Author : Young Writer Category : Tknovels
ana idarwa kuma ya dawo ɗakin Ummu still, saidai bai jima da shingiɗa akan sofar ba bacci ya ɗauke shi ba tare da ya shirya masa ba dan a nufin sa zai huta ne zuwa wayewar gari sai su tafi ɗauko Habiby tare.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 0816 584 2571.*
👑🩸 *BLOOD CROWN* 🩸👑
🔥 *{THE HEIRS APPARENT}* 🔥
_A heart-touching, yet unrelatable love story, set amidst powerful royalty, with a mysterious green snake slithering under the green grass, rivalry wars, and witches wielding ancient power._
⭐MALLAKIN⭐
*SULTYWRITES*
A-K-A
[YOUNG WRITER]✍️
___________________________________
*STARS TALENT WRITERS*.
_Marubuta masu amfani da salo na zamani, koyarwar addinin Musulunci game da faɗakarwa, ilmantarwa, nishaɗantarwa haɗe da wa'azantarwa! Salonsu ya banbanta! Suna tafe da sabon salo mai ƙayatarwa da ilmantarwa._
@wattpadd sultywrites22
STEP 1
PAGE _______ 49 & 50
Sai wurin rana su Reeslan suka iso Aurellon sultanate, a gaban wani tangamemen gate me masifar girma suka tsaya, dan idan da mutane ne zasu buɗeshi to fa sai an samu gardawa sama da talatin tukunna su iya motsa shi saboda faɗi da kuma tsayinsa, a samansa an rubuta WELCOME TO AURELLON SULTANATE da wasu irin glitters gems masu walwali. Automatic gate dan haka sai da ya gama screening motar tasu sannan ya buɗe da kansa suka shige ciki, wasu jibga jibgan securities ne tsaitsaye suna ta Kai da kawowa dukkansu sanye da uniform ɗin su red and dark brown. Sai da suka sake tafiya me ɗan nisa sannan suka isa second gate shi ma tsayawa sukayi yayinda wata computer ta fara magana cikin harshen larabci tana musu welcome. Shi kuwa gogan naku sai tsaki yake bugawa, dan da ace mutane ne ke jinkirtawa kafin su buɗe gate ɗin nan da tabbas babu abinda zai hanashi sauka ya haɗa kansu da gate ɗin saboda ba abinda ya tsana a rayuwarsa biyun jira. Sai da ta gama yan surutanta gate ɗin ya buɗe suka shige, hanya suka miqa kamar zasu bar gari, sosai sukayi tafiya kafin su isa gaban wani ƙaton round me kaman water fall sai fidda wani glitters sea blue waters yake gwanin sha'awa, roundabout ɗin ya raba hanya huɗu ne ta west, east, north da south, sai da suka zagayo sannan suka ɗauki hanyar da tayi north ɗin.
Bari kuji wani abun burgewa game da Aurellon sultanate, suna da matuqar tsafta fiye da yadda kuke zato dan tunda muka shigo banga ƙasa ko ƙura a cikin wannan masarauta ba, domin bayan shimfiɗadɗiyar kwaltar dake kan hanyar ko ina ka ɗaga ido ka kalla wani irin shinfiɗaɗɗen block ne kawai yake ɗaukan ido. Part ɗin Sultan suka nufa tun kafin sun ƙarasa suka dinga sakin horn dan sun san halin Reeslan, ai kuwa suna shigewa tun kafin motocin su tsaya wasu suka diro tare da kama murfin motar da yake ciki suka buɗe immediately motar na tsayawa saboda gudun Kar suyi laifi. Cike da sassarfa da kuma izza ya fito daga motar, take duk suka zube suna zuba masa kirari amma ko kallon su bai yi ba ya shige, Dan dama shi sun riga sun sani bayan Matan Abbu duk wanda zai shiga sai an masa iso amma fa banda Reeslan dan tsoron sa da kwarjinin sa ma bazai barsu su ɗaga Ido su dubeshi ba ballantana har suce ya jira a nema masa izinin shiga dan tsaf zai haɗa ma mutum jini da majina, kansa a sama yake baya ɗaukan wargi ko daidai da misalai zarratin, whl kuskure kaɗan zakayi sai ka gwammace kiɗa da kalangu.
A falon farko ya tarar da yan uwan sa da Ummu sai Abbu da ya fito da Niyyar zuwa fada domin janaizar mutanan da aka kashe wanda suka fita tare da Reeslan ɗin jiya amma jin cewa su Reeslan ɗin su na hanya ya sashi tsahirtawa. Da sauri su Albeenah suka nufeshi cike da farin cikin ganin sa sukayi hugging ɗinsa suna masa barka da dawowa lpy, hugging ɗinsu yayi back one by one sannan ya wuce wurin mahaifin sa ya yi hugging ɗinsa shi ma, ɗan bubbuga bayan sa Sultan yayi sannan ya ce, "Alhamdulillah tunda Ka iso lpy dama ku nake jira, ni yanzu zanje fada domin na samu janaizar mutanan mu da aka kashe, amma zuwa dare kazo ina son ganinka ".........."To Abbu ALLAH ya tsare ". Ya faɗa Yana komawa kusa da Ummu dake murmushin Farin ciki a zuciyarta kuwa ƙara godia takewa ALLAH da ya tsiratar Mata da gudan jinin ta.
Duk ALLAH ya tsare sauran yaran sukawa Abbu, ya amsa musu yana sa kai ya fice, fadawan sa suka rufa masa baya zuwa mota inda zai shiga su wuce fadar.
Kirjin sa ta ɗan daka cikin so da ƙauna ta ce, "Bakaji Ibny meysa zaka fita, duk cikin masarautar nan bai isheka zagaye da dokin ba?".......... Dafe wurin kafaɗar tasa yayi kusa da inda Ummu ta daka, a hankali ya furta, "Ouchhh Ummu zafi"........ Kallon sa tayi cikin kulawa ta ce, "Menene kuma? Bana son zolaya fa".........." Ummu I'm hurt here na samu rauni".
Ai take duk suka rikice suka shiga tambayar sa me ya faru dashi? me ya same shi? Sai dai a maimakon ya basu amsa sai cewa yayi , "Ummu ina Rouh? Ban ganshi anan ba?"........... Huyam ce ta ce, " Yana room ɗin Ummu yana bacci bai ma san an tafi ɗaukoka ba, da tare dashi za'a tafi, but ya Reeslan me ya same Ka ? A ina kaji ciwon?".......... Bai bata amsa ba ya juya da sauri yayi waje, bin bayan sa Ummu ma tayi tana faɗin, "Ki kiramun Dr Abyan yazo part ɗi na yanzu ya sake duba min shi". Da sauri kuyanginta suka rufa mata baya.
Ko da Ummu ta fita Reeslan har ya karɓi key mota ya fice daga part ɗin, dan dama shi dole take kamawa a tuqashi, yafi son yayi tuqin sa da kansa yadda zai ƙurewa motar gudu son ransa. Ganin haka ya sa Itama ta shiga nata motar da aka buɗe mata sauran kuyangin suka shiga sauran motocin biyu da suka zo a ciki, suka bi bayansa.
Yana shiga ɗakin Ummu ya wuce da ɗan gudu gudu wanda hakan ya ban mamaki ganin magajin kujerar Aurellon na gudu. To saura kuma wasu suce na fiya sa ido.
Yana shiga ya nufi wurin sofar tare da durƙusawa wurin kan Rouslan ɗin ya sanya hannu ya maida masa gashin kansa baya sannan ya ja hancinsa da faɗin, "Rouh! Rouhi I'm back, I missed you, wake up"........ A hankali yake jin sautin muryar ɗan uwan nasa kamar a mafarki wanda yasa ya fara buɗe idanuwan nasa masu cike da bacci a hankali har ya sauke su a kansa, zabura yayi ya miqe lokacin da ya gama tantance Reeslan ɗin ne a gaban sa, riqo shi yayi yana faɗin, "Habiby yaushe Kuka dawo, shi ne Ummu bata tasheni ba anje ɗauko Ka dani"............ " Easy Rouhi, ba gani na dawo ba, tashi mu tafi ɗakin mu".......... Girgiza masa Kai yayi da faɗin, "Habibyy you are not okay, please tell me me ya sameka sunyi ma wani abu ne?". Ya tambaya cikin damuwa. Bazai iya boyewa Rouslan komai ba dan haka ya cire rigar sa tare da nuna masa inda aka yanke shi sannan ya ce, "Ka gani yanka ne but I escaped it, ya ma fara warkewa".
Ɓata fuska yayi da faɗin, "Habibyy Please Ka daina fita ba tare da ƙwaƙwaran tsaro ba, ya kamata ace munje hospital an sake duba wurin fa"......... Riqo masa hannuwa yayi da faɗin, "Ni ma fa likita ne Rouhi ko ka manta ne? And nayi duk abinda ya kamata so karka damu, tashi muje ɗaki nayi wanka kai ma kayi dan nasan bakayi ba".
Ba musu ya miqe suka fito in da suka haɗu da Ummu na shigowa, idonta ne ya sauka akan ɗinkin dake shinfide a faffaɗan ƙirjin nasa ta wurin kafaɗa, hankalin ta ne yayi mummunar tashi duk ta rikice saboda ba ƙaramin yanka bane, dakyar suka kwantar Mata da hankali sannan suka samu suka wuce .
--------------------√
Tafiya takeyi da ƙafa, tasowarta kenan daga wurin aiki bata samu abun hawa da wuri ba shi ne take dan tattakawa gaba kaɗan ko zata samu, cincirundon mutane ta hango sun cika a bakin wani layi, ɗan rage tafiya tayi saboda yanzu duniyar ta zama abinda ta zama karta je bata son taron miye ba, Hakan yasa ta ƙarasa wurin wasu mutane dake zaune bakin wani shago suna shan rake, sallama ta musu suka amsa sannan ta ce, "Da ALLAH meke faruwa a can ?"......... Ɗaya daga cikin su ne ya ce, "Yaron Alhaji Hashim Darwin ne yake rabon kuɗi wai, mu Kuma duk hakan ba birgemu zaiyi ba yauwa, tunda duk anyi walkiya mun gan su a rana".......... Ɗayan ya amsa da faɗin, "To wa ma ya sani ko kuɗin tsafi ne kana karɓa ka ɓace, wai ba qanin su bane ake zargi da safarar mutane, to wa ya sani ma ko tare sukeyi suke neman su rainawa mutane hankali su nunawa duniya ba ruwansu".
"To ai su wa'annan fa yanzu ne ma suke wani mutumta mutane da suka ga zata kwaɓe musu gabaɗaya, Amma ada duk cikin su ba me mutunci gwara ma Amjad ɗin to ashe shi ma ladabin ɗan kunama ne da haka suke saye zuciyar mutane suna kwashe su, mu kuma dake yunwa ta kashe mu ana watsa mana tsaba sai mu bi su".
Ita dai Hushaima sallama ta musu bayan ta gama jin zancen nasu sannan ta cigaba da tafiyar ta cikin nutsuwa, gajiya tayi ta tsaya tana duba abun hawa tare da zaro wayarta ta fara ƙoƙarin kiran Sahnish saboda kar suga shiru hankalin su ya tashi.
Bayan Awais ya gama sallamar mutanan ya juya da Niyyar yi wa yaran sa magana idon sa ya sauka kan Hushaima, Ƙura mata ido yayi a daidai lokacin data samu Abun hawa kenan. "Zubairu ku shigo mota, ina so mu bi wancan mai tuktuk ɗin".......... Ba ɓata lokaci zubairu ya sanar da sauran suka shige ɗaya motar shi kuma ya buɗe wadda Awais yake ciki ya shiga mazaunin driver ya tada suka bi me tuktuk ɗin da Hushaima take ciki har suka ƙarasa gidan ta sauka ta biya me tuktuk ɗin ta shige ciki.
Ɗan nesa da gidan suka tsaya, Awais ya ce, " Zubairu fita ka min bincike akan yarinyar can data sauka a tuktuk ɗin can ta shige gida yanzu, shin matar aure ce ko kuwa dai irin tamu ce"......... "To ranka ya dade". Zubairu ya faɗa tare da buɗe motar ya fita ba tare da ya kashe ta ba. Wata yarinya ya tarar wurin kawu garba sai musayar maganganu suke irin nasu na yan duniya, sallama ya musu suka juyo suna kallon sa, Yarinyar ce ta ce, "Malam ya akayi ne?"
"Da ALLAH tambaya nake"........... "To tambaya kuma mu ba gidan Radio ba "......... Kawu garba ne ya karɓe da faɗin, "ALLAH yasa mun sani".
"Yauwa dattijo da ALLAH nasan kunga wata yarinya da me tuktuk ya sauke yanzu ta shige gidan can da ALLAH tambaya nake a kanta?"......... Kallon Yarinyar kawu Garba yayi da tambayar, "Akwai Wadda ta shiga gida ne yanzu?"........ Ɗan mere baki tayi da faɗin, " Ba Wadda ta shiga in ba tity ba (sun sawa Hushaima sunan tity ne saboda ƙarfin zuciya irin ta ta, rashin tsoro sannan in tace zata yi abu to ko sama zata haɗe da ƙasa sai tayi, TITAN shi ne asalin sunan suka yanke suke cewa tity, yana nufin Huge, powerful and unstoppable). Ita kuwa ba matar aure bace shegiyar kanta ce, in ma miji ta samu suke shirin aure har ya turo ka masa tambaya a kanta, to whl ka bashi shawara dan yarinyace me zaman kanta gata yar bala'i, yan sanda, yan daba, yan doka Kai har aljanu da shaidanu ma tsoronta suke ji, dan haka tun wuri ka naɗe malaman kafafunka ka Ƙara gaba".......... "Shikenan to Nagode ". Zubairu ya faɗa tare da barin wurin ya juya ya koma inda sukayi parking motocin su, yana shiga ya zayyane wa Awais abinda yarinyar can ta shaida masa kan Hushaima. Wani ƙayataccen murmushi yayi da faɗin, " To kai zubairu me kake jira, ai kasan irin su muke so, maza je ka ka sallamo min ita, dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe ".......... " Angama ranka ya dade". Zubairu ya Amsa tare da sake fitowa daga motar ya wuce ƙofar gidan, ƙwanƙwasawa ya shigayi tare da buga sallama.
"Wai waye ne ya ke damun mutane da bugun ƙofa da magribar Nan?". Gboy yaran baba ilerika ya faɗa yana fitowa daga ɗaya daga cikin ɗakin dake soron, ganin zubairu ya sashi faɗin, "To ya akayi ne?".
"Sannu, da ALLAH wata yarinya Tity nake so ka min sallama da ita".
"Kkaiii gidan nan ba'a yiwa kowa iso sai dai ka shiga ka isar wa kanka, Amma kafin nan zaka bada kuɗin ƙofa". Ya faɗa da Muryar dake nuna kamar a make yake. Hannu ya miqa masa alamar ya bashi kuɗin ƙofar, ba musu Zubairu ya zaro kuɗi daga aljihun sa masu yawa ya miqa masa, kawu adamu ne ya sawo Kai zai shige gidan ganin kuɗin da ake miqawa Gboy ya sashi yin caraf ya warce yana faɗin, " Wanna rabo na ne dama Ina bin ubanka bashin dubu goma ".........." Ahh kaii jagus ya haka ne, wancan ai abinda ya haɗaka da tsoho na ne, Kuma ehh can ku haɗe Amma ka bani kuɗi na, dan baka san ƴar buga bugar da nayi na same shi ba".
"Tsaya nan Kai tayi kaji, ɗan wahala"......... Kawu adamu ya faɗa Yana wucewar sa ciki ba tare daya kalli inda zubairu yake ba, bayan kawu adamu zubairu yabi domin shiga gidan ai da sauri Gboy ya shiga gabansa tare da bubbuɗe hannu ya ce, "Kai malam ya ne, ina kake neman shiga ai baka ban kuɗin ba"........." Kamar ya ban baka kuɗi ba, ina cewa a hannu ka wancan tsohon ya warce ba a hannu na ba".
"Kai kwarankwatsa dubu baka wucewa in baka bani kuɗin nan ba, Kai karka rainamin wayo fa ina iya ma balli balli na bajeka kamar banda alqur'an".......... Tsayawa zubairu yayi kamar ya koma amma yasan can ma ran Awais ne zai baci idan yaji akan kuɗi ya dawo dan haka ya sake zaro wasu kuɗin ba tare da ya sake magana ba ya damƙa masa sannan ya wuce cikin.
Ko da ya tsinci kansa a cikin gidan rasa inda zai dosa yayi sai kawai ya tsaya wurin su mama
Atine tare da faɗin, "Da ALLAH Tity fa?"......... Ƙofar ɗakin ta mama Atine ta nuna masa da hannu tana cigaba da bare gyadar ta. " Nagode". Ya faɗa tare da wucewa in da ta nuna masa, a zuciyar sa kuwa mamakin abinda uban gidan nasa ya gani a tattare da yarinyar dake irin wanna gida yake, shi da ke sa a kawo masa classic bebs kalar wacece yake so, daga kowani gari, yan mata masu aji yan kwalliya, amma shi ne kuma yau ya ƙare a local gidan karuwai irin wanna, dan shi kwata kwata zubairu a gidan karuwai ya ɗauki gidan su baba ilerika, dan yanayin sa da ya gani baiyi tunanin akwai matar aure ɗaya dake rayuwa a ciki ba.
Kwankwasa ƙofar ɗakin nata yayi, Hushaima data ɗaura zani tana kokarin shiga wanka taji bugun kofar ɗakin nata, dakatawa tayi da faɗin, " waye ne?"............" Ni ne, kinyi baƙo ne"........ Zubairu ya faɗa .
Ɗan shuru tayi kafin can kuma ta ɗauko hijab tasa ta nufi kofar ta buɗe, Ƙare masa kallo tayi tare da faɗin, "Ya akayi? Daga Ina?".
"Ba sai kinsan daga Ina ba customer ne zaki iya fitowa yana waje yana jiranki"......... Dan jim tayi kafin ta ce, " Okay jira ina zuwa". Ta faɗa tare da komawa ciki, a gurguje ta maida kayanta data cire sannan ta fito, tsaye ta sameshi yana jiranta, ganin fitowar ta ya sa shi shigewa gaba ita kuma ta rufa masa baya.
A gaban motar suka tsaya, Zubairu ya buɗe mata ƙofar baya, kama ƙofar tayi ta riqe ba tare data shiga ba, "To ki shigo mana, inaga ai sai yafi ko?".......... Faɗin Awais da ya zuro kansa, kallonsa tayi na wasu seconds kafin ta zura jikinta ciki ta zauna amma ƙafafunta duka a waje suke kamar yadda ƙofar motar take a buɗe, kamar zai sake magana sai kuma yayi shiru, can kuma ya ce. " Sai kuma ki min ƙwalele ki wuce, haka akeyi ? Ummm yam mata".
Idonta a kansa ta ce, "Ai bansan ka taya bane Alaji"........... Dariya yayi irin ta Alhazawan birni kuma gogaggun yan duniya sannan ya ce, " To Kar na ɓata miki lokaci da yawa ga wanna card ɗi na ne, in kin shiga ki Kirani sai nayi saving taki number ko".......... Juya idanunta tayi tare da faɗin, " Sai dai wayar tawa ce sai na kai gyara dan yanzu shiga ta ina ƙoƙarin shiga wanka ta faɗa ruwa".
"Ahh to karki damu ai kinga yaro na zubairu ko, zan aiko shi ya kawo Miki waya anjima kinji, wannan ai