin da, Yusuf yai mata a kauyen bobi gurin mahaifiyar ta yar kauye,
Wani irin ajiyar, zuciya maryam ta sauke mai kama da ta wahala,
Fitar Anty Dije a dakin shine shigowar Ejoma dauke da wani ghana most go,
Kaya ne irin dinki na musulunci, zalla akayi mata saboda tasamu sauki ibada,
Cikin murna ta aje kayan a gaban maryam tana kokarin nunawa maryam cikin jin dadi,
Sister ki diba kigani wanan kayan zan dinga sawa yanzu, zan koma kamar ku ni ma,
Tafada tana yar dariya, zama tayi gefen maryam tana cewa sister na dade ina son inshiga cikin ku amma sai ban samu damar haka ba,sam,
Tun ina karama wanan ijab da kuke, saw a kai yana burgeni sose,
Har ma da saya nayi , ranan eh, nasha duka sosai a gidan mu,
Tausay taba maryam da take fadar haka dole maryam din ta maida hankalin ta gurin sauraren Ejoma din,
Ejoma tace ba karamin duka nasha ba fa har da kaini gurin wani malam Aminu yayi,
Malam din wanda yashe, wai in yarda da Aminu aka zai sa iyayyena su yarda da musulun,ta ta,
Aminu ya cuce ni sister sai yanzu ne nake gane mistake wanda nayi akai,
Takare fadin maganar cikin tsigar kariyan zuciya da nadama,
Tace Aminu har ciki yai min na aihu, da shi, infada maki daga karshe sai ya yi rejecting nawa,
Shine brother Yusuf yadauke ni zuwa gurin shi, har Allah ya kawo min Ibrahim,
Haweye ne suka dan biyu a idon Ejoma, wace ke kokari hade yuwun bakin ciki,
Duk da warin bleaching da maryam ke ji gurin Ejoma bai hana ta kokarin dan dafa hannun ta ba tana cewa tayi hakkuri akwai Allah,
Daya bayan daya suke fitar da kayan suna dibawa acikin yabawa, da irin kyau su,
Marym a za ton ta Yusuf ya wuce ko amma may ?
Sai ganin Yusuf tayi zaune a falo ya tasa computer shi a gaba yana aiki a ciki,
Kamar ta koma baya sai ta gane cewa ya gan ta sai ,yadai nuna cewa bai ganta bane,
Maryam taye fes da ita ta na saye cikin wasu siket da riga na lace,
Dinkin dinkin siket din mai dan fitar da sura ne, balle rigar da shima dinkin shi,
Irin fited din siket din ne ya wani dan matse ta dagwas,
Sai dan kwalin da ta daura tun safe amma yanzu da yake a gida take tadan turo shi gaba,
Ta daure bayan a can kasan gashin da ke daure da ribon
Sai fuskanta ya fito wani dan feyau da shi kamar wata, A, class lady,,,
Sai kamshin turen tana Madina da take yawan amfani da shi
Da ya gauraye falon sai kamshi take yi kamar kulun,
Takalman ta na gida plat shoes suke saye a kafar ta,
Anty Dije tana kitchen tana tuka tuwon dare da take yin
Maryam sanu da taron bakuwar ki fa,
Nagode kwarai da yadda naga kin kar be ta a matsayin ta wace bata sallah kamar yadda nasan sam bakya,son hurda da irin su,
A sanyaye ta ce mai ai bakon ka rahama ce, a gare ka don baka san alherin da yazo ma da ita ba,
Ya lumshe ido ya sa hannun shi guda ya rufe computer ta shi a hankali,
Kallon ta yake yi a cikin natsuwa na yadda ta jera mai magana a,lokaci guda,
Ita ko maryam daga haka ta wuce abin ga zuwa gurin da suke aje abinci, ta bude kulan don taga ko may Anty ta dafa masu da rana,
Shinkafa ce dafa duka, dai dai lokacin da anty ta shigo falon ke nan da goyon Abubakar a bayan ta,
Maryam sai yanzu na tuna cewa dafa duka nayi ina Allah Allah in dan dafa maki wani abu sai kuma na shafa sat, wallahi
Cikin sanyin jiki maryam ta ce yar ta ai ba komai zata jira har a gama girkin dare ta ci,, ai,
Yusuf na jin su sai bai ko kalli inda suke ba yai kamar baiji abin da,sukeyi ba,
Bai wani dade ba yafita lokacin duk suna ciki gaba dayan su,
Sai, dawo, wan shi suka gane dauke da ledoji a hannun shi,
Kayan su fruit ne da snacks sai drinks kala,kala, leda guda,
A sanyaye yake cewa anty ga shi nan abawa kowa ya dauki abin da yake so,
Kuma abar Assalam yadauki duk abinda ran shi ke so a ciki,
Duk da anty dije tagane cewa saboda maryam ya sayo don yaji ana cewa bazata ci dafa duka ba,
Mamaki tayi sosai da irin halin halarcin rayuwa irin na Yusuf ,
Sai tunda yafita lokacin bai kara dawowa gidan ba har zuwa dare,
Anty ce tai karfin halin buga mai waya don taji ko lafiya bai zo cin abinci ba,
Sai cewa Anty ya yi tayi hakkuri ba zai samu zuwa ba ya tafi wani guri
Dariya take mashi a lokacin tana cewa kodai ya tafi gurin sarrakuwar ta ce,
Maryam wani haushi ya kama don dai ita kawai haka taji bata kaunar Sadiya a rayuwan ta,
Tafi mai kwadayin ya samu wata yarinya kaunan Safiya da ake cewa Sariya,
Sariya tana da kyau ga kuma ilimin addini sosai a tare da ita,
Amma wanan sadiya din inbanda fashion da nuna tsawo bata san komai ba,
Muryan Ejoma ce, kecewa gaskiya sister bana son zance yariyan nan da brother sam, sam,
Wai kin san may rana ya kirata a waya yace ga maman Choima su gaisa,
Kawai sai cewa tayi ita wai batasan yadda zata gaida ita ba gaskiya,
Amma kin san may wallahi ni nagane nufinta sarai saboda muna Christian ne fa,
Kin san wasu mutane basa iya boye kyamar su a gare mu,
Shiyasa nima da yace a wanan gidan zan sauka da farko har na shiga damuwa amma sai gashi daga baya yake ce min da kaina zan bashi labarin halinkirki naku,
Maryam na,jin su sai tai dariya kawai don tasan ta kuru da an raina mata hankali
Don dai da farko tayi niyar nuna rashin mutuncin hada ta daki guda, da Ejoma da akayi,
Gurin da zata ajewa Ejoma kaya take dan gyarawa,
Sim din da ta dade da boyewa, ne tagani ya fado daga inda ta boye,
Cikin sauri ta,dauka ta na dubawa a hankali cikin dubara ko wani abu ya samay shi,
Sawa tayi acikin wayanta don ta diba ta gani ko zai yi,
Kira guda ya shiga cikin muryan shi mai kama da mai jin barci,
Assalamu Alaikum, wani iri taji a zuciyar ta,da sauri ta kashe wanya takoma saman gado ta zauna,
Text ta rubuta mai kamar haka,
Tai,mako a cikin addini sadaka, ce ita sadaka riga kafin matsifu ce,
Ka, kara taimako a saman taimakon da kakeyi ka kara ganin alheri a rayuwan ka, @@
Ya dade yana kara nanata karantawa yana mamakin mai turo mashi da wanan texts din
Don yadauka tunda ya musulunta andaina ke nan ,sai gashi yau yaga mai
Shine a tare da,Sadiyar shi zaune a cikkn motar shi,
Suna hira don tun da yazo garin yaune karo na biyu da yazo gidan su hira,
Wani kanin mahaifintane yazo zai shiga gidan nasu a lokacin
Ganin bakuwar mota akofar gidan na su ne yasa shi da,katawa bai shiga ciki ba kamar yadda yai niya, shiga.
Yaran yake tambaya ko motar waye a kofar gidan nasu,
Wani dan yaro cikin wasu dinkin yadi blue yaje cewa baban nasu ai anty sadiya ce da saurayinta,
Kamar ya wuce amma sai wata zuviya tace yahe yagani kowaye,
Ganin shi tafe inda suke yasa Yusuf yai saurin fito daga cikin motar
Har kasa ya tsugun na yana gaida kanin mahaifin nata dace shike bi wa mahaifin ta gurin haihuwa,
Bai karba gaisuwar da Yusuf ke mashi ba sai nuna shi da yatsu yakeyi,
Yace kai Sadiya ashe abinda ake fadi a kan ki gaskiya ne,
Yanzu ace kin rasa wanda zaki jawo muna sai wanan Furen Jujin,
Dam gaban Yusuf yafadi don jin sunar da aka kirashi dashi, wai FUREN JUJI,
Mutumi yaci gaba da fadin wa zaki jawo abin kunya ke da mahaifinki,
Don mutanen gari su ce kwadayi yasa muka baki Dan Ka Tuba, watau, (TUBBABE),
Kuka Sadiya tafara yi wi,wi don jin kanin mahaifin nata yafara nuwa Yusuf halin shi,na jahilai ,
Barin fada maki gaskiya badai acikkn zurian mu ba Sadiya,
Don babu mai kawo muna dan gin kafirai a gida wai jikoki,
Ya juya inda yusuf yake duk kai a kasa don ji yayi kamar kasa ta tsage ya shige irin yadda yake ji,
Yace wa Yusuf din tun wuri kaje ka bidi irin naka ba a gidan nan ba kaji,,,
Juyawa yayi ya shige cikin gidan nasu yana ta zabga masifa shi daya,
A, hankali ya juya bude mota yashiga Sadiya wace kanta yake a duke tana ta faman rusa kuka wiwi,
Da kyat Yusuf yai gyaran murya ya ce ta yi hakkuri tabar wa Allah komai yafi,
Ita ko sai hakkuri take ba Yusuf din cikin kuka tana mai mashi magiya cewa kanin mahaifin nata baida hankali sosai ne,
A dadafe sukayi sallama da juna yatafi zuciyar shi a cushe kamar zata fito mai,
Don irin cin fuskan da akai mai yai mai muni,har ji yayi kamar ba,zai iya tuki ba,,,,
Tunda yadawo yake zaune a falon shi ji yayi tankar kan shi zai tsage mai a lokacin saboda irin ciwon da yakeyi mai,
Ga zuciyar shi na mai wani irin soya kamar zata fashe mai,
Zaune yake asaman kushin ya mai da kan shi baya saidai kuma yadafe goshin shi da hannun shi guda,
Wasu hawaye madu dumi yaji sun gangaro mai a fusaka saboda tuna sunan da aka kira shi dashi, wai FUREN KAN JUJI,
Ya Allah ya furta a hankali yace Allah kai kasan dalilin yina a haka,
Nakuma gode maka ya uba giji na da ka bani ikon bin hanya madaidaiciya,,
Idon shi ya kara lumshewa yana ma zubbda hawayen bakin ciki,
May ye laifin shi a yanzu kuma bayan dashi da su duk matsayin su guda a gurin ubangiji,
Da wanda yai she kara dari da wanda ya shigo yau duk abu guda suke a gurin Allah subbahanahu, wata,ala,
Dangin shi kuma ko ya suke shi ba zai guje su ba saboda sune nashi,
Bai san ko daga cikin su akwai mai rabon shiga musulunci ba a ta dalilin shi,
Irin tunanen da yai tayi ke nan har dare ya raba tsakiya ya kasa barci, ga wani daci da yake ji a makoshin shi,
Sai zafi da yaji jikin shi ya fara yi kamar wanda fever ke shin kamawa,
Kiran wayan shi take tayi tun tana jin yana,shiga sai ya katse layin da kan shi,
Anjima kadan kuma takara kiran shi amma sai taji ya katse, wayan
Daga karshe