BLOOD CROWN HAUSA NOVELS BY SULTY WRITES AKA YOUNG WRITER

Author :  Young Writer Category :  Tknovels

Chapter   9 / 53

24K to 27K   out of 156.9K words

bar station ɗin.

Abinda ya faru shi ne lokacin da Hushaima ta ga me tuk tuk ɗin nan wani makaho ya sauke, a gabanta makahon ya zaro dubu ɗaya ya bashi, laluba aljihunsa yayi kafin ya buɗe wurin ajiyar kuɗin su na cikin tuk tuk ɗin ya zaro Naira hamsin ya bashi, karɓa yayi a lokacin tare da cewa yaro ɗari da hamsin ka ɗauka kenan? Ba fa nisa daga inda ka ɗauko ni. Shi kuma yace iya abinda zai iya kenan, in ba nisa ka tako da ƙafarka mana. Makahon bai sake cewa komai ba ya juya yana dogara sandar da faɗin ALLAH ya kyauta. A lokacin ne ita kuma ta isa gaban tuktuk ɗin tare da faɗa masa inda zai Kaita nan yace ya shiga suje. Ya faɗa yana ɗan sunkuyawa duba wani abu a ƙasa a lokacin ne kuma canjin nan na ɗari uku suka zubo daga aljihun sa ba tare da ya lura ba ya fita domin goge glass din tuk tuk ɗin nasa, a lokacin ne ita kuma ta ɗauka ta saka masa a cikin ma'ajiyar kuɗaɗen. To kunji yadda akayi dai, fatan kuma kun fahimci dalilin Hushaima na saka me tuk tuk a tsaka me wuyar nan. WANNAN KENAN.

Gyara zama sargeant yayi bayan fitar me tuk tuk sannan ya ce, "Am da farko dai muna ƙara Godia da gudunmawa da kuma haɗin kan da kika bamu, domin yaran nan ba ƙaramin criminals bane saboda an same su da ƙwayoyi masu hatsarin gaske saboda binciken da akayi ya nuna ƙwayoyi ne masu saurin juya ƙwaƙwalwar dan Adam su sashi yayi abinda baiyi niyya ba, kinga kuma ba dan mun kamasu ba yanzu zasu iya cigaba da sayarwa matasa, su kuma suna saya suna sha suna aikata abinda bai dace ba, wanda hakan shi ke ƙara daƙushe mana tunanin matasan mu masu tasowa wanda ya kamata ace yanzu su ne ake damawa dasu a gomnati da sauransu. Mun gode kuma qasa na qara alfahari da samun irin ki".

Dan sunkuyar da kanta tayi tana ɗan murmushi kafin ta ce, "bakomai ranka ya dade sai dai......" Jin tayi shiru ya sashi faɗin, "Go ahead faɗi maganar ki ba damuwa".

"Ranka ya dade!, Kuna ƙoƙarin kama masu sha da sayarwa amma kuma kun taɓa tunanin a ina suke samu ? Su waye suke basu ? Minene dalilin da yasa ake raba musu irin wa annan ƙwayoyin? Saboda a yadda ka faɗa ɗin kaga kenan ƙwayoyi ne masu tsada ya za'ayi yan jagaliyar unguwa su dinga amfani dasu ".........shiru sargeant yayi kafin ya ce, "Muna iya bakin ƙoƙarin mu Hushaima, abun ne yake nema yafi ƙarfin mu, saboda yawan irin wa'annan case ɗin da ake yawan samu na kama matasa da kayan shaye shaye, da kuma case ɗin dabar nan da yayi yawa ga masu kwacen waya su ma, lamarin ƙasar Nifaz saidai addu'a kawai".

Numfashi ta sauke sannan ta dago da faɗin, "ALLAH yayi jagora ranka ya daɗe ni zan wuce"......... miqewa yayi ya ce, "Muje na taka Miki".

Tare suka fito har bakin kanta sannan ta musu sallama zata wuce ya tsayar da ita da faɗin, "Anya zaki samu abun hawa yanzu kuwa dare yayi sosai fa".

"Ba damuwa ranka ya dade me tuktuk ɗin da nazo dashi ɗazu yana waje ai".

"To shikenan, ALLAH ya tsare"........."Ameen". Ta faɗa tana ficewa.

A kofar station ɗin ta tarar da ɗayan me tuk tuk ɗin zaune yana gyangyadi yana ganin fitowar ta ya miqe yana faɗin, "Haba hajiya ya zaki zo ki shanyani a waje cikin sauron nan, ni da nasan irin dadewar da zakiyi ai da kin sallameni kawai na wuce".

"Kaga muje kawai da ALLAH"......... Shigewa yayi yana mata mita, bata ce dashi komai ba har suka ƙarasa in da zai ajjeta dubu ɗaya da ɗari biyar ta zaro ta bashi, tana ƙoƙarin tafiya ya tsaida ita. "Bangane ba hajiya ya dubu ɗaya da ɗari biyar kuma, ko dan zaman jiran da nayi ai ba kya bani dubu ɗaya ba".

"Au da ALLAH fa, yanzu a hakan ban ma adalci ba kenan na baka dubu ɗaya harda wata ɗari biyar sannan kuma ka tsaya kana ce min wai bai ma ba"........ Girgiza kanta tayi da faɗin, "To kawo ɗari biyar ɗin sai na baka dubu ɗaya"........kare mata kallo yayi duk da cikin duhu ne sai hasken wata daya hasko su kaɗan . "ki dauko dubu ɗayan tukunna".

Tsaki Taja da faɗin, "kai karka ɓatamin lokaci bacci nakeji, nama iya abinda zan yi wannan ɗin ma ka godewa ALLAH dan shi ya tsaga da rabon ka".........Ta ƙarashe tana ƙoƙarin barin wurin, hannu ya kai zai warci jakarta ta aikuwa ta daddage ta zabga masa mari. " Durun uwa (Ni kuwa nace salatin arna)". Ya faɗa yana dafe kuncin sa, saidai Kafin ya ɗago ba ita ba dalilin ta, raba ido ya shigayi akan layin da yake ba kowa shiru bakajin komai sai haushin karnukan ƴan vigilant. Ɗaga murya yayi da faɗin, "kuma ALLAH ya isa" . Ya ƙarashe yana komawa cikin tuk tuk ɗin sa da sauri faɗi yake, " Gwara na cikawa rigata tun da saura na, dan da alama yarinyar nan irin yaran nan ne da ake haɗa baki dasu a kawo ka lungu a bigeka a rabaka da machine ɗin ma".

Amfani tayi da spare key ɗin da take dashi ta buɗe gidan ta shiga, sannan ta maida ta rufe a hankali, ciki sanɗa ta shiga tsakar gidan ganin ba kowa tayi saurin faɗawa ɗaki, da Shazeen ta fara cin Karo a ƙasa tana bacci ga wayarta a gaban ta. Wayar ta ɗauka ta kunna flashlight sannan ta ɗauki Shazeen ɗin ta maidata Kan katifar tasu. Rage kayan jikinta tayi ta ɗaura zani ta ɗauko ƙwandon soso da sabulun su ta fita zuwa bayi dan watsa ruwa.



👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥



_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._


⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️



___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.

_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._



@wattpadd sultywrites22



STEP 1



PAGE _______11




12am daidai agogon birnin ƙasar Nifaz ya buga, garin yayi shuru sosai saboda ruwan da aka ɗauka tsawon awanni sama da biyar anayi, ko ina ya dau sanyi sosai, rahamar ALLAH ta sauka sanyin da talaka da mai kudi duk zai isa garesu, sanyin da baza Ka biya ko Sisi ba kafin Ka sameshi, shin wanna kaɗai bai isa mu dauwwama muna godewa ALLAH da niimarsa gare mu ba.

A bangare guda kuma wasu suna nan su na amfani da wanna yanayin ta hanyar morar sa akan gurbatacciyar hanya. MYSTIC HIDEAWAY shi ne sunan dake manne jikin tangamemen gate ɗin, wasu murɗaɗɗun garada ne majiya ƙarfi tsaye a kofar gate ɗin suna zazzare idanu, kana ganin tsarin wurin kasan club ne irin na ƴa'ƴan manya masu hannu da shuni, wani VIP underground room ne da ba kowa ake bawa hayar sa ba sai wane ɗan wane a cikin masu kuɗin ma. Wasu manyan mutane ne zazzaune a wasu kujeru da suke zagaye da wani ƙaramin table dake gabansu, kwalaban lemo ne da giya kala kala ga tumblers kowanne ɗauke da ƙanƙara a ciki, ɗakin ya ɗau sanyi sosai har raɓa raɓa yake dan dukda sanyin gari hakan bai hana su ƙarawa da na'urar sanyaya ɗaki ba wato AC, sai dai wurin akwai ƙarancin haske sosai haka zalika duk dukan kiɗan dake tashi a maka makan speakers ɗin dake sama su fa a wannan underground ɗin basa wani jinsa sosai.

Kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da wani abu me muhimmancin suke tattaunawa. Ɗaya daga cikin su ne ya ce, " Ni fa a ganina an kashe maciji ne ba'a sare kansa ba, dan wai mun durƙushe yaron can a idon duniya ba hakan na nufin mun durƙushe ahalin sa bane fa, kuna gani ma kamar wata dama muka bawa wa'annan ƴan uwan nasa tunda gashi har ɗaya daga cikin su ya fara kokarin kafa kansa. kuma kunsan sunan Hashim Darwin ba zai kankaru a jikin su ba.

Nisawa ɗayan yayi kafin ya ce. "Wato ba wai na tari numfashin ka bane Hajj zawaad, Amma ba wai fa mun dusashe taurarin yaron nan bane kawai saboda kar su goga damu a fagen kasuwanci ah ah, Hasali ma dai mun jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya a bangaren sir Ahuoyzah yana kallon hakan a matsayin damar sa ta samun more customers tunda an kashe kasuwar Hashim Darwin sannan kuma zai samu damar karɓar end of the year award na higher export percentage, Amma mu kuma ta fuskar mu, munyi hakan ne saboda sirrin mu dake hannu mahaifin sa, wanda a ganin mu kusancin sa da Amjad ɗin yasa muke tunanin yasan komai game damu kuma a kowani lokaci zasu iya tona mana asiri a idon duniya, tunda kunga ai already kafin mu bi ta kan yaron sai da muka kwantar da uban ko?".

"Maganar ka haka take Alhaji Abid, Amma yanzu to miye Abun yi?".

Wanda aka Kira da alhaji Abid ne ya ce, "Abinyi anan shi ne yanzu ba wurin wanna yaron ya kamata mu maida hankalin mu ba, saboda kunga ko tafiyar da yayi ta sirri ce bare ace mutane zasuyi ca wurin zurfafa bincike infact banda mu ma inajin ba wanda ya san yayi tafiyar".

"Amma dai kasan sir Ahuoyzah bazai kasa sani ba, saboda ko da ya samu aiki ba fa ya ɗauke idanunsa bane akai". Faɗin Alhaji Huzaif.

"Dan ya sani ai duniya bata sani ba, akace ma shi ma munafukar tafiya yayi ai, dan haka ba abinda ya taɓa shirin mu, kawai mu ƙara sa masa ido shi kuma batun sir Ahuoyzah sai mu maida hankali kan su julaybin ɗin domin su ne yanzu suke son shigowa gaban sa".

"To Kai Hajj zawaad ba kace aminin shi Awais yake ko wa mutumin ka bane Kuna having good time?".

"Sosai ma !"........Hajj zawaad ya amsa.

"To Kabi ta wajansa mana ka samo duk wani information na Agenda ɗinsu".

"Baku da damuwa, komai zai tafi yadda akeso"...........Hajj zawaad ya amsa sannan Alhaji hammoud ya karɓa da faɗin, "kaiiiiii an sha gwagwarmaya fa, wai ma waye farko ya bada shawarar a yaɗa cewa yaron nan Human trafficker ne".

Wata muguwar dariya Alhaji Abid yayi da faɗin, "kaga mugun nan".......Ya ƙarashe yana nuna Hajj zawaad.

Girgiza kai Hajj zawaad yayi yana kai tumbler da ya zuba stute cranberry juice a ciki ya ce, "To ai ji nayi ana ta kai kawon yadda za'ayi da shi Amjad ɗin da ubansa, ana neman hanyar da za'a kassara su bayan ga hanyoyi mafi sauki shi ne kawai na kawo shawara".

"Baka da kyau mutumi na"........ Alhaji Abid ya faɗa yana miqawa Hajj zawaad hannu suka tafa.

"To yanzu ya maganar exporting crude oil ɗin? kunyi magana da sir Ahuoyzah din ne?"....... Hajj zawaad ya tambaya.

Alhaji Hammoud ne ya ce, "Eh munyi magana da safe, nayi masa bayanin customers ɗin namu dake ƙasa, yace zai Bamu AP sai mu haɗu dashi mu tattauna gabaɗaya, kunga daga nan ma sai mu shigar masa da bayanan su Julaybin ɗin ko?".

"Hakan yayi. Kai ina John ya ƙaro mana ice cube ɗin nan mana"........ Alhaji Hammoud ya faɗa yana kurɓe ragowar wine ɗin dake cikin tumbler ɗin sa.

Wani Wanda tunda suka fara magana baice komai ba sai kurɓe kurɓen sa da yake ne ya ce, "Kuna ta magana Amma baku duba cewa akwai inda burin mu bai Kai ba"........Alhaji huzaif ya ce, " Na me fa?"

Gyara zama yayi da faɗin, " Mun fito mun shaidawa duniya Amjad na ɗaya daga cikin manyan masu safarar mutane na ƙasa da ƙasa sannan duk kasashe sun ɗauka, an ɗarsa zargi a zuciyoyin al'umma Sannan an haddasa cece kuce, munbi ta ƙarƙashin ƙasa mun sanya ana ta bincike akan sa, ƙasashe sun zuba ido suga iya gudun ruwan ƙasar Nifaz saboda Abu ne da muka bayyana na matsayin ƙasa da ƙasa, kuma har ƙasar Belgium ta fito tayi ikirarin in ƙasar Nifaz bata kammala bincikenta tayi abinda ya dace ba to su a basu shi suyi masa hukuncin da ya dace, Saboda su ma sun samu sunan sa a sawun Farko. Abu na farko mu a iya ƙasar Nifaz shirin mu ya tsaya, ya akayi ƙasar Belgium ta samu sunan sa a sahun farko na masu laifukan safarar mutane da akeyi a ƙasarta? Abu na biyu meysa bakuyi tunanin yadda akayi ya samu visa ba a wannan lokacin? Abu na uku ya akayi ya fita daga ƙasar Nifaz?"......... Ya ƙarashe yana komawa yayi relaxing jikin kujerar da yake zaune.

Shuru ɗakin yayi ba kajin komai sai sautin numfashin su dan ba ƙaramin dukan zuciyoyin su zancen Alhaji Malayin yayi ba. Can dai Alhaji Abid yayi ƙarfin halin faɗin, "kana nufin anyi sara kan gaɓa kenan?"..........da sauri Hajj zawaad ya ce, "Tabbas nima abinda na fara tunani kenan, in na fahimta mu ɗin kawai mun fitowa da duniya abinda ke ɓoye ne, mun kuma yaye musu duhun dake zagaye dasu, tunda gashi sanadin abinda mukayi yasa suka ƙara faɗaɗa bincike har suka tono Abinda ke ɓoye ".

Shi dai Alhaji Malayin bai sake cewa komai ba sai su Hajj zawaad ɗin ne suke sake tattauna Maganar.



_____________Daga nesa suka ajje motar sannan suka fito suka shiga takawa da kafar su, suna sanye da wata qatuwar baƙar jacket da bakin wando, sun rufa hular jacket ɗin a kansu, suna zuwa securityn ya bude musu ƙofar gate ɗin suka shige, kallon gabas da yamma sukayi kafin ɗayan ya kaiwa securityn bugu take ya zube kasa wanwar kamar wanda ba rai a tattare dashi, kulle gidan ɗayan yayi sannan suka kalli juna tare da yin wata alama da ido, nufar building ɗin sukayi suna zuwa suka fara buga ƙofar da ƙarfi kamar zasu sauketa ƙasa.

Bugun kofar da ake ya farkar dasu daga bacci, a tsorace Mumu ta ce, "Alhaji kaji abinda naji kuwa?"......... Cikin rawar jiki ya shiga maimaita innalillahi wa inna ilaihir raju'un, "Mun shiga uku Hajiya Latifa, wa yake mana irin wannan bugun tsakar daren nan, tashi maza kije ki tashi yaran nan ki haɗasu daki ɗaya ki kulle"......... Ya faɗa Yana tashi da sauri ya warci wayar sa domin Kiran yan sanda saidai ba service kan wayar ko kaɗan. Har takai bakin ƙofar fita ya ce, " Hajiya Latifa ina wayar ki, yi sauri da ALLAH miqomin".

"Ka ɗauka gata can "........ Ta faɗa cikin rawar murya tana buɗe Ƙofar ɗakin ta fice.

Bugun Ƙofar farko a kunnen ta ya sauka wanda hakan ya sanya ta yin wani juyi sai gata a ƙasa cikin tashi hankali ta fara neman switch ɗin light, hanyar ƙofa ta nufa sai Kuma ta dawo a guje ta ɗauki wayarta, har ta ɗaura hannunta kan handle ɗin ƙofar sai idonta ya sauka kan screen ɗin wayarta da ya kawo haske, dafe kirjinta tayi tare da sauke wani naunauyan numfashi, cikin sanda ta bude ƙofar ta fita da sauri ta sauka downstairs, da lalube ta gano ƙofar falon a hankali ta ɓude sannan tayi sauri ta faɗa kitchen ta kulle.

Ko da suka shigo maida ƙofar Philip yayi ya rufe yayin da Danny kuma ya kunna hasken falon amma har zuwa lokacin ba'a iya ganin fuskar su saboda hular jacket ɗin data rufe kusan rabin fuskar.

A ƙofar ɗakin suka haɗu tana kokarin dawowa yana kokarin fitowa, ko Ina na jikinta kerma yake ta ce, "Alhaji banga Nayrah ba, babu kowa a dakin ma".

"Kamar ya bakiga Nayrah ba ? Ina take to? Ina su nashwan?".

Zuwa lokacin hawaye ya fara zuba a idanunta, ta ce, " Duk suna Nan Amma ba Nayrah in..........." Maganar da sukaji a ƙasa ana basu umarnin saukowa ne ya sanya su kallon juna yayin da mumu ta ɗaura hannuwanta a baki a ƙoƙarin ta na tare Kukan da ya taho mata. Dad ne yayi ƙarfin halin jan Ƙafa ya nufi downstairs ɗin Yana tafiya kamar me tsoron ƙasa, bin bayansa mumu tayi tana riqo rigarsa, a haka suka sauko falon ƙasa, suna kokarin zama a ƙasa Danny ya ce, " Have a seat"........ tare da nuna musu kan kujerar, cikin rawar jiki suka Ɗaura jikinsu, har lokacin mumu maqale take da dad. Janye hulunan sukayi baya wanda hakan ya bayyana fuskokin nasu.

Philip ne ya ce, "Bamu zo da niyyar cutar daku ba hasali ma saqo ne daga Boss"......... Kallon kallo akayi tsakanin mumu da dad kafin dad yayi ƙarfin halin furta, "saqo Kuma ? Wani irin saqo ne haka? Daga Ina Kuma?".

"Daga Boss"......... Shuru yayi Yana juya sunan a bakin sa kafin a ƙarshe kamar wanda aka matsa ya ce, " AMJAD HASHIM DARWIN"......... Zabura dad yayi ya miqe da faɗin, "Okay ashe armed robbers ma a karkashin sa suke, shi gashi tijararre shi ne zai aiko mun barayi tsakiyar dare cikin gidana tsabar wulakanci saboda shi bai gaji arziki ba ko......."

"Alhaji ka bari"......... Mumu da har lokacin a tsorace take ta faɗa. Bige hannunta yayi ya cigaba da faɗin, "ke rabu dani in yi magana, ba uban da nake tsoro kinji, in banda rashin gsky da duniya ma ta shedeshi da ita, ya aiko mutanan arziki mana ko yayi aiken ido na gani ko Kuma shi yazo da kansa, ohhh ashe fa shi yanzu gudun ceton rai yake ko, to ka koma ka faɗa masa in ya isa yazo da kansa Ina jiran sa, ƴata Kuma ko zata tsufa a gida bana bashi auran ta yauwa".

A fusace Danny ya ɗaga hannu kamar zai kaiwa dad mari, saurin riqo hannun Philip yayi tare da saukeshi yana girgizawa Danny Kai sannan ya ce, " Bamu da lokacin da zamu

9 / 53