Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
goshin shi,
Maganganun da maryam taita jero wa mahaifin ta a gaban idon shi suke mai yawo a cikin kwakwalwa,
Baba may zai sa ai mun haka a cikin yan uwa na da kowa ?
Baba ko don banda uwa a gidan za aimun irin wanan a gidan,
Ritse idon shi yayi maganar na ci mai rai,
Baba kasan cewa ina da wanda nake so yake so na, zan aura,
Don may za ai mun irin wanan hadin tankar wace bata da gata,
Subbahanallah ya furta ya furzar da iska mai zafi daga bakin shi irin iskan da ke sauke relief a lokaci guda,
Shi Yusuf mai ke faruwa dashi ne haka da har zai zama abin kyama a lokaci guda,
May mutane ke kyama agare shi da har suke gudun shi haka
Yau gashi har da mutanen da a yanzu yake jin su tankar wani sashe na cikin jikin shi,
A gaban idon shi maryam ta nuna bata kaunar shi sam
Duk da dai shima din bawai kaunar ta yakeyi ba, amma ai bai dace tai wanan kalaman a gaban shi ba,
Wata zuciya tace, kyamar ka takeyi ita ma ai,
Da sauri kuma zuciyar shi ta raya mai da cewa kai yarinya ce shatab, shi ya kawo hakan,
Kawai sai yaji wasu hawaye masu dumi suna bin fuskan shi,
Yau shi Yusuf dake jin kanshi a cikin dubu akewa gudun asali irin haka,
Gam ya ritse idon shi mai yasa mutane ba su da fahintar maganar Allah ne,
May aciki don shi yana musulmi yan uwan shi na Christian,
Har kan su da ban tashi daban kuma ma ai yana fatan a ce su ma sun musulunta, din
Karan da wayar shi tayi ne yasa shi sauri dagowa daga cikin zurfin tunanen da ya shiga,
Anty Dije ce ke kiran nashi kamar ya share ta sai yaga rashin kyautawar haka fon dai ita batai mai komai ba ai,
Yana dauka batare da ko sallama ba yaji muryan ta tana cewa,
Yusuf kana ina ne wai baka shigo ba tun da zu gashi dare nayi,
Sai a lokacin da yaji tace hakan ne ya daga ido ya dubi window dakin yaga gari duk ya gauraye da duhu,
Zubur ya mike saboda sallah da bai yi ba na magrib da isha,i
Cikin yanayin magana wani iri kamar wanda ya dade yana jinya
Yace ina gida ai Anty bazan samu zuwa ba zan dan fita unguwa ne yanzu,
Ba,wai ta yarda da zancen shi ba ta amsa mai da cewa, ok to Allah ya tsare,
Ya ansa da fadar ameen yana mai kashe wayar shi saboda bai son yakara koda wani kalma ne a kai,
A dadafe ya isa cikin kuryan dakin shi bai tsaya komai ba yafada bayi don ya gabatar da alwala yai sallah,
Sai washegari yasamu shigowa gidan anty don ya karya,
Duk da bai ganta ba kawai sai ya tsunci kan shi yau da jin nauyin sukamar may daga Anty har Maryam din,
Saboda dai shi yanzu yasan cewa abin tausayi yake, don har da yar karamar yarinya tana kyamar shi,
Gaisawa kawai yayi da Anty sai yaji bama zai iya hira da ita ba yau sam irin yadda su ka saba yi,
Ita dai Anty Dije tsayin lokaci tana zaune a gefe tana shayar da yaron ta,
Babu wanda ya iya cewa kala daga cikin su falon yai shiru, in ka cire karar na,urorin dake aiki a ciki
Sai ko ajiyan zuya da,su keyi a jefi jefi,
Anty Dije ce ta kau da shirun na yadda taga Yusuf din ya daure fuska yakuna sauya mata yau
Tagumi ta dan zuba tana mai kura mai idon ta
A gogon dake daure a hannun shi, ta ga ya kalla,sai kuma ya ja wata yar tsuki,
Anty Dije ta dan dago kai ta dube shi tace haba Yusuf ban zaci cewa kaima zaka biyewa halin yarinta irin wanda maryam tayi jiya a gaban kowa ba,
Murmushin yake ya ka,karo a fuskan shi yace haba Anty ba wanan zancen ke damuna ba
Sada kan shi yayi kasa kamar mai tuna nen wani abu mai nauyi,
Kan shi ya dago daga kasan da yasada din yana mai kokarin kara kakaro murmushi,
Murya kasa kasa ya ce Anty na fahinci kowa na guduna yanzu,
Kasan cewa ta acikin al,umman hausawa kuma musulmai,
Maryam wace tun shigowar shi gidan idon ta biyu tana sauraren su,
Wani irin abune ya soki kirjin ta don jin abinda yace a gamay da kan shi,
Da sauri Anty Dije ta tare shi da cewa haba Yusuf ban taba tsan manin jin wanan kalamin daga bakin ka ba,
Maryam sam ba nufin ta ke nan ba a,kan ka, ita irin yadda baba yai matane a gaban mutane zai ce wai ya baka ita idan kun shirya,
Alhalin kuma yasan cewa tana da wanda take so tun farko a rayuwan ta,
Sakin wani murmushin takaici yayi yace, haba Anty akwai fa alamar tambaya a irin yadda maryam ta dinga magana a gaban baba jiyan,
Sanin halin ta da kowa yayi cewa yarinya ce mai ladabi ita,
Wani irin tausayin shi Anty Dije taji a lokacin da yake wa yan nan maganganun,
Da sauri tace Yusuf na fadama cewa ka daina irin wanan tunanen hakan zai saka shiga cikin wani yanayi har ka fada sabon Allah,
Baice kala ba again sai ma mikewa da yayi da nufin wucewa alokacin
Tambayar shi Anty tayi cikin kulawa kamar yadda yaya takan yiwa dan kanin ta idan ya shiga wani hali,
Tafiya zakayi yanzu baka bari har zuwa anjima idan rana yai sanyi,
A nutse yace mata gida zan koma in dan kwanta,
Sai dai abin da bata sani ba shine cewa daga nan gidan ta Abuja ya wuce direct.
Sai zuwa dare da bata ga ya shigo ba tai mai waya yake sheda mata cewa ai gashi ya kusa shiga garin Abuja
Sosai ran Anty Dije ya baci sai kawai ma taji bataji dadin wanan zancen da baba yayi ba,
Don kada ya tarwatsa masu zumuncin su da suka dade sunayin abin su gwanin ban sha,awa,
Tafiyan shi ya yi wa maryam dadi sosai don koba komai zata dan samu enough time na tunane ta dan sake jikin ta,
Sati biyu da wannan zance maryam ta dan sake jikin ta yanzu saboda taji ba wanda ya kara zance,
Saidai matsalar ta kawai shine baba, don har yanzu bai karba mata gaisuwar ta kamar da,
Amma hakan baisa ta damu ba don ta san cewa wata rana zasu shirya ai,
A cikin haka Anty Dije ta samu baba da zancen don ganin irin yadda ya dauzafi ga maganar,
Baba yace duk wanan abin da kikaga nayi Dije don Allah nayi sai kuma na biyu don ke da shi yaron,
Yanzu wa kike ganin zai dauki yar shi yaba shi kai tsaye a irin yadda aka san halin mahaifin shi,
Amma idan maryam ta aure shi duk wani mai ganin cewa baida asalin kwarai zai daina hangen hakan,
Ko don ita matsayin ta na yar kasa zai sa jama,a da dama kara hurda dashi har addinin,shi yakara karfafa,
Ajiyan zuciya Anty Dije tayi don jin irin hikimar da yasa baba yankewa yar kaunata dakuma Yusuf wanan irin matakin,
A gaskiya itama zata dauki nata irin matakin gurin, ganin cewa ta yi wani abu akai don karfafa wanan zancen,
Yusuf yana Lagos saboda wani aikin da ya tafi yi gurin, depot din su,
Don yanzu ya koma harkan business din mai sosai fiye da da,
Don an gyara masu gurin matatar man su, da suke business tun farko,
Wayan Anty Dije ne ya shigo mai alokacin yana tsaka ga aikin a cikin wasu takardun su,
Fuskan shi dauke da yalwataccen fara,a tankar Antyn tana kusa dashi a,lokacin,
Nan ya shiga sosai ranan sukayi hira inda yake sheda mata cewa yanzu businesses din shi na Lagos ya tashi sosai zai ci gaba da harkan man petroleum,
Tai mashi murna sosai sai daga karshe ne takira sunan shi a cikjn natsuwa, hakan ya tabbatar mai da cewa za tai serious magana dashi ke nan,
Anty Dije tace Yusuf may yasa yanzu ka daina duk wani korin irin yadda kake yi gurin sada zumunci da sauran su,
Shiru yayi a lokacin da take maganar tankar bai saman layin sai da tace hlo taji ya ansa, sanan ta tabbatar da cewa yana saman layin,
Amsa mata yayi da fadi, No, wallahi ba hakana bane,
Kawai dai aiyuka ne sukai min yawa amma da zaran na samu chains zan shigo insha Allah,
Shigowar su Assalam yaji muryan su ta cikin wayar,
Hakan yasa shi cewa abashi yaran su gaisa da su,
Sosak sukayi hira da su Assalam din inda yaran suka ce mai ga Anty Naimat da little Mum,
Maryam da ke kokarin kwankwatsa waken da za suyi miya a cikin turmi, tai wani irin saurin juyowa cikin watsa masu harara,
Ya dade da Naimat suna waya sai daga baya taba maryam din,
Wace a lokacin tana bakin famfo tana wanke kayan miya,,
A hankali yakira sunan ta yana mai tambayar ta lafiyan jikin ta inda ta ansa mai da cewa da sauki
Ya kuma tambaye ta ya karatu ta ansa shima da fadin lafiya lau,,,,
Sai kuma shiru ya biyo bayan zancen don baida a bin fada mata kuma,,,,
SEENABU ZEEE MAKAWA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
6⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
IYYA,KA NA,ABBUD WA,IYYAKA, NA,STA,INN
BAZAN IYA MAN,TAWA DA KE BA YAR UWA MASOYIYA, (ANTYN NICE,)
Wanan wayar da sukayi yakawo karshen nauyi da kunyar da kowan su ke faman dako a cikin zuciyar shi,
Da sannu suka dan fara sakewa da junar su kamar yadda suke a da, indan yai waya da kowan su, zai gaisai,
Wanan shigowar ba karamin shigowa yusuf yayi ba don yashigo da shirin auren Naimat,
Sosai jama,a ke murna da zuwan shi saboda irin yadda mutane ke a cikin matsuwa,
Baida wani hutu atare da shi kasan cewar shine uban amarya da ango gaba daya,
Gida na musan man ya sai masu inda ya mallakawa Ibrahim shi a kyata,
Anty Dije ita ce uwar amarya don itace komai na amarya,
Sosai take gyaran amarya irin gyaran mutanen kasar kwantagora na asali bawai na zamani ba,
Don ita da kanta tasa a samo mata ganye don yin hadin da kanta,
Kamar yadda ko wace amarya yar asali take zama yayin zaman lalai haka itama Naimat ta koma inda tasha wankan lalai da turare sai sheki takeyi,
Su maryam da safiya da wata sister din mijin anty sune a matsayin abokan amarya,,
Sai zirga zirga sukeyi akan duk wani abin da ya dace suyi,
Shigar wasu shadda maryam tayi masu ruwan pink colour,
Sai wani farin lece da akai mai ado dashi kamar flower,
Farin gyale ne tadan yafa a kan,ta da takalmi farare masu dan tsini a baya,
Daga gurin sayen kayan da zasu rabawa friends din su da suka gaiyata suke tare da safiya amma safiya tadan tsaya sayen wasu kayan
A gajiye ta shigo falon hankalin ta a kwance tana mai cewa wassshhh wallahi anty nagaji ga mai manshin din da na hau yana ta tsula gudu da,,,,,
Makalewa maganar tai mata don ganin Yusuf wanda ke zaune,a falon su biyu zaune shi da Anty Dije
Sam bata tsan manci ganin shi ba a folon don motar shi bata gurin balle tagane cewa yana cikin gidan
Daganin ya na yin zaman su ,kasan cewa magana sukeyi mai muhinman ci ,
A tsakanin su don Naimat ma bata gurin alokacin,
Tun bayan wancan rikicin, sai yau sukayi ido biyu da junar su shi, da ita,
Kamar ta juya baya ta koma amma sai ta daure, kawai tasa kai ta shiga,
A sanyaye ta yi sallama ta shigo falon idanun ta sunyi, wani lub da su saboda kwaliyar da tayi,
Fuskanta babu yabo babu fallasa, ta,gaishe su a cikin girmamawa,
Yusuf ne ke cewa daga ina take haka take cewa ana gudu da ita a mashin,
Maryam ba kyaji ko ?
Har yanzu baki bar hawan mashin ba ko a dinga wulwulaku a titi,
Yakarasa zancen shi a cikin nuna bacin rai
Juyawa yayi inda anty take yana mai facing din ta ya ce,
Anty ku koyi tukin mota mana pls a , aje maku mota a gida yafi hakan ?
Dariya ma maganar shi ya ba Anty a lokacin irin yadda ya hakikance yana faman fada,
To Yusuf in banda abinka abinda mutum bai,dashi ai sai ya yi hakkuri,
Maryam na jin yadda yake ta faman sababi sai kawai ta juya, zuwa dakin su,
Duk sauran zancen da sukeyi a kai maryam wace ke ta ciki tana jin su duk ranta abace,
Don dai ko A,A wanda zai aure ta ai ba zai zake yana mata irin wanan masifan ba,
Shigowar safiya a dakin ita agajiye yasa ta dan sakewa ta daina kumburin da takeyi,
Sosai suka baje kayan da suka sayo don na su irin sha,anin suna dibawa, gaba dayan su har anty,
Muryan Anty ce maryam taji tana kiran ta bayan sun gama kallon kayan da arranging din komai,
Da sauri maryam din tace naam Anty,
Bata kara cewa komai ba sai kuma tai shiru tana mai kurawa kaunar naya ido,
Kamar mai tunanen wani abu can sai tace, wa maryam din,
May yasa dazun Yusuf yana maki fadan hawa mashin kika wuce ki ka barshi batare da kin tsaya ba,
Wani irin tsoro ne ya lullube maryam din don jin an anbaci sunan Yusuf wai kuma tai mashi laifi,
A hankali maryam ta janye hannunta asaman wani kwalin sweet da tadora akai,
Kanta ta dukar kasa tana dan wasa da yatsun ta a saman ties,
Karo na biyu takara kiran su nan ta tace, kina jina kuwa,
Maryam sam bana son ki nunawa Yusuf wani mugun tsana wanda har zai zaci ko kyamar,shi kike ji kamar yadda yake zato,
Dan juyawa Anty ta yi inda Safiya take tana mai,cewa don Allah dai safiya idan mutum,
Ya nuna cewa ya damu da kai a matsayin dan uwa ko kuma wani nashi can,?
May ya kamata kai kayi mashi a lokacin,
Safiya tace kai ma kabashi kulawa mana fiye da yadda ya nuna ma,
Masha Allah, inji Anty amma ita kinga sam bata gane hakan ba a rayuwar ta,
Kin gani yadda ki kayi dazun sam wallahi bai yi daidai ba
Hakan zai iya fusata shi yadauki zancen da baba yayi akan ku bilhakki da gaskiya,
Kin ko san cewa baba zai iya yin komai ba tare da amincewar ki ba,
Tagumi maryam tayi tana sauraron Antyn nata acikin natsuwa,
Inda Anty da safiya sukaci gaba da kawo mata musalai kala,kala akan zama da mutane
A sake murya a raunane tace yanzu yaya zanyi anty in kaucewa gudun magana,
?
Abinda anty ke son ji ke nan dama sai tadan gyara zaman ta tace,
Ki nuna mai cewa ke yanzu baki da dan uwan da ya wuce shi,
Shawaran ki, ki dinga sanar da shi don jin ra,ayin shi
Kissa dai irin ta mata zaki dinga gwada mai tankar ba komai a tare da zuciyar ki,
Kinga koda baba zai kara waiwayan zance shi Yusuf din da kanshi zai nuna wa baba rashin dacewar hakan a tsakanin ku,
Cikin sauri maryam ta daga kai takalli anty dije tace,
Amma anty baki ganin idan baba yaga haka zai zaci cewa ko na yarda ne,
Murmushi anty dije takarayi tace, ai shi Yusuf din sam bazai yarda har hakan yafaru ba,
Ke wayo fa za muimasu shi da baba din , ke dai iyaka kiyi kokarin nuna mai cewa ba komai na jin kyama a tsakanin ku,
A sanyaye maryam tai ajiyan zuciya tace nagode anty,
Wallahi har naji wani sanyi a zuciya ta
Anan sukaci gaba da hiran duniya saiko ga Naimat wace ta shiga family house din su mijin Anty ta shigo gida,
Duk hiran da sukeyi ita maryam hankalinta na can tana tunanen yadda zata fara bullowa Yusuf din,,,
Zaune take saman kujera mai zaman mutun biyu,
Hannunta rike da waya tana cewa safiya tazo mata da, wani mango drink datake yawan son sha,
Safiyan na cewa ita bazata koma baya ba tunda ta wuto gurin ko,
Tsuki taja tana cewa macuyiya don kawai kimin keta kin san ban shan duk irin da kika,sayo zaki ce bazaki sayo min ba,
Muryan shi taji daidai saitin