Author : Young Writer Category : Tknovels
yaga shigowar su, ledar pure water da ya Sha magani ya ajje gefe yana faɗin, "Amla kece tafe?"........." Ni ce Sahnish, ya kake? ya jikin?".
" Da sauki Alhamdulillah"...........Ita kuwa Hushaima ɗan kwalin kanta ta cire tare da zama tana faɗin , "Sahnish kasha magungunan naka?"
"Na sha yanzu, ga wanna ragowar na kasa cinyewa whl "........... Ya faɗa yana nuna Mata ƙosan da ya rage mata, dan yasan bata ci ba kawai ta faɗa ne.
Janyo ledar tayi tana faɗin, "Ai baka ci komai ba akwai abinda kake ji ne?".
"Babu komai whl kawai baki na ne ba dadi".
"Zazzabin nan ne ko?".............Amla ta tambaya tana bin ɗakin da kallo.
"Shi ne whl, Shazeen ce ta fara sannan ta miqamin"........... Sahnish ɗin ya yi saurin tarar zancen gudun Kar Hushaima ta faɗa zancen abinda ya faru jiya da daddare, dan shi Sahnish mutum ne me shegen son sirri.
"Gsky Hushaima banajin daɗin abinda kike min".......... Faɗar Amla.
Gyara zama tayi tana buɗe ledar ƙosan ta ɗauka ta fara ci da faɗin, "Me nayi kuma ni da kullum a cikin laifi nake a wurin ki".
"Shin wai miye laifi a ciki dan kina da bukatar Abu kin tambaye ni ne".
"In ina da bukata kikace, ni kuma alhamdulillah".
"Shikenan ya Miki kyau Hushaima nagode, yanzu dukkan Ku anan ɗakin kuke?".
"Dakin Sahnish ne nan, ni da Shazeen kuma ɗakin dake farkon wanna".
"Zan sake yiwa Mommy magana, gsky yaso ko kafin a samu wani gidan ne sai Ku dawo wurin mu".
Dakatawa tayi da cin ƙosan da take ta ce, "Amla dan ALLAH karki matsawa mommy lalle saita amince mun zo mun zauna a gidan Ku, mu bar maganar nan dan ALLAH in dai har ba kina so ta gane har yanzu muna tare ba ki shiga matsala kuma".
Shuru Amla tayi can kuma ta ce, "shikenan Amma dai......." Dan shuru tayi can Kuma ta ce, "Dama abinda ya kawoni Kan batun thumb print ɗin su Sahnish ne da za'ayi yau shine na zo muje, kuma Naga bashi da lpy, ya za'ayi kenan?".
"Zai iya mana, in lokaci ya wuce kuma ai zamu saki asara, Abu dai na dan lokaci Sahnish tashi kaje ka watsa ruwa ka shirya, bari ma na Kai ma ruwan".
"To ai kema sai ki shirya mu tafi taren".......... Kamar zatace ah ah sai kuma dai tace to tare da tashi ta fita da ledar ƙosan, bata jima ba ta dawo ta dauki bokitin ruwan data ɗaibo masa dazu ta Kai toilet ɗin tsakar gidan, ta dawo, tashi yayi ya dauki kayan wankan ya fita ita kuma ta ce, "Muje daki na, na shirya kafin shi ma ya gama" .
Tashi Amla tayi tabi bayanta suka wuce ɗakin su. "Ke kuma me ya sameki a hannu"....... Amla da sai a lokacin ta lura da hannun Hushaima da take ta boɓɓoyewa dan kar Amlan ta gani.
"Ki bari fa yanke wa nayi da ƙarfen ƙofa jiya da daddare"........kamo hannun tayi tana dubawa ta ce, "Amma fa ta yanke ki sosai, kinyi allurar TT?".
Zame hannun tayi tana faɗin, "Ina da ita ban dade da yi ba ai". Ta ƙarashe tana rage kayan jikinta ta wuce bathroom ɗin.
A gurguje tayi wanka ta shirya sannan ta ɗauki gyalenta da wayarta suka fito ta kulle ɗakin ta jefa makullin a aljihun doguwar rigar atampar dake jikinta, ta wuce ɗakin Sahnish domin sanar dashi suna jiransa.
Basu jima ba suka fito tare shi ma ya shirya, ita ta kulle masa ɗakin sannan ta miqa masa makullin suka jero zuwa waje, yayinda mutanan gidan suka bisu da ido ganin Amla a tare dasu dan basu taɓa Tunanin suna da wani dan uwa ko abokin arziki me kuɗi ba.
Suna Kai wa soron ƙofar gida yan sanda na shigowa tare da Jamcy dasu lady cyama, "Yauwa gata nan ita ce".......... Jamcy ta faɗa tana nuna Hushaima da hannu.
Wani irin kallo Amla ta yiwa Hushaima kafin ta ce...........
----------------------√
Amjad ko da ya bar asibitin gidan sa ya koma a can ya samu Hunaiz zaune cikin mota yana jiransa. Bayan Kamal yayi parking ya fito ya buɗe masa shi ma ya fito, direct wurin Motar Hunaiz ɗin ya nufa, Yana zuwa ya ɗaura hannunsa kan murfin motar dake buɗe, kyakyawan matashin saurayi ne zaune yana latse latse a waya, ɗaya hannunsa Kuma riqe da can ɗin coke da yake sipping kaɗan kaɗan, ɗagowa yayi jin kamar tsayuwar mutum a Kansa, ganin Amjad tsaye ya sashi sakin dan murmushi da faɗin, " Yaushe ka shigo ne, tun ɗazu nazo akace baka ƙaraso ba sai kawai nace barin jira, har na fara tunanin ko ka wuce can gida wurin su Anah".
Dan girgiza kansa da ke masa ciwo kaɗan yayi da faɗin, "Nop, muje ciki".......... Ya ƙarashe tare da sakin ƙofar ya juya ya wuce ciki, sake gyara zama yayi yana cigaba da abinda yake kamar bai san cewa Amjad ɗin na jiransa ba, har saida kiran sa ya shigo wayar, dan bata fuska yayi alamar irin an katse masa wani abu me muhimmanci da yake yi, kashe wayar yayi ya fito yana tafiya cike da ji da kai irin na samari masu tasowa yan 24-25, Yana shiga ya same shi a falon farko yana zaune ya zubawa ƙofar shigowa ido alamar shi yake jira. Zama yayi da faɗin, "Sorry na ɗan tsaya duba wani abu ne"........bai bi ta kan zancen sa ba ya ce, "komai ya kammala ne?".
Gyaɗa masa kai yayi alamun tabbatar wa kana ya ce, "Yes ni dai na gama nawa, duk abinda kace shi nayi, sai kuma muce ALLAH ya nuna mana goben lpy".
"Nagode bros, ALLAH ya saka da alheri"........ Murmushi ya ɗanyi sannan ya ce, "Juraysh ya Kira ni yana tambayata wai me ke faruwa ko sunyi magana da Anah ne ko yaya ne, Ni ban fahimce shi sosai ba, sai nace masa ina tare da abokai na i will call him back, saboda tunda naji yana tambaya nasan maybe bakuyi waya bane".
"Yea, bamuyi ba, Amma zan kirashi anjima in Sha ALLAH".
"To shikenan ni bara na wuce".
"Alryt sai mun haɗu goben"........ya faɗa Yana miqewa sukayi sallama da Hunaiz ɗin ya wuce, shi ma ɗaki ya wuce, kusan kaman 30 minutes ya sake fitowa ya zauna, daidai lokacin Nazbeer yayi sallama ya shigo, wuri ya nema a ƙasa ya zauna da faɗin, "Gani boss ".
"Ina bayanin da nace Ka samo?".
"Boss kamar yadda na gaya ma ne wancan motar ta qone ƙurmus, Amma duk binciken da akayi ya nuna babu mutum a ciki lokacin data tashi da wutar".
A hankali ya fitar da numfashi kafin ya ce, "Ya speed ɗin su yake a lokacin da sukayi accident ɗin? Sannan kuma daga bugawar tasu motar ta kama da wuta ko kuma an dau lokaci?".
Gyara zama Nazbeer yayi kana ya ce, "Ita wancan motar ta ƙure gudun ta dan kamar da gangan ta tunkaro motar data fita gidan nan, sannan kuma anja kamar seconds 100 kafin motar ta kama da wuta"......... Shuru yayi tare da daga kansa sama tsawon wasu mintuna kamar me wani lissafi, can ya ce, " Shikenan, jeka Ka turomin jack".
"Okay boss"........... Ya faɗa tare da tashi ya fita, shima tashi yayi ya shiga ɗaki ya ɗauko ƙaramar system ɗinsa ya dawo ya zauna, kaɗan kaɗan yake danna keyboard ɗin kamar me tsoron wani abu, cikin wanna yanayin jack ya shigo, bai ɗago ba saida ya gama shigar da abinda yake sannan ya dago, wasu takardu jack ya miqa masa, karɓa yayi ya fara dubawa tare da Kai hannunsa goshi a hankali yake buga goshin nasa da yatsansa manuniya yana sake bin rubutun kafin ya rufe ya dago yana kallon Jack daya nutsu cikin shirin amsa ko wace irin tambaya. " Jack, are you sure no one knows what we discussed and what you were gonna do?”.
"No one boss, infact ban ma tafi da motar gidan Nan ba, sai na ari ta wani aboki na"........ Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon wayarsa dake haske ya ce, " you can go, I will call you later"........" Okay boss "...........Ya fada tare da tashi ya fita, ɗaukan wayar sa da system ɗin sa yayi ya wuce ciki tare da locking ƙofar sannan ya rage light ɗin ɗakin, sannan ya ɗaga wayar, daga daya bangaren Kamar wanda aka sawa bindiga a kai Widad ya ce, " Wai meysa baza a taɓa ma kira ɗaya ka ansa bane, ka san uzurin da ya sa na Kira kan ne".........Shuru yayi kawai dan shi bai iya ja in ja ba a rayuwar sa, ko kuma ya tsaya yiwa mutum explaining reason dan Ka fahimce Shi. "Ina jinka". Ya faɗa tare da yin shuru yayinda shi ma widad ɗin yayi shuru daga ɗayan bangaren, Neman wuri yayi ya zauna dan yasan halin Widad, Saida ya gama dibidibitun sa sannan ya masa bayanin dalilin kiran.
"Ka nemi wayar Ash ko Ace, zasu faɗa ma dan ni tunda na dawo ma banbi ta kan aikin nasa ba, dan nan ma na tarar da wani a gaba na"........takaici yasa Widad kashe wayar ba tare da yace komai ba ganin kayan haushin da Amjad ɗin yake neman cusa masa, ace damar da suka daɗe suna nema yanzu ta samu Kuma ya tsaya yana musu wasa da hankali.
Shi kuwa Amjad ba komai ya sashi faɗawa Widad haka ba sai sanin cewa in yace shi zai masa bayani Widad ya dinga masa iskanci kenan, haka Kuma in ya haɗashi da kiara yasa kumammu biyu ya haɗa dan Kiara tafi Widad iskanci, gwara gwara ma Ace duk da shi matsalarsa rashin ɗaukan Abu serious kafin ya bawa abu mahimmanci sai ya dinga tsokane tsokane kenan, ita Kuma Ash matsalarta da widad wanna miskilancin nasa da take ɗaukan hakan kamar girman Kai, Amma dai gwara wa'annan biyu suna iyawa dashi.
Ɗakin sirrinsa ya wuce Kai tsaye, bashi ya fito ba sai wuraren 2:30am sannan ya fito ya wuce kitchen ya haɗa coffee ya dawo falon ya zauna tare da Kunna TV, Yana sha yana kallo har sai da ya shanye sannan ya tashi ya wuce ɗaki, wanka yayi sannan ya sauya Kaya ya sake fitowa cikin shirin fita, zuwa lokacin karfe wurin 3 da wani Abu.
Shi fa Amjad ba ruwan sa da dare saidai idan bashi da abun da zaiyi ne, amma in dai yana da Abubuwa a gabansa to shi lokacin ne ma ranar sa, dan yafi jin dadin aiki da daddare ma fiye da rana. Ni kuwa nace aikin dare ai na maras gaskiya ne in dai ba tsayuwar dare zakayi ba.
Shi kaɗai ya fita dan ko Kamal bai ɗauka ba, sai 6am ya dawo gidan, ɗakinsa ya wuce baifi 10 minutes ba ya sake fitowa, yanzu tare dasu Kamal da Aram suka fita, main house ɗin su suka nufa. Ana buɗe masa kofar motar ya fice bai tsaya ko Ina ba sai ɗakin sa, ya shige yayi kwanciyar sa sai 9am ya fito ya sake ɗaukan wanka cikin tattausan yard Marar nauyi milk colour ya daura black p cap ɗinsa data zame masa dole, hannunsa sanye da wani diamond watch, kafarsa kuma sanye da wani Italian slip on sandal brown.
Anah dake tsaye tana magana da masu aiki hango shi yasa ta sallamesu, ƙarasowa yayi yana faɗin, " Good morning Anah".........." Babban mutum dama a gida Ka kwana". Gyada Mata Kai yayi alamar eh sannan ya ce, "Yanzu ma sauri nake fita zanyi".
"Ai kuwa ba inda zaka sai kayi break, dan jiya na tabbatar baka samu damar cin komai ba, ga idanun ka ma sun nuna baka samu bacci ba".
Shafa fuskar sa yayi da faɗin, "Zanci fa in na fita Anah whl ina sauri ne".......... kallon sa kawai ta tsaya yi wanda haka ya sashi sunkuyar da kansa ƙasa, mamaki take yau Amjad ne ake cewa ya tsaya yaci abinci yana cewa sauri yake in ya fita zaici, sai kawai ta riqo hannun sa ta wuce dinning dashi, yana ɓata fuska yana komai haka ta sashi a gaba saida ya taba kayan karin duk da baici sosai ba dan daga jiya da magriba zuwa yanzu kwata kwata baya sha'awar komai, haka ya samu ya silale ya fita.
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______30 & 31
"Ranka ya dade meke faruwa?". Amla ta tambaya tana binsu da kallo.
"In munje can zaki ji, ke wuce muje". Dan sandan ya faɗa yana nuna wa Hushaima hanya da hannu, ni kuwa nace um um yallabai bi a sannu.
"Dan ALLAH ranka ya dade me tayi?". Sahnish ya faɗa yana riqo hannun Hushaima.
"Faɗa sukayi da wanna ta fidda mata hakori, dan haka dole sai muje can".
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un". Sahnish ya fada yana kallon Hushaima data ɗauke Kai kamar bata san anayi ba .
"Ranka ya dade in ba damuwa ina so mu ɗan keɓe da ɗaya daga cikin ku muyi magana". Amla ta fada. Da sauri Jamcy da kumburarren bakinta ta ce, "Ranka ya daɗe ni fa ba zan yadda ba, duk ma wani abu da za'ayi sai anje can station yww".
"Ke wai waya gaya Miki Ina tsoron station ko yan sandan naki da kika ebo, ni wanna ba baƙon wuri bane a wuri na, na saba dashi dan haka bana tsoron zuwa". Hushaima ta faɗa tana watsa wa Jamcy wata banzar harara.
"Wai dan ALLAH baza kiyi shuru bane Hushaima, ranka ya daɗe muje daga wajen two minute please".
Ɗan sandan nan na farko ne ya bita suka fita, saida suka kwashe kusan minti biyar su Hushaima na tsaye sai harare hararen juna suke har ɗan sandan ya dawo Amla biye dashi, kallon su Hushaima ɗin tayi da fadin, "ku muje Kar muyi late ko" .
"Ke baiwar ALLAH kuje Ina, ranka ya dade ban gane suje ba".
"Barsu suje, bashir jira mu a waje bari muyi magana, ke ma baiwar ALLAH ɗan jira mu "............Ya faɗa yana kallon ɗaya ɗan sandan da lady cyama, fita sukayi kamar yadda ya buqata, Dan already su Hushaima har sun fice.
Sai da suka hau hanya Amla ta ce, "Yanzu fisabilillahi Hushaima baza ki daina abinda kikeyi ba".........Sahnish dake back seat ne ya cafe da faɗin, "Whl Amla kamar kinsan abinda ke raina amma ban isa nayi magana ba sai ta taso min da faɗa Wai na zama soko, ni ba namiji bane waye waye "..........." Hmmm, ALLAH ya kyauta". Kawai Amla ta faɗa daga nan suka yi shuru dama Hushaima bata ce dasu ci kanku ba tunda suka shiga motar. A cikin wata babbar makaranta tayi parking sannan ta buɗe ƙofa tana faɗin, "Muje ko".
Buɗewa sukayi gabaɗayan su suka fito, da kallo suka dinga bin makarantar har suka isa wani ƙayataccen office. "Welcome Miss Amla ". Wata mata da akan table ɗin nata naga wani tag name da aka rubuta Mrs Jenny a ƙasa Kuma aka rubuta PC wato principal, cikin karramawa ta tare su, bayan sun gaisa ta ce. "Have a seat". Ta faɗa tana kallon su Sahnish ganin kujerar data nuna musu yasa suka gane me take nufi, zama sukayi Mrs Jenny ta ce, "is he the one, Miss Amla?". Ta faɗa tana nuna Sahnish.
"Yes he's"........." Alright to amma zai ɗan jira saboda suna da ɗan yawa".
"Gsky Mrs. Jenny, we're in a hurry, and he's not even feeling well. Can you do us a favor and let them go ahead with it now?".......... Ɗan shuru Mrs Jenny tayi kafin ta ɗauki waya ta kirawo wani Mr Anis, Ba'a jima ba ya shigo, nuna
Sahnish tayi da hannu tare da faɗin, " Kuje dashi yayi thumb print nasa yanzu suna sauri zasu tafi bai jin daɗi ne".........." Okay ma'am ". Mr Anis ya amsa sannan yace, "let's go". Da sauri Amila ta ce, "Sahnish kuje ayi ma". Miqewa yayi suka fita tare da Mr Anis su Kuma suka jirasu anan, basu daɗe ba ya dawo har anyi an gama, sallama sukayi wa Mrs. Jenny sannan suka fita.
Amla ce ta kalla agogon hannun ta da faɗin, "Wayyo na shiga uku".
Saurin kallon ta sukayi Hushaima ta ce, "lpy dai? me ya faru?" .
"Whl daddy ne ya bani saqo na kai wani wuri so na ɗauka zamu gama da wuri kafin lokacin gashi yanzu har time ɗin da ya bani na ƙoƙarin shigewa, dan ALLAH ku ɗan min hakuri muje na kai aikar sai na kaiku gida".
"Kash Whl Amla wani lokaci kina da ban haushi, to miye a ciki Kuma, har sai kin wani ce muyi haƙuri ai da kin faɗa ma saqon zaki fara kai wa, yanzu muje mazaa kar mu ƙara ɓata lokaci"...... Da sauri suka ƙarasa wurin motar suka shiga Amla ta tada aka buɗe musu gate suka fice.
Sunyi tafiyar kamar minti talatin kafin su tsaya gaban wani qaton gida kamar dai guest House haka gidan ya tsaru kamar a turai. Horn sukayi a gate ɗin security ne ya leqo tare da ƙarasawa ta side ɗin Amla. "Daga Ina?". Ya tambaya yana ƙare musu kallo.
"Na kawowa me gidan naku saqo ne"..........Sai da ya sake Ƙare musu kallo sannan ya ce, "Ya san da zuwanku?".
"Ban sani ba, amma kace masa daga alhaji Zawaad"...........Juyawa yayi ya koma ciki ba daɗewa sai gashi ya dawo, buɗe musu gate ɗin yayi suka shiga, a makeken parking lot ɗin da zai iyacin sama da mota 20. Parking Amla tayi tana kallon yanayin gidan wanda daga can gefe aka fasalta shi kamar wani Chambers, buɗe dashboard storage ɗin motar tayi ta ɗauko