Furen Juji Book Compelet Zainab Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   36 / 84

105K to 108K   out of 251.8K words

rike da wani leda da suka dauko ta dan kwantar da kai zabban tausayi,
Saida yaga cewa an zaunar da ita, a hankali cikin motar sannan ya dan dago kai ya kalle ta,
Fusksnta duk ya canza yana yi saita baka tausayi
Kwana guda a kauye duk ta jemay tayi wani irin fau, da ita,
Badake za,a tafi bane don bamu san ya abin zai kasance ba a can,
Tajuyo ta dan kalle shi alamar kamar zatai kuka, alokacin,
Cikin rawar murya tace, bari su tafi zan shigo motar haya yanzu in samay ku,
A raunane yace no, bari dai abawa namiji kudin mota ya samay ko,.
Don mata biyu da maza har uku ne suka matsa suka shige a wanan dirkekiyar Jeep din,
Wacce tunda aka saye ta bata taba daukar loadi irin haka ba sai yau,
Da sauri karamin yace shipa gaskiya ba zai sauka ba don dai dashi za,a tafi,
Karamin ne yace ba matsala barin sauka, maryam da duk wanda ke cikin motar basu so hakan ba,
Saboda Awalu yana da kokari sosai don kusan komai shike zuwa nemowa ,
Ya na sauko Yusuf ya ciro kudi dubu biyar cur yace ka shigo mota kasamay mu a asibitin tagwai pls,
Ai ba kunya kuma sai Isah yayan shi da yace ba zai sauka ba,
Yai caraf yace a,a shima motar kasuwa zai shiga ya fasa bin su,
Wata mata tace amma dai kaikan ,Isah anyi mutumin kawai,
Baka ji kunya ba, yace kedai kikaji dan nace kawai na fasa nima,
Dariya suka sa alokaci guda duk wanda ke gurin, shiko isah ko a jikin shi,
Shima dubu biyar aka bashi kudin motar kamar yadda akaba Awalu,
Hakan yasa su samun fili su wala yadda suke so batare da sun matse ba,
Baya maryam ta zauna tare da sauran matan dake baya,
Yusuf ya tada motar shi inda suka fara tafiya sauran mutane na ta masu fatan adawi lafiya,
A,hankali yake tuka motar cikin gwanin ta da kwarewa,
Babata wani lokaci suka isa, cikin gari direct asibitin suka nufa,
Sai da yafara fita yaga likita ba bata lokaci saiga wasu nurse da keken daukar mutane suka kama mama suka wuce ciki da ita,
Suna shiga Maryam bata tsaya ba saboda duk a rude take a lokacin,
Mashin ta hau sai unguwar su ganin ta kawai anty tayi, a lokacin,
Da mamaki anty ke kallon ta saidai kafin tai magana tagane cewa maryam a cikin tashin hankali take,
Dan natsuwa ta tattaro guri guda sanan tafara bawa anty bayanin zuwan su da kuma yadda suka kwana da maman jiya,
Ita ma Anty Dije nan da nan ta rude ta hau shiru don su tafi,
Saida suka fara zuwa gurin baba suka sheda mai tukun ,

Sannan suka wuce zuwa asibitin, ba tare da bata lokaci ba,
Sun samu an daura mata ruwa, ana mata kari,
Amma tana barci a lokacin don haka suka dan fito daga waje don gudun kar su ta da ita daga barci,
Ganin yadda suke a tsa,tsaye tasa anty Dije shawaran zuwa gida don dauko masu, tabarma da dan sauran abin bukata,
Tare suka fito ita da maryam a lokacin tanawa maryam fada cewa ta kwantar da hankalin ta dibi yadda ta koma jiya zuwa yau,
Motar Jibrin ce agaba sai ta Yusuf din, nabin shi a baya,
Ganin su yasa Anty Dije tsayawa don su gaisa taimai godiya,
Both suka ga an bude tabarmi ne har da su filo sabbi yasayo masu sai kuma dangin kayan abin ci da sha,,
Baki bude Anty Dije ke kallon shi cikin mamaki da abin da idon ta yaganar mata,
Fa murmushi ya karaso gurin dauke da kaya a hannun shi wanda karasowar tashi tai daidai isar maryam kusa tana mai mika hannuwar ta takarba,
Maryam tana barin gurin Anty Dije tace Yusuf waban irin dawainiyar haka, ?
Saida yadan goge hannuwar shi da kyale, tukun sanan ya na murmushi yace,
Anty wanan ne kawai irin damar da mutun ke samu ya taimakawa mabukaci, wallahi,
Idan ba anan nazo naga mutane acikin yanayi ba a ina zan gansu a can tunda ba shiga cikin mutane mukeyi irin haka ba,
Tausayi so,sai, maganar shi taba Anty Dije wace sai faman kada kai tajeyi don gamsuwa da zancen shi,
Tace to amma dai ai zaka fada min kaga sai in dauko nawa agida ko, basai kasawo ba,
Yadaga hannun shi guda guda na acikin aljihun shi yacewa anty dije,
Haba dai No, no no, ai ya zama wahala hakan kawai a siyu yafi sauki,
Ajiyan zuciya kawai ta samu yi tana mamakin halin rayuwa irin na wanan bawan Allah,
Maryam ce ta karaso gurin tana rungumay da hannayen ta saidai fuskanta acikin damuwa yake,
Alokacin Yusuf kecewa Anty Dije likita yace malaria ne ke damun ta so,sai shine sukuma wai sun cire mata hakin wuya,
Ido daga anty har maryam suka fitar don mamaki jin maganar,
Yadan kara gyara tsauwar shi ya na fuskantar su duk su biyun yace,
Wallahi Anty mutanen mu na kauye suna kashe kan su da bata,
Shiyasa bature ke cewa African people killed themselves by risks, before there, time,
Kawai sun tashi kashe tane da lokacal treatment fa,
Tun jiya dana ganeta hankalina bai kwanta ba,sam, wallahi,
Yakare zancen yana dan siririyar, dariya ba mai tsawo ba,
Kai, kai kauye dai gaskiya akwai jahilci sosai wallahi,
Maryam tace cikin siriyar murya,
Yanzu mai likita yace akai ?
Dan kallon gefen da take ya yi sai yaji duk yarinyar takara bashi tausayi,
Saboda duk yadda mahaifiyar ka take kana son abin ka,
Yace nop likita da wai zai bamu magani akoma ai treating din ta a gida,
Sai nace mai a,a yabarta kawai a nan mugani ko zata dan kara covering, zuwa gobe sai mu koma
Ya kalli inda anty dije take tana gyara goyon Abubakar yace ina ga haka zai fi da ace su,koma gida a haka,
O, O YUSUF mun gode kwarai wallahi Allah dai ya saka ma da alherin sa
Haba, haba anty ki bari dan Allah wanan ai ba komai bane dai,
Maryam ce ta hango mijin maman ta zai je bidan ruwa ya kewaya, wa,
Da sauri maryam tanufi gurin inda taga ya dauki wani tsohon buta, takarba taje samo mai ruwan,
Ido, suka bita dashi gaba dayan su yarinyar tana basu tausayi duk da tana kokarin danne damuwar ta,

Shi ya maida Anty Dije gida don taje, ta yi girki, kafin yara,su dawo saboda bakowa gida,
A hanyar shi ta dawowa ne ya ratse ya sai masu ruwan GOJE WATER, mai yawa da sabuwar buta, Da nama gassasa mai yawa tare da drinks, sai su fruit kala,kala,
Maryam wace ke zaune saman steps din da zaka hau ka shiga cikin asibitin,
Tadan yi tagumi da hannu ta biyu ba,abin da takeyi sai tunanen halin da mahaifiyar ta take ciki,
Ga talauci ga wahala, ga kuma ciwo yazo ya shigeta haka lokaci guda,
Badon Allah ya gyara ba da kilama surasata, ta wanan ciwon
Maryam bata ga lokacin da ya iso ba don tati nisa a tunanen da takeyi,
Saidai ganin mutum da tayi a gaban ta wanan karon yati wanka ya cire kanan kayan da yasa a jikin shi,
Sannu da dawo wa ta ce mai cikin , karamar murya mai nuna damuwa,
Ledar dake dauke a hannunshi ta mike tana kokarin karba daidai lokacin da mijin mama ya fito daga cikin asibiti hannun shi dauke da tasbaha,
Ko bata bude ba kamshin da ya daki hanncin ta ya sanar mata cewa gassan nama na cikin ledar,
Gurin da masu jiya suke zaune ta nufa da ledar, duk sukayo mata caaaa da ido
Don suga komay aka dauko a cikin ledojin da ya shigo da su,
Tunda tafara budewa sai da gaban ta ya fadi don ganin yawan abubuwan da yakawo masu,
Shim shi wani irin mutum ne wanda baida jin zafin kashe ma wani kudi,
Sun dade cikin dakin da aka kwantar da mama tare da likita da mijin maman,
Dole haka tasa kai ta shiga don ta kai mata fruit din da nama kozata ci,
Mijin mama ne yake cewa maryama cikin tausayawa, ina ganin fa yau duk baki ci komai ba, fa,
Murmushin yake tadan yi tace na karya a gida ai kafin mu fito da,safe,
Zai kara magana sai wayar ta dake a cikin yar jakar ta tai kara,
A,A dun tane yakira duk da akwai mutane a dakin amma sai tadan daure tace hlo, daga haka tai hanyar fita waje,
Ba gaisuwa ko wani abu sai cewa yayi a gadaran ce ya mai jikin,
Da sauki tace mai a hankali, gamu nan asibitin tagwai, da ita,
Tun yaushe kuke nan ya tambaya cikin dan nuna concern din shi,
Tace mai yau da safe ne aka kawo ta saboda jikin nata ya kiya,
Ok to zan shigo idan na rarage abinda nakeyi, Allah ya sauwaka daga haka ya kashe wayar shi kawai,
Sam ta mantacewa a kusa da kofar dakin ta tsaya tana kashe wayan tadago kai sai caraf idon ta akan na Yusuf wanda ke kokarin,bude wani ledan magani, don aba mama,
Jibrin ma wanan karon a cikin shiga ta mutunci shima ya shigo dakin yana mai gaida mama,
Muryan Yusuf ne ke sallamar su yana cewa zasu dan je wani guri su dawo,
Maganar Safiya ce ya fado mata arai azuciyar ta tace lalaima can zasu tafi ke nan gurin ganawa da mahaifan safiya din,

Sai kusan bayan la,asar sosai A,A yazo asibiti cikin shigar shirt sky colour, da wando baki sai tie da yasa a wuyan shi kawai,
Maganar shi a gadarance yake yin shi yana mai nuna cewa shi din wani ne,
Tambayar mujin mama takeyi yasukabar har ciwo ya ci ta haka gasu ba wani nisa suke dashi ba da gari,
Yace ai yanzu ba,a wasa da ciwo komai kan,kantar shi,
Sai mijin mama yace to ko muna son zuwa asubiti da may zamu zo,
Ko yanzu aida taimakon Alhajin nan ne muka samu mukazo in bashi ba ai da saidai yadda Allah yayi kawai,
Kagashi nan da nan yagane cewa sai munzo asibiti ba na gida bane yanzuma gashi tasamu sauki,
Da har zamu koma sai shi Alhajin tace mu bari har gobe sai ta dan kara samun sauki,,
Lokacin jin tana ta cewa Alhaji Alhaji yasa shi waigawa gurin maryam wace ke dan rakube a gefen bango,
Yace waye yake magana halan sai cewa maryam tayi a hankali,
Yusuf ne, yakawo ta,
Nanata sunan yayi yace Yusuf,
Wani Yusuf ke nan, wai halan, ?
Tace mai Yusuf wanda ya musulunta mana, maizuwa gidan mu,
Ok Joseph ?
Kai kawai ta gyada mai alamar eh,
Mijin mama yace a,a a daba musulumi bane shi din,?
AA yace kafiri ne yazo ya musulun ta koda yake har yanzu bawai an yarda da musuluntar nashi ba ne ai,
Sai a lokacin maryam tadaga kai ta kalle shi saboda kalamin da ya fadi,
Sai mijin mama yace a,a kai ko may za,aiwa shakka aciki tunda dai yariga ya musulunta,
Mikewa yayi tsaye da kyau daga rankwafawar da yayi saman karfen gadon da mama take a kwance,
Yace Arne fa ko ya mysulunta ai ba abin yarda bane,
Jin kalamai da yakewa Yusuf ne sai taji kawai bataji dadin su ba sam,
Don haka sai, tadan duka ta dauko wani leda tana kokarin fita daga dakin
Ina zaki tsata mu tafi don gida nake son zuwa indan watsa ruwa wallahi duk nagaji,
A tare suka fita daga dakin inda ta takai mai zuwa gurin motar shi,
A nan suka dan tsaya suna hira a gagauce saboda ita ranan gata nan dai ne kawai,
Shigowar motar suce tare da su jibrin da wasu abokan shi yasa su duka kallon inda suka tsaida motocin su,.
Dakin suka shige gaba dayan su don su diba maijiki,
A,A bai kara wani lokaci ba ya ja motarshi yabar gurin tare da Alkawarin zai dawo ya kara diba ta,
Ba ai wani dadewa ba su jibrin suka fito amma ba da, Yusuf ba,
Tana son taje dakin amma, sai tana jiran su fito saboda duk mazane acikin dakin,

Kan ta na saman ciyar ta, ta dan duka tana tunane,
Bakomai take tunawa ba sai mutumin ta watau A,A
Wai shi wani irin mutum ne, hakana, ta kasa fahintar shi har yanzu,
Gashi a fuska zakace ai baida matsala, sam,
Kafin ta karasa sai jin muryan mijin mama tayi yana cewa,
Maryam aida kinzo ya sauke ki gida ki dan huta tunda gamu nan da yawa ai,
Kamar tace a barta kawai sai taga musu da babba baida dadi,
Kuma ko banza tana da bukatar son watsa ruwa ajikinta, don tadan ji sanyi,
Tafe suke su biyu a motar, a hankali yake tuki don marance ya fara abin hawa sunyi yawa a hanyoyin,
Wani irin sanyi AC da kamshi ya gauraye motar, sai Qira,an dake tashi na Ahmed Suleiman kano,
Kamar daga sama taji muryan shi yana cewa,
Kiyiwa saurayin ki magana yadaina kirana da tubabbe pls,
Batare da ya kalleta ba yake magana, zaka zata mako bada ita yake magana ba,
Da,sauri Maryam, ta dan dube shi tankar zatai magana sai kuma ta fasa kawai tai shiru,,,
Idan kasa zai tsage zata shiga don kunya wanan maganar,
Wai ma ta ya ya ji wanan zancen, da akayi,, don dai baya nan a,lokacin,
A rau,nane ya, yace ban san may guy din nan ke ji dani ba wallahi,
Maryam dai har zuwa yanzu kala batace mai ba,
Sai dai jin da tayi, ya furzar da iska har sautin shi ya iso inda take,
Sai,dai,dai kofar gidan su,ya tsaya da motar shi, a yadda tagani duk rayuwar shi ya baci matuka,
Dan Allah kayi hakkuri ban san lokacin da ya fada ba,
Shima bai yi mata magana ba saidai ko karin Parker motar da yake yi,,
A hankali ta bude, kofar batare da kara kalon inda yake ba,,


ZEEE MAKAWA,,,
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
FUREN JUJI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
4⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

Assalamu Alaikum yan uwa musulmai tare da fatan kuna liya,
Da plsn girman Allah yan uwa marubuta da makaranta kubani, dan hankalin ku dan pls
Wallahi muji tsoron Allah musan cewa wata rana zamu gammu a gaban shi,
In yanzu in anjima in gobe,
Anytime kwanan mu yakare,
Wallahi littafan batsa sunyi yawa yanzu sai mun kula mun gyara kada barna yai wa a sanadin rubutun mu,,, Amma idan maganata akwai laifi aciki ku yafe min pls,,,,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

Alhamdullahi washegari mama tasamu sauki sosai don haka ta samu sallama daga likita amma zata dawo bayan kwana hudu,
Sam Yusuf bai nuna gajiyar shi ba sai ma kokarin nuna tankar shi dan gida ne cikin su,
Duk da bawai magana mai tsawo yake yi da su sosai ba amma zuwa yanzu sun dan fahinci halin shi,
Idan ka gan shi zaka dauka wulakanci ne sai ka dan zauna dashi zaka gane miskilanci ne,
Baban su maryam ne ya umarci Anty Dije da ta bar maryam ta, tafi ta kula da mahaifiyar ta tunda suna hutu, yanzu,
Don haka maryam wace, suke wasan boya da Yusuf tun jiya da ce tafadawa saurayin ta yafita harkan shi,
Sun isa kamfanin Bobi ana, shirin yin sallah azahar ,
Sai fitar su a cikin motar ne maryam taga, ashe duk kayan nan da yasaiya masu na amfani a asibiti suk sun kwaso abinsu sun zo da shi gida,
Sosai ta jin,jina mai saboda bakaramin namijin kokari yayi ba gurin ceto mata mahaifiya daga halaka
Da sauri maryam tashiga don ta gyara dakin mahaifiyar nata, inda sauran matan gidan ke ta mata sannu ya jiki,
Saidai may turus maryam taja ta tsaya saboda ganin wani irin dindimay,may katifa sabo fil a cikin ledar shi,
Da mamaki takarasa gurin inda daya dafa cikin matan ke sheda mata cewa, ai daga can kwantagora akazo da shi ance na mamantace,
Ga sabon randar roba ta ruwa, ga kujerun roba farare guda uku, da filolin su,
Jiki ba kwari zuciya fam da tunane maryam ke aikin dakin,
Ko ba, a tambaya ba tasan cewa aikin Yusuf din ne haka,
Kafin wani lokaci dakin mama yakoma kamar wata yar birni, can,
Sai zuwa dare maryam ta samu dan hutu bayan ta tabbatar cewa mahaifiyar ta tadan yi,wanka tasha magani,
Washegari da safe maryam na idar da sallah, asuba bata zauna ba fitowa tayi don taimakawa kishiyar mama da wasu aiyuka,
Saida ta tabbatar tagama komai ta koma daki don ta taimakawa mahaifiyar ta,
Kafin gari ya karasa haske duk maryam ta kammala komai a nata fan,nin,

36 / 84